14 Nikaah marriage for the
by @hanaady
NIKAAH
(Marriage for Rent)
By
HANAADY
(Rahama Aminu Bala)
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
Page 14
Not edited.
Yanzu abunda nake so dake shine ki fad'a mun menene kika fahimci cewa yana d'aukar hankali sa akan ki ,daga kanta tayi alamun tunani,gashi na ta furta cikin kunya dariya Jummai tayi sannan tace yooo menene abun kunya kuma , yanzu abunda ya kamata shine bari na baki kayan aiki akan gashin nan naki ,wani turaren sakawa gashi ta bata wannan abun fa cewar Karime turaren gashi ne gaskiya bana son amfani da wani abu da ya shafi sihiri,dalla can idan bakya so na ajiye abuna akan me zan cuce ki.
Ni kaina duk abunda ya shafi sihiri bana ta'ba fatan amfani da shi.
Turaren ta ansa had'i da saurin shafawa gashin kanta, me yake sakama cewar Karime, murmushi Jummai tayi sannan tace yana saka natsuwa da kuma nishadi,da haka Jummai taita dora ,Hjy Karime hanya.
"Around 8:30 Ramadan yayi parking k'ofar gidan Jummai kiran number ta yayi ba tayi picking ba cikin fushi ya kuma kiranta gaf da zata katse ta d'aga idan baki shirya tafiya ba nayi tafiya na ,on my way ta fad'a had'i da katse kiran,baki galala yabi wayar da kallo lallai yarinyar nan raini ya fara shiga tsakanin su.
"Ji yayi ransa ya sosu dole ya koya mata hankali,harta isa ta katse masa kira ,sosai yaji ransa ya dad'a b'aci duba da dama Sadiq ya harzika shi .
Shugowa tayi cikin motar fuska a murtuke!ya bita da kallo ,bata ce dashi komai ba illa jingina jikin mota da tayi tana mai kallon sa , lumshe idanuwan yayi yana mai jin dad'in kamshin dake fitowa daga jikinta, jare mayafin kanta tayi had'i da binsa da wani irin kallo wanda a yau d'innan Jummai ta ankarar da ita.
Neman fushin sa yayi ya rasa ,kin fara raina ni koh Karime.
D'an cizon lips d'inta tayi sannan tace Nina na isa na raina mijin Sa'ada kawai ka kira ina k'okarin fitowa that's why da farko ban d'aga kiran ba .
Come here ya furta yana mai nuna mata saman cinyar sa , matsawa tayi a hankali nayi maka kyaune mjin Sa'ada had'e yawun bakinsa yayi sannan yace ya Sa'ada ?
Tayi bacci ta fad'a tana mai k'okarin komawa wajen zaman ta ri'ke mata hannun yayi please stay jin furucin shi yasa ta bisa da kallo ba tareda tace komai, slowly take kallon fuskar sa saukar da idanuwan ta tayi saman lips d'insa, ji yayi duk wani fushi da b'acin ransa ya fara barin jikinsa, baki ya saki yana mai binta da kallo
D'an murmushi tayi cikin ranta domin sosai ta fahimci darasin Jummai ya fara aiki, zuciyar ta dukan ukku ukku take but still haka ta daure , d'an matsawa tayi zuwa daf dashi, baki ya bud'e da zimmar magana tafin hannun ta, tasa tareda rufe masa baki ,then she stepped forward and wrapped her arms around his neck ,he was speechless dai dai kunnen sa ta d'aura lip's d'inta,in sexy and romantic way tace why kake son koma mun Ramadan d'in dana sani farkon zuwa na gidan ku d'ago fuskar ta tayi had'i da shafa fuskar sa, you are very handsome,......
"Tsayawa tayi domin she was struggling ta furta abunda ke ranta, mutunan naku kuwa binta yake da kallo domin dai yau ba magana , sai data tattaro courage sannan tace Mijina d'ago idanuwan sa yayi yana kallon ta d'an murmushi tayi had'i da shiga jikinsa, zaro idanuwa waje yayi meya canza masa Karimen sa a yau kodai tayi gamo ne , sosai take jin bugun zuciyar sa , d'an murmushi tayi had'i da cewa cikin ranta ,ina matuk'ar godiya Jummai na domin tabbas taji yanda heart beat nasa ke wani irin gudu ,duk abun data aikata tunda daga kin d'aukar kiransa zuwa yanzu da take kwance saman jikinsa was planned by Jumma and Jummai ta fad'a mata the last thing da za tayi shine hugging nasa if abunda tayi masa yayi amfani za taji bugun zuciyar da lokacin da tayi hugging nasa ,if hakan ta faru suna da hope sosai akan sace zuciyar Ramadan.
murmushi Karime take cikin ranta sosai take jin wani sabon yanayi had'i da farinciki mai tsanani .In sha Allah she will fight for this man , in sha Allah she will.
K'okarin zare jikinta take shi kuwa a lokacin ya fara jin dad'in yanayin sabida haka k'ara matse ta jikinsa yayi after some minutes d'ago kanta tayi tana fuskantar sa , shafa fuskar ta yayi ba tareda yace komai ba,juyawa tayi had'i da d'aukar mayafin ta , mayafin ya ansa ,saurin kallon sa tayi murmushi yayi in a sexy way yace kin kama seducing nawa?
Zaro idanuwa waje tayi had'i da rufe fuskar sannan tace yaushe nayi seducing naka, murmushi mai sauti yayi had'i da jawota saman cinyar sa shinshinar gashin kanta ya shiga yi, matsar da lips d'insa yayi dai dai kunnen ta , yes Karima,kinyi mun laifi shine kika zo da salon seducing d'ina but i like it yana idasa maganar ya d'ago kansa kallon ta yayi cikin wani yanayi yace i love this side of you , kin yi controlling anger d'ina a cikin lokaci kad'an.
