MY BEST FRIEND'S DAD

Episode 1&2

by @deeyamerh10

✨✨MY BEST FRIEND'S DAD ✨✨
By Khadijah Umar Muhammad (DEEYAMERH)
Page 1&2
Yarinya ce da bazata wuce 15years ba take tsala uban Gudu cikin Hasken Asuba da yake ketowa Allah ya bata ikon guduwa daga hannun wanda suka dauketa.
Take daya daga cikin su yagano ta cikin daga muraya yace"guys ta gudu kuzo mu bita kafin Oga jagwa yazo"Ai kafin kace me sun rufa mata baya.
Jin sun biyota yasa ta kara Gudu take iya karfin ta dan ko gabanta bata kalla burinta kawai tasami inda zata boya a cikin dajin da ba gida gaba ba gida baya, irin gudun da take na tseratar da rayuwarta da mutuncin ta ne.
Sosai take gudu tun tana waiwayawa har ta daina Domin suma bilhaki gudu suke irin nasu na mazajan da suke ji da tashan karfi...
Numfashinta da kyar ake fita dan gudu bata duba da kawayoyin da take takawa ko raunin da yake kafar ita kai wai tasamu ma fita.
Cikin uban gudun dake tayi tuntube da wani katan itace na bishiya murginawa take sosai dan gurin kamar gurin gangara yake cikin daga murya wacce duk saboda kuka tayi laushi Amma saboda tserarta da rayuwa "Please… someone help me!" Help me Muryarta haka tayi Amsa kuwa cikin dokar dajin da bawani hallitta ta dan adam da yake rayuwa a ciki Amma hakan take neman tai mako ko Allah zai kawu mata shi.
Jin jina tayi da jikin bishiyar da tsayar da ita daga gangarawar cikin wahala da bushewar baki yake kallonsu domin ko tayi kuka ba wahaye.
Mutanen da suke biyota daya daga ciki yasa kafa ya take mata hannu Wani ihu tasa nazaba domin akan gwalba ya taka hannun ..
Shi kuwa daya yana zaga yuwa ya Dalla mata mari sai da fegen bakinta ya fashi Cikin azaba ta tattaru raguwar yawun da yake bakinta me hade da jini ta tufa masa a fuska..
Shi kuwa Dayan tsayawa yayi yana kallonta kafin yasa hannu ya fito da sigari ya kunnata kafin ya zauna akan wata gajeruwar bishiya ta ɗora kafa daya kan daya sigarin yake zuka yana fesarwa yana kallona idanunsa yayi ja tabar babalawa cikinsa hayaki da yake.
Wata shigarin ya dauke da niyar kunnawa gashi ya barsu tsaye kallon suke kawai domin ya mai dasu yan iska yaza'ai sun kamata kuma ya zauna shan sigari tunda aka kawota wajan su aka fada musu me zasuyi mata Amma ya tsaya iskanci duk da sun san ba wani mahaluki da zai iya shigowa dajin saboda hadarinsa...
Cikin Muryar Tantirai daya yace" Lauje ya kamata kawai mukaddamar mata tunda har tasami damar guduwa kada musake sake ta gudu dan har yanzu da sauran jarumtarta ko yakace Saka"?.
Wanda aka kira da Aska ya cabe zancen da "Ni ban san me lauje yake nufi ba eh yarinya sai wahalar damu take Amma ya tsaya zukar sigari mum da duk muna sha Amma muka barta dan zatai Ammani idan mun gama da wannan yar shilar dan raina ya biya kuma sai naci".
Duk abinda suke yana jinsu sai da ya gama sukar sigarin kafin ya jefar da raguwar yasa kafa ya taketa nufar inda suke yake kafin yasa hannu ya ture Aska tsayawa yayi a gaban yarinyar yana kare mata kallo kafin ya lashe bakinsa.
Belt din wandansa ya fara cirewa kafin ya kalleso yayi masu wata signal da harshe wanda na take naga sun ja kafar yarinyar suna kokarin tale mata kafa su zare dogon wandan da ke jikinta.
