MATAR GIDA PAGE 57
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P57
Tafiyar mintina talatin ne daga gidan Ɗalha zuwa islamiyyar,a hanyar tafiyar su Unaisa ta riƙa kalle kalle ganin islamiyya da makarantar koyan mota da ta yi regester babu nisa,nan take Unaisa ta ji hankalinta ya kwanta,bayan Ɗalha ya ajiye ta a islamiyya ofishin shugaban islamiyyar Ɗalha ya wuce yana tafe Unaisa na biye da shi bayan shigarsu,cike da girmama Ɗalha da shugaban islamiyya suka gaisa ita ma Unaisa ta gaida shi, zama Ɗalha ya yi bisa ɗaya daga cikin kujeru da aka tanadar dan baƙi ita ma Unaisa waje ta samu zauna kan wata kujera,sabuwar hijab yaɗi huɗu da rabi kalar ƙasa tare da niƙab da safar hannu da ƙafa shugaban makaranta ya dauko cikin wata leda ya miƙawa Ɗalha ya ce ''wannan shine uniform ɗin mu'' ƙarɓa Ɗalha ya yi tare da miƙawa Unaisa, "zata iya zuwa aji yanzu,aji huɗu za mu sa ta, ka ce ta yi sauƙa ko?" Ɗalha ya ce ''eh ta yi sauka'' ya kare magana yana kallon Unaisa da itama shi take kallo ''malama in kin fita ki kalle ɓarin hagu za ki ga classes jeri wanda aka rubuta class 4 nan za ki shiga'' kamar wata mutumiyar arziƙi Unaisa ta ce ''to Mallam'' daga haka ta fita daga ofishin bata wani sha wahala wajen gano ajin,bayan shigarta waje ta samu ta zauna kafin ta gaisa da sauran matan dake cikin ajin,niƙab ta ciro daga ledar hijab ta rufe fuskarta kafin ta dauke wayarta daga jakarta ta kunna data yayinda da yawa daga cikin matan ajin suna bitar karatu kaɗan ne daga cikinsu suke hira, kasancewar Malamin da ke daukar su bai shigo ba tukun na,a can wajen Ɗalha kowa bayan fitar Unaisa daga ofishin sallama ya yiwa shugaban islamiyya daga haka ya fita daga ofishin layin Unaisa ya kira bata ɗaga ba hakan yasa ya tura mata saƙo cewar ba zai samu daman zuwan daukanta ba in sun tashi ya tura mata kuɗi naira dubu hudu ya ce ta hau mota,sosai Unaisa ta ji daɗin hakan saboda zata samu damar zuwa makarantar koyan mota har ba yau za a fara koya mata motar ba,bayan komawar Ɗalha gida tarɓa mai kyau Amirah ta yi masa nan cikin parlour ya zauna yana mayar da numfashi ya cewa Amirah ta kawo masa abin kari,nan cikin parlour ya zauna ya ci alale da kunu,unin ranar gaba ɗaya a bangaren Amirah Ɗalha ya yi abin da ke fitar da shi sallah da ya idar zai koma ɓangarenta ya zauna cikin yara su yi ta wasa, misalin ƙarfe huɗu na yamma Ɗalha na zaune tare da Sudais suna buga game cikin wayarsa duka yara sun kewaye sa,a natse Amirah ta fito daga ɗaki tun da ta tashin da safe take aikin gyare gyaren gida da girki ga kuma hidimar yara sai yanzu ta gama,kasancewar har sannan garin da sanyi sanyi,Amirah sanye take ciki wata less ja da aka yiwa ɗinki half bubu riga da sikit,sosai ɗinkin ya yi mata kyau, lokaci guda ƙhamshinta ya gauraye parlour a hankali Ɗalha ya ɗago ya mayar da dubansa gareta yana ƙare mata kallo hannuta riƙe da waya tana waya ɗayar hannu riƙe da jakar da take sa uniform ɗin su Sudais,har ta shiga cikin parlour Ɗalha na satar kallonta daga karshe dai Sudais ya karɓi wayar sun cigaba da buga game tare da ƴan uwansa,bayan Amirah ta gama waya ne ta sakarwa Ɗalha murmushi ta ce ''lafiya? irin wannan kallo haka'' a hankali ya yunƙura tare da tashi tsaye ya nufi inda take shimfiɗa tafurma da zani,gogan uniform ɗinsu Sudais take son yi,waje Ɗalha ya samu ya zauna kan kujera one siter bayan Amirah ta gama shimfiɗa zani kan tafurma ta dauki uniform zata fara goge bayan ta jona ayon da soket,mayar da dubanta ta yi ga Ɗalha ta ce ''gobe in Allah ya kaimu zan koma aiki hutun da na dauka ya kare''shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''Allah ya kaimu goben ya bada sa'a'' Amirah ta amsa da ameen shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni can Ɗalha ya ce ''wa zai min hira wa zai dafa min abinci gobe?" cike da mamaki Amirah ta ɗago ta mayar da dubanta garesa ta ce ''ban gane ba'' gyara zama Ɗalha ya yi kafin ya sake tambayar ta kamar yadda ya yi da farko murmushi