D'aurewa tayi tace Mijina ne kai koh?
Dariya maganar tata ta bashi ,bayan ya d'an dara cewa yayi yes Karime I'm your husband and you are my wife , murmushi tayi had'i k'okarin sauka daga jikinsa, please don't go cikin wani yanayi yayi maganar sosai taji har cikin ranta ,i want to you to stay ya fad'a cikin alamun rad'a,ina son zaunawa ne ,da a tsaye kike ya fad'a yana mai binta da kallo.
Harshe ta fiddo had'i da lasar lip's d'inta na k'asa ,kona ta kura miki Karima?
Kai ta gyada sannan tace nifa takace so bana tunanin akwai abunda zaka mun ya takura mun ,he don't know how zai iya bayyana yanda kalaman ta su kayi ta siri a cikin zuciyar sa ba and sosai yaji sun k'ara saka shi cikin wani yanayi wanda baya tunanin irin haka ta ta'ba faruwa da shi .
Cikin mutuwar jiki ya d'aura hannun sa saman gashin kanta had'i da fara shafa shi , d'ago kanta tayi tana kallon sa , your hair smell so good ya fad'a yana mai had'e fuskar su , me kika sakawa hair naki,ban ta'ba jin yana wannan kamshin ba , cikin inda inda tace baka kula bane amma a kullun haka gashina yake. Ban yadda ba Karima ,ta yaya za kace haka ,bayan gashin nan akaina yake hancin sa ya goga saman tana sannan yace , nafi ki sanin ya gashin ki yake ,so please stop arguing with me, ina matuk'ar kaunar gashin kanki Karima,cikin wani yanayi yayi maganar wanda sosai furucin sa yasa yaji tsikar jikinta ta wani memmike , i love it ya kuma maimaitawa, ada kamshin shampoo yake ,a yanzu fa ta fad'a tana mai kankame jikinta , bai bata ansa ba illa saukar lips d'insa taji saman wuyan ta , kissing wuyanta ya shiga yi, jikinta kyarma yake ahaka tana k'okarin daurewa, Let's go home Karime ya fad'a cikin wani yanayi, saurin komawa mazauanin ta tayi ,kansa ya d'aura saman stairing mota, d'an satar kallon sa tayi, ajiyar zuciya yake lokaci zuwa lokaci, after like 10 minutes d'ago kansa yayi had'i da mi'ka mata hannu alamun tazo , matsawa tayi kanta a k'asa sosai yanayin yasa ta jin wata irin kunyar mijin Sa'ada ko nace mijin Karime lol......
Had'a ta da jikinsa yayi ba tareda yace komai ba ya fara driving ,shuru tayi tana mai jin wani sabon nishadi ,a haka yake driving d'in har suka isa gida.
Bayan yayi parking,fitowa yayi had'i da k'okarin ansa kiran daya shugo wayar sa,Hjy Karime kuwa zaman ta tayi , juyowa yayi da zimmar cewa ta shiga cikin gida,wayam babu Karime k'ofar motar ya bud'e had'i da saurin tura kansa ,zaune take hankali kwance, d'an rufe speaker phone d'in yayi had'i da cewa ki shiga cikin gida zan biyo bayan ki if na idasa ,Ummm ta furta tana mai shagwabe fuska, ,i will call you back Alia ,Alia ta furta had'i da tamke fuska, zama yayi tareda shafa fuskar ta ,ko bakya son nisa da mijin ki ne shuru ta masa , hannun sa ya d'aura saman tummy d'inta ko kina jin yunwa ne zun'buro baki tayi sannan tace ce maka akayi bana da aiki sai cin abinci, murmushi yayi sannan yace Hmm akwai takeaway na abinci dana siyo mana jin furucin sa tuni taji yawu ya tarar mata a baki , but tunowa da maganar sa akan babu abun data iya sai cin abinci yasa tace naci abinci gidan Jummai ,ohhh ya furta yana wani murmushi , then mijin ki kike jira koh Karima ?
Turo baki tayi sannan tace kayi wayar ka nina tafi ,da haka bud'e mota tayi tareda ficewa , d'an murmushi yayi had'i da d'aukar takeaway d'in dake bayan motarsa ,kiran sunan ta yayi takeaway d'in ya mi'ka mata tareda cewa ki shiga ciki ina zuwa tamke fuska yayi tareda cewa bana buk'atar wani abinci a yanzu , ringing wayarsa ta kuma yi ganin yanda ta zura masa ido ne yasa ya mi'ka mata wayar please ki shigar mun da ita ,ina zuwa ana kiranka ka fa ta fad'a lokacin daya mi'ko mata wayar , i will call her back,da haka motar ya nufa , d'an siriren tsaki taja had'i da banka ma wayar harara. Kayan d'inkin tane yabi wajen friend d'insa ya anso mata tunda ya taho ta take binsa da kallo da nauyi koh tace dashi lokacin daya k'araso inda take, ji take kaman ta rage masa kayan hannun sa but tunowa da maganar Jummai akan mace y'ar gayu ce da hutu yasa ta d'aure,yau baki taya mijin ki d'aukar kayan ba ,ya fad'a cikin alamun zolaya , shagwabe fuska tayi sannan tace nifa mace ce ina naga k'arfin d'aukar abu mai nauyi haka,kallon mamaki ya bita da shi domin dai idan zai iya tunawa Karime bata jin wahalar d'aukar abu mai nauyi,satar kallon sa tayi lura da yanda ya fad'a duniyar tunani yasa tayi saurin cewa zan d'auka mijin Sa'ada murmushi yayi had'i da cewa na koma mijin Sa'ada kuma ,naga few minutes ago mijin ki kika ce mun ai kai d'in mijin mune nida ita , d'an murmushi yayi had'i da fara tafiya , ajiyar zuciya Karime tayi had'i da dukan bakinta da hannu ,da gaskiya Jummai da tace ba lokaci d'aya zata canza ba if tace zata canza behaviours nata lokaci d'aya za yayi saurin ganewa.
