18.
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*18.*
Sosai Saudat ta zage ta gyara wa Sauban part ɗinsa, duk da cikin sanyinta take aikin amma ko'ina ya yi masa fes yadda yake so, duk inda ta yi yana biye da ita da ido tare da ƙirƙirar tsurfa iri-iri, a gajiye tilis ta kammala ta fice, sai a lokacin ta ji ta saki numfashi yadda ya dace, don kasancewarsu da shi su kaɗai jin ta take kamar a kurkuku. Da ƙyar ta gane hanyar da suka biyo ta koma ɗakin da aka sauke ta, a bakin gado ta zube tana jin ƙafafuwanta kamar an reɗe mata su, ko'ina na jikinta ciwo yake mata, ga yunwa ga pad ɗin jikinta da ta dame ta, takure jikinta ta yi ta saki kukan da ba ta san ranar daina shi ba, hankalinta ya kasa kwanciya da zaman gidan nan kwata-kwata, yau kaɗai amma ba ƙaramin ƙuntata ta yi ba, ga kewar Mama da ta gida da ta fara.
Tana ji aka turo ƙofar ɗakin amma ta kasa ko da motsawa, sai da ta ji an dafa ta sannan ta ɗago a firgice, matar ɗazu da ta yi mata Jagora zuwa sashen Sauban ta gani, ajiyar zuciya ta sauke ta fara share hawayenta da ƙasan hijabin jikinta.
"Me ya sa kike kuka?" Matar ta tambaye ta cikin kulawa.
Hanci ta ja ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba.
"Wani abun ya yi miki?"
Ta girgiza kai.
"Ki yi haƙuri, aiki a ƙasan wani dole sai ka yi haƙuri ka ƙara, babu yadda za mu yi da ƙaddara, amma duk wanda kika gani yana aikatau ba don son ransa ba ne, babu yadda zai ne kawai."
Numfashi Saudat ta sauke ta ce. "Bana jin zan iya jurewa, saboda abu ne da ban taɓa hasaso kaina a ciki ba, ban taɓa tunanin rayuwa a gidan wasu bayan gidanmu ba, bare kuma waɗanda ban taɓa sani ba, ban taɓa gani ba, ta yaya zan iya rayuwa a wannan gidan? Daga aiki sai dawowa zaman ɗaki na zauna na yi jigum, ga shi ko wayata ban taho da ita ba bare ta dinga ɗebe mini kewa."
"Ƙaddarar kenan, ki yi haƙuri, in sha Allah komai zai wuce." Matar ta faɗa tana shafa kafaɗarta alamar rarrashi.
Hawayen idonta ta goge ta ce. "In sha Allah na gode sosai."
"Babu komai, Sunana Hansai, ina aiki a ɓangaren kitchen, girki ne kawai aikina a gidan nan, sai kuma raka baƙi wani sashen kamar yadda na yi miki, ko kuma wani aiki na musamman idan ya taso, ki tashi mu je ki ci abinci."
Kai Saudat ta jinjina ta ce. "Na gode da kulawa Aunty Hansai, amma bana jin yunwa."
"Ko ba kya jin yunwa sai kin ci abinci don ba za ki kwanta haka ba, bare ma na san kina ji."
Saudat ba ta saba musu da wanda ya girme ta ba, hakan ya sa ta yunƙura ta tashi, Hansai ta kama hannunta, har ta taɓa ƙofa za ta buɗe su fita ta dakata ta ce. "Yawwa na manta ban faɗa miki ba, sai kin yi taka-tsan-tsan, don akwai CCTV camera a ko'ina, har wannan dakin da za ki dinga kwana, don haka sai ki kiyaye ko don saboda sauya kaya da wasu abubuwan na sirrin ɗan Adam." Ido a waje Saudat ta ce. "Ban gane ba, a bedroom ɗin ne da Camera? Kuma a haka za a kwana?" Hansai ta ce. "Haka duk muke rayuwa shekara da shekaru, sai dai idan muka yi wanka mu shirya a toilet sannan mu fito."
"To bacci fa? Idan mutum ya yi wata kwanciyar da bai ma sani ba fa? Wadda bai kamata wani ya gani ba"
"Haka dai muke lallaɓawa, ai da lura muke yin komai, ke ma sai ki lura."
