Chapter Three
by @suttie0
Wacece Ammi?
Haifaffiyar garin Katsina State ce, cikin ƙaramar hukumarsu ta Katsina. Mahaifinta Alhaji Tajudeen Babangida ya kasance tsohon attajiri a fannin mai tun 1970s. Su uku ya haifa da matarshi Aïchatou ƴar Tuareg, (Kel Gres) na Niger Republic, Nasirudeen (Nasir), Zahradeen (Zaid) da ita Hauwa (Jidda).
Sun kasance masu alaƙa da sarautar garin Katsina amma ba ta jini ba, honorary tittle ne aka bama Alhaji Tajuddeen din don karramashi bisa dawainiya da gudummuwar da yakeyi da mutanen garin da jikinshi da dukiyarshi.
Allah Yayi mishi tsawon rai daidai gwargwado ba kamar mahaifiyarshi ba da ta rasu tun yana ƙarami, har ya aurar da autarshi ƴar lelenshi Hauwa ga Abubakar ɗan wanshi Jaafar bayan ta kammala University, inda ta karanci Business Administration aka kuma rantsar da ita cikin kamfanin mahaifinta na mai Taj Oil and Industrial Resources Ltd domin jagorantarda kasuwancin tareda yayyinta.
Abubakar ɗa ne ga wan Alhaji Tajudeen, Jaafar Babangida. Su biyu kenan maza a gidansu, Jaafar da Tajudeen sai sauran ƴan uwansu mata 14. Mahaifinsu Kamaludeen Babangida jajirtaccen ɗan kasuwa ne mai mata uku, ƴaƴanshi guda 6 daga uwargidanshi Uwaani ne; mata biyar sai babban ɗanshi Jaafar, 4 daga matarshi ta biyu Maijidda; mata uku da ɗanshi na biyu Tajudeen, sai wasu 6 daga amaryarshi Balaraba; duka mata.
Bayan rasuwarshi mazan dai biyu su ke ɗawainiya da jagorantan ahalinshi har Allah yayi musu nasu buɗin inda shi Tajudeen yayi fice fiyeda ɗan uwanshi Jaafar.
Yayinda Tajudeen ya auro Aïchatou ƴar abokin kasuwancin mahaifinsu, Jaafar kuma ƴar uwarshi ya aura daga Adamawa can wurin dangin mahaifiyarshi. Shima dai maza biyu Allah Ya bashi Abubakar da Nafi'u waɗanda sukazo a karshe bayan ƴaƴanshi mata huɗu; Nafisa, Shafa'atu, Halima, Sa'adatu. Wani mugun hali da Allah Ya jarrabi Uwaani shine kwaɗayi da rashin wadatan zuci duk tsabar dukiyar da Allah yayima mijinta da ɗanta. Halinda ta fesama ƴaƴanta kenan suma saidai waɗanda suka fita zakka.
Auren zumunci ne tsakanin Ammi da Abubakar bisa umarnin Uwaani ga ɗanta Jaafar domin Ammi da Abubakar basuyi tsammanin wannan haɗin ba amma sun zauna cikin aminci da amana dukda babu soyayya a tsakaninsu saidai kauna irinta yan uwantaka na jini. Watanni kaɗan bayan auren Ammi na fari Allah Ya dauki ran mahaifinta Alhaji Tajudeen bayan yayi wata zazzafan zazzabi farat ɗaya irinta ajali.
Ammi da Aichatou sunsha kuka ba kaɗanba tunda shi ba wani mai ciwo bane kasafai inba mura ba sai abunda baza'a rasa ba har shekarun girmanshi, amma tashi ɗaya ciwo ya kwantar dashi lokacin Ammi na laulayin cikin Imaani a tsaitsaye dan bama tasan tana ɗauke da juna biyu ba. Nasir ne mai karfafa musu gwiwa, shima ba da iyawan kanshi ba. Zaid shima duk ya kiɗime, ashe sallamarshi ta karshe kenan da Babanshi bayan yakaishi airport zai wuce garin Port Harcourt inda akayi posting dinshi kasancewanshi Soldiern ƙasa.