Even though ana son hakan but dole ayi abun cikin tsari,bayan ta dawo duniya tunani bin bayan sa tayi tana mai cewa Allah ka kawo na d'aukar maka. Cikin gida ya shige yana mai cewa No yayi miki nauyi, time d'in data idasa cikin living room baya nan da mamaki tace Mijin Sa'ada,ansa mata yayi da here jin muryar sa cikin bedroom d'in ta yasa tayi saurin nufar bedroom d'in ,kayan dake cikin jakar daya shugo daga motarsa yake fiddowa ,cikin mamaki Karime tace wai kayan d'inki nane juyowa yayi fuska a sake ya shafa fuskar ta sannan yace yes da haka cigaba da arranging nasu yayi cikin wardrobe nata ajiye tarkacen hannun ta tayi had'i da d'aukar wani lace a jikinta ta d'aura gwon d'in murmushi ta saki , cikin yanayin jan hankali tace wow tayi mun kyau matuk'a,da kallo ya bita fuskar sa d'auke da murmushi, ko zaki trying nasu a jikin ki ,yes ta bashi ansa cikin farinciki, ok ya furta yana mai zagayowa inda take mayafin jikinta ya cire , k'asa tayi da kanta cikin inda inda tace bari naje bedroom naka na canzo a can , yatsan sa ya d'aura saman lips d'inta shhhhhhhhh ya furta yana mai binta da wani irin kallo, k'asa tayi da kanta zuciyar tana dukan ukku ukku,cikin natsuwa ya d'aura hannun sa saman kafad'un ta zare gwon d'in jikinta yayi idanuwa ya saki yana mai binta da kallo, white inner wears n a jikinta, tsaye take a sandare kaman zombie,jin saukar hannun sa saman bra d'inta yasa ta sami courage d'in cewa Mijin Sa'ada zan iya sakawa da kaina cikin sarkewar murya tayi maganar d'an murmushi yayi had'i sadda kansa dai dai kunnen ta he whispered softly and slowly let me please,sosai hakan ya haddasa mata shiga wani yanayi, d'ago kansa yayi yana mai sakin murmushi, sosai ya sami kansa cikin tsananin farinciki, jan hannun ta yayi zuwa bed ,sosai ta fara tsorata da lamarin Mijin Sa'ada, lura da yanda yanayin kallon sa ya fara canzawa yasa ta fara k'okarin magana,he didn't let speak ,Shhhhhh Karima ,let me da haka had'e bakinsu yayi , kissing nata ya shiga yi as he pinned her down on the bed,sosai ya shiga yi mata wasu abubuwa, ta tsorata matuk'a,kuka ta saka masa ,jin sautin kukan ta yasa ya dakata da abunda yake yi rungume ta jikinsa yayi he is surprised akan yanda yake zama affected by her sam baya gane shi d'in wanene idan yana tareda ita ,he can't help his desires whenever he is with her still kuka take hakanne yasa ya tashi zaune had'i da jawota jikinsa tana fuskantar sa , kukan na menene Ummm , kasa d'ago kanta tayi, d'ago fuskar tata tayi saurin lumshe idanuwan ta tayi d'an murmushi yayi sannan yace kin d'auka aure wasane ,daga just few minutes ago kika gama seducing nawa and here you are an miki abunda kike so , instead kiyi mun godiya shine kika bud'e baki kina mun kuka , d'ago kanta tayi tana kallon sa as their eyes looked on each other, kunya ce ta rufe ta saurin shiga jikinsa tayi d'an murmushi Ramadan d'in yayi sosai yake mamakin kansa akan yarinyar nan.
After some minutes of silence, d'ago ta daga jikinsa yayi still idanuwan ta a rufe suke , d'an murmushi yayi had'i da sauka daga saman bed d'in, toilet ya, nufa after some minutes fitowa yayi ba tareda yayi magana ba d'aukar ta yayi zuwa toilet ,sauran suturar jikinta ya cire kasa magana tayi sosai take jin kunyar mijin Sa'ada,sakata cikin kwamin wanka yayi ,kanta a k'asa ya rad'a mata kiyi wanka ,da haka ficewa yayi zuwa bedroom d'in ta ,cigaba da arranging kayanta yayi cikin wardrobe,bayan ya kammala tsaf ya kyara mata bed d'inta domin duk sun hargitsa shi .
A bangaren Karima kuwa jin shuru babu alamun motsin sa yasa ta bud'e idanuwan ta, dafe saitin zuciyar ta tayi ,kome ta tuna oho murmushi ta saki had'i da saurin rufe fuskar ta.