"Tabdijan!" Saudat ta furta, a ranta tana cewa. "Wannan wanne irin abu ne? Camera a ɗakin bacci? Yanzu da Hansai ba ta faɗa mata ba haka za ta rage kayan jikinta idan ta za kwanta wasu can su gama kalle ta? Ƙyamar zaman gidan ce ta ƙara cika mata zuciya, tana tantamar anya za ta bari ko kwana ɗaya ta yi kuwa? Ba za ta gudu ba kawai a neme ta a rasa?
Lafiyayyen abinci Hansai ta ba ta, tutturawa kawai ta yi ba don yana yi mata daɗi ba, sai dan tursasawar Hansai da kuma tsaron tashin ulcer ɗinta, ita ta ba ta pad ta sauya ta raka ta inda za ta yar da wadda ta cire, sai a lokacin ta ji dadin jikinta, tare da ɗan samun relief kaɗan saboda kulawar da Hansai ta ba ta.
Sauban kuwa sai yau ya ji yadda yake so a part ɗinsa, har wata sabuwar fresh Air ya ji tana ratsa shi, sai yanzu ya san ya samu mai aiki irin wadda yake so, bararrajewa ya yi a kan gado cikin nishaɗi, ba karamar kwana biyu da yake kwanciya a ɗarare ba saboda gudun taɓa datti, don Mom ita ma gyaran sauri take yi masa, ba ta ƙalƙala yadda yake so, cike da walwala ya kwana gami da mamakin da ya ƙi barin ransa, na yadda Saudat ta iya karanta abin da ya rubuta tsaf alhalin da turanci ya yi rubutun.
***** *****
Amma tana zaune ita kaɗai a tsakar gida, hasken ƙwan solar ya haske ko'ina, ƙafafunta take mammatsawa saboda tsamin da suka yi mata, ga bayanta sai da ta saka pillow ta jingina da shi saboda ciwo, gama suyar awararta kenan ta dawo ta watsa ruwa ta yi sallar isha'i, lissafin kuɗaɗe ta zauna don ta yi, amma gajiyar da ke addabar ta ya sa ta fasa ta bari sai zuwa anjima.
Jigum ta yi kaɗaici duk ya ishe ta, tana kewar Hasina sosai, tunanin rayuwarta ta fara, ba ta ankara ba ta ji hawaye a kuncinta, sharewa ta yi da sauri ta janyo wayarta ta lalubo numbern Hasina ta kira, a ƙoƙarinta na kawar da tsohon mikin da yake son taso mata, amma har ta ƙari ruri ta gama ba ta ɗauka ba. Girgiza kai ta yi ta ce. "Allah ka shirya mini wannan yarinya, Allah kare ta daga faɗa wa halaka saboda ruɗin duniya da son ƙyale-ƙyale." Ta ƙarashe maganar tare da kara wayar a kunnenta, bayan ta danna wani kiran an ɗaga, fuskarta ɗauke da murmushi, idanunta kuma cike da ƙwalla.
"Zakina." Ta ambata tana ƙara sakin murmushi mai sauti.
"Mom!" Ya faɗa cikin dauriya yana sauke numfashi.
"Na'am ɗan albarka, ya karatun?"
"Alhamdulillah!"
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya ba da sa'a, ina zaune ni kaɗai na ce bari na kira ka yau ba a ba ni labarin jarabawa sosai ba."
Yunƙurin tashi zaune ya yi amma yadda kansa ya sara masa ya sa ba shiri ya koma ya kwanta, muryarsa a ƙasa ya ce. "Jarabawa tana ta daɗi Mom, Ina Hasina? Har yanzu ba ta dawo ba? Ba ta zo ta duba ki ba ma ko?" A sanyaye Amma ta ce. "Ba ta dawo ba, ta ce ba yanzu ba ai." Danne ɓacin ran da ya taso masa ya yi ya ce. "Zan kira ta, ta dawo ta yi jinyar ki, har yanzu ba ki gama warwarewa ba, na ji a muryarki."
"Jikina Alhamdulillah Zaki, na ji sauƙi sosai, ka rabu da ita kawai, kar ka matsa mata don Allah, ai ba wani daɗewa ta yi ba, idan aka takura sai ta dawo Aminu ba zai ji daɗi ba."
