KALUBALE BOOK 1

Page 111

by @yargidanimam

Babu wanda yayi ma wani Magana. Sai daga bisani Umar ya dan dube shi yace "Muhseen ka zauna ka yi tunanin abinda kake tunanin aikatawa kuwa?”, ya karasa magana yana kafe shi da ido Muhseen yace. "Kai Umar, wai me yasa baka son ka fahimce ni ne, ni fa a zatona, gani nake in akwai wanda yakamata ya fahimceni akan wannan al’amarin , kai ne, tunda ka yarda da ni, ka san halayyata, Kwatankwacin yadda Malam da Hajiya suka sanni. To me yasa ba zaka nuna min irin yardar da ka yi min ba?” Yayi shiru, ransa a bace, Umar bai ce uffan ba, illa zama daya gyara Muhseen ya ci-gaba da cevva "Shekarata nawa, ban yi aure ba? Saboda dalilin rashin samun wacce nake so? Ka fi kowa Sanin ban taba kallon wata ya mace da sunan ina sonta ba. Matata Haneefa har na aureta, ba na sonta, sai da ta sami Ciki , sannan na fara sonta, wanda a yanzu idan nace ba na sonta. nayi karya, saboda kuma 'yar dake tsakaninmu ne, Iman. Kuma duk da haka bana jin wani shahararren sonta a zuciyata ina yi mata riko ne kawai irin wanda Allah da manzonsa suka ce nayi mata,kafi kowa sanin inda zuciyata ta karkata”,

Ya dakata cike da fushi ya ci-gaba da cewa "Tunda ka ga nace yau ga wacce nake so da kaina, na kuma fada mugun hali da rashin sukuni da rashin kwanciyar hankali a kanta, ai yakamata ace ka gasgatani, ka tausaya min, ka kuma goya min baya, don tana karuwa, al bai kamata ka rufe idonka akan kasa fahimtar halin da nake ciki akan kaunarta ba. Idan ban sami kwarin guiwa daga gareka ba, wajen wa Zan samu? Idan ba ka fahimci damuwata ba, waye zai fahimta? Ko an gaya maka ni ma ina jindadin abinda ke faruwa ne? Babu yadda zanyi ne da hukuncin ubangiji ni haka Allah ya tsara min rayuwata cike da garari,na gama da jarafta akan auren Haneefa yanzu kuma idanun da kullum nake addu’ar haduwa da su yau sun bayyana a inda bai dace ba, a kamalata da inda na fito nasan ba kimata ba ce , a ganni a irin wadannan wajen, amma tunda Allah yasan abunda ke cikin zuciyata ya kuma san niyyata to Alhamdulillah ba ni da damuwar komai, amma akalla yakamata ja zama karfin guiwata ba ka juya min baya ba a lokacin da nake bukatarka”

Jikin Umar yayi sanyi, tausayin Muhseen ya kama shi. gaskiya ne duk abinda ya fada, yakamata kuma ayi masa uzuri, Tun da dai kowa ya san Muhseen bawan Allah ne. Mutumin kirki ne.Allah kuma kadai ya san abinda yake nufi da hada kauna tsakanin sa da Tee-baby ba babu kuma abinda ya fi bukata, illa addu’a. A dalilin hakan Umar ya saki ajyar zuciya yace "Ka yi hakuri Muhseen , idan na dasa bacin rai a zuciyarka, ka yi hakuri, na fahimce ka Ina rokon Allah ya kade fitinar dake ciki, ya kuma hadamu da alherin dake cikin lamarin Allah, kuma yayi gaggawar bayyana Tee-baby." Muhseen ya cika da farin-cikin fahimtar da Umar