Nuwayrah the foreigner’s passion

A New World

by @zahrabmrs02

Bayan Awwani a sama ,da tsaya tsaye da komai karfe 5:25pm  agogon london Mimi ta sauka  a  filin jirgin sama na Heathrow Airport Yau gata  ita kadai  Babu Rayyan, babu Mubeen, babu kowa nata . All alone by her self ,Tana fitowa daga sashen karɓar kaya (baggage claim), ta hango wani ma'aikaci sanye da unifom yana riƙe da takarda rubuce da sunanta NUWAYRAH YUSUF MODIBBO — AURA & HERITAGE COUTURE.. Direban  da kamfanin fashion house suka tura a ɗauko ta. Bayan ya amshi manyan akwatunanta guda uku ya sanya a bayan motar, suka ɗauki hanyar unguwar South Kensington, inda masaukin ta yake .

A hanyarsu ta tafiya, Nuwayrah ta maƙale a jikin tagar motar tana kallon gine-gine na zamani da tsofaffin gine-gine masu ƙasaita, ga sanyin garin na daban yana bugun motar. Ta tuna kalaman Rayyan ranar da yazo mata sallama , inda ya sauya mata wasu kuɗaɗe zuwa Dala (US Dollars) ya ba ta a hannu, yana cewa Big Head, kar ki yarda ki shiga matsala a kwanakinki na farko. Na san za su ba ki komai, amma kasancewa da kuɗi a hannu a sabuwar ƙasa dole ne."

Suna isa kyakkyawan flat na zamani a unguwar South Kensington, direban ya taimaka mata da manyan akwatunanta har gaban ƙofar  apartment din godiya sosai tayiwa Baturen Direban ,door bell ta Danna tunda already an fada mata tana da roommate ,kofar aka bude ba tare da magana ba ,nuwayrah ta fara kici kicin shigo da boxes dinta daya Bayan daya 

Gidan ya tsaru sosai falo ne babba da set din sofa 🛋️ ga carpet me Laushi da tv gefenta kuma dining ne mai kujeru 4 sai , buɗaɗɗen kitchen na zamani, da ɗakuna biyu. 

Tana tsaye a tsakiyar falon tana ƙara dube-dube, sai ga wata ta fito daga ɗayan ɗakin. Daga ganinta  Indiya ce doguwa amma ba sosai , dogon gashinta kwance a bayanta sanye da rigar sanyi da da dogon wando mai taushi .wato itace ta bude kofa ta juya basu gaisa ba kenan ?ganin yarinyar ta mata shiru 

Nuwayrah ta ɗan faɗaɗa murmushinta  ta nufi inda take tsaye  Hello! Good evening, I am Nuwayrah. (Sannu! Ina wuni, ni ce Nuwayrah).

Kiara ta tsaya ta kalli Nuwayrah daga sama har ƙasa cikin nutsuwa 

"Hi. I'm Kiara malhotra Sannu. ta amsa a taƙaice, muryarta a daskare.

Daga haka ta juya abinta ta koma cikin ɗakinta, ta rufe ƙofar a hankali.

Nuwayrah ta kalli kofar da mamaki ,Ta ja akwatunanta zuwa ɗakinta wanda ya kasance mai faɗi ,ta fara buɗe kayanta tana  unpacking Wanda zata iya Kafin ta samu lokacin karasa sauran 

Tana tsaka da gyaran , ta lura lokaci ya ja. Ya kamata tayi  Sallar Magrib da Isha'i.

Ganin tana cikin sabuwar ƙasa kuma ba ta san ina Alƙibla take ba, ta ciro wayarta daga jaka ta buɗe wani Qibla Finder app (manhajar nuna Alƙibla). Ta zagaya cikin ɗakin har sai da alamar manuniya ta nuna mata daidai saitin Alƙibla.

Ta shimfiɗa sallayarta ,ta sanya hijabinta , sannan ta fara  da sallolinta .

Bayan ta idar da sallah, gajiyar tafiya da sauyin lokaci (jet lag) suka fara taso mata. WiFi ta kunna automatically kuwa ya kama Ta ciro wayarta ta kira su mama video call 

Mama na  ɗaga wayar, take ta  shiga jera mata tambayoyi ?Auta kin isa lafiya? kin ci abinci? Yaya masaukin? kin kulle ƙofarku kuwa? 

