RU'UYAA (The dreams we never lived)
...Ya xanyi ... 🖊️
by @autum17
Tsayawa nayi zuciyata na duka da ƙarfi, ina jin labarai daban daban yanda aka sace yan mata ana yi musu fasadi kala kala? toh ko nima layi ya biyo ta kaina?
jinayi tsoro ya shige ni musamman dana ga an buɗe motar su uku suka fito, duk da duhu ya sauko hakan bai hanani gane suba,gayen nan ne dana tura ma cokali ɗaya na barkono a baki tareda ƙawayenshi...
juyawa nayi zan gudu yayi saurin cafko hannu na,ihu na fasa ina shilla ƙafafu dan ɗauke ni yayi kamar yar tsana ƙawayenshi na dariya suna tafi da shewa '' tsuntsu daga sama gasashshe!" ɗayan su ya faɗa
hawaye suka wanke fuska ta zuciya ta na bugu da ƙarfi har cikin kunnuwa na...'' bani kika sakawa barkono abaki ba,yau zan rama ne then babu wanda zai sake kallon ki shiga cikin mutane sai ya mike wahala!" yayi maganar yana ƙoƙarin turani cikin motar su
kuka nake da iya ƙarfi na dan ba ƙaramin matse ni yayi ba,
'' Hakane guy, kayi mata abinda bazata sake iya fita cikin mutane ba!" inji abokinshi dake wasar hauru kamar anyi watsin masara kan titi
'' Bara in buɗe maka ƙofa!" ɗayan dake tsaye kusa kusa yayi maganar shima yana buɗe mashi ƙofa
'' kai daya kamata ka buɗe mashi ƙafafunta!" wanda yayi maganar da farko ya faɗa yana sheƙewa da dariya
'' ataimake Ni... jama'a a taimaka... wayyo Allah na...na shiga uku...'' ganin ina ihu zan iya taro musu mutane yasa yayi saurin toshen min baki aɗan zafafe ya kalli ƙawayen nashi yace '' wai dalla kun barni da ita,ni kaɗai zan sha gara ne?" '' haka fa!" aboki 1 ya faɗa tareda matso wa ya kama ƙafafuna sai zillewa nake zuciya ta a ƙuntace,a kace a wannan zamani mace takai mutuncin ta gidan miji ya ta ƙare bare ace ta tafi fanƙo...? nasan idan wani abu ya same ni Mama zatayi kuka... sannan ta ɗaura ma kanta alhakin komai zata shiga damuwa sosai
ƙara ƙarfin kuka na nayi duk da ya rufe min baki...samu sukayi suka turani cikin motar tare, gayen da nasa ma barkono a baki ya shigo shima..wani irin faɗuwa gabana ya shiga yi hawaye suka dena fita tashin hankali ya ziyarci ilahirin gangar jikina ganin yana zare belt da sauri sauri finciko ni yayi na gantsara masa cizo a hannu,yarfe hannun sa yayi kafin ya yarfa min mari '' shegiya mai baƙar zuciya!" ya zage ni a zafafe ya ƙara finciko hijabi na,riƙe hijabin nayi ina rushewa da sabon kuka
daga sama aka buɗe ƙofar juyawa yayi don ganin waye wani irin naushi ya sauka a fuskar shi,kafin ya warke aka wani finciko shi daga motar, ana cigaba da naushin shi,maƙewa nayi a ƙarshen mota jiki na na tsuma tsoro na ya ninku dan gani nake bayan su sai ni
a hankali iska ya dinga ɗaukar ƙamshin turaren shi zuwa hancina, Ibrahim ne ya leƙo cikin motar idon mu ya haɗu...'' Oh...kitten!" ya furta da mamaki a fuskar shi
fashewa na sake yi da kuka fiye da wanda nayi a baya, sassanyan murmushin shi ya sakar min ya miƙo min hannun shi,a tsorace na kama ya taimaka min na fito daga motar
'' Shhh... it's okay!" ya furta da sanyayyar murya hakan ya ƙara ma kuka na sauti... daga can gefe naga wannan gayen dake sa fes mas yana ta jibgar gayen dana zuba ma barkono a baki... wani irin sanyi naji araina ina furta Alhamdulillah dabadan Allah ya kawo suba da shike nan
'' shiga mota in sauke ki gida!" maganar shi ta katse tunani na da sauri na zare hannu na daga nashi ina girgiza kai alamar a'a..dan sun taimake ni yanzu baya nufin zan sake faɗawa motar su,nasan kosu wane irin mutane ne?shima baya taɓa rutsani a ɗaki ba?
