Episode 3&4
by @deeyamerh10
✨✨MY BEST FRIEND'S DAD ✨✨
By Khadijah Umar Muhammad
(DEEYAMERH)
07070647236
Page 3&4
Kan Bike din yahau ya sake nausawa cikin jejin fiya da gudun da yayi dazu tunda ya dau hanya yake tunani yadda zai samar mata kayan da za ta sa Bai san girman jikinta ba, amma ya yi ƙoƙarin tuna irin yanayin da ta kasance kafin ya bar ta.
Ya tsaya a wani shago da ke sayar da kayan mata, ya sauka daga kan Bike ɗin.
“Do you have something simple and comfortable for a lady?” ya tambaya mai shagon ta fara nuna masa kaya iri-iri.
“Wannan fa?” yafada yana kallon kayan sai kuma ya girgiza mata kai
“Something simple. Maybe a long dress… and a hijab.”
Bayan ya zaɓi wasu kayan, ya biya kuɗin, ya ɗauki jakar sannan ya koma kan Bike ɗinsa.
a zuciyar yake tambaya kansa wai meyasa yake mata duk wannan abubuwan?ko da yake tana Bukatar taimako sannan yarinya ce.
kunna Bike ɗin ya juya, yana komawa inda ya bar ta dan zata iya farkawa ko wani lokaci.
Bayan wasu mintuna ya dawo inda ya bar ta. Ya kashe injin ɗin Bike ɗin sannan ya sauka, jakar kayan tana hannunsa ya shiga cikin daki
Yana shiga cikin ɗakin, ya same ta zaune a gefen gadon a zaune ta jingina kanta da kafafunta sosai ta fada duniyar tunanin dan har shigowarsa bata jiba.
"Have this" taji saukar muryarsa kanta da kallo take binshi domin har yanzu bai cire handkerchief da ke fuskarshi ba.
hannuwanta biyu tasa ta karbi jakar kafin ya mai da idonta cikin cikin jakar Doguwar riga ce mai sauƙi sawa tare da hijabi.
“Thank you…” ta faɗa a hankali.
Ya gyada kai kawai ya juya yadda zai bata samar sakewa tasa kayan.
ƙoƙarin miƙewa domin tasamu ta canja kayan amma zafin raunin da yake kafata yasa ta koma cikin sauri ta zauna.
kalle ta gefen ido kafin yace mata “Okay. Kar ki tilasta kanki.” bari na fita yana fita ya rufo mata kofar
Bayan ɗan lokaci ta fito cikin sabon kayan ta kalle kanta cikin shigar wasu hawaye Masu zafi suka sauko mata hannu tasa ta share hawayan kafin tasa hajjiy ta rabba sallah dan bata tunanin shi yana Sallah.
Kinda ita idar zaune tayi garin tana so tayi masa magana ya mai da ita gida Amma batan taya zata fada masa ba.
Tunanin ya ne ya yatsaya cak jin yana tambayar da abinda take kissimawa cikin ranta.
“Where do you live?”
Cikin sanyi tace masa" Gwarinpa"
Zaki iya tashi muje na kai ki, i know, your parent, are worried for not knowing Your whereabouts.
Gyada masa kanta kawai tayi tana me kewa a hankali cikin daurayi tace"Please Who are you"
"Damian" yana fada yajuya ya ficewarsa.
Tana dingisa kafa ta bishi har inda yake kan Bike din yana jiranta tsaya wa tayi tana kallonsa dan bata san ta yadda za'ayi ta hau ba,ganin tana bata masa lokci kawai yasa hannun kamar ya dauki yar tsana ya durata kafin ya gyara da kyau ta tashi Bike din.
Cikin sauri tasa hannunta wajan rike shi ɗan jita kamar zata fado,lura da hakan yasa kawai ya cire jerker din jikinsa ya zagayo da ita kamar ya goyata ya daure rigar a cikinsa kafin ya ja bakin din cikin 360 idanu ta runstsu saboda tsoron.
