Page 112
yayi masa,sannan yayi masa godiyar addu'ar da yayi masa, ya kuma sami kansa da kara mutunta Umar. Tun daga wannan ranar, walwala da natsuwar Muhseen tayi karanci, hatta karatun da abokan aikinsa ke dauka a wajensa na addini,da zaran sun yi nawar zuwa, ko blyu ya ba karatun, tattarawa yake ya shige gidansa, komai nasa ya canja. Kullum sai yayi waya da Ummancy. Yana tambayarta inda labari ya kwana? Amma babu wani labari me dadi, har tsawon makwanni biyu, wanda zuwa wannan lokacin, komai ya kara cabewa ga Muhseen. Ya rame, ya kara fari, hakan ya kara tabbatar ma da Umar al'amarin ba na lafiya bane, don haka ya dage da yima abokinsa addu'a.
Ranar laraba misalin karfe biyar da rabi na yamma. Muhseen na zaune a harabar kofar gidansa, hannunsa na rike da dan karamin Alkur'ani me tsarki yana karantawa. Fitan Umar kenan, wayarsa ta shiga neman agaji, sannu a hankali ya fito da ita. A gaban aljihunsa, ganin sunan Sakina ya fito, yasa yayi gaggawar dauka. "Sakina ki na lafiya? Ummancy tayi gaggawar cewa "Muhseen duk inda kake, ka aje komai ka taho yanzun nan wajen da ka fara ganina, ina tare da Tee-baby." A gigice. Muhseen yace "Sakina, don Allah ki taimaka min, kada ki bari ta bi kowa, kada kowa ya dauketa.' " Ummancy tayi murmushi, tana kallon kyakkyawar fuskar Tee-baby. Tace "Ban yi zaton ita ma za ta iya bin kowa ba, ba tare da tayi ido. Biyu da kai ba, domin na gaya mata irin wuyar nemanta da muka yi na kuma tabbatar mata ban yi zaton za ta sami wanda ke kaunarta kamar yadda kake kaunarta ba, to ina tunanin hakan ne. yasa ta ji tana da sha'awar ganinka, ita ma. Don haka zuwanka muke jira" Murmushi kawai Muhseen yake, yana jin dadin kowa ce kalma dake fita daga bakin Ummancy "Gani nan tafe". Ya kashe wayar, ya tashi da sauri yana yabon Ummancy, akan irin alkawarin da mutunta shin da tayi, cikin kankanin lokaci.