Lokacin data fito baya cikin bedroom d'in,a gurguje ta shirya domin yunwa take ji sosai , bedroom d'insa ta nufa cikin daurewa , tsaye ta tattarar dashi bakin mirror alamu sun suna wanka ya fito kanta a k'asa tace zan kwanta ,bai bata ansa ba illa shirinsa da yaci ba ganin haka jiki a mace da bar bedroom d'insa,kasa cin abincin tayi ,ta dad'e zaune saman bed ganin ba sarki sai Allah yasa ta tashi domin ta cika tunbin ta , kitchen ta nufa ajiye takeaway d'in yake d'aya ta d'auka tareda juyewa cikin plate ,cikin sauri ta nufi bedroom d'inta domin bata son su had'u, bayan ta kyara cikin ta ajiyar zuciya ta saki sosai ta shiga damuwa akan fushin Mijin Sa'ada,ta gaji matuk'a sabida haka kashe hasken d'akin tayi tareda rufe idanuwan ta koda bacci zai d'auke ta .
A bangaren Ramadan kuwa haushin kansa yake ji akan yanda yake kasa kama kansa a gaban ta ya sani duk abunda za tayi bata yin sa intentionally duba da bata wayewa akan wannan harkar ajiyar zuciya yayi had'i da kwanciya ,baki d'aya bacci ya kaurace masa cikin wani yanayi ya tashi zaune bedside table ya bud'e photo album d'insu shida Sa'ada ya fiddo , pictures d'in yake kallo na mai jin wani zafin rashin mace mai hak'uri juriya da kawaici , tun kafun Sa'ada ta sami gurbi a zuciyar sa ta aminta dashi ,a duk lokacin da yayi ra'ayin ta'ba bayada shakku ya sani ba kowace mace bace zata iya lamuntar wani namiji daya rinka ta'ba ta if babu soyayya tsakanin su but Sa'ada taba ta'ba nuna masa bata so ba yana ta'ba ta duk da lokacin yana tare da Alia , but Karima bata iya jure hakan bata iya jure yana ta'ba duba da ba sonsa take sa ,ya kasa gane dalilin yasa jikinsa ke matuk'ar son kasancewa da Karime wanda a yanda ya fahimta ita hakan baya gabanta ,he is in pain a yanzu missing Sa'ada ya dawo masa sabo .
Lumshe idanuwan sa yayi tareda furta ina missing naki Sa'ada, a bangaren Karime kuwa
Ganin ta kasa bacci ne yasa ta nufi d'akin sa even though wani side na zuciyar ta tsoron hakan yake but ta kasa hana kanta ,kallo d'aya tayi masa ta gane tabbas yana cikin damuwa and ta sani ita ce sila , dafa shi tayi bud'e idanuwan sa yayi tareda kafeta dasu k'asa tayi da kanta hannu yasa tareda ture hannun nata tashi yayi had'i da janta zuwa k'ofa,turata waje yayi had'i da rufe k'ofar da k'arfi , knocking k'ofar ta shiga yi Dan Allah ka bud'e mun mijin Sa'ada d'an Allah ,banza yayi da ita bashewa da kuka tayi yau taga ta kanta meta jawowa kanta , kuka take wiwi .
After like 10 minutes bud'e k'ofar yayi had'i da komawa saman bed shugowa tayi still kuka take ,rage hasken d'akin yayi tareda kwanciyar sa , jiki a mace ta nufi bed d'in hawa tayi tareda kwanciyar daf dashi ganin still fushi yake yasa ta k'ara volume d'in kukanta, tashi zaune yayi seeing how tears flowing from her eyes yasa d'an sassauta fushin sa he gazed at her and then he cupped her face da hannuwan sa and then wiped hawayen fuskar ta da tafin hannun sa, it's ok Karima kukan ya isa hakanan ,magana take son yi but kukan yaci k'arfin ta , stop crying Karima please he begged ,ka yafe mun laifin dana maka Dan Allah mijin Sa'ada,he just pulled her in his embrace without saying a word.
Dan Allah ta kuma furta dago kanta yayi tana fuskantar sa ,ya wuce Karime baki yi mun laifin komai na sai yanzu na gane bai kamata naji haushin ki ba duba da babu soyayya tsakanin mu ,bana sonki Karima haka zalika kema bakya sona , lumshe idanuwan ta tayi tana mai jin radadin zancen sa wai baya son ta , Sa'ada ce kad'ai ta amince mun da hakan duk da a lokacin bana sonta and shuru yayi for some sec sannan yace and i don't know why I'm so bold akan ki Karima . Kallon sa tayi hawaye shabe shabe akan fuskar ta ,bata iya describing halin da zuciyar ta take ,sake goge hawayen fuskar ta yayi let's sleep my wife, da haka janta yayi zuwa jikinsa , kwanciya su kayi babu mai iya cewa kamoi , da haka bacci barawa yayi awon gaba da su.
Monday
Ya riga ta tashi tsura mata na mujiya yayi yana mai tuno scenarios d'in jiya, d'an murmushi yayi tunowa da mafarkin sa ,tuni ya kama fahintar how affected jikinsa yake akan Karima, duba da yanda tazo masa a mafarkin sa , idan bai karya ba yesterday night was the first night daya sami kansa da wet dreams ,all because of Karime , ganin ta d'an motsane yasa ya zare jikinsa slowly baya son tada ta duba ba da da d'an sauran lokaci a kira sallah Subh .
Wanka yayi had'i da tayarda sallah, bayan ya idar ne ta bud'e idanuwan ta , tozali da fuskar tayi zaune yake saman darduma yana karantun littafi mai girma , k'asa k'asa yake karatun Qur'an domin baya son tayar da ita , sosai take binsa da kallo ajiyar zuciya tayi tana mai tuno kalaman sa na jiya ,bayan ya ajiya Qur'an d'in kallon side d'in da take yayi had'a ido zu kayi saurin janye nata tayi had'i da cewa ka tashi lafiya .
