Fuska biyu angel and Boss
CHAPTER 11️⃣
SABREEN
“Game da mahaifinki.”
Kamar an zuba mata ruwan sanyi haka Sabreen ta tsaya cak.
Wayar na manne a kunnenta, amma idanunta suna kan mutumin da ke gabanta.
“Zayyad…”
“Angel, listen to me carefully.”
Muryarsa ta yi tsauri.
“Kar ki yarda da duk wanda ya zo wajen ki da maganar mahaifinki. Ki yi hattara.”
Sabreen ta kalli mutumin.
“Amma…”
“Sabreen!”
Ya katse ta.
“Na ce ki yi hattara.”
Kafin ta sake magana, call din ya yanke.
Ta sauke wayar a hankali.
Mutumin dake gabanta ya yi murmushi.
“Yanzu kin ga shi ma yana bincike.”
Sabreen ta daure fuska.
“Waye kai?”
“Sunana Faisal.”
“Faisal me?”
“Faisal is enough for now.”
Sabreen ta matso kusa da shi.
“Ni bana son wasa. Idan da gaske ka san wanda ya kashe mahaifina, ka fada min.”
Faisal ya kalli Zara.
“Ba a gaban kowa ba.”
Sabreen ta kalli Zara.
“Zara, ki bamu minutes biyar.”
“Boss…”
“Please.”
Zara ta yi shiru ta nufi kitchen.
Da zarar ta fita, Sabreen ta koma kallon Faisal.
“Now talk.”
Faisal ya zauna.
“Abinda zan gaya miki zai canza komai da kika sani game da mahaifinki.”
Sabreen ta zauna a gabansa.
“I'm listening.”
“Sheikh Muhammad Kabir bai mutu saboda siyasa ba.”
Sabreen ta daure fuska.
“Then saboda me?”
Faisal ya numfasa.
“Saboda wani sirri.”
“Wanne sirri?”
“Black Market.”
Sabreen ta kafe shi da idanu.
“Black Market?”
“Eh.”
Ta tuna Alhaji Bara’u.
Ta tuna Zayyad.
Ta tuna Musty.
Komai ya fara hade mata.
“Musty yana ciki?”
Faisal ya yi shiru.
Sabreen ta kara cewa,
“Bara’u fa?”
“Dukansu suna da connection.”
Zuciyar Sabreen ta buga.
“Who killed my father?”
Faisal ya kalli kofar parlour.
“Ba zan iya fadin sunansa yanzu ba.”
Sabreen ta mike cikin fushi.
“Then why did you come here?”
“Saboda ina son ki san cewa kina cikin hadari.”
“Ni?”
“Eh ke.”
Ya zaro wata tsohuwar photograph daga aljihunsa ya mika mata.
Sabreen ta karba.
Da zarar ta kalli hoton sai jikinta ya yi sanyi.
Mahaifinta ne.
Amma ba shi kadai ba.
A gefensa akwai mutane hudu.
Daya daga cikinsu ta san shi.
Ta san shi sosai.
“Impossible…”
Faisal ya kalleta.
“Kin gane shi?”
Sabreen ta kasa magana.
Hannunta ya fara rawa.
“Wannan…”
Ta kasa karasa.
“Who is he?”
Faisal ya ce a hankali:
“Mutumin da yake kusa da mahaifinki a lokacin da aka dauki wannan hoton…”
Ya dan yi shiru.
“Shi ne wanda ya bada umarnin a kashe shi.”
Sabreen ta zura ido cikin hoton.
Kuma mutumin da take gani ba bako ba ne.
---
ZAYYAD
Zayyad ya ajiye wayarsa a kan table.
Bash yana tsaye gabansa.
“Boss?”
“Fada min komai.”
Bash ya bude wani file.
“Na samu wani tsohon record.”
Ya mika masa.
Zayyad ya karba.
“An rubuta cewa shekaru goma sha bakwai da suka wuce Sheikh Muhammad Kabir ya samu wani financial discrepancy a cikin wasu accounts.”
“Continue.”
“Wasu makudan kudade sun bace.”
“Daga ina?”
“Government project.”
Zayyad ya dade yana kallon takardar.
“Wa ya sa hannu?”
Bash ya nuna wani wuri.
“Ga sunan.”
Zayyad ya karanta.
Sai ya mike tsaye.
“Impossible.”
“That's what I thought too, Boss.”
Zayyad ya sake karantawa.
“Sabreen bata san wannan ba?”