gayen nan mai facemask ya ƙaraso inda muke,yana ganin nice ya min kallon uku saura kwata ya juya ya shige motar su,oho ko a slippers ɗina
share fuska ta nayi hankalina ya koma gida me zan faɗa ma Mama? idan fa tashiga damuwa saboda wannan aikin da narasa ko tace zata fara zuwa neman aiki? a'a! Dole inyi wani abu
tafiya nake da sauri sauri hankali na a ɗauke ban masan cewa ya biyoni ba '' su waye su?" muryar shi ta sauka a kunne na har saida na razana..sai kuma na tsaya juyowa nayi ina kallon shi, murmushi yayi min, shi bai gajiya da murmushi? Naji haushin sa ya kamani... '' ban san suba! ashe baka tafi ba? '' na tambaya bayan na amsa tashi tambayar '' raka ki zanyi!so ashe sunan ki Abeedah?"...ƙanƙantar da idona nayi '' oh..haka fa...na ɗauka Khadeejah ne!" ya miƙa hannu zai shafa fuskata,share hannunsa gefe nayi tare da ɓalla mashi harara..na juya na cigaba da tafiya
'' ya akai kuka..'' katseni yayi da faɗin '' motar muce ta samu matsala daga wurin shine na sauko zan amsa waya naji ihu...so we came to your rescue!" na fahimci abinda ya faɗa daidai inda yasako turanci notikan kaina suka kwance na tsare sa da ido alamun ban gane ba '' nifa bana so anamin magana ana haɗawa da turanci!" nayi maganar da iya gaskiya ta,shafa ƙeyarshi yayi murmushin shi na ƙara faɗaɗa '' sorry..my bad!" guntun tsuki naja ƙasa ƙasa yanda bazaiji ba..
'' Na gode zaka iya tafiya '' na furta daga baya ina cigaba da tafiya jin an fara kiraye kirayen isha'i amma bai tafi ba ya cigaba da bibiya ta
gyaran murya yayi yana faɗin '' zamu iya zama abokai '' daidai mun kawo wata kwana me duhu, ban amsa shiba na cigaba da tafiya caraf! ya riƙe hannu na na juyo zan sauke mashi kwandon rashin M na gacewa kusancin mu yayi yawa,duk da tsawona na koma yar ƙarama gabanshi,dai dai nan aka yado mu da Torchlight... '' ABEEDATU..??" a ɗan firgice na juyo,na haɗe fuska ganin maman su nusaiba munafukar anguwar mu, ta wani riƙe baki ido waje irin taga wani mugun abu..nasan sallallami take a ranta
kallon maman su nusaiba Ibrahim yake ba alamun damuwa a fuskar shi kuma har yanzu riƙe yake da hannu '' Me ya faru?" na tambaya ina waro mata ruwan tokan idona tsoro ya bayyana a fuskar ta, na ƙwace hannu daga riƙon Ibrahim na matsa kusa da ita '' me kika gani?" na tambaya ina juya idona kamar ba mutum, girgiza kai tayi tana ƙifta ido tace '' b..bb..babu komai!" gyaɗa kaina nayi cikin ƙasa da murya nace '' Wallahi tallahi idan kika kuskura maganar nan ta fito musamman idan Mama taji...hmm'' kallon cikinta nayi duk da bansani ba ko tana da ciki ko bata dashi nace '' wannan abun bazaizo duniya ba zan hallaka shi tun cikin ciki!" jkinta ne ya fara tsuma ta dafe cikinta '' don Allah kiyi haƙuri na maki alƙawarin babu wanda zan faɗa mawa!" tayi maganar da magiya na jinjina kaina tare da nuna mata hanya kamar wata uwarta '' oya bita nan!" ta fara tafiya da sauri sauri har tana cin tuntuɓe
ajiyar zuciya na sauke bayan tafiyarta Atleast nayi maganin ta idan ba haka ba zama a unguwar nan tsaf zai gagare mu dan ba abinda ta gani kaɗai zata faɗa ba harda wanda bata gani ba
juyowa nayi wurin wannan Ibrahim ɗin ina mashi faɗa cikin duhu duk da ba wani ganin fuskar shi nake sosai ba '' woah!yanzu fa muka taimake ki!" yayi maganar yana matso ni
'' na roƙe kune? in sunbaci ƙafafunku dan kun taimake Ni?'' da mamaki a fuskar sa ya kalleni sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace '' shike nan amma zamu iya zama..''