Sosai yake gudu har taji alamun sun fita daga cikin bakin dajin nan kafin ya hau titin dotar domin kai ta inda tace.
Tunda suka fara tabiya bai ce da ita uffan ba har sai da yashigo cikin unguwar Gwarinpa cikin dake wa yace "Get nawa zan ajiyeke"?
Cikin sauri ta bude idonta jin da gaske sun zo cikin zakuwa tace Get 5 family House din SHATTIMA".
Lokacin da yazo sai dai Get din a lokacin mazan cikin family sun fito zasu masallaci wacce suka gani a gabansj ana ƙoƙarin saukata a machine fuskar ta duk a kumbure yasa yaciin sauri sukayo gunta tare ta murnar ganin wacce aka dade ana nema wajan 2week kenna.
Sosai itama take murnar ganinsu kafin wani kuka ya kwace mata, da sauri tayo gunsu kamar yadda sukai mata sai dai ita ba damar dauri saboda cikin da yake hukunta.
Tana gama dauka ko kallansu bai tsaya yiba bare Amsa tambayar da suke mata nacewa waye shi din?juyawa tayi da zimmar yi musu bayanin Ko waye wayam ba kowa sai hangoshiyi ya kusa ficewa a bakin Get din.
Part din su kai da ita Inda labari ya isarwa ko wani part nan fa gidan ya kace da murnar ganinta,duk wanda yazo tambaya biyu zuwa uku shine wuye suka dauke ta?kuma ina suka kai?waye wanda ya dawo da ita? dan su ji labarin wanda ya kawota.
Ta rasa Amsar da zata bayar shiysa kawai ta rungume Ummme kawai ta fashe da kuka Domin tana fadar wanda yayi mata wanna dan yan aiki tabbas wani sabon rikice ne zai tashi a gidan.
Ganin yadda kowa yazo da tambayar da za'ai mata sa Iyaye mata suka ce abarta ta huta kafin Baffa yazo shi zata bashi Amsa idan yaso duk dai suji.
Haka kuwa akayi inda Ummee wacce take a matsayin mahaifiya a gareta tayi part dinta da ita,da kanta tai mata wanka da ruwan zafi mai zafin gaske,ta hadu mata Tea mai kauri ta bata maganin tasha ta kaita dakinta ta kwanta.
Da gajiya a tare da ita shiyasa tana kwanciya bacci ya dauketa ne cike da mafarkinta Amma yanzu tunda tana gidansu kuma dakinta dole tayi baccin gajiya.
Sai dafda magariba tashi haka Ummee ta sake bata Tea tasha kafin ta tai maka mata tayi alwala rama sallar da ake Binta,a gurin da tai sallah anna tahau tunanin Damian ko ya koma cikin wanna dajin? ko wani gurin ya tafi bata sani ba?haka kawai taji takasa dai na tunaninsa Muryar Ummee taji yo tana fadin" HOORAIN idan kin gama kizo su Baffa suna jiranki".
Cikin yanayi na karfa kanta kwarin gwiwa Domin ta tayi alkawari bata furta komai domin zata jira idan lokacin furta War yayi to tabbas zata furta.
SHATTIMA FAMILY ESTATE...
Gida ne Babba wanda yake dauke da Part ,It was more like a private family estate, wanda aka gina shi tun shekaru da suka wuce domin ya kasance gida ɗaya da dukkan ’yan gidan za su iya rayuwa a cikinsa.
Get ne mai girman gaske kallon babban hanyar da take shinfide da kwalta.tana da security house a gefe biyu. Bayan an shiga gate ɗin, doguwar hanya ce mai faɗi wadda take kaiwa zuwa babban ginin gidan.
Gidan yana da manyan parts guda biyar, kuma kowanne part na ɗaya daga cikin ’yan’uwa maza biyar ne.