kawai Amirah ta yi cikin zuciyarta tana ƙara mamakin Ɗalha murya can ƙasa ta ce ''ikon Allah'' a zahiri kuma ta ce ''Unaisa'' shiru tana kallonsa kamar yadda shima ke kallonta can ta daura da ''kamar yadda ka sani gobe zan fita girki wajen ta zaka koma gobe,saboda haka ita zata dafa maka abinci ta yi maka hira'' taɓe baki Ɗalha ya yi kafin ya ce ''za dai ta dafa nata amma ni a nan zan ci nawa duk abinda za ki daga gobe ki dafa har da ni'' hannu Amirah ta kai ta kashe soket daga haka ta mayar dubanta ga Ɗalha ta ce ban fahimci ka ba'' a takaici ya ce ''kin fahimta cewa na yi a nan zan ci abinci gobe,ba iya gobe kaɗai ba kai kullum ma a nan zan riƙa cin abinci wahalar ta isa haka bazan iya ba'' ya kare magana tare dauke kai gefe numfasawa Amirah ta yi kafin cikin kwantar da murya da wannan yanayin nan nata na sanyi jiki ta ce ''wahalar me fa?" shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba ganin bai da niyyar amsa ta yasa Amirah faɗin ''ka yi hakuri ba zan iya ba, kana da duk wata dama na cin abinci duk inda ka ke so mu duka biyun matan ka ne,amma ka sani bana son tashin hankali duk wani abinda zai haɗa ni rigima da kishiya bana son wannan abun,dole Unaisa baza ta ji daɗi ba in har ta fahimci baka cin abin ta sai nawa,in da akwai wani abu da take maka wanda baka jin daɗi ka faɗa mata sai ta gyara ba zan so ka yi min haka ba,saboda haka ba zan bari ka yi mata ba,ka yi hakuri ba zan iya ba'' tana gama faɗin haka ta kunna soket ta cigaba da gogan uniform da take cike da mamaki Ɗalha ke kallon Amirah kamar ba zai ce komai ba sai kuma
Ya ja wata doguwar ajiyar zuciya mayar da dubansa ya yi ga Amirah yaga ko kaɗan fuskarta babu alamar wasu hakan yasa ya gyara zama kafin ya ce ''bata iya girki bane babu abinda ta iya sanda muke Kano...saurin dakatar da shi Amirah ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu tsabar bata son jin zancen idanunta rufe ta ce ''no..no..no Please stop dan Allah ka yi shiru bani son ji, matar ka ce koma mainene wanna tsakanin ku ne,in bata iya dafa abinci ba wannan ba abin damuwa bane zan sa Aina'u ta riƙa nuna mata har ta iya,da ita nake waya ɗazu daman gobe zata dawo'' shiru Amirah ta yi tana nazari can ta ce ''me zai hana duk ranar girkin Unaisa ta je ta taya ta aiki nima kuma ranar girkina ta zo bangare na ta taimaka min,ina ganin hakan zai fi in ta zo gobe zan ce mata ta je can bangaren Unaisa ta taimaka mata'' shiru Amirah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''ina ganin ka kira Aina'u da kanka ka faɗa mata hakan zai fi'' taɓe baki Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ba ki san wacece Unaisa ba bafa zata yi girkin ba kitchen ɗin ma ban ce zata shiga ba,a takaice dai abinci ƴar aiki zan riƙa ci duk ranar girkin Unaisa'' ya ƙare magana yana girgiza kai gyara zama Amirah ta yi cike da mamaki kafin ta ce ''kamar yaya baza ta shiga kitchen ba?" murmushi kawai Ɗalha ya yi kafin ya ce ''za ki riƙa samin abinci kullum ko kowa?" ya kare magana yana kafeta da ido a takaice Amirah ta ce ''a'a ba zan iya ba'' daga haka ta cigaba da gogan da take cike da mamaki da kuma ɓacin rai Ɗalha ya tashi ya bar parlour ya wuce ɗakin sa yana mamakin Amirah tun da yake da ita bata taɓa yi masa musu ba duk abinda yake so shi take yi tabbas Amirah ta sauya hali,zama ya yi bakin gado ya kira layin Aina'u bugu ɗaya ta ɗaga cike da girmamawa ta gaida Ɗalha bayan sun gama gaisawa ne Ɗalha ya yi mata bayani kamar yadda Amirah ta faɗa wacce keda girki zata riƙa taimaka mata da aiyukan gida godiya Aina'u ta yi kafin suka yi sallama da Ɗalha,a can wajen Unaisa kuwa karfe sha biyu dai dai ana tsaka da karatu a islamiyya ta nime izini wajen malamin su cewar zata fita ta siya ruwa malamin ya ce sai ta dawo bayan fitar Unaisa makaranta koyan mota ta nufa,dai dai kofar makarantar ta ciro wayarta ta kira layin wanda ta tura masa kuɗi shekaran jiya bugu ɗaya ya amsa kiran nan Unaisa ta yi masa bayani kanta nan take