Ko kawa suka fara da ita tana kai musu duka ta ko ina wajan kawatar akanta Askane ya Dago kara sharara mata mari take idanunta sukai taruwa jinni kafin yasa karfi ya danne ka fafunta dayan ya zagoyi ya wara hannunta sannan ya hade su da jikin bishiyar wata karar azama tasa Kafin cikin taguwar karfin da yake dashi ta sake furta HELP MEEE.
Wanna Amon yafi na farko domin sai da gaba daya dajin ya motsa da kalmar help me da ta ambata.
Ƙasa yayi da wandon yana kokarin sa hannun ya cire wandon kawai sukaji saukar murya a bayansu wajan fadar“Step away from her.”
Komai yayi shiru a wanna lokacin kafin sujuyo cikin tashin hankali domin wanna dajin hatsarinsa yakai matukar da mutane bàsa shigarshi sai dai tantirai masu Aikata barna..
mutum suka gani a tsaye Dogon ne Broad shoulders Ƙirjinsa ya cika da ƙarfi, hannayensa kuma sun yi kauri kamar na mutumin da ya saba da training. Veins sun fito a hannayensa, kuma yadda yake tsaye ya nuna cewa ba mutum ne da ake son gwada ƙarfin dashi ba dan daga tsayuwar da yayi zaka dan karkarfane.
 jikinsa sosai ya nuna alamun discipline ba kiba ba ce Muscles ne na mutum da yake training.
 A hankali ya ɗaga kansa inda Fuskarsa ta bayyana amma rufe take da black da handkerchief da tambarin kan lion a jiki wanna dalili ne yabawa idanuwansa damar bayyana masu cike da Fushi Idanuwa ne Cold Sharp Dangerous..
Lauje ne cikin tsageranci yace "Who the hell are you?”
Shiru ba amsa.
Cikin ihu lauje yace"guys ka cire mun Abin fuskarka Sannan kusa yayi Neel Down Ciba gaba da kallon lauje yayi.
Cikin Deep voice yace" nace ku bai karasa ba Aska ya kawo hannu zai cire handkerchief din kawai yasa hannun ya rike hannun Aska kafin yasa daya hannun wajan bude hannun aske kawai ya murdesu ihun da Aska yasa da yadda hannun sukai kara shi zai baka tabbacin sun karye..
Ganin haka yasa dayan shima zuwa da gudu domin kai masa duka,Ai yana zuyowa yahada masa wani jalihin gware a goshi take jini ta hanci ta baki kafin yasa kafarsa ya dake kafar nan take ta lankwashi ita ta tashi daga aiki.
Ganin abinda yayi musu yasa Lauje nufushi shima Amma kagin ya kai ga zuwa gare shi yasa kafa kawai ya daki tsakiyar Dick din shi Wani uban ihu da lauje yasa take ya zube a wajan sumamme..
Kallon abin take kamar A mafarki duk da a tsore ce take dashi domin shima bata dan waye ba Amma dai ya burgeta mutuka ba a ta taɓa ganin mutum yana motsi haka ba Kowane movement ɗinsa yana da control Kamar ya saba da faɗa
Ko kuma jikinsa ya san abin da zai yi kafin hankalinsa ya yanke shawara.
Bayan ƴan mintuna ta kalli kasa duk mutanan da suke kokarin cutarta duk gasu a gabanga a zube kamar kiyashi Amma to shi wanna waye?daga ina yake meyasa ta tai maketa?ko shine ogan nasu..
Tunanin ya katse lokacin da taji sautin takowa gareta saurin firgita tayi tana kokarin yin baya.  tsayawa cak yayi da tafiyar kafin ya sauke numfashi mai zafi har tana garin turirin fituwarsa domin da karfi ya sauke numfashi juyar da kansa yayi.
A wannan karon, yarinyar ta fijin tsoransa fiye da mutanen da suke zube a gabanta ganin yadda jikinta ya hau karkarwa yasa ya kara taki biyu zuwa baya kafin cikin yace“Don’t be afraid.”
Muryarsa ta kasance low deep kuma strangely calming jacket jikinsa ya cire ya cilla mata domin ta rufe jikinta dan duk kayanta sun yage har ana iya ganin wani bangare na jikinta wanda bai kamata ya gani ba.
“Ki rufe jikinki.”Yarinyar tadauka hannayen ta na rawa.
