MY BEST FRIEND'S DAD

Episode 7&8

by @deeyamerh10

✨✨MY BEST FRIEND'S DAD ✨✨ 
By Khadijah Umar Muhammad 
                     (DEEYAMERH)
07070647236
Page 7&8
‎A wannan daren, babban mutum mai cike da business, meetings da responsibilities ya manta da komai,babu waya,ba driver balle security da suke biye da shi tamakar Shugaban kasa amma ya zauna da yar sa yana dariya da guje guje dan debe mata kewar mahaifiya.
‎Sosai suka dade kafin suyi wajan siyan Ice cream din da yake da dan mutane a gun,wanda yasa Dad jira kamar yadda sauran mutane sukai.
‎Bayan sun gama yawon wasan da suka yi a Magicland, Dad ya kalli Hana da ke gefensa.
‎“Ready to go home?”
‎Hana ta gyada kai, amma sai ta tuna da wani abu.
‎“I want ice cream before we leave",ta fada cikin sauri domin tunawar ba'asai abin daɗin ba.
‎“Alright. Let's get one" ya fada yana mai nufar wajan da ake siyar da ice cream difference colours ice a gun..
‎Ko da suka karasa wajen  cika da mutane. Wasu daga cikin 'yan mata ne tare da 'yan uwansu, wasu saurayi da budurwa ne,suna jiran order ɗin su.
‎Komawa gefe yayi domin jiran layi yazao kansu,Hana kuwa ta shiga cikin layin, yayin da Dad ya tsaya yana kallonta daga ɗan nesa.
‎A cikin wannan cunkoson ne matashiyar take tsaye tare da wasu daga cikin 'yan uwanta mata. Su ma sun zo ne domin su sayi ice cream kafin su koma gida.
‎Matashiyar burwace a gefe ita da yan uwanta tana dariya da ɗaya daga cikin 'yan uwanta, Tsayawa cak da Dariyar da take takeyi jin Kamshin turaran da ko mafarki tayi tana jin kamshin sa,cikin sauri ya juyo Amma wayam babu kowa sai Kamshin da yake gurin,raba ido take ko Allah zai sa taga mai amfani da turaran ko zatayi katari da abinda ke take nema tsawan shikaru.
‎Cikin mutane ta kusa tana bude kofofin hancita ko Allah zai sa ta sake jin Kamshin wanna turare.
‎Da Baya Daya ba take tafiya,har taji da bige mutum cikin sauri ta jiyo bata kalli fuskar wacce ta bige ba tai saurin tsugunawa domin dauko mata rubar Ice cream din da tafadi har rabin ice din ta zube,cikin damuwa ta dago tana cewa "Sorry wallahi ban ku......bata karasa abinda take niya ba fuskarta ya sauka a cikin ta Hana wacce itama ta zaro ido tana saurin fadin "Besty
‎Itama cikin mamaki tace "Hana"sai kuma suka rungume juna cikin jindadin ganin juna kafin BESTY ta cikata tana janta gefe"ke dawa kuka zo nan gurin?.
‎Cikin farinciki Hana tace"Ni da Dad ne kingane shi can yana jirana"Dago da kai Hoorain tayi domin ganin Dad shi kuma a lokacin ankirashi a waya ya juya baya dan haka bata sami damar ganin fuskar ba sai bayansa.
‎Sosai zuciyarta take bugu da karfi kafin ta dauke idonta daga bayansa ta mai da Kallonta ga Hana"Ummm ai nayi fushi ko nema na bakiyi bare kixo gidan mu ko"?ta fada tana hararanta.
‎Dariya Hana tayi kafin tace"to uwar masifa kinan da halinki yanzu dai samun number ki saboda tafiya zamu gashi kin zubar mun da ice cream Dina kawai"?ita ma ta maka mata harara,dariya suka duka kafin su hada baki su ce 1-1,karbar wayar tayi tasa mata Number inda tayi Dial har number ya shigo cikin wayar ta sanna ta mika mata kafin tace tashi muje gurin me ice cream din kada ya kare wllh".
‎Da sauri suka mike kafin suyi gun me ice cream din,Besty ta ta kalli ma'aikaciyar tace"Chocolate ice cream, please.”
‎Ma'aikaciyar ta ɗan kalle su cikin murmushi tace"I'm sorry, the chocolate flavour is finished.”
‎Besty ta kalli Hana wacce tai shiru kafin Hana tace"What about vanilla?”
‎"Finished too"ma'aikaciyar tace.