Lafiya ya ansa atakaice , zan je masallaci da haka ficewa yayi jiki babu kwari ta sauko daga saman bed d'in,room d'in ta ta nufa acan ta watsa wanka had'i da kabbara salla.
A bangaren Ramadan kuwa bayan sun idar da sallar sashen Momy ya nufa , yau kuma flat d'in Momy za'a cewar Sadiq cikin sakin fuska,banza Ramadan d'in yayi dashi domin haryanzu haushin sa yake ji ,sosai Sadiq yayi danasanin yiwa d'an uwan nas magana.Bayan sun gaisa da Momy cewa yayi please Momy ki fad'awa Abba yau,ba zan sami tsayawa breakfast ba nida Karima, lafiya dai cewar Momy ,Eh zan kaita school ne tayi registration ,wane school kuma Momy ta fad'a da mamaki akan fuskar ta Alqalam University ,dama tayi karatune ? Eh Momyna tayi karatun that's why nake son tayi joining University,Masha Allah ka kyauta Allah ya bada sa'a Ameen Ramadan ya ansa yana mai ficewa.
Bazan yadda Hjy Mariya ta san cewa Karima ta shiga makaranta ba ,dole na sami hanyar boye hakan domin nasan halin Hjy Mariya ba kyau ne da ita ba ,na gama wahala b'atawa yara kan wata banza , sosai Momy taji maganar Abba akan rage shiga cikin rayuwar auren yaranta and this time around she is ready ta b'ata da Hjy Mariya akan farincikin yaran ta .
Bayan ta kammala gyaran gidan had'i da saka turaren wuta mai kamshin dadi' bedroom ta nufa domin watsa ruwa , lumshe idanuwan sa yayi jin yanda kamshi ke tashi , yunwa yake ji matuk'a wannan dalilin ne yasa ya nufi kitchen domin kirka abun da za yaci.
Fridge ya bud'e had'i da d'auko fish cikin minutes kad'an ya gama sarrafa shi ,juyewa yayi cikin foodflask, k'okarin fita yake Karime ce ta fad'o masa a rai hakanne yasa ya ajiye kayan hannun sa tareda bud'e fridge for the second time kaza ya d'auka had'i da fara gyarata bayan ya kammala soya kazar kaman yanda ya soya kifin sa ,ficewa yayi zuwa dining table jejjera komai yayi kafun ya kuma komawa kitchen d'in gyara kitchen d'in yayi .
Bedroom d'in Karima ya nufa bayan yayi knocking k'ofar tasayaw yayi yana mai jiran a bashi izini ,tunda taji knocking k'ofar sa ta d'an ji dama dama but ga mamakin ta bai shugo ba , hakanne yasa ta nufi k'ofa bud'ewa tayi had'i da gashe dashi cikin yanayin tsoro da kuma shakkar Mijin Sa'ada. Bai ansa ba illa cewa yayi ki same ni a dining da haka gaba yayi abunsa,ta shiga damuwa matuk'a da dukkan alamu mijin Sa'ada still fushi yake da ita ,jiki a mace tabi bayan sa ,kujera yaja mata bayan ta zauna serving nata yayi , Bismillah yayi had'i da fara cin breakfast d'insa.
Ba tada za'bi daya wuce ta fara yin breakfast d'in,shuru kake ji babu mai magana cikin su bayan ya kammala breakfast d'insa mi'kewa yayi had'i nufar bedroom d'in sa , hawayen da take boyewa ne suka sulalo saman fuskar ta ,tashi tayi tareda d'auke abubuwan da su kayi amfani dasu , kitchen ta nufa jiki na kwari ,bayan ta kammala gyaran komai d'akin sa ta nufa , karatun Qur'an yake , tsaye tayi nesa dashi saida ya kai aya sannan yace kina buk'atar wani abu?
Kai ta gyada alamun aaa,ki shirya by 8:00 zamu fita toh ta ansa tana mai juyawa zuwa bedroom d'inta.
Karatun ya cigaba shi kansa baya jin dad'in wannan yanayin da suka sami kansu sai dai hakan shine dai dai baya son taking advantage d'inta duba da ya fahimci yanda gangar jikinsa ke yaudarar sa akan Karime .Tayi jugum tayi tana mai sakawa da warwarewa akan yanda zata shawo kan mijin Sa'ada. Tunowa da yace zasu fita yasa ta ajiye damuwar for now , shiryawa ta shiga yi ,ta rasa wane kaya ya kamata ta saka kwana 2 ya shagwaba ta wajen fitar mata da kayan sawa , jiki ba kwari ta nufi bedroom d'in, ya gama shiryawa kenan ta shugo ,koma kiyi sallama ya fad'a cikin d'aure fuska, jiki na kyarma ta koma had'i da yin sallama ansawa yayi yana mai tsare ta da idanuwa , inda inda ta kama ta tsorata matuk'a, what do you want,ya fad'a yana mai k'ara kafeta da idanuwan sa masu rikita mata lissafi .
Dama na rasa kayan sakawa ne, kije bedroom naki ina zuwa ,saurin ficewa tayi har tana had'e k'afa, d'an murmushi yayi domim ta matuk'ar bashi dariya, majewa yayi had'i da bin bayan ta , zaune ya tarar da ita da rafka tagumi,zare tafin hannun ta yayi daga saman fuskar ta , wardrobe d'inta ya nufa ba tareda b'ata lokaci ba ya fiddo mata lace d'in jiya wand tayi trying, mayafi yayi choosing mata wanda ya shiga da lace d'in,ajiye mata yayi saman bed, juyawa yayi zuwa ma'ajjn bags d'inta jaka ya d'auko mata had'i da flat shoe kalar jakar.