“Are you okay?”ta sake cin kayo muryarsa.
ta kasa amsawa saboda wasu Hawaye da suka zubo mata na farinciki da jin wanna ba irin mutanan da suke gabanta zube a yashe ba.
Mutumin ya durƙusa a gabanta, amma ya bar tazara a tsakaninsu domin kada ya ƙara tsorata ta.
“Look at me.”
A hankali ta ɗaga idanunta da jini ya kwanta a ciki wanda baka iya ganin farin idon.
Idanunsu suka hada wanda ta kasa daina kalllon cikin kwayar idonsa domin na shi idanun cike suke da nutsuwa, amma a ƙarƙashin wannan nutsuwar akwai wani abu mai duhu—wani irin fushi da har yanzu bai huce ba.
"Daga ina suka daukoki?
 ta haɗiye ƙwallar da ke makale a makogwaronta cikin rawar murya tace“Who… who are you?”
Ya yi shiru ina kallon idanuwantawda jini yayi kwance ciki ga shatar hannuwa a lamun maruka da tasha ganin bazata bashi Amsar tambayarsa ba yasa ya miƙe daga rankafawar da yayi.
 juyawa yayi da niyar bar mata wajan yarinyar da kallo ta bishi inda ta hango Tattoo Lion din da ke gefen wuyansa.
kafe gun da kallo Zanen da bazata iyaanta da shi ba domin da wanna Tattoo din kawai zata ganeshi Amma bayan shi batajin zata iya nunawa duniya cewar ga wanda ya ceci rayuwarta a lokacin da tasadakar da rayuwa.
 Cikin galabaitar da tafara yanzu na tsawan kwanaki da tayi ba ruwa ba abinci yasa muryar ta fara kasa domin idanuwanta sun fara rufewa alamar zata sume "Your neck…”sai Kuma diff.
Tsayawa yayi da tafiyar kafin yasa hannu ya taɓa gefen wuyansa, sannan yace“Forget you saw it.”
Jiyuwar da yayi da niyar sake bata wata Amsar kawai ya hangota a sume cikin zafin nama ya koma ya sabata a kafada domin barin karamar yarinya kamar wanna hadari sosai cikin jejin nan.
cikin tafiyarsa zaka hango nutsuwa amma duk da haka motsinsa yana nuna irin ƙarfin da yake da shi. Ya isa inda ya ajiye power bike ɗinsa, ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya yagyara mata zama a kafadarsa kwata kwanta bata da nauyi.
Without wasting a second, ya hau machine ɗin hannunsa ɗaya yasa kawai ya kama handle ɗin, ɗayan kuma yana rike da ita sannan ya kunna injin machine din.
VRRROOOOMMM! Sautin karar Power bike ɗin ya karade cikin dajin bebi ta b hanya ba wacce zata dashi da titin sai yayi yanke ya shiga cikin wani jejin da ba kasafai ake ganin mutum yana wucewa ba Itatuwa sunfi yawa a wajan iska tana kadawa a hankali, sai ƙurar hanya tana tashi a bayan machine ɗin.
Sosai yake sharra gudu cikin jejin kamar wanda ya saba da hanyar hango wata siririyar hanya yayi wadda idan ba wanda ya san wurin ba, zai ɗauka kamar babu hanyar da za ta kai ka ko'ina cikin kara bawa Bike din wuta yabi hanyar. 
After several minutes, ya fara hango Gida ba irin gidan da mutum zai yi tsammanin yana tsakiyar jeji ba ne a'a an gina shi ne da kataho, amma akwai wani abu mai ban tsoro game da yadda aka tsara shi. Gidan yana kusa da wani babban ruwa inda kayi gidan a gefen ruwan.
 Rage gudun machine ɗin yayi a hankali ya isa bakin gidan, ya kashe Bike din kafin yasauko daga kai duk wanna uwar tafiyar dayi da ita bata farka ba kuma shi bai gaji ba.
Shiru wajan yake sai kukayen tsuntsaye dake tashi sai kuwa karar ruwan dake wajan da suka mamaye wajen.
 Kallon wajan yake domin Wannan waje nan yake zuwa ya huta idan ya gaji da hayaniyar mutane guri ne da ba kowa ne zai iya rayuwa a wajan ba Amma yanayin wajan da sanyayiyar iskar wajan yasa yake masifar son gurin.