‎“Then what do you have?” Hana tasake tambaya cikin addu'ar Allah yasa ya samu ko da villah.
‎Ma'aikaciyar ta nuna mata sauran flavours,Hana ta kalli ɗaya bayan ɗaya, amma babu wanda take so a ciki.
‎A wannan lokacin Besty dake gefenta tace"Ki ɗauki nawa"
‎Hana kalleta da sauri "kefe?.
‎"Badamuwa Ni dai na dauki a cikin raguwar flauours din".
‎“Thank you so much.”
‎“You're welcome"Besty tace yana mai mata cup din da yake hannunta,ta karba kafin ta jiyo taga har yanzu Dad yana waya sai kawai ta cewa Hoorain"zumu ku gaisa da Dad yau dai bada labarinsa ya kare".
‎Murmushi Besty tayi tana me bin bayanta domin zuwa gaida Dad din Hana,kusa da shi Hana ta je duk da waya Amma haka take masa maganar akan ya juye Kawarta zata ganshi,
‎A lokacin da Besty ta dago da zimmar gaisawa da Dad din Hana aka kirata a waya ganin First love ya fito akan screen din wayar yasa tayi picking tana kai wayar kunnan ta,shikuma a wanna lokacin ya juye domin ganin kawar Hana sai akasamu akasi ita Besty ta juya tana amar wayar kafin cikin daga murya yadda Hana zataji tace"Hana Byee ana jiranmu zamu tafi sai munyi waya" dan har tana hadawa da gudu wajan isa inda yan uwanta suke jiranta domin wucewa gida.
‎Ganin shima na ya jiyo tana waya yasa shiya juyawa yana wayar yana nufar inda motar da take,ganin haka yasa Hana mara masa baya.
_________
HOSPITAL 
Duk wani abu na binkece domin ganin lafiyar mutum sai da akai wa Hoorain har da dubata domin ganin sunyi mata fyade ko a'a inda Allah ya tai maka basuyi mata komai ba sai kawai ciwankan da suka jimata,sosai Ummee da Ammey sukai murnar jin Hoorain ƙalau take,tsaya sukai suka karbi magunguna har da na ido domin yawashi daga jan da yayi
Suna hanyar komawa Hoorain ta kalli Ammey cikin kwalla yace" Ni bana bin maza..Wlh Allah Hoorain bata bin maza"hawaye ke tsiyaya a idanuwanta tana kallon Ummee da duk ta shiga damwa.
Hannun ta Ammey ta kama tace "ki kwantar da hankalin Wallahi Hoorain ban Haifeki ba Amma nasan abinda zakiyi nasan abinda bazakiyi ,ko ina kika shiga nasan bazaki taba bin maza kishare Hawaye kinji".
Kai ta daga domin indai kaga Hawaye akan fuskar Hoorain to tabbas ta hango damuwa akan fuskar Umme to zaka ga Fitarsu daga Idanuwan ta.
kuka sosai tayi abu Daya yafi Tsaya mata arai Cewar da Mama tayi tana bin maza tasan tana da magana Amma shima ga wanda ya santa sannan rashin kunya da Taurin kai Amma shima koya tayi daga baya Sabod su Noor amma Wlh maza basa gabanta Domin tayiwa kanta alkawari cewa shi kadai zata mallakawa kanta ko da baya sonta da kaunar ta ita zata soshi ta zauna da shi,Amma ita tsakaninta dasu sai goge reni Domin har ayanzu Hoorain bata jin da namijin da zai kai mata farmaki Batai kokarin mayar masa da martani.
Sosai Hoorain ta basu tausayi,dole ta damu sosai domin ko da ace bi take ai abinda sukai mata tuzarci ne bare kuma ba halinta bane.
Haka suka isa gida kowa da irin damuwar da ke dankare a zuciyarsa,lokacin da motarsu ta tsaya a farfajiyar gidan har su Mamey da Mama na riga rigan dage labulan window duk da ko wanne na part dinsa ganin duk yanayin sai suka sami kwarin gwaiwar cewa abinda suka kafada ya tabbata kenan.
Kamar yadda Baffa ya tarasu haka ma aka sake zaman yanzu domin jin Result din Hoorain,inda kallo daya Baffa yayiwa katin asibitn ya sauke ajiyar zuciya domin komai lafiya kalau,haka yabawa yan uwansa kowa yagani baban Safna shine karshan ganin result din shiya ya rike shi a hannunsa dan har Mama na mika hannu ya bata,irin kallon da yajefe tashi ne yasata shiga hankalinta.