"Baffa ya kira ki?" Ya tambaya don shi ma abu ne da yake ci masa rai, ko ya so ya share sai ya kasa, duk da sanin halin mahaifinsa ko shekaru nawa zai yi ba ya gari indai ba wani abu na buƙatar kansa ba ne ba zai taɓa kiran Amma ba, ko su ba ya kira, shi ya sa shi ma ba ya kiran shi, Hasina ce ƴar ɗakinsa da ma, ita ma sai su shafe watanni ba su yi magana ba.
Yana jin gwauron numfashin da Amma ta sauke kafin ta ce. "Bai kira ba, ni ma na kwana biyu ban kira shi ba." A raunane ya ce. "Shikenan, ki kwanta ki huta Mom, na san kin gaji, kina nan kin miƙe ƙafa...."
"Amma babu mai yi mini tausa." Ta katse shi da faɗin haka don ta san abin da zai ce kenan. A tare suka yi dariya, Aliyu ya gyara kwanciya ya ce. "Ki yi mini addu'a Mom."
"Kodayaushe cikin yi maka nake, ba dare ba rana."
"Ki ƙara!"
Yadda ya yi furucin ya sa ta yi saurin cewa. "Akwai wata matsalar ne?" Ya ce. "Babu komai My mom, kawai ina buƙatar addu'ar taki ne fiye da komai a rayuwata."
"Aliyu! Na ji muryarka wani iri fa, mene ne? Idan da wani abu ka faɗa mini mana."
"Don Allah kar ki tashi hankalinki Amma, babu komai, gajiya ce da tunanin jarabawa kawai."
"Tom shikenan, Allah ya yi maka albarka, ya kare ka daga dukkan sharri da abin ƙi, Allah ya dawwamar da walwala da farinciki a rayuwarka ya cika maka dukkanin burikanka."
"Amin ya rabb, Allah ya yi miki tukuici da aljanna." Ya faɗa yana jin fargabar matakin da Dr. Dubiya za ta ɗauka a kansa ya ragu, kamar an saka takobi an zabtare fiye da rabi, wani irin ƙwarin gwiwa na tunkarar ta da duk abin da ta zo da shi ya shige shi. Sallama suka yi ya katse kiran, sai a lokacin ta lura da an kira ta suna cikin wayar, Hasina ce da mutumin da take aune-aune a wajensa, kiran Hasina ta fara bi.
***** ******
Kamar yadda Women leader ta buƙata Umma ta bar Ahayan ta huta sosai, ba ta aiki sosai, ga bacci ishashshe da cima mai kyau, kullum daga safe har dare sai Women leader ta yi mata aiken lafiyayyen abinci, ga magunguna da take sha akan kari, ta samu lafiya sosai, ta fara dawowa hayyacinta, damuwarta kawai ciwon Sabira, don jikin yarinyar ya yi tsanani sosai.
Yau da safe bayan ta gama gyaran ɗaki ta fita ta zubar da sharar da ta kwashe, ta dawo ta ga Umma ta ɗauko Sabira a hannu ta kwantar a kan shimfiɗar da ta yi mata a tsakar gida, gabanta ne ya yanke ya faɗi, don sai ta ga kamar babu numfashi a jikinta. Da sauri ta cillar da fakar hannunta ta ƙarasa ta tsugunna ta fara tattaɓa wuyan Sabira da fuskarta cikin tashin hankali.
"Aunty Ahayan ke ma kin ɗauka ta mutu ko?"
Raudah da ke tsaye a ƙofar ɗaki ta faɗa a raunane.
Kai Ahayan ta ɗaga mata tana sakin ajiyar zuciya.
"Jikinta ya yi tsanani sosai Umma, don girman Allah a kai ta asibiti."
Cike da damuwa Umma ta ce. "Asibiti ne cin kuɗi Ahayan, ni kuma yanzu akan kuɗi ƙalilan sai dai a ɗaure ni saboda ban da su, wanda Women leader ta kawo a yi miki cefene gabaɗaya na yi biyan bashi da su wallahi, a haka ma ban gama biya ba, wanki kuma kin ga ya tsaya, da ma ke ce ƙarfin yi, ni bana iya yi da yawa."