His secret place guri ne da babu wanda ya san dashi babu wani mahaluki da yake zuwa wajan sai shi.
ɗaga kansa sama yayi yana kallon gidan, kafin ya yi ɗan murmushi mai wuyar fahimta.
Yadda ya dauko ta haka ya shigar da ita gidan wanda babu abinda babu na more rayuwa komai a kwai yadda mutum zai iya rayuwa a wajan.
Kai tsaye kan Bed ya durata kama west dinshi yayi yana tunanin shin me zai mata yanzu tasamu ta farfado domin Allah Allah yake ya rabu da ita gaba daya wanna abinda yayi yasa kansa har ya fara ciwo.
Kallonta yake na ƴan seconds kafin ya sauke ajiyar zuciya.
Ya buɗe drawer ɗin dake gefen gadon, ya fito da ƙaramin first-aid box. Sai kuma ya buɗe freezer ɗin dake cikin ɗakin ya ɗauko kankara ya saka a cikin clean cloth.
A hankali ya dawo kusa da ita ya zauna a gefen gadon, ya ɗaga ƙafarta cikin taka-tsantsan domin ya duba inda ta ji rauni.
Kallon ƙafar yayi.
“Damn…”
Ya ɗora kankarar a hankali a kan wajen da ya kumbura sanyi kankarar da yashige ta sai hakan ya taimaka wajan farfaduwar tata duk da bata bude idonu ba amma yadda yaji ta sauke numfashi ya bashi tabbacin ta farfado Amma baccin wahala ya dauke ta.
ɗan motsa ƙafartayi cikin barci.
“Easy…”
Muryarsa low ce“It's going to hurt a little.”
Ya riƙe ƙafarta a hankali, yana matsa kankarar a hankali a kan wuraren da suka kumbura.
Bayan ya gama, sai ya ɗauki hannunta.
Akwai ƙananan raunuka a tafin hannunta saboda ta taka kan duwatsu da ƙaya lokacin da take gudu.
Ya buɗe first-aid box ɗin ya ɗauko tweezers da scissors.
Ya fara cire ƙananan ƙayayoyin da tarkacen da suka shiga cikin fatar hannunta ɗaya bayan ɗaya.
Yarinyar ta ɗan murɗe ke fuska cikin ciwo.
“Sorry.”
Ya tsaya na ɗan lokaci gudun karta farka ganin ta koma bacci yasa ya ci gaba a hankali.
Wani ƙaramin abu ne ya makale a gefen tafin hannunta. Ya cire shi da tweezers ɗin, sannan ya goge wajen da antiseptic.
“Almost done.” ya fada ya fesar da numfashi bayan ya hannunta, ya duba ɗayan ƙafar akwai ƙananan ƙananan gutsuren gilashi da duwatsu suka shiga cikin fatar ƙafarta fuska ya sake daurewa kamar tana ganinsa.
Ya fara cire waɗanda suka fi kusa da saman fata, yana yin hakan a hankali sosai kada ya ƙara mata ciwo.
Duk lokacin da ta motsa, sai ya dakata har sai ta kara komawa bacci sai ya cigaba Bayan ya cire na ƙarshe, ya goge wajen sannan ya shafa magani.
ya ɗauki bandage ya fara ɗaure mata ƙafar bayan ya gama, ya koma kan hannunta shima haka yayi mata.
Tsayawa Kallonta kawai yakeyi young girl ave tana shiga irin wanna hadari wanda badan yazo wuce wa ba da ba wannan zancen ake ba.
Irin raunikan da yake jikinta shi kansu abin kallo ne a tausaya mata Hannunsa ya matse cikin karfi.
“Those bastards…”
Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya sake mayar da hankalinsa gareta.
Ya ɗauko wani clean cloth ya jika da ruwa, sannan ya goge jinin dake gefen fuskarta a hankali.
A karon farko tun lokacin da ya gan ta...
fuskarsa ta nuna wani irin tausayi da bai saba bari ya bayyana ba ya gyara mata gashin da ya manne a goshinta saboda zufar datakeyi ganin bacci take sosai yasa ya fita domin ya samo mata kaya wanda zasuyi mata dai dai..
 fita yayi rufe ƙofar a hankali kafin ya dane Bike din yayi cikin gari.