Sosai Baffa yayi bayani inda yasake janwa yaran mata da maza kunne a haka taro ya tashi kowa yayi part din
( Part Din Mama....)
Ai Mama na shiga part din ta sai jin Mamey tayi a bayanta tana cewa"Kinga wata manakisa anbawa kowa ya gani Amma mu shiru saboda abinda muka fada ya tabbata oh ni suwaiba"cewar Mamey tana zama a daya daga cikin kujerun Mama.
Ummm"kayi magana kace baka da hankali Amma abinda sukai ai dolene mu zarge su,Ni wllh nazata ma zakiyi magana akan Auran Kabeer din najiki kinyi shiru har taboki nayi fa".
"Kinsan hankalin yana gun abinda zamugani ai bari kiji" cewar Mamey tana gyara zama"So nake sai ta warke sun koma makaranta sai lokaci daya na hada meeting gagarumi yadda zan dagawa kowa hankali sai dai lokacin yayi".
"Ni kinsan me yake bani mamaki yadda ubanta yake zaune tunda aka fara wanna badakalar bai ce uffan ba tun da ya sunkuyar da kai kamar wanda yake gaban sarki har aka gama sannan ya meke ya fice".
Yo Banda abinki maman Noor uban me zai ce ai yasan jarabar da ya haifa,yayi magana ke kuwa hmmm kibarshi kawai Allah yasama ba hadin baki sukai da shi ba dan a sace yarinyar Kinga ai kudin fansa daga jikin mazajan mu zasu fita ko?.
Innalillahi kinsan sai da kika fada danna kai na ya kawo wuta tirkashi Amma Allah ya kyauta" cewar mama.
Mekewa Mamey tayi tace "bari na wuce daman abinda ya kawo ni kenan".tana cikin magana sai ga Noor ta fito Kallonta yake kafin tace"a'a ai idona ne yake mun kizau ko kuwa Noor ce ta koma fara haka kema bleaching din kika fara?.
Baki gaba Noor ta zunbura cikin kokoni da baki tace "ai tare mukeyi da ameerah bataji me take cewa ba Amma tabbas tasan magana take yi.
Cikin sauri Mama tace"kewa ai dole kadan shafa saboda samarin sun fison me haske yanzu kuma ai karin kyau ne ko ke bikiga yadda take daukar ido ba?
"Eh kam nagani kam sai daukar ido take Amma duk hasken nata idan dare yayi bata haska muku daki ba?.Mamey ta fada tana ficewa daga dakin.
Wata uwar Ashar mama ta dankara mata kafin cikin fushi tace"dan kutumar ubanki matar da muke so ta zama sirikarki shine ɗan ubanki tana magana kina mata kukuni Wllh Noor kikai mun sanadiyar da matar nan ta ki yadda kin Aure Kabeer wallahi sai namiki dukan da zaki kasa tashin yar bura'ubar yarinya ana hango mata arziki tana niyar kai cewa".daga haka tayi cikin ɗakinta.
Kallon Nasreen tayi kafin su tabe baki a tare nan suka zauna zaman hirar samari inda Nasreen tace"ke na hadu da me zafi a Snap wllh guy ya hadu iya haduwa fa".
"Ah ba tayaki murnar Allah yasa mai sakin kudi ne dan ke duk masu maimakon kike damuwa"cikin fusata Nasreen tace"garani ai gani akai akace ana so ke da ke kokarin Turawa wanda ko inda kike baya kalla"mtsss taja tsaki tana bin hanyar dakinsu,baki bude Noor take Kallonta wato ita zataiwa gore to da ita take magana,ta gyara kwanciyar ta akan kujera dan idan tace zata bi Nasreen to zasu raba hali ne Amma zata gane shayi ruwa ne.
(One month ago...........)
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da samun saukin Hoorain inda wata rana ta fito zata part din Mamey domin ta karbi book din Ameera domin tana don ta duba wani Assignment tunda ita suke Department daya da Noor Da Nasreen suna tare mazan gidan kuwa duk suna kasuwa tare da iyayensu maza.
(Part din MAMY.......)
Tafiya take tana kallon yan ya tsunta da sukai fari wanda suke bukatar lalle take kallo jin tayi karo da Mutun tai saurin dagowa wazata gani...mutumin da sunan yana amsa sunan dan uwanta ne Amma zata iya cewa Gara ace mutuwa yayi da shi idanuwa ta runtsu tuno abinda take kokarin matanawa,bude su tayi inda shi kuma ya kafeta da nashi idanun,cikin dakiyar da tasawa kanta tace"yaya Kabeer ina yini andawo lfy ya kabaru Mutun Spain"bata tsaya taji Amsar ta zata bashi ba kawai ratsa ta gefensa ta wuce cikin part din su.