Hakanan dai aka hakura, rayuwa ta cigaba Nasir yaɗauki gwagwarmayar dukiyar mahaifinshi wanda Allah Ya sanyawa albarka ta bunƙasa ciki da wajen Nigeria harma sunbuɗe sababbin reshen kasuwanci na shige da ficen kayan ƙarafuna, na'urorin wuta (electrical appliances) da textile.
Watanni kaɗan bayan rasuwar Alhaji Tajudeen, Abubakar mijin Ammi ya gamu da hatsari a hanyar Zamfara yaje duba wasu kayan kasuwancinshi, to a hanyar dawowa ne ajali ya riskeshi da ƙaninshi Nafi'u da kuma drivernsu. Nafi'u ne kaɗai ya tsira amma sauran biyun basu sha wahala ba rai yayi halinshi.
Lokacinda da labari ya riski Ammi kusan ɗan karamin hauka tayi abun tausayi! Ta rasa mahaifinta da mijinta watanni shida tsakaninsu, shekarunta 23 kacal a duniya. Aïchatou (Tamghart) tayita tausarta da haƙuri da tawakkali har Allah Ya sauketa da Imaani 2 months after rasuwar. Imaani taci sunan mahaifiyar Tamghart wato Eeman kaman yadda Ammi ta buƙaci marigayi Abubakar lokacin yana raye.
Wannan suna baiyima danginshi ba especially Mama Uwaani, domin a ganinta kamata yayi asa sunanta tunda Abubakar babban jikanta ne kuma ƙwallafa rai, gashi ƴa mace ta haifa ba namiji ba. Duk burinda ta ɗauka kan dukiyar Abubakar zai dawo hannun Nafi'u yayyen Ammi Nasir da Zaid suka kafe kan a rabashi bayan haihuwar Imaani, su zasu kular mata dashi sanin halin Uwaani da Nafi'u. Baba Jaafar kasa taɓuka komai yayi yana can yana ji da rashin ɗan uwanshi da ɗanshi.
***
Ammi ce zaune cikin palournta tana waya da ƙanin mahaifin Imaani, Kawu Nafi'u. Cikin natsuwa take sauraren maganan da yake tsara mata har yagama yakashe bata bashi wani ƙwaƙƙwaran amsa ba. Mamaki ya kashe mata baki dan bata taɓa tunanin zantukan da zaizo mata dashi kenan ba yau. Tana cikin wannan yanayin wayarta ya ɗauki ƙaran kira, dubawa tayi taga ɗaya daga cikin ƙannen Abbu ne Amatullah. Amsa kiran tayi ta kara a kunnenta.
Daga cikin wayan akace, "Assalam alaikum Ammi ina kwana antashi lafiya?"
Murmushi Ammi ta sakimmata, "Lafiya kalau Amatullah, ya gida ya yara? Fatan kowa na lafiya?"
"Lafiya kalau Ammi yasu Shukrah da Imaani?"
"Duk suna lafiya, ya shirin biki, kinshigo gari ne?" Ammi ta tambaya kasancewan ana shirin bikin ƴar Abba ƙanin Abbu kenan.
"A'a zuwa Friday dai zanshigo saboda ranan Saturday za'a karbi lefen Muhibban anan gidan Daada."
"Okay, nayi zaton anriga an amsa ma saboda naji shuru Hamida bata cemun komai ba."
Wata ƴar dariyar kunya Amatullah ta saki, "A'a Ammi ai ba'a tsayar da ranan amsan ba sai last week, kiranma kenan danayi miki."
Ammi tace, "To ba laifi Allah Ya kaumu Saturday din."
