MY BEST FRIEND'S DAD

Episode 5&6

by @deeyamerh10

✨✨MY BEST FRIEND'S DAD ✨✨ 
‎By Khadijah Umar Muhammad 
‎                     (DEEYAMERH)
‎07070647236
‎Page 5&6
‎MAITAMA
‎unguwa ce mai cike da manyan gidaje, akwai wani katafaren gida wanda kallonsa kaɗai zai iya nuna irin arziƙin da ma mallakin sa yake da shi.
‎Gidan ne bene uku,an gina shi da salon American luxury mansion, mai manyan glass windows da dogayen ceilings. Babban gate ɗin gidan automatic ne, yayin da doguwar katangar da ta kewaye gidan take ba shi cikakken privacy.
‎Da zarar an shiga gate, akwai wata doguwar hanya mai kyau wadda take kaiwa zuwa babban entrance. A gefen hanyar an jera flowers da green lawn, sannan a tsakiyar compound akwai fountain mai kyau da yake fitar da ruwa a hankali.
‎A gefe ɗaya kuma akwai babban parking space da zai iya ɗaukar motoci da yawa,babban entrance ɗin gidan yana buɗewa zuwa wani large foyer, wanda yake da dogayen stairs masu kyau da suke kaiwa zuwa upstairs.
‎A ground floor, akwai babban parlour mai faɗi sosai, wanda aka tsara shi da manyan sofas, glass centre tables, chandeliers da manyan windows da suke kallon compound.
‎Akwai kuma wani formal sitting room na musamman, dining room mai girman gaske, sannan kitchen ɗin zamani mai cike da kayan aiki. A bayan kitchen ɗin akwai dirty kitchen da pantry.
‎Guest rooms guda biyu suna nan a wannan floor, kowannensu da bathroom nasa, sannan akwai visitor's toilet, laundry room da kuma rooms na ma'aikata.
‎Da aka hau first floor, yanayin gidan ya ƙara yin shiru da private.
‎Akwai master bedroom mai girma sosai, tare da private sitting area, walk-in closet da babban bathroom. Sauran bedrooms guda uku suna nan a wannan floor, kowanne da bathroom nasa.
‎A tsakiyar floor ɗin kuma akwai family lounge mai faɗi, sannan manyan glass doors suna kaiwa zuwa balcony wanda daga nan za a iya kallon babban compound ɗin.
‎Second floor kuwa an ware shi ne domin nishaɗi da kuma baƙi.
‎Akwai babban home cinema, game room, private library, gym da home office. Haka kuma akwai bedrooms na baƙi guda biyu tare da bathrooms ɗinsu.
‎A saman gidan kuma akwai rooftop lounge, inda aka tanadi sofas masu kyau, dining area da ƙaramin garden. Daga nan ana iya kallon hasken garin da dare.
‎A bayan gidan kuwa akwai babban swimming pool, poolside lounge, outdoor kitchen da BBQ area. A gefe kuma akwai garden mai faɗi da ƙaramin gazebo na zama.
‎Tsaron gidan kuwa ba ƙaramin abu ba ne,akwai CCTV cameras a kusan kowane bangare na compound, security guards suna aiki dare da rana, sannan akwai security control room, electric fence, motion sensors da alarm system.
‎Gidan yana da komai da zai sa mutum ya ji cewa ba gida kawai ba ne kawai a'a mansion ne da aka gina domin luxury, privacy da complete security.
‎Ƙarar alarm ce ta fara tashi cikin ɗakin, amma yarinyar da ke kwance cikin gadonta ba ta motsa ba.
‎Hannu tasa ta kashe alarm din da ya ishe ta da ƙara,jan blanket ɗin jikinta tasake juyawa gefe guda ta cigaba da baccin ta.
‎Ƙofar ɗakin ta hau buɗe a hankali, wata mata da bazata wuce 35yearh ta shigo da kayan makaranta a hannunta yasha guga.
‎Nufar window tayi ta buɗe curtains ɗin window,hasken safiyar ya ratsa cikin ɗakin,cikin lallashi tace"Wake up, sweetheart. It’s school time fa".
‎Yarinyar ta buɗe idanuwanta kaɗan, sannan ta rufe su cikin shagwaba tace "Five more minutes…”
‎Matashir tayi murmushi tace"Five more minutes ɗin naki ya wuce tun da dadewa,maza tashi ki yi wanka kafin ki makara ko nakira DADY na fada masa".
‎Cikin sauri ta yaye  blanket ɗin daga jikinta, da sauri ta ta sauka a godon ta nufi inda matashir take domin har ta dauko mata towel,hannu tasa ta karba da gudunta tayi  bathroom.