Ki same ni flat d'in Dada da haka ficewa yayi da idanuwa ra raka shi har ya bace mata da gani.
A sashen Dada kuwa , da gudu Little tayo kan Mahaifin ta my princess ya fad'a yana mai d'aga ta sama , Dady ina Momyna ? Shafa fuskar Sa'ada yayi cikin sakin fuska yace babu gaisuwa my little Sa'ada, good morning Dady morning my dear ya fad'a yana mai ajiye ta k'asa,rage tsawon sa yayi had'i da kama kunnuwan sa I'm very sorry my princess for yesterday,washe baki little Sa'ada tayi sannan tace aina yafe maka tun jiya , dagaske my daughter ya fad'a cikin sakin fuska kai ta gyada sannan tace Dada tace kai da Momy kun yi mun yawau ne a jiya because kuna son tafiya sawo mun baby ,zaro idanuwa yayi yana mai kallon Dada wacce ke zaune d'an nesa dasu 40 Rabbana ne a hannun ta ,a yanzu baya mamakin Dada domin tuni ya fahimci yanda tsohuwar sam bata jin kunyar sakin wasu maganganun, Dady ina Momyna ina son ganin Babyn da kuka siyo , suna cikin haka Karima tayi sallama rugawa little tayi had'i da rungume Karime, Momy ina babyn ?
Baby Karime ta furta tana mai saurin kallon Ramadan , Aaaa Karime barka da zuwa cewar Dada wacce ta katse azkar d'in safinta jin Karime ta shugo.
Kai kuwa ka bata wuri ta zauna cewar Dada tana mai kallon Ramadan ,Dada ba zama za muyi ba gaba muka ci cewar Ramadan , Karime ya jikin naki ,Dada ta fad'a cikin sakin fuska, da mamaki Karime tace Dada aini lafiya na qlau .
Aaa kina son ce mun babu abunda ke damun ki Dada ta fad'a cikin rage fara'ar fuskar ta, eh Dada cewar Karime tana mai sadda kanta k'asa,jiya nayi tunanin ko asibiti kuka je ,munje barka gidan kanwata Jummai ohhhh cewar Dada cikin wani sabon nishadi, kice mun saura ke in sha Allah, kasa bama Dada ansa Karime tayi domin abun yafi k'arfin ta .
Dada sai mun dawo ko Ramadan ya fad'a yana mai k'okarin fita ,kai dakata ina kuma zaka ana fira mai matuk'ar mahimmanci, Dada please sauri nake ya fad'a yana mai kallon Dada kaman mai shirin kuka, wallahi na fad'a ma, ka dai hanzar ta domin idan kai baka buk'atar wasu y'an y'an ni ina buk'ata ganin naka yaran , bayan haka Sa'adatu nata buk'atar y'an uwa , bai bata ansa ba illa saurin ficewa da yayi.
Karime kuwa k'okarin bin bayan sa take Dada ce ke kuma na dawo kanki ,washe baki Karima tayi sannan tace Dada nayi laifi ,rufe mun baki mace kaman ba mace ba , yaushe za kiyi hankali , shuru Karime tayi ganin da gaske ran Dada ya b'aci , babu mai laifi sai ke ,ina amfani Dada ta fad'a cikin fushi .
Dada kiyi hak'uri dan Allah cewar Karime, d'an sakin rai Dada tayi sannan tace Karime bakya zazzabi ko tara yawu bana yi Karime ta fad'a kai tsaye, bakya jin tashin zuciya ,eh Karime ta fad'a,,wannan ba maganar sauri bace maza jeki yana jira , ma cigaba idan kika dawo .
Bankwan nayi musu cikin sauri ta nufi sashen su ,"tana shiga yana kunno kai da motar sa ganin ya tsaya yasa tayi saurin nufar inda yake , bud'e motar yayi ta ciga shiga tayi tareda sakin ajiyar zuciya, kallon ta yayi kaman zai ce wani abu sai kuma yayi shuru.
Daga gida direct company suka wuce,cikin girmamawa maikatan sake gaishe da Ramadan ansa musu yayi kaman yanda ya saba,,,, sosai tsari da kyawon company d'in ya burge ta,,, yana gaba tana take masa baya suka isa office d'insa ,a kujera ya nuna mata akan ta zauna , yasan dole ta gaji sabida stairs da su kayi amfani dashi duk da akwai lift a company d'in kawai yaso suyi amfani da stairs d'in.
Zaunawa tayi kaman yanda ya buk'ata, system d'in office d'insa ya bud'e had'i da cigaba da latse latse , bayan 30 minutes ,ficewa yayi daga office d'in, bata kuma ganin saba sai after 1 hour , bud'e k'ofar office d'in yayi had'i da cewa muje , saurin tashi tayi ,kara kallon office d'in tayi for the last time ta sani daga yau kuma bata tunanin ,zata kuma samun damar zuwa office nasa.
Baki Karime ta saki tana mai kallon school d'insu ko a mafarki b'ata ta'ba tunanin shiga Alqalam University ba ,Amma yau gata a cikin ta a matsayin student, lura da yanda take farinciki yasa yace ,ina son ki mayarda hankali sosai akan karatun ki ,in sha Allah ta furta cikin farinciki .
Da taimakon friend d'insa aka mata komai kasancewar private University ce shiyasa suka bata admission ba tareda Jamb ba but zata kawo Jamb kafin ta kammala school d'in.