Sallama sukayi da Amatullah, Ammi na yaba halinta na kirki wanda yasha bambam dana wasu daga ƴan uwanta. Da Amatullah bata kirata ta faɗa mata ba, aka amsa lefen banda ita wani wutan za'a kunno mata wurin Daada. Dama sunce tafi ƙarfin Abbu, ita take juyashi yadda taso shiyasa bata shiga sha'anin gidan sai taso. Ita kuma Ammi girmanta take kamawa saboda tun farkon aurenta da Abbu wasu daga ƴan uwanshi sun nuna adawa da ita, barinma matar Abba wacce tare aka aurota da mahaifiyarsu Rafeeq kuma akwai ƙawance mai ƙarfi tsakaninsu har yanzu.
Tashi tayi ta sauka ƙasa don ta kammala ma Abbu dinner kafin yadawo.
***
Saida taji dawowan Abbu tukunna Imaani ta fito daga library ɗauke da littafin data ɓata lokaci wurin karantawa tunda ta shiga. Already Rafeeq yadawo har yasake fita baiyi mata maganan documents ɗin hannunta ba.
Bayan tayi sallar Maghrib ta leƙa sashin Ammi ta tarar tana kammala sallanta tareda Shukrah datayi kane-kane ajikin Ammi tana binta wurin karanta Adhkar ɗin bayan sallah. Tashi Ammi tayi, tana nannade sallayar Abbu yashigo kai tsaye Ammi yanufa ya nannaɗeta da hannuwanshi. Bashiri Imaani taja hannun Shukrah daketa murnan ganinshi sukayi waje.
Imaani ta kammala saka Shukrah a babyseat ɗinta na dining kenan bayan Isha'i Abbu ya sauko riƙe da hannun Ammi cikin casual wears na zaman gida Polo t-shirt da wandon Chinos. Already anjera abincinda zasuci, Abbu yajama Ammi kujeranta ta zauna tana thanking ɗinshi. Sai yayi customary greetings ɗinda yakema ƴaƴanshi wato sumbatar kawunansu cikin kulawa.
Suna cikin cin abinci Abbu yayi realising Asma'u batanan kuma yasan babu indazata bada saninshi ba.
"Boɗɗo am ina Asma'u take?"
Sai lokacinma ta tuna da wata Asma'u, "Abbu ni I've been in the library all day amma naganta a parlour ɗazu darana tareda kawarta."
"Kawarta kuma?" Yayi directing tambayanshi ga Ammi.
Ammi ta amsa da, "Ɗazu Shamsiyya tazo tacemin zasu je da ita Asma'un can gidan Abba. Muhibba ta aikesu karban sako a car park, kasan anfara shirin bikinta."
Kirane yashigo wayan Abbu. Ɗauka yayi, daga yanayin maganarshi za'a gane da Abba yake waya. Yana mishi bayanin wasu takardu da Rafeeq zai zo mishi dasu Abbun ya duba. Bayan ya kammala ne Rafeeq ɗin yashigo daga corridorn maindoors ɗin palourn cikin takunshi na natsuwa sanye da cream color din yadi, ɗinkinshi na maza masu tashen ƙuruciya da ji da Naira. A bayanshi Asma'u ce kaman munafuka itama tashigo cikin boubou irinna ƴanmata masu tashen kuruciya da ɗankwalinnan na kaddara ɗaure a kanta.
Hanyan stairs ta nufa Rafeeq ya kira sunanta a dake, "Hala bakya ganin mutane a nan ne da zaki kama hanyan sama?"
"Au.." ta amsa tana warware dankwalinta don ta yanashi kaman mayafi kafin ta ƙarasa dining Arean.
"Sannu da zuwa Abbu ina wuni, ina wuni Ammi."
Kafin Ammi ta amsa Abbu yace, "Da izinin wa kika fita? Bance kada kisake barin gidannan batare da sanina ba?"
"Abbu kayi hakuri dan Allah, Adda Muhibba ce-"
"Okay, umarnin Muhibba na gaba da umarnin mahaifinki kenan?"