‎Ruwan shower ya fara sauka a jikinta, yana kore mata ragowar baccin da ya mamaye ta,sai da tai wanka sosai kafin ta fito cikin fresh clothes, ta zauna a gaban dressing mirror yayin da matashiyar ta taimaka mata wajan busar da gashin kanta da tajiko da ruwa.
‎Bayan komai ya kammala, ta saka uniform ɗinta da takalman makaranta, ta ɗauki school bag ɗinta sannan ta sauko downstairs.
‎Tana sauƙowa dining room ta nufa domin yin  breakfast a kan tebur din ta zauna take ta hadu mata  pancakes, eggs, sausages, fruits da fresh juice.
‎Zama tayi ta fara  abincinta cikin natsuwa bata wani ci da yawa ba ta ture gefe hannu tasa ta tsiyayi  juice a cup kafin ta shanye ta goge bakinta,sannan ta tashi ta ɗauki school bag ɗinta ta nufi entrance.
‎Tana fitowa ta hango driver yana tsaye kusa da motar, yana jiran ta,bayan motar da zata kaita school sai wasu a bayanta da zasuyi musu raki ta security.
‎  buɗe mata ƙofar baya driver kafin cikin  girmamawa yace mata "Good morning.”
‎morning to tace tana mai gyara zama cikin motar ɗaura seat belt tayi kafin driver ya shiga ya kunna motar.
‎Babban gate aka buɗe a hankali, motar ta fice daga compound,yayin da motar Security ta rufa masu baya.
‎Haka motocin biyu suka ci gaba da tafiya cikin titunan Abuja, har zuwa makarantar da take a Maitama.
‎A jere suke tafiya har suka iso Get din makarantar inda ka rubuta sunan makarantar The Centagon International School.
‎driver ya fito ya buɗe mata ƙofa,ta sauko da school bag ɗinta a kafaɗa gyara uniform ɗinta, sannan ta nufi Get din akan idansu tashiga cikin makaratan kafin Driver da security su juya motoci suka bar wajen.
‎Allah Allah take tashiga class dinsu ko zata ga kawarta Wacce sukai mugun sabo,gashi bata da number har gidan su bata sani ba ita bata jin ma ta tafada mata sunan unguwar bare tasa akai ta.
‎Haka dai   ta zauna cikin kadaici har lokacin daukatar yayi suka wuce gida a hanyar ta komawa ne ta ce wa driver"baba bala Ni kuwa ko kasan gidan su kawar nan yawa dake baka labari wajan 2week rabonta da makaranta gashi bansan komai nata ba ko kai kasani?tayi tambayar tana jiran Amsarka.
‎Dariya yayi kafin yace"Madam ta ina  zan sani tunda bikice mun nabita naga gidan su ba kawai dai nasan kuna tsayuwa a bakin get har nazo daukarki Amma Madam naji kwanaki kamar wanda yake zuwa daukata ita yana maganar ko batan ko me ban dai tsaya gaskiya na ji meyake cewa na wuce shi amma bayan wanna bansan komai ba game da ita".
‎Shiru tayi yana danasani rashin samun wani abu da zai ba shidar sanin inda take Amma Bari Ya koma ta Kira DADY taji wata shawara zai bata.
‎Har suka isa gida tana wanna tunanin wanda a fuskarka sai da sauya,shiyasa tana shiga matashir nan tahau tambayarta"Hana wani abu ne ya ke damunki ko wani ne ya tabaki eh?gaba daya ta kide me wajan tambayarta abinda dake damaunta kafin ta bude baki cikin damuwa tace"kawatace ta daina zuwa skull kuma mun shaku sosai har alkawarin mukai wa juna bazamu rabe ba Amma Kinga Aunty lokaci fara Exam namu ya gabato amma bata dawo makaranta gashi Ni ban san gidan su ba".
‎Baki Wacce aka kira da Aunty tayi kafin tace"to Banda abiki Hana tunda kika jita shiru to tabbas da abinda ya tsayar da ita kuma inshallah zata dawo kafin a fara Exam din a'a waya ga Hana an gama skull sai University Kuma "ta fada domin ta kawar da wacan tunanin.
‎Ai kuwa take ta warware suka cigaba da hirar Dad domin tana don ai ta bata labarin Dad din dan bata gajiyawa da jinsa, tambaya daya da har yanzu bata sami amsarta ba itace shin ina mahaifar ta take?shin Meye sa bata bude ido ta ganta a cikin gidan ba sai Dad da Aunty kuma sunce mata tana da rai amma ace bazata iya zuwa ta ganta ba sai dai photo amma ba a zahiri ba.