'' ba zamu iya ba!" na katse shi kafin ya iyar na ɗaura da faɗin '' ban san dalilin ka nason ƙulla alaƙa dani ba,ina roƙon ka daka rabu dani ,saboda kai saura kaɗan in zama abin faɗa a unguwar nan ka rabu dani dan Allah!" Ya kalli hannayena gira a ɗage kafin ya dawo da idonshi a fuska ta
..matsowa yayi kusa dani sosai numfashin sa na dukar fuska ta '' I don't give up easily kitten! Sai mun sake haɗuwa!"
Daga nan ya juya yayi tafiyar shi, shiya San abinda yake nufi Allah yasa kada mu sake haɗuwa duk da wani sashe na zuciya ta yaƙi yace Ameen ga wannan addu'a...
ina shiga gida duk wani abun daya faru ranar ya dinga dawo min ji nayi hawaye sun fara zirara daga ido na, jin sheshsheƙar kuka na shirin kama Ni yasa na ɓoye bayan ƙofar mu ta kara ina goge hawaye '' waye nan? Abeedah?" Mama da alamu yanzu tagama salla dan saye take da hijab ta tambaya hannunta riƙe da tasbih
da sauri na shigo gidan na ajiye hijabi na a gaggauce na ɗauki buta kamar mejin kashi na faɗa toilet na toshe bakina da hannu na na duƙe ina kuka inajin Mama tana faɗin '' Allah ya shirye ki Abeedah '' dafe kaina nayi ya zanyi yanzu? na daɗe a bayen ina fitowa na ɗibi ruwa bucket na sake shigewa cikin duhun bayen wanka nake naji wani abu me ɗumi na bin ƙafafuna... lokacin haila tane
dogon numfashi naja sannan na wanke ƙafafuna na iyarda wankan na fito samun mama nayi tsaye a tsakar gida tana jirana fuskar ta ɗauke da alamun tambaya,daidai nan aka dawo da nepa da ƙarfi
tsakar gidan mu kamar rana Mama ta kalle ni da kyau da kyau,ƙasa nayi da kaina nakasa kallon ta '' wani abu ya faru ne Abeedah?" ta tambaya tana ɗaura hannun ta a kafaɗa ta ɗayan kuma ta ɗago haɓa ta tana kallon shatin marin dake kumatuna, Asma'u ta fito ta tsaya daga bakin ƙofa '' yimin magana Abeeda" mama ta furta muryar ta cike da damuwa fashewa nayi da kuka har da jan majina
Hankalin Mama da Asma'u ya tashi matsowa tayi itama tana tambaya ta meya faru, Hawayen da na gani a fuskokinsu yasa na shanye kuka na'' wani yayi miki wani abu ne Abeedah? meyasa ki kayi wanka daga shigowa?waya taɓa ki? ina ganin shatin mari a fuskar ki ''Mama ta tambaya a tsorace tana ƙara dubani gaba da baya...ganin jini a rigar jikina yasa ta ja baya hawaye na wanke fuskar ta haka ma Asma'u
'' A..aabeedah?" ta kira a rarrabe,da farko bansan mezan faɗa ba, dalilin wanka na da kuka na, ganin hankalin su ya tashi nace cikin Muryar kuka '' jini nane yazo ina tsaka da aiki shine mutane suke ta min dariya,na kunya ta Mama!!" bayani na yasa Mama sauke wani irin nannauyan ajiyar zuciya a bayyane ta miƙe tana ƙara kallo na sai kuma tace '' kin tabbata?" gyaɗa mata kai nayi amma kamar bata yarda ba'' muje in duba!"