Ta fara inda inda, yace, "Get your knees on the floor upstairs in my parlour, now!"
Ai dasauri takama hanyan sama gabanta da faɗuwa, lallai ta fusata Abbu ainun Allah ne kaɗai zai ceceta yau. Ta tabbata hadda laifinta na jiya wanda Mama ta janyo mata da ita kanta haushinda Abbu keji da Mama ya ƙara fusata Abbu shine zai huce akanta. Abun takaicinma agaban Shukrah salon taƙara rainata da matsiyaciyar nan Imaani Abbu yake mata haka.
A ƙasa kuma Ammi ce take shirin sauko da fushin Abbu amma ya ɗaga mata hannu yana faɗin, "Kinga Jidda, karki ƙara fusatani. Ban haifi ƴarda zata rinƙa bijiremun ba, ita Imaani da ban haifaba tana bijirema umarnina ne sai Asma'u? Sai yaushe zatayi hankali? Bafa yarinya ƙarama bace, to tana buƙatan in gyara mata zama."
Rafeeq ne ya mikama Abbu files ɗin hannunshi bayan ya zauna. Gaisawa da Ammi yayi ta amsa mishi.
Ya juya wurin Imaani da take gaidashi tana adduan kar yatuna da assignment ɗinta awurinshi, "Lafiya kalau Boɗɗo, ina aikinda nabaki?"
Da sauri tace, "Yana sama ban ƙarasa ba."
"To jeki ɗauko ki ƙarasa."
"To Hamma." Ta amsa mishi tana tashi tunda tarigada ta kammala. Dauke plate ɗinta dana Shukrah tayi takai kitchen, ta kira Halita dan taima Shukrah shirin bacci. Kafin tadawo Abbu da Ammi sun kammala har sunhau sama. Rafeeq ne kaɗai ke cin abinci.
Da sauri taje ɗakinta ta karasa keɓantaccen wurin ayyukanta ta ɗauko files ɗin ta sauko ƙasa. A hankali taje wurinshi taja kujera ta zauna.
Ai tunda Rafeeq yaga ɗarinda takeyi yasan ba abunda ta duba balantana tayi. Miƙa hannunshi yayi batareda yace mata komai ba.
"Hamma.."
Tsareta yayi da kakkaifan idanunshi dake sa gabanta faduwa.
"Hamma dan Allah kayi hakuri, wallahi yanzunnan zangama inbaka."
Baice mata komaiba, ganin haka yasa ta miƙamai kawai.
Dubawa yayi, baimayi nisaba ya maido mata. Amsa tayi ta miƙe zata library dan ba ƙaramin shakkan wannan shurun nashi takeyi ba.
"Dawo kizauna." Rafeeq ya faɗa a kausashe.
Ba shiri ta koma tafara dubawa. Documentation ne da ake gudanarwa a border duk lokacinda aka shigo da kaya. Kuma wanda zata duba ba kaɗan bane tunda kayan ba kaɗan ake shigodasu ba. It took her at least 3 hours dan tun wurin to 9 saida shabiyu tawuce tukunna ta kammala. Tana nan har taji hayaniyan Asma'u da Abbu lokacinda yake zaneta, don shi Abbu yaro baya taɓa girma indai wurin hukunci ne.
By then Rafeeq yakoma parlourn dake gefe yana duba Tablet ɗinshi, TV akunne yake a Channel ɗin News.
Bacci nacin idanunta ta rufe takardun ta ƙarasa wurin Rafeeq wanda idanunshi suke shar kaman tsakar rana ne yanzu.
A shagwabe tace mishi, "Na gama."
Nuna mata yayi da ta zauna ta jirashi saiya kammala abunda yakeyi. Kaman tayi kuka ta zube a Sofan bayanta. Ƙarar takun Abbu suka jiyo yana saukowa zaiyi zagayen da yasaba duk dare na duka gidan dukda tarin securityn dake karaɗe ko ina.