A tsakiyar gidan kuwa akwai Main Family House—babban gini mai hawa biyu wanda shi ne zuciyar gidan. A nan ne babban parlour, dining hall, family sitting room, babban kitchen, guest rooms da kuma babban courtyard suke.
A gefen dama akwai First Wing, inda babban ɗan gidan yake zaune tare da matarsa da ’ya’yansa.
A gefen hagu kuma akwai Second Wing, wanda yake da nasa bedrooms, family lounge da kuma private sitting area.
Bayan su kuma akwai Third Wing da Fourth Wing, kowannensu yana da nasa rooms da wuraren zama domin iyalan ’yan’uwan biyu su samu privacy.
Sai a ƙarshen estate ɗin akwai Fifth Wing, wanda shi ma yake da girman da zai iya ɗaukar cikakkiyar family.
Duk waɗannan parts ɗin ba a raba su da katanga mai nisa ba. An haɗa su da dogayen corridors da covered walkways, wanda yake sa duk gidan ya kasance kamar one big family home, amma kowane iyali yana da nasa private space.
A tsakiyar parts ɗin biyar kuwa akwai wani babban family courtyard, wanda shi ne wurin da ake taruwa idan akwai wani babban abu.
Akwai garden mai kyau, swimming pool, playground na yara, da parking area mai faɗi wanda zai iya ɗaukar motoci da yawa.
Saboda haka, duk da cewa mutane da yawa ne suke zaune a gidan, babu wanda yake jin gidan ya cika.
Five brothers. Five wives. Their children. One huge family house.
Cikin dingishi kafa ta karasa kusa da kafar Ummee ta zauna domin ba karamin mamakin tayi yadda suka cika Parlon ga kallo da suke binta da shi,cikin Muryar da ta jigata da har yanzu bata washe ba daga dushahewar datayi"Baffa Barka da dare"haka ta bi duk yan párlon da gaisuwa.
Amsawa sukai dukan su kafin cikin Gyaran Murya wanda aka kira da Baffa yayi kafin ya yi shiru na wasu seconds, kamar yana neman kalmomin da suka dace wajan furtawa.
“Mun gode wa Allah da Ya dawo mana dake cikin Amince da addu'ar Allah ya dawo ma dake da ranki to Alhmdullah Allah ya amsa Addu'ar mu duk da irin raunukan da suke tare dake Hakan zai tabbatar da bakaramin wahala kika sha ba".
Hoorain ya kirata sunta cikin sanyin murya" ki yi haƙuri abin da ya faru da ke ya isa ya razana kowa,Amma Alhamdulillah, yanzu hankalin kowa zai kwanata sai addu'ar Allah ya kara karewa.
ya kalli fuskarta na ɗan lokaci, sannan ya ce"Ba za mu matsa miki ba domin kina bukatar hutu Amma akwai wasu abubuwan da muke son sani domin mu fahimci abin da ya faru shin wani abu suke nema a wajan mu ko kawai batagari ne da suka saba dauke ya'yan mutane suna garkuwa da su".
Hoorain ta yi shiru tana kallon ƙasa domin wanna tambayoyin batasan ta ina zata fara.
Baffa ne ya katse tunanin da take"Kin san mutanen da suka daukeki?
Kai ta girgiza a hankali ta girgiza kafin tace"Bansan suba Baffa domin lokacin da suka dauke Ni muna jiran Driver yazo ya dauke mu sai naga me Ice cream wajan naje na siyo ne sukuma suka faka mota suka tura Ni ciki.
"Kin taɓa ganin ɗaya daga cikinsu a baya?.Baffa ya sake jefu mata tambaya.
Kai ta girgiza alamun A'a
Baffa ya ɗan ja numfashi Yana fesarwa domin abun da daure kai ace duk yaran da suke wajen basu dau kowa ba sai ita ga dukkan alamu sasu kai kenan?
Shiru Parlon ya dauke in banda kakar Ac ba abinda yake tashi a cikinsa.