Nuwayrah na dariya ta riƙa ba ta amsa ɗaya bayan ɗaya, har Abba da Yaya Sadiq suka ƙaraso suma Sai tambayoyi suke mata 

Rayyan ta Kira Shima video call yana ta tsokanar ta Mimi in  London .bayan Sun gama wayar , Nuwayrah ta kwanta a kan gadonta mai laushi, tana kallon saman ɗakin... Sabuwar ƙasa, sabon gida, sabuwar rayuwa haka tayi bacci ko abincin dare bata  chi ba ,duk dai ba wani yunwa take jiba tayi ciye ciye a jirgi 

Washegari (Next Morning)

Ringing! Ringing! Ringing!

Ƙarar alarm din wayarta ya tashe Nuwayrah a gigice Ta buɗe idanunta tare da maida gilashinta fuskarta ta kalli agogo—7:45 AM

"Innalillahi!" Nuwayrah ta faɗa cikin fargaba. Ta kusa  makara a ranarta na farko direct tayi bandaki  . Wanka tayi sharp sharp ta tayar da sallar asubah wacce tayi missing ,ta sanya doguwar Rigar atamfa  danwali da   mayafinta a hannu , tana fita falon idanunta suka kai kan wani ƙaramin sticky note (takardar saƙo) da aka liƙa a table .

Anyi   rubuta da biro a taƙaice

Your keys are here. — Kiara

(Ga keys dinki . — Kiara)

Nuwayrah ta saki murmushin mamaki ta ɗauki mukullin. "Wannan Kiara Akwai bakin hali dai ,maimakon ta tashe ni? dakin  ta rufe ta fito cikin  hanzari.  tana isa bakin titi sai ta tsaya cak, tana tambayar kanta yanzu ya zaayi na karasa fashion house din ?A take ta tuna da kuɗaɗen  (US Dollars) da Rayyan ya ba ta. Mai  taxi ne ya sauke wata a gefen ta ,nuwayrah tayi saurin tsayar dashi tana nuna  adreshin Aura & Heritage Couture, South Kensington.,tana shiga motar da saki ajiyar zuciya dankwalin ta daura a nutse ta dauko yan kunne ta a Jaka ta sa ,lip gloss ta shafa tare da eye pencil,sai humran data dan Kara gogawa 

Tana isa ginin Aura & Heritage Couture, Nuwayrah ta tsaya for few seconds tana kallon ginin. Gine ne babba mai hawa uku, gaba ɗaya an ƙera shi da gilasai masu daukar hankali  sunan fashion din shi kadai abun Kallo ne .

Nuwayrah ta tura ƙofar gilashi ta shiga harabar reception (wajen karɓar baƙi). Receptionist ɗin ta karɓe ta cikin girmamawa. Bayan Nuwayrah ta gabatar da kanta halen  ta duba kwamfutarta sannan ta ce ta bi ta domin kaita sashen gudanarwa.

Aka kai Nuwayrah zuwa wani ofis mai kyau inda wata mata Wanda a kalla zata shekara 45 ke zaune tana duba takardu. Ita ce mataimakiya ta musamman (personal assistant) ga Chris, sunanta Mrs. Elizabeth Hemsworth.

Matar ta tashi da fara’a ta miƙo mata hannu Welcome to London! You must be..." (Barka da zuwa London  ke ce...) Mrs. Elizabeth ta buɗe fail ɗin hannunta tana ƙoƙarin karanta cikakken sunan Nuwayrah. "Nuu... Nuwaay... oh dear, pardon me!" (Nuu... Nuwaay... ki yi hakuri!)

Nuwayrah ta saki ƙaramin murmushi tana gyara gilashinta. "Nuwayrah Yusuf Modibbo."

Mrs. Elizabeth ta yi dariya  tana girgiza kai. What a rich, beautiful name, but my British tongue will surely struggle with it! Since this is a professional space, do you mind if I call you Miss Modibbo?

(Wanan  suna naki mai daraja da kyau, amma  harshena na Birtaniya zai sha wahala wajen ambatonsa Tunda nan wajen aiki ne  ko za ki amince ina kiranki Miss Modibbo?)