Bakin wata super market yayi parking ,yaushe ake sunan kanwar ki? Jibi ta bashi ansa , ficewa yayi daga motar da kallo ta bishi sosai zuciyar ta ke mata ciwo akan fushin Mijin Sa'ada, after some minutes dawowa yayi d'auke da wasu ledoji k'ofar baya ya bud'e had'i da ajiye kayan daya siyo,key yayi wa mota zuwa Batagarawa wato garin su Jummai tafiya bata kai ta 9 minutes ba.
After Magrib zan dawo d'aukar ki ,hannu yasa had'i da d'aukar bag d'inta daga saman cinyar ta kud'i ya saka sannan yace ki zama cikin shiri don bana son ana bata mun lokaci, kai ta gyada tareda cewa na gode bud'e motar tayi shima haka ,kayan daya siyo ya mi'ka mata sannan yace ki bama kanwar da haka mota ya koma tareda ficewa daga layin su Jummai.
Shiga gidan tayi jiki a mace, cikin farinciki Jummai ta tare ta , bayan sun zauna kwashe duk abunda ya faru tsakanin tada mijin Sa'ada tayi ta fad'awa Jummai idasa maganar tayi shuru Jummai tana mai tunani abun cewa ,wane dalili gare ki akan hanasa ta'ba jikin ki a matsayin ki na matarsa, Jummai bana son wani abu ya shiga tsakanin mu ,akan me Karima wane dalili gare ki akan hakan , sabida mijin Sa'ada baya sona ,amma nayu tunanin mun wuce wannan zancen cewar Jummai ta yaya ,zaki mayarda hannun agogo baya ,kiyi hak'uri Karima duk tsanani yana tareda sau'ki bayan haka, bana tunanin Mijin ki zai wuce gona da irin duba da labarin da kika bani akan yanda soyayar sa da Sa'ada ta fara , kibi komai a sannu , fushi yake dani ,dole yayi fushi dake duba da yanda kike treating nasa kaman ba mijin ki ba sosai Jummai ta kwantar mata da hankali akan subi komai a sannu .
Haka Ramadan ya shiga ga share Karima , tuni Rumaisa ta fahimci hakan ita ma dai sosai ya kwantar wa Karima hankali akan tayi hak'uri da sannu komai zai zama tarihi.
3 weeks kenan da canzawar mijin Sa'ada sosai damuwa ta nuna tareda Karima domin duk ta canza bata walwala ,yau ta kama Thursday zaune ta tarar da Mijin Sa'ada, system yake latsawa hankali kwance, d'an nesa dashi ta tsaya,cikin yanayin tsoron sa tace Dan Allah ina son zuwa gidan Jummai babyn bata ji dadi' ba a dawo lafiya ya fad'a ba tareda ya kalle ta ba wane kaya zan saka ta fad'a tana mai sadda kanta k'asa.
Duk wanda yayiwa ranka ki sosai furucin sa ya tada mata hankali duba da bai ta'ba mata haka ba duk da baya sakar mata fuska shine mai choosing mata kaya but ya fad'a mata ba'kar magana.
Ficewa tayi zuwa bedroom d'inta saida ta sha kukan ta kafun ta fitar da wata atamfa halb bubu da straight skirt, mayafi ta saka tareda ficewa , tafiya take kaman wacce aka zarewa lakka , ta gabata yayi parking motarsa Sauke glass d'in motar yay had'i da kiran sunan ta , takawa tayi zuwa gare shi ,key yayi wa mota ba tareda ko wanen su yayi wa d'an uwansa magana ba .
Bayan yayi parking cewa yayi by 5:00 yan zo d'aukar ki toh ta ansa tana mai ficewa , da kallo ya bita har ta shige gida.
Parking yayi gefen titi kansa ya d'aura saman stairing mota ,yau d'innan sosai rashin jituwar sa da Karima ke damun sa karar shugowar sms a phone d'in sa ne yasa ya d'aga kansa had'i da duba wayar zaro idanuwa waje yayi mota key zuwa company.....
Kasancewar yau Monday sosai maikatan company suka zo aiki duba da yanda aiki ya ta sosu gaba , parking space ya nufa bayan yayi parking,saurin fitowa yayi, ainafin building d'in ya dosa cikin sauri sauri , company ne na gani na fad'a,tsarin company d'in kad'ai zai bayyana maka cewa nera tayi kuka , private lift d'insu ya nufa ,in a couple of minutes ya isa office d'in Sadiq ,saurin tashi P.A. d'in Sadiq tayi good morning sir ,bai ansa gaisuwar taba illa cewa yayi where're is Sadiq , office d'in ta nuna masa shigewa yayi had'i da banko k'ofa, ajiyar zuciya Tina ta saki domin tasan yau akwai drama .
He is seating comfortably saman sofa, hot coffee ne a hannun sa jin an banko k'ofa yasa ya d'an saki murmushi,fad'owa cikin office d'in Ramadan yayi,ganin yayo kansa kaman zai duke sa yasa yayi saurin ajiye hot coffee d'insa, k'okarin shigewa toilet yake saurin cafke shi Ramadan yayi ,wai menene haka cewar Sadiq ?
Jansa yayi zuwa sofa,seat ya furta yana mai had'e fuska, Bayan Sadiq ya zauna alert d'in da aka turo masa ya nunawa Sadiq what is the meaning of this?