Yace, "Baku gama ba har yanzu Rafeeq?"
"Abbu she's serving punishment for procastinating. Bata ɗaukan aikin seriously tunda taga akwai masu mata."
Buɗe baki tayi zata ma Abbu ƙorafi Rafeeq ya wulla mata harara, haɗe rai tayi ta rufe bakinta.
Abbu yace mishi, "Dakyau." Kafin ya fita waje.
"Zo kimun bayanin abunda kikayi."
Ai dasauri ta matso kusada shi, tana jiyo kamshin daɗɗaɗan turarenshi na Dior Sauvage Elixir kafin tafara bayani dalla dalla.
Dasafe Imaani ta shirya cikin black Abaya da aka ƙawata da blue and white stones sai bold flowers a hannaye, kasan rigan da gefen mayafi. Dama ta riga ta sanarma Abbu da asuba wurin karatu cewa ansa musu lectures jiya da daddare.
Kiran Mr. Samuel ne yashigo wayarta ya sanar da ita yana waje yana jiranta. Hand bag ɗinta ta ɗauka na YSL sai Tablet da Notepad na rubutun kowane lectures. A cewarta ai tawuce daukan school bag kuma yanzu, tunda Master's takeyi, school bag sai su Shukrah.
Saukowa takeyi cikin natsuwa sanye da takalman heels na Givenchy, dan Imaani ma'abociyar heels ne dukda matsakaicin tsayinta. Breakfast ta tarar ƴan gidan sunayi harda Asma'u da idanunta sukayi luhu luhu domin kwana tayi tana kuka.
Ƙarasawa tayi dan musu sallama kafin ta tafi. "Abbu zan wuce yanzu Mr. Samuel yana jirana."
Sauke cup ɗinshi Abbu yayi, "Karfe nawa ne lectures din?"
"9 to 11 sai 12 to 1. Sannan inaso naga supervisor na akan Project defence ɗina bayan Zuhr."
"Yaushe Cynthia zata dawo? Banason yawonnan da kukeyi babu ita amma bari zansamu Samuel ɗin kawai." Sai ya juwa ya kalli Rafeeq dakeshan Coffeenshi na ƙaddara, "Ka ajiyeta a school, Samuel saiya biku ya jirata sudawo tare."
Rafeeq dake sanye da kayan zuwa aiki Italian Suit kaman Abbu yace, "Okay bari muwuce yanzu kawai. Ammi sai anjima."
"Adawo lafiya Rafeeq." Ta amsa mishi, shi kuma saiya shafa kan Asma'u da Shukrah affectionately yabi bayan Imaani datayi waje.
Tana fita a gaban porch taga motar Rafeeq parke baƙa wulik sai sheƙi takeyi, Audi RS5 ce. Auwal ne ɗaya daga cikin masu hidima a gidan tsaye agaban motar, yayi saurin buɗe mata ƙofar gaba, daga gani yayi warming motar ne kamar yadda ake ma motocin gidan duk safiya. Shiga tayi bayan sun gaisa ta gyara rigarta kafin ya kulle kofan.
Rafeeq daya biyo bayanta ya tsaya yana magana da Mr. Samuel inda yake bashi sakon Abbu. Shigowa motar yayi ya tada, ya juyo yana kallon Imaani da tayi masifar kyau kwarjini, haiba da kamalarta duk sun bayyana, tabbacin rainon Ammi kenan. A zuciyarshi yake fatan Asma'u tayi koyi da ita ta dawo daga rakiyar mahaifiyarsu.
Da fillanci ya faɗa mata ta saka seat belt ɗinta kafin shima yasa nashi, ƙa'idarshi kenan duk sanda zai tuƙaka a mota saika saka.
Da dakakkiyar muryarshi yace, "Kinyi breakfast?"
Girgiza kanta tayi, "Zamuje Café da Naseemah idan mungama first lecture ɗinmu."