"Not at all, Mrs. Elizabeth . Miss Modibbo is perfectly fine," (Ko kaɗan, Mrs. Elizabeth Miss Modibbo din ya yi daidai sosai)

Abin dariya, ko sunan 'Modibbo' ɗin ma sai da Mrs. Elizabeth ta ɗan dakata kafin ta fito da shi da kyar saboda harshen be Saba fada bata ,oh kuma kayan ki sunyi min kyau da abinda kika daura a Kai you look like a princess Mrs Elizabeth ta fada tana shafa atamfar nuwayrah ,sosai hakan ya faranta wa nuwayrah rai 

Mrs. Elizabeth ta kewaya da ita ta nuna mata muhimman wurare a kamfanin daga baya suka Kara dawowa office din Mrs Elizabeth din inda ta nunawa nuwayrah Kujerar ta .

Sai Wajan 2pm aka fara shirin  Lunch Break ma'aikatan wajen duk suka fara shirin fita cin abinci. Nuwayrah ta koma wani teburin aiki a gefe ta zauna ita kaɗai, ba ta san inda za ta je ba ,ita sallah ma take so tayi ga yunwa Rabonta da abinci tun jiya .

Mrs. Elizabeth ta shigo  ofis din tana sanye da coat (rigar sanyi) ɗinta, ta ganta a zaune ita kaɗai.

Miss mo di Bo ,, aren't you going for lunch?" (Miss Modibbo, ba za ki fita cin abincin rana ba ne?) ta tambaya tana ƙarasowa kusa da ita.

Nuwayrah ta girgiza kanta a hankali. "I... I don't really know where to get food around here yet." (Ni... ban gama sanin inda ake samun abinci a kusa da nan ba tukunna).

Mrs. Elizabeth ta yi murmushi Come with me. The company covers all official staff meals at our executive dining hall across the street. You don't have to worry about a thing.

(Kada ki damu! Muje tare. Kamfani ke  biyan dukkan abincin ma'aikata a gidan cin abincinmu da ke ƙetaren titi.  ki damu da komai).

Suka fita tare zuwa  restaurant ɗin da kamfanin . Ga  abinci daban-daban na Turawa—salads ,steaks (gasasshen nama), da sandwiches.

Mrs. Elizabeth ta taimaka mata wajen zaɓar abincin halal (Wanda ba naman alade )da kyar  nuwayrah  take cin abincin! Yadda aka yi  salads ɗin da sauyin ɗanɗanon abincin Turawa gaba ɗaya ba su kwanta mata ba 

ba maggi Salam amma taga ko a jikinsu sai chi suke hankali kwance .

Tana tsaka da  cusan abincin ,  idanunta suka hango security na buɗe kofa  cike da girmamawa.

A nan ne Nuwayrah ta hango Christopher "Chris" Alexandria Whitmore yana shigowa  wajen cin abincin tare da wasu manyan ma'aikata.

Chris matashi ne mai shekaru 29 dogo, fuskarsa cike  kwarjini da natsuwa . Sanye yake da wata  tailored suit 

Yana tafiya  a nutse , Mrs. Elizabeth ta ɗaga masa hannu . Chris ya juyo ya dubi sashensu, idanunsa suka ɗan tsaya  a kan Nuwayrah—, wadda ke wasa da abincinta  ya bi ta da kallo  na sakan biyu , sannan ya dagawa Mrs Elizabeth hannu  ya ci gaba da tafiyarsa ,Wanann shine ceo dinmu miss mo di Bo yana da kirki fiye da yadda kike tunani yanzu ma yayi zuwan bazata ne dan yaga ingancin abincin da restaurant suke ba maiakata ,Gyada Kai nuwayrah tayi cikin gasgata maganar  Mrs Elizabeth ganin yadda Chris din ke gaisawa da workers dinsa cikin sakin fuska ba ,thank god ba irin wanda take karantawa a littafi bane ,CEO mugu mara dariya ta ayyana a ranta .

Bayan sun koma fashion house Mrs Elizabeth ta kalli nuwayrah tace 

Miss mo di Bo , gobe  ƙarfe tara na safe za mu gudanar da taron gabatarwa  ga sabbin designers dinmu —ke da Kiara itama Yau ta fara aiki duk dai tun last week tazo London ,design studio suka Nufa , Nuwayrah ta hango Kiara tana aikinta. Kiara ta ɗago kanta ta kalli Nuwayrah, sannan ta maida kanta ƙasa ta yi kamar ba ta san ta ba!

Nuwayrah ta tsaya tana kallonta da mamaki .

Me yasa Kiara ke nuna  kamar ba ta san taba? Haka nuwayrah ta zame ta koma office dinsu gefen kujerar ta nema Qilba ta shimfida dankwalin ta tayar da sallar azahar da laasar