KALUBALE BOOK 1

Page 115

by @yargidanimam

Har ta bude motar za ta fita, ta juyo suka hada ido da Muhseen, yace "Ya aka yi? Tayi kasa da murya tace "Don Allah taimakeni da dubu goma, wanda zan bata, don ba za ta taba yarda da cewa tsawon wannan yammacin ban yi ciniki ba." Ba tare da yace uffan ba, ya mika mata dubu goman, ta amsa ta fice da sauri. A yayin daya bi ta da kallo har ta shige cikin gidan, ya kwantar da bayansa a kujerar motar, zuciyarsa na azalzalarsa, da kuna me yasa Allah ya hada soyayyarsa da karuwa wani irin mugun kishi ya shiga turnuke zuciyarsa , yana jin tsanar duk wani namiji da ya taba mu’amala da Tasleem. take ya samu kansa da alkawarin ko ta wane hali ma, sai ya rabata da karuwanci da ikon Allah, domin gaba daya Tasleem bata yi kyau da karuwanci ba, tana da wata boyayyiyar kamala. Bai gushe cikin wannan tunanin ba, ya ji Tee-baby na kokarin shigowa motar, jakar hannunta dauke da kayan sawa da kayan shafan jikinta, kuma ta canja kaya, tasa kananan kaya riga da wando matsattsu, gaba daya tsarin halittar jikinta duk sun bayyana. Muhseen ya dauke idonsa a kanta, cikin rashin yaba kwalliyarta, tace "Mu tafi". Ta fada a gajarce. Nan da nan ya ja motar suka bace ma unguwar, babu wanda ke magana a motar, har zuwa lokacin da Muhseen yayi (Parking) a harabar wani karamin hotel, haka zalika hotel din karamin ne, sai dai yana da kyau, ya kuma mallaki abubuwan kawa masu daukar hankali, daki na talatin da takwas ya samu, ya amshi makullin, sannan a hankali suka shiga dakin, ya kuma maida kofar ya kulle. Dakin na dauke da gado dan madaidaici da kujera guda daya, sai T.V da frij da kuma tebur dauke da wayar sadarwa. A bakin gadon Tee-baby ta zauna gami da aje Jakarta a saman tebur, tana yi masa wani irin rikitaccen kallo, wanda ya fara rikita Muhseen...

To laifin dadi karewa ga dai Muhseen usman jigawa nan a hotel waye zai samu galaba kan wani tsakanin Tasleem da shi.

Wannan shine karshen littafi na daya littafi na biyu da na uku zasu zo ne a document duk me so zai tura dari biyar dinsa ta wannan opay bank 8065990904 Abubakar Aliyu Wakili, sai a tura shaidar biya ta number ta ko ta number manager ta jamila umar janafty ta WhatsApp. Kuma garabasar ma itace idan ka biya full document zaka samu harda 1 maimakon 1k nace ku bada 500 amma iya yan cikin group dina kawai.

Nagode nagode nagode yar gidan imam na kaunar ku duka

Yar gidan imam din ku ce.