Daya daga cikin matar da suke zaune ta kawar da shirun ta hanyar tambayar Hoorain din cikin Izgilance"To kuma da suka daukeki babu wani abu da sukai miki ila wanna raunikan da suke jikin ki Nifa Sai nake ganin kamar sun mata fyade ko mamey baki kula da yadda tafiyarta ta canja ba?.
runtse ido Hoorain tayi domin wanna kalmar ta dake ta ba kadan ba.
Wacce ka kira da Mamey tace"Nima dai tunda take fitowa nake kallonta domin ba yadda za'ai ace 2week tana gurinsu Amma ace ba wani abu da sukai mata gaskiya a bincika gudun kada tadauko mana wata cutar muna zamamu azo a shafawa 'ya'yan mu".
Wacce take kusa da Ummee tai magana cikin bacin rai "Haba dan Allah kuna manya kuma irin wanna maganar eh yarinya da kananun shikaru ace tana wajan mutanan da ba'asan waye ba anzo ana su aji ta bakin ta amma kin zauna kuna jifanta da bakaken maganganu yanzu idan a cikin yaranku akaiwa haka zakuji dadi".
"A'a kull wallahi bazamu ga wannan masifar a cikin zuri'ata ba itama da hakan ya faru da ita wayasani ko rashin kunya tayi musu da har suka dauke ta".
Tsawa wanda yake kusa da Baffa ya yi, kafin ya ɗaga hannunsa yana nuna su da yatsansa ɗaya bayan ɗaya.
Cikin fushi ya fara magana"kaf din mu ba wanda wuce wannan ƙaddarar da ta faɗa wa Hoorain, Kuma wallahi ba wayanku ba ne ya sa Allah ya kare mu ku 'ya'yan naku, Don haka, ko wacce ta kama kanta tun ban sabar muka ba wanna ai hauka ne su 'ya'yan naku na gold ne"?eh nace na golde da su Allah bazai jarabce su ba".
Da sauri wanda yake kusa dashi yace"dan Allah Baban safna kayi hakuri fushi bai kamata a wannan yanayin ba dan Allah kayi shiru".
Bai sake magana kawai ya girgiza kansa yana mai kallon Baffa domin duk abinda suke yana jinsu.
Maganar tasa ta sa ɗakin ya kara daular shiru fiye da dazu domin wanda aka kira da Baban Safna ba karamin mafada ci bane shiya sukai shiru kuma da dukkan alamu da kawai matarsa a cikin wanna maganar shiysa ya fusata sosai.
Baffa ya ɗan sunkuyar da kansa kafin cikin bada umarni yace "sa'adatu dake da Hafsat ku dauki Hoorain ka kaita asibity ayi duk wasu binkice da yakamata ina jiran Result din".
Daga haka ya meke cikin tafiyar da tazame masa kamar ta sarauta ya bar Parlon,haka mazan suka mara masa baya.
Nan fa hayaniya da karade cikin Parlon domin Mamey sosai take jefan Hoorain da bakaken maganganu har tana rantsuwar ba wani mahaluki da zai Aura wa dan ta wanna raguwar yan kidnapping din dan wllh baza'a kaka bamasa masifa ba ta inda take shiga ba tanan take fita ba haka ta fita tana dababi kala kala.
Da kallon Ummee ta bita idanuwanta na tauro da hawaye domin Allah ya hadata da facalolu yan masifa.
Wacce aka kira da Sa'adatu ce ta dafa kafadarta tace"dan Allah kada kibari su zubu, domin zubuwar su tamkar gazawa ce kada ki nuna rauninki tun a yanzu dan Allah"ta karshe tana mai jinjina mata kai.
Murmushi Umme tayi kafin cikin karfin hali tace" Ammey Bansan me na tsare musu ba mijin kowa da ban amma komai nawa yana idonsu sunki bari na sake sunan ina cikin gidan mijina" kawai kuka ya sarke mata.