“Ban sani ba.”
Zayyad ya rufe file din.
“Bash, akwai wani abu da nake so ka yi.”
“Me?”
“Ka saka ido kan Sabreen.”
Bash ya dago gira.
“Boss…”
“Ba don in cutar da ita ba.”
Zayyad ya sauke numfashi.
“Ina jin tana cikin hadari.”
“Okay.”
Bash ya juya zai fita.
“Bash.”
“Sir?”
“Idan wani abu ya faru da ita…”
Zayyad ya tsaya.
“Don't let her face it alone.”
---
SABREEN
“Waye wannan?”
Faisal bai amsa ba.
Sabreen ta daga hoton.
“Na tambaye ka, waye wannan?”
“Mutumin da mahaifinki ya fi yarda da shi.”
Sabreen ta kalleshi.
“Then how did he betray him?”
Faisal ya sauke kansa.
“Saboda kudi.”
Sabreen ta yi dariyar takaici.
“Money?”
“Ba kudi kadai ba.”
“Then what?”
“Power.”
Shiru ya cika parlour.
Sabreen ta koma ta zauna.
“Faisal…”
“Yes?”
“Me yasa kake taimaka min?”
Ya kalleta.
“Saboda mahaifinki ya taimake ni shekaru da suka wuce.”
“Ta yaya?”
Faisal ya mike.
“Lokacin da kowa ya juya masa baya, shi ne mutum daya da ya kare ni.”
Sabreen ta sauke idanu.
“Then tell me everything.”
Faisal ya girgiza kai.
“Not today.”
“Why?”
“Saboda akwai wani mutum da yake bin diddigin duk wanda yake binciken mutuwar Sheikh Muhammad Kabir.”
Sabreen ta kalleshi.
“Who?”
Faisal ya bude kofar.
“Ki tambayi Zayyad.”
Ya fita.
Sabreen ta tsaya a wurin tana kallon kofar.
“Zayyad?”
A lokacin Zara ta dawo.
“Boss, waye wannan?”
Sabreen ta kalli Zara.
“Mutumin da ya zo da labarin mahaifina.”
Zara ta razana.
“Me ya fada?”
Sabreen ta duba hoton dake hannunta.
“Ya ce wanda ya kashe mahaifina yana cikin wannan hoton.”
Zara ta matso.
“Boss…”
“Hmm?”
“Waye?”
Sabreen ta dago kanta.
“Ban sani ba.”
Ta kalli hoton karo na biyu.
Amma wannan karon idonta ya tsaya kan fuskar wani mutum dake bayan hoton.
Kamar tana kokarin tuna inda ta taba ganin shi.
Sai kwatsam…
Wayarta ta yi ringing.
Unknown number.
Sabreen ta daga.
“Hello?”
Ba a amsa ba.
“Hello?”
Sai aka ji numfashin mutum.
Daga bisani wata murya ta ce:
“Sabreen… ki daina binciken mutuwar mahaifinki.”
Sabreen ta daskare.
“Who are you?”
“Idan ba ki tsaya ba…”
Muryar ta yi shiru na seconds.
“Zayyad zai mutu saboda ke.”
Call ya yanke.
Sabreen ta zubawa wayar ido.
Zara ta gane cewa wani abu ya faru.
“Boss?”
Sabreen ta dago a hankali.
“Zara…”
“Yes?”
“Ki kira Zayyad.”
“Yanzu?”
“Yanzu.”
---
ZAYYAD
Wayarsa ta yi ringing.
Ya duba screen.
ZARA CALLING.
Ya daga.
“Hello?”
Muryar Zara tana rawa.
“Sir… Boss ta ce in kira ka.”
Zayyad ya mike.
“Me ya faru?”
“Ta samu threatening call.”
Fuskar Zayyad ta sauya.
“Threatening call?”
“Eh.”
“Me suka fada?”
Zara ta yi shiru.
“Zara!”
“Suka ce… idan ta ci gaba da binciken mutuwar mahaifinta…”
Ta kasa karasa.
“Me?”
“Suka ce za su kashe ka.”
Zayyad ya rufe idanunsa.
A hankali ya bude su.
“Tell Sabreen…”
“Me?”
“Ina zuwa.”
Ya dauki key din motarsa.
Bash ya kalleshi.
“Boss?”
Zayyad ya ce:
“Yanzu ne wasan ya fara.”
TO BE CONTINUED…
MISS NASIR ❤️✍️