Maganan da security yayi mishi a bakin gate kafin a buɗe ne ya dakatar dashi daga amsata.
Suna fita yace, "Okay, by 11 zaku fita bazaku tsaya class din 12 ba kenan."
Ɗan ware idanuwanta tayi, faɗa kawai tayi fa dan yabar zancen.
"A'a Hamma ina nufin idan mungama lectures wai."
Bai sake cemata komai ba ya duba agogonshi yaga akwai kaman minti arba'in kafin 9 yayi.
Shuru motar yayi a zuciyar Imaani gulmarsa takeyi ƴan miskilancin na kusa kenan. Tana cikin tunani kira ya shigo wayarta, dubawa tayi taga Naseemah ce, course mate ɗinta kuma ƙawarta dasuke Master's tare. Itace ƙawarta mafi kusa bayan Khadija dasukayi Cresent Height's tare kuma suna nan tare har yanzu.
Ɗagawa tayi daga cikin wayar taji ance, "Wai kina inane yanzunnan aka saukeni kinsan nace miki inaso ki dubamin assignment ɗina kafin nayi submitting shiyasa nace kishigo dawuri."
Rolling eyes ɗinta Imaani tayi, tayi kasa da murya, "Ai kyayi sallama idan bazaki tsaya mu gaisaba ko. Ina hanya ne."
Naseemah tace, "Assalamu alaikum antashi lafiya ya kwanan yara? Mtseww, ni dama ki zomin da abinci wallahi bansa komai a cikina ba na kasa natsuwa naci saboda assignment ɗinnan."
Satar kallon Rafeeq Imaani tayi, ahankali tace, "Nima banyiba Hamma ne zai kawoni ba Mr. Samuel ba."
Naseemah tace, "Oh Lord, nariga nasan babu abinda zan taɓuka a class ɗin yau saboda yunwa, idan kinshigo sai musan yadda zamuyi."
Imaani tace, "Okay." Kafin ta katse wayar.
Parking ɗin motar Rafeeq yayi agaban wani bakery house a hanyan makarantarsu Imaani ya fita, murmushi Imaani tayi dama tayi tunanin bazai bari tatafi school hakanan ba. Haka halin Rafeeq yake kaman Abbu he always feels responsible ga ƙannen nashi.
Mintuna kaɗan yafito ɗauke da paperbags a hannunshi, ya buɗe seat ɗin baya ya ajiyesu. Ƙamshin gasashshen fulawa bugun safe ya baɗe motar. Yashigo ya tada motar suka cigaba da tafiya.
Har bakin department dinsu na Hospitality Management a cikin Northern Gate University Kaduna yakai Imaani. Daga gefen building ɗin akwai wani garden inda ɗalibai ke hutawa, can ta hango Naseemah tasa laptop agaba, saura kaman minti ashirin kafin lecturern yazo.
Juyawa Rafeeq yayi yana kallonta ganin bata fita ba, turo bakinta tayi gaba, "Hamma to bakace indauka ba."
Harararta yayi yace, "Me kenan?"
Ƙin ansawa tayi, ɗauke kanshi Rafeeq yayi yace, "Dauka, gobe ma ki ƙara fita bakici abinci ba."
Murmushi tayi har dimple ɗinta guda ɗaya dake haɓarta na hagu ya lotsa, "Thank you Hamma."
Ɗaukar jakarta tayi da tarkacenta ta fita, ta buɗe kofar baya ta ɗauka paperbag biyu tabar ɗayan kaman yaji wayar da tayi da Naseemah. Ba abin mamaki bane sanin yanada kaifin ji sosai. Ta kulle motan kafin ta ɗaga mishi hannu tayi gaba wurin ƙawarta.
Da ido Rafeeq ya rakata har inda ta nufa kafin yaja motarshi, yasama Mr. Samuel daya samu wuri yayi parking a gefen department ɗinsu signal ya wuce.