KALUBALE BOOK 1

Page 113

by @yargidanimam

Muhseen ya fito cikin tsararriyar shiga, sai tashin kamshi yake cikin cikar kamala, ya fada motarsa, ya figeta kai tsaye sai inda Ummancy da Tee-baby suke.

Can ya hangosu, su biyu a ware, ba su hadu da sauran karuwan wajen ba, hakan ya tabatar masa da cewa shi suke jira, kamar yadda Ummancy tace, a gabansu ya tsaida motar, ya sami kusan mintoci biyu bai fito daga motar ba, yana kare ma Tee-baby kallo. "Wa'iyazu billah! Allah yay halitta! Tee-baby kyanki, gidan miji, me ya ja miki wulakantar da kanki, akan karuwanci." Ya bude kofar motar, ya fito cikin cika kwarjini, ya nufosu, idonsa na dore kan Tee-baby, kamar yadda ita ma nata idon yake kafe a kansa, a zuciyarta. Tasbihi take ga Ubangijin daya tsara halittar Muhseen. Namiji ne, daya da daya abin alfaharin duk wacce za ta kira kanta da mace, ta ko wace fuska, ya hadu, tun kafin ya karasa gaban nasu, yayi matukar kokarin boye zalama da murnar ganinta. Ummancy ce ta fara tasowa tana murmushi tace "Ka iso? Yayi dan murmushi yace "Na iso Sakina, na gode. Allah ya saka miki da alherinsa". Tace "Ameen, to shi kenan, ni zan tafi. Allah ya bada Sa'a". Muhseen yasa mata ido yace "Ba na son alakarmu ta kare daga yau, domin ba zan taba mantawa da kokari da gudunmawar da ki ka ba ni ba, don haka za mu rika yin waya." Yasa hannu a aljihu, ya mika mata Naira dubu ashirin yace "Ki sa kati, sai na kiraki na gode". Ta amsa tana godiya, sannan ta dubi Tee-baby da ta shagala da kallon Muhseen, tace "To Tee-baby, shi kenan sai wani lokacin". "Na gode Ummancy." Karo na farko kenan da Muhseen ya ji muryarta, tamkar ana busa sarewa, saboda zaki, ta ko wace fuska Tee-baby ta hadu. Ummancy na tafiya. Muhseen ya matso inda Tee-baby ke zaune, yace "Sunana Muhseen Usman Jigawa". Ta lumshe idanunta masu kama da tana jin barci, tace cikin sanyin murya "Sunana Tee-baby." Yayi dan murmushi yace "Na dade da sanin