Idanun Ahayan a cikin na Sabira da ta zuba mata su ta ce. "Daurewa za mu yi Umma mu kai ta ko na gwamnati ne, ni zan ci gaba da wankin yanzu, na ga gidansu Asma'u ai sun kawo ɗazu, bari na yi ko na mota muka samu sai mu tafi." Raudah ta ce. "Gaskiya dai, ko kuma mu tambayi Baba, ai shi yana da kuɗi." Ummi tana daga ɗaki ta ce. "Hmm, Baban da ko nuna ya san tana ciwon bai yi ba, ko sannu bai taɓa yi mata ba, saboda ma kar a tambaya shi kuɗin magani, yana kallo tana mashashshara amma yake tsallake ta ya wuce." Cikin ɓata fuska Raudah ta ce. "Ga shi Inno ba ta nan, da Umma ta roƙe ta ko rance ne ta ba mu, wallahi jiya bacci rabi da rabi na yi, saboda yadda take sanƙarewa sai na ga kamar ina tashi gawarta zan tarar." Tagumi Umma ta rafka ba ta ce komai ba.
"Sannu Sabira, Allah Ubangiji ya ba ki lafiya." Ahayan ta faɗa tare da kama hannunta, wani irin zafi ta ji ya ziyarce ta, ban da idanu da take juyawa da wani irin haki da take yi babu inda yake motsi a jikinta.
"Jikinta ya yi zafi da yawa, sai ka ce wuta fa!"
A sanyaye Umma ta ce. "Shi ya sa nake tunanin maganin Hausa kawai zan yi mata, wannan ciwon nata kamar ba na asibiti ba ne." Da sauri Ahayan ta ce. "Mu dai fara kai ta asibitin."
"Da wanne kuɗin wai? Ko so kuke mu je a wulaƙanta mu?"
Shiru duk suka yi, har lokacin hannun Sabira yana cikin na Ahayan, tana jin yadda zafin jikinta yake ratsa ta amma ta kasa sakin ta, wani irin tausayin ta take ji, saboda ita kaɗai ta san azabar da take sha.
Gabaɗaya sun yi jigum-jigum kamar za su fashe da kuka, sun saka ta a gaba kawai suna kallo, ita kuma ta tsayar da idanunta ƙyam akan Ahayan.
A haka Ummi ta fito daga ɗaki ta tarar da su, jiki a mace ta ce. "Umma ko waya za mu aro mu kira Yaya Saif, shi kaɗai ne zai iya taimakarmu a yanzu, kuma yau weekend ba ya zuwa gurin aiki, ina kiran shi zai zo." Tagumin da Umma ta rafka ta sauke ta ce. "Ko kin kira shi ma ba zai zo ba, saboda Inno ta ce duk ranar da ya sake zuwa gidan nan ba ta nan ba ta yafe masa ba, saboda ta fuskanci yana kawo mana abubuwa a duk lokacin da ta yi tafiya, kuma yau kwana uku ba ta nan, ba ta wuce wannan kwanakin a duk tafiyar da ta yi, don haka za ta iya dawowa a yau, idan ta tatar ya kai Sabira asibiti kun fi kowa sanin abin da zai faru."
"Da ma kawai mu ga Abba Adam ya zo." Cewar Raudah.
Umma ta ce. "Shi kaɗai ne kuwa zai taimaka mana kuma babu wanda ya isa ya ce don me."
Ahayan dai ta yi shiru kawai tana sauraren su, tunani take na ya za a yi ta samo kuɗi? Wanne aiki za ta yi a biya ta nan take? Don yadda Sabira ta zuba mata ido gani take kamar tana ƙalubalantar su ne na rashin samar mata magani da ba su yi ba, kamar tana faɗa mata sun gaza, sun kasa a matsayinsu na waɗanda ba ta da kamar su a duniya.