kuwa ya gane ta nan ya ce da ita ta shigo,bayan shigarta har ofis ɗinsa Unaisa ta je nan suka ƙara gaisawa ya yi mata ƙarin bayani kan tsare tsarensu daga haka ya dauki ld card ɗinta ya bata, daga nan Unaisa ta yi masa sallama tare da tabbacin gobe zata fara zuwa,bayan fitarta daga makarantar gidan Hajiya Bilƙisu ta nufa sai da Unaisa ta kira ta a waya ta tabbatar tana gida,bayan tafiyarta gidan tarɓar mai kyau Hajiya Bilƙisu ta yi mata ta cikata da abubuwan ciye ciye zama suka yi cikin parlour,yadda Hajiya Biƙisu ke sakin jiki da ƴan kunyarta manya ciki da yara masu ƙananun shekaru irin su Unaisa yasa duk ƴan kungiya sun fi sakin jiki da ita fiye da Hajiya Zulfa'u ita bata cika fara'a ba,Unaisa tare da Hajiya Bilƙisu sun baje a parlourn ta ga kayan ciye ciye tare gabansu ga wata wormer cike da farar shinka da miya babban tv dake manne da bango parlour yana kunne iskar fanka na hura su,a hankali Hajiya Bilƙisu ta ajiye kofin da take riƙe da shi tana yiwa Unaisa wani irin kallo can ta ce ''mai ki ka ce ban ji ba?" gyarar murya Unaisa ta yi ganin yadda yanayin Hajiya Bilƙisu ya sauya lokaci guda ta ce ''cewa na yi a ƙara min lokaci bani da hanyar samu kuɗin siyan mota a halin yanzu a ƙara min ko shekara ɗaya ce na tabba zuwa lokacin zan haɗa kuɗaɗe masu yawa''wata irin murmushi Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''sai ki fita kungiya in kin samu ƙuɗin sai ki dawo'' ta kare magana tana daukar meat pie ta kai baki cike da kiɗima Unaisa ta ce ''Allah ya huce zuciyarki bai kai ga haka ba insha Allah zan kokarta mma watanni biyu sun yi min kaɗan,yau na je makarantar koyan mota da kike haɗa ni da su na tambaye sa kuɗin mota mai araha ya ce min za a iya samun mota mai sauƙin ƙudi naira miliyan uku da rabi zuwa hudu sai dai ire iren waɗan nan motoci wahala suke ba mutum zan yi ta faman gyara,shi yasa nake gani in za a ƙara min kwanaki zan iya samun mai kyau ko ta miliyan biyar ce zuwa shidda'' tsaki Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''mijinki bai sa maki gold bane a kayan lefe?" a hankali Unaisa ta girgiza kai alamar a'a ''ba ki da wani abu mai daraja da za ki siyar ki haɗa kuɗaɗen?" jiki sanyaye Unaisa ta ce ''babu'' gyara zama Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce lefenki fa? nawa mijinki ya kashe wajen haɗa maki lefe?" shiru Unaisa ta yi tana nazari can ta ce miliyan biyar ya turawa yayata ta haɗo min'' wani irin murmushi Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''ki faɗi gaskiya'' da sauri Unaisa ta ce ''da gaske nake a gaba na ya tura mata kuɗaɗen sannan tare da ita muka yi siyayyar'' Hajiya Bilƙisu ta jinjina kai kafin ta ce ''oky in kin amince zan siya kayan lefenki kan naira miliyan huɗu,akwai wani yaro ɗan yahoo ya kawu min tallar motarsa hasali miliyan goma ake siyar da sabuwar motar a kasuwa ƴar hannu kuma miliyan bakwai zuwa takwas ake siyar da ita,to kin san masu yahoo basu damuwa da riba ko hauɗuwa,na taya motar miliyan biyar ya aminci motar bata sha wahala ba dudu watanni uku da siyan motar kuɗi yake bukata shi yasa ya sa motar a kasuwa,in kin yarda gobe zan aiks a dauko min lefenki sauran miliyan ɗaya sai ki biya ni a hankali ko ki duba wormer's ɗin ki masu kyau da tsada tare da iron pot da na gani a kitchen ɗin ki na sani kowanne tukunya zai iya kaiwa dubu ɗari da talatin zuwa hamsin'' shiru Hajiya Bilƙisu ta yi tana nazartar yanayin Unaisa can ta ce ''ki yi nazari ki gani,ina ganin hakan zai fi maki sauƙi'' ta kare magana tare da ɗaukar ayaba tana ɓare bayansa,Unaisa ta dauki sama da mintina biyar tana tunani can ta ce ''in na siyar da lefen me zan sa?" taɓe baki Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''materail za ki samu irin yaɗin ɗan Abbah ki yi masu ɗinkuna masu kyau ki yi ta sa kayan ki,ke da za ki riƙa yawo a mota ina ruwan ki da sa sutura masu tsada'' shiru Unaisa ta yi tana nazarin maganganun Hajiya Bilƙisu har cikin zuciyarta tana son kayan lefenta
SHUUKRAN