zaro ido Asma'u tayi nima haka murya na rawa Asma'u tace '' Mama me zaki duba?" kallon da Mama ta watsa mata yasa tayi shiru..ban faɗa muku ba ko? haka Mama take idan har bata yarda ba saita duba ba tun yau ba haka take mana tun muna yara..na ɗauka yanzu tunda mun girma zata dena ashe ba haka bane...wasu abubuwan basa canja wa
a kunyace na shiga ɗakin itama ta shigo,kasa motsi nayi duk kunya ta kamani '' Mama wallahi ba abinda kike tunani bane ''
'' me nake tunani?" ta tambaya tana min wani kallo ƙasa nayi da kaina kafin na kwanta ɗin,ɗage rigar tayi nikam na runtse idona..wani irin azababbiyar kunya na kamani
dumƙe zanen gadon nayi a hannu na ina cije baki can naji tace '' shike nan!" miƙewa nayi zaune na kasa kallon ta '' ba wai nayi hakan bane dan in kunya taki ba,ko don Ban yarda dake ba,a'a ni uwace dole in tabbatar da lafiya da ingancin rayuwar ya'yana Abeeda...idan wani abu ya same ku bansan ya zanyi da kaina ba ku riƙe min Mutuncin kanku ina roƙon ku!" ta faɗa tana kallona da kuma Asma'u dake tsaye bakin ƙofa
dukan mu kawunan mu ƙasa muka amsa da '' insha Allah !'' fita tayi zuwa tsakar gida tana tattara kayan dake nan takai su kitchen,
wata doguwar rigar atampa da ta ƙoƙe na ɗauko nasa sannan na duba cikin kayan mu wani pad da aka taɓa bamu a makaranta na ɗauka tareda baƙin pant nasa na haye gado na kwanta...da ƙarfe biyun dare na farka nakasa komawa..sai tunani nake daban daban mezan cewa Mama? ya zamuyi da abinci daya kusa ƙarewa? abubuwa da yawa suka shamin kai
da safe bayan sallar asuba nida kaina nayi share share na haɗa mana abun kari, Asma'u ta shirya zuwa makaranta amma ni? '' yau bazaki tafi makarantar ba?" Mama ta tambaya tana kallona '' ban jin daɗi Mama!" na bata amsar a gajarce '' Allah ya sawaƙe!" Asma'u ta faɗa na amsa da Ameen,bayan ta gama ta ɗauki jakarta da hijabi ta tafi makaranta
wanke wanke nayi sannan na koma ɗaki,ji nayi fuska ta na ƙaiƙayi na sosa.. can naji ta ƙara fara ƙaiƙayi fiye da ɗazu na dinga sosawa kafin nayi amfani da ruwan gishiri na wanke fuska ta '' Abeeda ko zakiyiwa manager'n wurin aikin ku magana ya baki wani abu daga sallary'n ki kinga shima garin kwakin ya kusa ƙarewa!" Mama ta faɗa daga kitchen,dum! naji gabana ya faɗi murya na rawa nace '' ai basuyin haka Mama..jiya na tambaya'' nayi ƙaryar wani irin nauyi na sauka cikin zuciya ta kamar an ɗaura dutse
'' Allah ya kyauta '' na amsa da 'Ameen ' tareda faɗawa saman gado inaji duniyar tayi min zafi ya zanyi ne?