‎Ganin Mood dinga ya canza yasa Aunty ta sa kai ta barta domin kuwa abu daya ne yake sauya tashi tunuwa da mahaifiyar da take yi wanda sosai take bata tausayi ace yarinya kwata kwata ta taso a hannun wa ba,sai uba wanda  shima ba zama yake tare da ita ba sai idan ya bushi iskar hakan.
‎Haka taja jiki tayi dakinta inda ko kayan jikinta bata iya cirewa ba ta dauko photo mahaifiyarta tana kalla tabbas mahaifiyar ta ba yar Nigeria bace?Yadda kamanta suke gashi har baya sannan cikin shigar kanun kaya,to tana ina?meyasa ta ajiye ta a hannun me Aiki?me tai da zafi haka? Ganin ba wanda zai bata amsa yasa ta miki cikin sanyi jiki ta hau cire kayan magarantar kafin ta nemi riga mara nauyi tasa,cin bata jin dadi yasa tayi kwanciyar take lulawa duniyar tunani.
‎Sosai tayi zurfi a tunani har batasan lokacin ya zauna a kusa da ita yana Kallonta,ganin sosai ta tafi duniyar tunanin kuma ga photon mahaifiyar ta dai yabashi amsar tunanin nata.
‎Hannu yasa ya fara zare photon da sauri ta mai da kallonta kasan kafin da sauri ta meke zaune tana mai murmushi na jin dadin ganinsa yasa cikin murana" Dad yau shi ka shigo?banji shigowar ka fa tafada tana mai roko hannunsa.
‎Kanta yasha da hannunsa daya kafin ya sumbace goshinta"ummm tun lokacin da kika fada duniyar tunani.
‎Kallonta ya sake yi yana mai roko hannunta cikin nasa ya dura da ce"Hana a kullum ina mai fada miki ki cire tunanin mahaifiyarki a cikin zuciyar ki Domin ke baki cikin wzuciyarta dan da kina ciki da ta wai waye ki tun lokacin da kika tsumman goyo,so ki cire duka wani tunani a ranki ki tsaya kiyi exam tayi  kyau ni nasan me zan Miki kinji my Princess"ya fada yana mai matsa mata kumatu. 
‎Murmushi don boye damuwarta tace"Dad ina da kai ai ka isheni komai na rayuwa ta".
‎Kallonta yake cike da tausayi kafin ya meki yace maza ta ta shirya su fita shan ice cream,tsalle take da murna zata fita tasha iskar duniya,cikin sauri ta zira Abaya ta feshin jikinta da turare kafin ta bi bayan Dad.
‎A kasa tasa me shi inda suke magana da Aunty ganinta yasa tayi shiru tana kallon ta,shima ido ya zuba mata kafin ya mika hannunsa alamun tazo.
‎Jerawa sukai inda suka nufi kofar Parlon Suna tsayuwa a gun Ƙofar ta buɗe a hankali, kafin Dad ya fito tare da Hana a gefensa.
‎Sanye yake cikin wata black kaftan mai kyau, agogon hannunsa yana haskawa ƙarƙashin hasken fitilun gidan, Fuskarsa kuwa cike take da nutsuwa da irin confidence ɗin mutumin da ya saba kamewa.
‎hannunta riƙe da ƙaramin handbag ɗinta, tana bin sa a hankali,nufar inda ka fito masa da black Rolls-Royce Cullinan Black Badge,Gilashinta tinted ne, sai kyalli take da daukar ido.
‎A tsaye yasamu Driver security suna jiran fituwarsa a kame suke suna jiran umarni daga uban gidan su.
‎Suna ƙaraso kusa da motar, driver yayi  sauri ya buɗe ƙofar baya domin zaman Oga,ya buɗe masa ƙofa, amma Dad ya dakatar da shi da hannu.
‎"It's fine. I’ll drive tonight".Driver ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya gyada kai
‎juyawa yayi ya kalli security ɗin da ke kusa da motor ya sake cewa"None of you is coming with us. I just want some time with my daughter.”
‎“Sir" security din ya fada yana me kame jikin sa sosai.
‎“I said no security.”
‎Muryarsa ba ta da ƙarfi, amma kalamansa sun isa su sa kowa ya fahimci cewa ya yanke hukunci.
‎murmushi Hana tayi kafin cikin jin dadin cewa ita da Dad kawai zasu fita"Really, Daddy? You're driving?”