Sosai Ammey ta rungumeta tana bata hakuri tare da nuna mata me hakuri shike da riba har yafasa dutse yasha da wanna nasihar Umme ta share hawayenta tayi daki ta dauki mafi domin kai Hoorain asibity kamar yadda Baffa ya bada umarni.
Haka suka sata a gaba sukai wajan da driver yake jiransu,suna zuwa suka shiga ciki aka bude masa Get ya cina hancin motar zuwa kwanta.
Duk abinda sukeyi Mamey da Mama suna Kallonsu ta window dakin Mamey kafin mama ta doka wani uban tsaki da fadin"munafukai shiyasa kullum basa cigaba jiya iyau idan banda an rai na mana hankali wai ace kidnapping din ta kawai ko kuma ta tafi yawan iskancinta dan daga ganin idon Hoorain ba sai nace maka ta saba da maza ba".
Hmmm ki ba kawai wallahi har cikin raina ban so yarinyar nan na tsani na bude ido na ganta a cikin gidan yarinya sai kyan tsiya"mtsss haka tajan tsaki tana zama cikin kujerun parlon.
Shiyasa ai nazo na baki shawara wallahi kada ki sake kiyi gangancin yadda a Aurawa Kabeer ita dan wallahi yar kallo zaki koma kamar yadda ubanta ya koma sulo'biyo saboda anga yanzu yake tashan kudi shiyasa za'a ƙaƙaba masa ita inda Allah ya tai ma kike baya kasar da wallahi sai abinda hali yayi"ta fada tana kafa uban tagume.
Girgiza kafa kawai Mamey takeyi kafin tace"Ai wallahi muna na dake ba wanda ya isa yayiwa Kabeer Auran Dole dan ko ita Hajjiyar wallahi sai dai tayi hakuri Amma ba wanda ya isa yayi mun iko da 'da' danni Nasha wahalar haihuwarsa baza'azo ayi mun taka haye ba, kabar ni da su dai dai nake da kugun kowa har Baffa wallahi da suka mai dashi tamkar ubansu.
Mekewa Mama tayi kafin tace"to Ni dai bari na wuhuce bangare na kafin su dawo muji cikin sati nawa ne, Ni dai na fada Miki idan kinji kanki idan kuma kin tsaya sanya to ruwanki Kinga tafiyata".tasa kai tai ficewar ta kafin ta nufi bangaranta tana shiga ta tarar da Yaran mata suna zaune ko wacce tana danna waya dariya ta sheke da ita har da tafawa kafin tace "mahaikaciya haka zanta zugaki ana ganin bakinki cikin wanna famliy kafin na kara karka tar miki da hankalinki wajan son hada aure tsakanin Kabeer da Noor dan wllh bazansa ido naga wanna dukiya ba kuma ace bazan muraba ina san bazata sabo ba".
Kallonta yaran suke kafin daya tace"wllh shiya mama kike burgeni komai kinsani wallahi bikiji murnar da nayi ba da Hoorain ta bata domin nasan dama ce na samu wajan karkatu da hankalin yaya Kabeer kai na ko Nasreen"ta fada tana kallon yar uwar Tata.
Ah"to ke da me zaki jira ai bude masa wuta yadda baya ganinta kafin ya dawo daga Spain sai dai suji tashi zance kawai" cewar Nasreen tana Kallonta.
"Yawwa yan albarka shiyasa nake sanku,gashi dai ku biyu Allah yabani, Amma kuma kun zame mun tamkar maza Goma,nidai fatana duk wani karatu da nake biya muku yazama kuna dauka, domin kudi shine madafar jin dadi, sai kana da shi kake iko to su nake ke Noor ki mai da hankali gun Kabeer sosai, yadda zai mutu akanki cikin sauki zamuji dadin tatsar kudin a hannunsa kamar banza kinji ko"?.
Haka tasa yaran a gaba tana yimusu huduba kala kala har akai kiran azahar duk suka watse su yaran sukai dakinsue itama tayi nada daki tare da cin alwashi kala kala akan Mamey da Kabeer.