Baba ne tsaye a gaban wani mai siyar da abinci a bakin titi, Bayan an zuba masa a plate ya koma inda aka tanada domin cin abincin ya ajiye plate ɗin akan table, sai da aka miƙo masa ruwa da lemo sannan ya ware abin da aka naɗe abincin ya ɗauki cokali ya fara ci hankali kwance. Wasu dattiwan maza ne kamar shi suka ƙaraso gurin, da fara'a sosai suka dube shi tare da duƙawa. "Alhaji Barka da rana, ka zagayo nan kenan?" Sai da Baba ya taune laumar da ya saka a bakinsa sannan ya ce. "Wallahi kuwa, na ɗan fita ne na dawo na ji cikina a rarake, shi ne na tsaya na ɗan ƙara masa nauyi."
"Ah ma sha Allah, Allah ya ƙara sutura da wadata."
Ya amsa da Amin tare da duban inda ake siyar da abincin ya ɗaga murya ya ce. "Lawalli zubo plates biyu kamar yadda ka zuba mini." Sannan ya dawo da kallon shi kan mutanen ya ce. "Bismillah Malam Ɗahiru ku zauna a kawo muku abincin kuma." Don ya san abin da ya kawo su kenan, godiya suka shiga yi masa, ya amsa kamar ba shi ne mai maula a gurin wasu ba, don ba ƙaramin fasuwa kansa ya yi ba, yadda su Malam Ɗahiru suke godiyar ya sa hankalin mutane dawowa kansu, abin da yake so kenan, sai ya ƙara baza babbar riga da sauya salon cin abincin zuwa na izza da basarwa.
Ya ɗauko cinyar kaza zai kai bakinsa ya ga Umma Lantana a gabansa kamar an cillo ta, gabaɗaya ta fita daga hayyacinta, ƙafafunta sun yi furu-furu da ƙura, ta yi zuru-zuru kamar korarriya, takalmin ƙafarta ɗaya a tsinke, fuskarta ɗauke da hawaye shaɓe-shaɓe. Murtuke fuska Baba ya yi, yana jifan ta da wani mugun kallo ya ce. "Ke! Mene ne haka?" Girgiza kai ta fara yi amma ta kasa magana sai kuka kawai take, da ƙyar ta daure ta nuna shi da hannu cikin shashsheƙa ta ce. "Kai ba ƙaramin baƙin mugu azzalumi ba ne! Ina can na kasa zaune na kasa tsaye na rasa inda zan saka raina, amma kai kana nan kana warkajaminka alhalin kai ka jefa ni a halin da nake ciki, kai ka siyar mini da ƴ......"
"Ke bana son hauka? Mene haka za ki biyo ni nan kina yi mini wasu sokiburitsu da shirme?" Baba ya katse ta a tsawace.
Gigitataccen kuka ta saki ta ci gaba da magana a haukace. "Sama da sati ba mu san inda ƴarmu take ba amma kake da lokacin cin abinci har da kaza? To wallahi ba ka isa ba, sai ka nemo mini ƴata, duk inda ka kai ta ma ka je ka ɗakko mini kayata, mugu azzalumi macuci! Allah ya isa! Allah sai ya saka mini! Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba!" Ta ƙarashe maganar tare da ɓarar da abincin gabansa, ta dinga dukan table ɗin kamar mahaukaciya tana ci gaba da faɗa masa maganganu. Hakan ya janyo hankulan mutane aka fara taruwa a na tambayar lafiya, Baba dai ya yi tsuru-tsuru don mutane sun san Umma Lantana matarsa ce, wasu mata masu dafa abinci ne suka ƙaraso da sauri suka rirriƙe Umma Lantana, tana ƙoƙarin ƙwacewa amma suka hana ta. Cike da borin kunya Baba ya ce. "Saboda zan ƙara aura kika zaɓi ki yi mini wannan cin mutuncin a gaban jama'a? To kin ji daɗi kin tara mini mutane, amma ki sani kanki kika yiwa, ke kika zubar da mutuncinki ba nawa ba, mahaukaciyar banza da wofi." Tsayawa kawai Umma Lantana ta yi tana kallon shi saboda tsananin mamaki, ganin yadda ake ba shi haƙuri shi kuma yana ta bayanin abubuwan da ya yi mata na faɗar kishiya da kuɗaɗen da ya ba ta, amma duk da haka ta ƙi haƙura sai tayar masa da hankali take yi. Tana ji tana gani ya juye laifin kanta, aka fara yi mata faɗa da nasiha.