‎Bai bata Amsa ya buɗe mata ƙofar motar da kansa yace "Get in, princess.”
‎Hana ta shiga cikin motar cikin farin ciki, Dad kuma ya zagaya zuwa driver's seat,sai da ya shiga ya zauna,kafin ya kunna motar da kansa.
‎Kallon ta yayi sannan yace"Ready for your ice cream? Murmushi tayi" yes Dad  i'm ready!”murmushi yayi kafin ya cinna hancin kan motar kan titi.
‎Bai tsaya da su a ko ina ba,sai gurin wasan Magicland, Hana tsayawa cak tayi na bin gurin da kallo na yan seconds .
‎Hasken rides ɗin yana walƙiya cikin duhun dare, ana jin kiɗa daga wajen arcade, yayin da dariyar yara ta ƙarar mutane ke cika wajen. A can gefe kuwa, babban Ferris Wheel yana juyawa a hankali, fitilunsa suna haskawa daga nesa.
‎“Daddy… look!”tai saurin kama hannunsa tana jansa, kallon wurin Dad yayi kafin ya saki  murmushi cikin jin dadin yasa Hana murna yace"Slow down, princess. We have all night".
‎"Really?" Tana tsalle dan bakaramin dadi taji ba.
‎“Yes" yana mai janta zuwa guri Carousel,wakan da ke tashi akan carousel suna hawa suna sauka yayin da yake juyawa, Hana tana dariya sosai. Dad kuwa ya zauna kusa da ita yana kallonta, har shi ma ya kasa hana kansa murmushi.
‎Bayan sun sauka, Hana ta nuna Bumper Cars"Daddy, that one!”
‎Dad ya ɗaga gira"You want to crash into me?”"
‎"Yes!"Dad tana dariya mai haɗe da gwalo.
‎"Okay. Let’s see who wins".Suka shiga motoci biyu. Da aka fara, Hana ta tura motarta kai tsaye zuwa tasa.
‎“Hey!”
‎Ta fashe da dariya.
‎“Got you!”
‎Dad ya girgiza kai yana dariya.
‎“You're dangerous.”
‎Daga nan suka nufi Wonder Wheel, babban Ferris Wheel ɗin da ke ɗaga su sama a hankali. Yayin da motarsu ta hau sama, hasken Abuja ya bayyana a nesa.
‎Hana ta matse fuska da gilashin.
‎“Wow… Daddy, look at the lights!”
‎Dad ya kalli garin na ɗan lokaci, amma daga baya sai ya kalli Hana.
‎“Beautiful, huh?”
‎Hana ta gyada kai.
‎“Very.”
‎Bayan sun sauko, Hana ta sake nuna wani ride.
‎“Daddy… that one looks scary.”
‎Dad ya bi inda take kallo. Pirate Ship ɗin yana lilo daga gefe zuwa gefe, mutane a ciki suna ihu da dariya.
‎“You scared?”
‎Hana ta girgiza kai da sauri.
‎“yeah!” murmushi Dad yayi kafin yace"Then let's go".
‎“Daddy!"tafada tana dan matsawa bayan duk da ƙorafin da take masa na ita bata Amma haka ya kama hannunta suka hau Bayan Pirate Ship, suka gwada Flying Tower, sannan suka wuce wajen Roller Coaster. Wannan karon Hana ta kara jin tsoro sosai.
‎Cikin sauri tace" Dad Bana son wannan Please"ko sauraranta bai ba ya durata akan coaster ɗin ya fara gudu sosai Ihu Hana tasa sosai inda hankalin mutane ya dawo kan su,dan har wasu sun fara mata video domin yadda take kuka sai abin ya burge su gashi Dad din yana na mata dariya sai abin ya bata kalar burgewa.
‎“DADDYYYY!”
‎Dariya yayi yana kafin yace "I thought you weren't scared!"
‎"I HATE YOU!"ta fashi da kuka tana rike karfen sosai,ko da ta sauka hannunsa ta rike  tana dariya, gashinta ya hargetse sabida tsoro,duk wanna wahalar da tasha Amma sai ta suka sake hawan Fun Arcade, inda akwai games daban-daban na motoci, motorcycles da sauran wasannin cikin gida.
‎racing game Hana ya zaba domin tasan duk wanna abubuwan ba damunsa sukai ba, Kallonta yayi yace "oh You're challenging me now?”
‎“Of course" tace tana masa gwalo wai ita a'la dole sai ta rama abinsa yayi mata yanzu haka sukai game din cikin farinciki kasan cewar da 'ya' daya tilo da Allah ya bashi