bada daɗewa ba Asma'u ta dawo kasancewar yau juma'a,tana murmushi ta shigo gidan '' Mama an taso!" ta faɗa tare da ɗaukar buta ta shiga toilet,'' sannu da zuwa'' Mama ta bata amsa daga inda take zaune nikam kwance nake saman gado na juya baya duk da ba bacci nake ba ga ƙaiƙayin fuska daya shamin kai
shigowa tayi ta zauna bayan ta cire hijab tana murmushi tace '' Mama akwai wani spelling bee competition da za'ayi a makarantar mu kuma an zaɓe Ni!" Mama tayi dariya tace '' haba dai?" Itama Asma'u tana dariya ta bata amsa da '' Eh'' sannan ta ɗaura da faɗin '' akwai kyauta kuma,wanda yayi na ɗaya za'a bashi miliyan ɗaya da gida irin na yan gayu,na biyu dubu ɗari takwas da gida shima amma baikai na ɗaya ba,na uku da na huɗu suma. haka...mama wallahi duk gidan na huɗu shine mara kyau...nidai ban sonshi... kuma dubu ɗari biyu kawai za'a bashi'' juyowa nayi ina kallon ta da murmushi nace '' nikam da zan shiga gidan na huɗu nake so...'' katseni tayi da faɗin '' yo ke ana maganar masu ƙwaƙwalwa ina ke ina sako baki Tuwo?''
'' ba'a son wulaƙanci!" Mama dake sauraren mu ta faɗa tana ranƙwashin Asma'u '' Ouch!" Ta shafa wurin tare da turo baki
juyar da kaina nayi ina kallon gadon mu hawaye suka ciko idona maganar ta tayi min zafi amma ya na iya? da gaskiyar ta...kuma ma wane abune na iya? meye amfani na?...ciwo zuciya ta tafara na lumshe ido na hakan yaba hawayen dake maƙale damar silalowa ban san meya faru ba amma dai nasan bacci ya kwashe ni..da ƙarfe biyar na farka kitchen nashiga na jiƙo gari ba suga
nazo na zauna ƙarƙashin baranda inda su Mama Asma'u kwance a ƙafarta tana shafa gashinta,suna magana akan abinda ban sani ba
kallon su nake su biyun kamar su sak kamar an tsaga kara an ajiye kawai Mama tafi Asma'u tsufa ne, itama gashinta har ya wuce wuyanta amma ƙila saboda tsufa bai kai yawan na Asma'u ba sannan duk furfura ta cikashi
'' ya dai da kallo? kinga yan mata kyawawa biyu ko?" Asma'u tayi maganar tana ɗadɗage min gira da wani murmushi maƙale a fuskar ta
ji nayi na kasa shan garin sai juya shi nake tashi zaune tayi tana kallon Mama tace '' wai ita wannan dawa take kama? kodai da baba take kama? Amma baba yana da kyau kuma kema Mama kina da kyau amma Abeeda... hideous!" sanin bana jin turanci yasa Asma'u ƙarasa maganar da turanci amma daga yanda take kallo na zan iya cewa na fahimci abinda take nufi '' kedai Asma'u Allah ya shirye ki.. Tuwo tana da kyau wallahi kawai dai itace bata ganin hakan!" Mama ta faɗa tana tashi daga wurin ta ɗauki buta tashige baye
murmushi wanda ya ɓoye asalin zafin da zuciya ta take min nayi nace '' Asma'u zaki yarda dani cewa zaifi idan mutum na da kyakkyawar zuciya da mummunar fuska sama da ace yanada kyakkyawar fuska da mummunar zuciya!" dariya Asma'u tayi sosai
'' pftt! babu wanda zai zaɓi hakan Tuwo,kowa yana so yayi kyau wa'yanda keda irin wannan tunanin.. they're losers! sun san basu da kyau shine suke fakewa da kyakkyawar zuciya bla bla bla.... kamar dai ke yanzu!'' Maganar ta kamar an daɓa min wuƙa a ƙahon zuciya.....
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️