"Wannan wanne irin kishi ne Hajiya? Da girmanki da komai? Don za a yi miki kishiya ai ba ajalinki aka ce za a kawo miki ba." Cewar Malam Ɗahiru cike da haushin ta, saboda ta yi sanadin da abincin da aka siya musu ya tarwatse a ƙasa.
A fusace Baba ya ce. "Ai mahaukaciya ce wadda ba ta da girma sai na jikinta."
Haƙuri aka ba wa Baba, zuciyar Umma Lantana kamar za ta fashe ta dubi Baba cikin kuka ta ce. "Allah ya isa, na bar ka da Allah wallahi." Daga haka ta bar gurin tana ƙara ɓarkewa da sabon kuka, kukan da ba ta san ranar da za ta daina shi ba, duk inda take tunanin za a taimaka mata da neman Zeenat ta je amma har yanzu shiru, har report ƙawarta Salame ta raka ta ta shigar, gidan Malamai kuwa sun je ya kai goma, amma ko'ina da abin da za a faɗa musu, kuma ta fahimci duk kame-kame ne, ga shi ita ba yan'uwa a kusa ba bare su taya ta da wani yunƙurin, don ƙawayen nata sun gaji sun fara janye jikinsu, Baba kuma bai ma nuna ya damu da ɓatan Zeenat ɗin ba bare ya yi wani abu akai, kullum faɗa mata yake ba wata matsala, ita take damun kanta.
Tana wannan uban kukan ta koma gida ta zube a tsakar gida ta dinga rusa shi, yaran da suka biyo ta tun daga waje suka tsaya suna kallon ta, sai Ummi ce ta kora su, tashin hankali kashi da kashi ya ƙara haɗar wa su Ahayan, don duk da ba sa shiri da Zeenat amma ɓatan ta ya jefa su a ruɗani.
***** ******
Director General ne Zaune a gaban wani mutum da yake duban shi fuska babu walwala, cikin girmamawa DG ya dube shi ya ce. "Ranka ya daɗe kamar yadda na fara yi maka bayani a waya akwai wani yaronmu, yana ta zaƙulo ayyukan da aka yi a baya da na yanzu yana gabatar mana da su, ya dage kamar wanda ya san wani abu da ke ƙasa sai an bi diddigin su an gano abubuwan da aka binne an ɗauki mataki." Numfashi mutumin ya sauke ya ce. "Labarinsa ya zo mini, AD JURAIJ ne, tun kafin ya kawo wannan matsayin yake shigar mana hanci da ƙudundune, tun a lokacin Maitama kafin a kawo ka, yaro ne mai tsananin naci da taurin kai, and he's very smart."
"Exactly Sir, shi ya sa kawar da shi ko ɗaukar mataki a kansa sai an yi aiki sosai da ƙwaƙwalwa, ya matsa mana sosai akan kisan Sheikh Adnan da yaran da aka ƙwaƙulewa ido, musamman ma kisan Adnan, kuma ya fara zaƙulo wasu abubuwa da za su iya hargitsa komai."
"Ku dakatar da shi, idan ya ƙi za mu yi amfani da makusantansa da muke tare mu haɗa masa tarkon da zai ƙare rayuwarsa a prison, tun a wancan lokacin mun samu abin da za mu iya amfani da shi gurin daƙushe shi, mun ƙyale shi ne kawai saboda tunanin zai gaji ya haƙura, amma idan ya dage kawar da shi abu ne mai matuƙar sauƙi don muna da makamin da za mu yaƙe shi cikin ruwan sanyi, ɗan ƙaramin alhaki kamar shi bai isa ya zame mana ciwon kai ba."
***** *****
Women leader ce zaune a inda suke haɗuwa da matashin nan yana yi mata bayanin aikin da za su yi da Ahayan, a rikice ta miƙe tun kafin ya kai aya ta ce. "What! Ka san me kake faɗa kuwa? Ta yaya zan shiga har guri irin wannan mu aiwatar da abin da kuka buƙata mu fito lafiya ba tare an kama mu ba?" Murmushi ya yi tare da faɗin. "Ke ma kin san an gama aiwatar da komai, ƙaddamarwa ce kawai taki, an kammala duk wani shiri ke kawai ake jira ki saka rana a yi abin da za a yi a wuce gurin, ina mai tabbatar miki lafiya ƙalau sumul za ku yi ku gama, ita wannan yarinyar ita ce kawai nake tunanin za ta iya shiga hadari, ita ma akwai dalilin da ya sa aka saita komai a haka, akwai waɗanda ake son a tsikara, ake son a saka musu baƙinjini a idon al'ummar da suke mulka." Ajiyar zuciya Women leader ta sauke ta ce. "Amma wannan aikin manyanka za su iya yi da kansu cikin ƙiftawar ido, me ya sa za su buƙaci mu ƙananun ƙwari mu yi musu?"