Da sallama ta shiga inda ta sami Mamay da Ameera sun kallo gaida Mamey tayi ta amsa kadaram kadaham ta juyar da kai.
Kallon Ameerah tayi kafin tace'dan Allah anty Ameera littafin psychology zaki bani zan duba Assignment din da yabayar".
Zaraf Mamey ta karbe zancen kafin Ameera tayi magana tace"ke lokacin da aka bada Assignment din idan ubanwa kika je?wato ke dai bazaki nutsuwa ba daga wacan na miji zuwa wancan ko?.
Shiru Hoorain tayi kafin ta meke ta nufi hanyar ficewa a parlon ameera tace"kitsaya kirba daman nace zan baki Dan lokacin da kuje clinic ya bayar tsaya na dauko Miki".
A'a barshi kawai kada na taba Miki littafin kema ki koma bin mazan"tasa kanta tai ficewar ta.
Kallon mamey Ameera tayi kafin tace"wallahi Ni mamey bansan me Hoorain ta tsare Miki ba,idan da zakije makarantar Kiga Abinda su Noor suke da zaki gane banbanci tsakaninsu".
"Dalla can rufe mun baki ke har kin isawki fadamun yadda halayar su take yarinya kina kallonta idonuwa a tsaye kamar nonon maza sannan kice mun ga zance ga magana idan biki hankaliw da shiga har kar yarinyar na ba wllh wataran sai na ballaki"
Cikin kukuni Ameera tayi dakinta"kinyiwa ubanki kukuni kinji danni ba'asar yinki bace".
Daga kofar Parlon taji saukar muryarsa"nagode Daman Ni suwaiba kinji nace ke sa'a tace,Indai har halin aibata yara kike kada ki manta kina da su,wasu suna gidan miji ga wata a gabanki".
"Aaaaa dan Allah baban safna kidaina aibata mun yara ahto domin kuwa Ni dai bazanga lala tacce a zuri'ata ba,dan mugun abu ace yarinya tana abinda baya dacewa kuma ace baza'a fada mata gajiya ba".
"Hmmm ba fatana nake Miki ba,amma zakiyi da nasanin ai bata wannan yarinyar da kike,kuma da kikewa tana abunda bai dace ba,kifadan kin taba kamata turmi da tabarya bari kice,jinina ce indai har Hoorain zatai zina to kisawa ranki Nima zanyiwa domin jinin da yake yawo a jikinta shine a nawa"yana gama fadin haka ya shige dakinsa.
Cikin kasa da murya tace" to wayasani Abu a duhu"daga cikin dakin ya sake cewa"Nagode suwaiba.
Cikin sauri tayi dakinta domin wallhi batai tunanin zai ji ba...
Yadda Hoorain tabar yaya Kabeer a tsaye haka takuma samunsa a tsaye sai dai wanna karan shi da Noor ne ana ta kwarkwasa shi kuwa yana faman danna waya.
Saurin gyara fuskarta tayi daga yanayin da tafito daga part din Mamey dan karau gane da wani abu.
Sai da tazo gafda zata wuce sai kuwa Noor cikin dan sautin da zata iya ji tace" MY Allah kana shagwabani da yawa fa to ka nuna mun picture din da kai mun nagani Indai nayi kyau"tana mika hannu wajan karbar wayar yaya Kabeer.
Dagowa yayi da zimmar yaci ubanta sai kawai idonsa ya sauka kan Hoorain ta ke giftashi wata uwar dariya Hoorain ta saki tana me cewa"Ikon Allah inda ranka kasha kallo"da kallo yabi kugunta yadda suke juyawa cikin doguwar riga.
Inda yake kalla Noor tabi da idonuwa ganin haka yasa ta cilla masa wayar da tana barin wajan cikin kuka tayi part din su.
Da kuka ta shiga dakin inda mama take zaune tana danna waya cikin sauri ta dago jin yadda Noor ta zube a jinta tana fadin "nashiga uku mama har yanzu yaya Kabeer hankalinsa yana kan Hoorain wayoo Allah"haka tasa m
A gaba tana zanda ma mata ihu.
Kiyi shiru ki fadamun me tayi miki,nan ta kwashe karya da gaskiya ta fada mata habawa tuni ta ja hannunta sai part din Ummee....