"Na faɗa miki akwai dalilin hakan, akwai waɗanda ake son a ta'allaƙa aikin da gazawarsu, idan za ki iya mu gama magana a yanzu, idan kuma ba za ki iya ba na nemi wata, don umarnin da aka ba ni an ce dole sai mata ake so, amma kar ki manta kamar yadda na faɗa mini akwai tarin arziƙi a wannan tafiyar, idan kin amince ki shawo kan yarinyar sai ki zo na yi miki bayanin yadda za ku aiwatar da komai."
Numfashi Women leader ta sauke cikin nazari, har yanzu ba ta dawo daidai daga razanin da ta shiga ba, jikinta har rawa yake saboda shock, tsoron ta ɗaya kar a samu akasi a kama su, duk da ta san hatsabibancin wanda yake zaune a gabanta da na iyayen gidansa, amma tana tsoron kufcewar rana. A hankali ta dube shi bayan ta yi wani tunani ta ce. "Na amince! Ka ba ni nan da kwana biyu, zan zo tare da yarinyar."
"Good!" Ya faɗa tare da ɗaukar wayarsa ya latsa, a take ta ji alert, da sauri ta duba tare da waro ido saboda kuɗin da ta gani. Murmushi ya sakar mata ya ce. "Somin taɓi kenan, ki jira ragowar bayan kammala aiki." Dariya ta saki tana jin duk wani tsoro da fargaba sun kau daga ranta, wannan kuɗin ya wanke mata su tas.
***** *****
Tsaye suke su bakwai a cikin wani guri mai tsananin duhu, gabansu ga wani ƙaton rami da wuta take ci a cikinsa, babu komai a jikinsu sai wani jan ƙyalle da ke ɗaure a ƙugunsu, sanduna ne a hannunsu sun riƙe gam suna kewayawa da su a cikin wannan ramin, wani irin abu yana zagwanyewa daga jikin sandunan yana ƙara hauhawar balbalin wutar, a hankali a hankali sanda ɗaya ta fara ƙamewa, abin da yake zuba daga cikinta ya fara raguwa. Gigitacciyar ƙara mai haɗe da tsawa ce ta gilma a cikin kunnuwansu, lokaci ɗaya tartsatsi ya wulga a saman kawunansu kamar walƙiya. Cikin wata irin burkitacciyar murya aka fara magana.
"A cikin rayukan da kuka salwantar akwai guda ɗaya da yake tare da goɗiyar da Ƙanzula ta daɗe ta nema a halin yanzu! Tana ɓata mana wannan aikin ba tare da ita kanta ta sani ba! Shi ya sa muke buƙatar ta a wannan tsibirin da gaggawa amma kun gagara kawo ta! Akwai sirrika masu tarin yawa a tattare da ita! Ayyukanmu da dama ba za su yiyu ba matukar tana rayuwa a wani gurin ba a cikinmu ba, sannan kuma za ta yi ta lalata mana shiri a duk lokacin da aka yi katari irin wannan! Don haka a hanzarta kawo ta cikin gaggawa kafin fushin Ƙanzula ya sauka a kanku!" Kamar busawar iska haka wani abu ya wuce shuuu kafin ƙarar ɗazu ta ƙara ƙwallara, sautin ya ɗauke gabaɗaya, sandunan hannunsu suka faɗa wannan wutar da take ta ci kamar ana tittile mata fetur. Sautin muryoyin mutanen da suka sadaukar ne suka fara yi musu amsa kuwwa a cikin kansu, kowanne yana kuka tare da kiran sunan wanda ya bayar da shi cikin tsananin azaba.
*#Zeey Kumurya*
*#****