Murmushi Sadiq yayi sannan yace kasan cewa dai this company belongs to two of us ,so bana buk'atar ansa maka tambayar ka , k'ara tamke fuska Ramadan yayi ba k'aramin k'okari Sadiq yayi wajen ri'ke dariyar sa ,kana son ce mun kowa ya kama gaban sa ,yes hakan nake nufi , d'an murmushi Ramadan yayi sannan yace fine ,tashi Sadiq yayi had'i da d'auko wasu papers i have already signed the documents , signature naka kad'ai ya rage ,ba tareda Ramadan yace komai ba ya anshi papers d'in sign yayi tareda jifar Sadiq da papers d'in juyawa yayi zai fita Ramadan Sadiq ya kira sunan sa ba tareda ya juyo ba yace i don't want to hear anything from you, April fool Sadiq ya fad'a cikin wata irin dariya, murmushi Ramadan yayi had'i da bin Sadiq ,guje guje suka fara kaman wasu yara , Ramadan ne ya fara zama sai uban haki yake ,Sadiq kuwa dariya ya ke ,i swear Sadiq you will pay for this.
Bana iya jure fushin ka ,and kai kaman jira kake mu sami sab'ani ka cigaba da shareni , d'an murmushi Ramadan yayi sannan yace do you have to scared me , kasan cewa komai na tara, komai na zama, ba zan ta'ba samun sukuni ba har sai idan kana tare dani . Murmushi Sadiq yayi sannan yace ,had it been ban maka haka ba ,i swear shareni za kayi ,Hmm kayi nasara a yanzu but i have to punish you for this , please don't punish your other half wata kya'kyawar murya ta fad'a saurin juyawa Sadiq kayi Alia Sadiq cewar Sadiq , murmushi kya'kyawar balarabiyar tayi had'i da saurin k'arasowa , Ramadan kuwa lumshe idanuwan sa yayi ba tareda yace komai ba , rungume Sadiq tayi had'i da cewa miss you Twiny ,miss you too ya fad'a yana mai zareta daga jikinsa.
Zama tayi daf da Ramadan ganin haka yasa Sadiq ficewa , waya ya d'aga jikina kyarma ya kira Rumaisa fad'a mata yayi Alia ta wanzu , cikin tashin hankali ta kira number Karime.
Tunda Rumaisa ta fad'a mata wannan sa'kon tashin hankali, toilet Karime ta fad'a, after some minutes fitowa tayi tareda kwanciya saman sofa,wai me aka fad'a miki a waya Jummai ta tambaya cikin mamaki Alia ta dawo yanzu haka suna tare , tana idasa maganar ta kuma komawa toilet domin tunda Rumaisa ta fad'a mata dawowar Alia cikin ta ya kad'a.
A bangaren Ramadan kuwa zare hannun Alia yayi daga jikinsa , tashi yayi tareda k'okarin fita rungume shi ta baya tayi had'i da saka kuka , ta san weakness d'insa baya son kuka most especially kukan mace ,juyowa yayi tareda cewa it's ok Alia menene abun kuka kuma daga isowar ki .
Ba kai bane Alia ta fad'a cikin shagwaba d'an murmushi yayi sannan yace me nayi kuma Alia murmushi tayi had'i da shiga jikinsa , rungume shi tayi sosai kasa d'aura hannun sa saman jikinta yayi please hug me back Alia ta fad'a cikin yanayin jan hankali, slowly ya fara matsar da hannun sa saman jikinta lumshe idanuwan ta tayi jin saukar hannun sa a jikinta.
After some sec kyara murya yayi had'i da zare ta daga jikinsa , shagwabe fuska tayi sannan tace please muje ka raka ni ,zuwa ina ya fad'a fuska ba yabo ba fallasa, please ta kuma fad'awa tana mai k'ara shige masa, sauri ja baya yayi had'i da cewa ok muje kama hannun sa tayi muje koh , zare hannun sa yayi tareda saurin ficewa, is not simple as it seems ta furta tana mai bin bayan sa .
A mota kuwa , music Alia ta kunna tana mai shafa dogon gashin kanta, bai ce da ita komai ba hankalin sa na kan driving d'insa
Can you please stop driving? Da mamaki yace why ?
Please Alia ta kuma cewa ,ok ya furta yana mai parking gefen titi please close your eyes ta furta cikin yanayin jan hankali, shuru yayi yana kallon ta daga bisani rufe idanuwan sa yayi, saukar lips d'inta yaji saman nasa saurin janye fuskar sa yayi had'i da cewa menene haka Alia ,cikin yanayin fad'a yayi maganar, kuka ta saka masa why are treating me like this ,sai hantara na kake tunda nazo please stop crying Alia , i want to kiss you Ramadan , please let me ta fad'a cikin yanayin kuka , babu kyau Alia abubuwan da suka faru a baya tsakanin mu bana tunanin idan zasu kuma faruwa try to understand me , aure fa za muyi ta fad'a tana mai tallafo fuskar sa , please i have been dreaming akan kissing naka please let me , Alia please bata bari ya idasa maganar ba ta kuma had'e bakinsu , this time around bai hanata ba .
A bangaren Karime kuwa kwance take saman sofa gidan Jummai, dan a yanzu jikinta is very weak duba da yanda lokaci d'aya, cikin ta ya kad'a, Karime ki kira mijin ki muje hospital kin ga ciwon nan yaci k'arfin ki .
D'aukar wayar Karime Jummai tayi tareda kiran number sa har kiran ya katse ba ayi picking ba sake kira tayi still ba ayi picking ba , k'arya tayiwa Karime cewa is not reachable.
Tun tana sa ran zuwan mijin Sa'ada har ta cire rai domin har dare yayi .
Yau sosai suka sha yawo cikin garin Katsina , around 9:30 na dare suna hanya fira suke shida Alia daf da zasu shiga G.R A Karime ta fad'o mas a rai ,cikin sauri yayi reverse lafiya Alia ta fad'a da mamaki bai bata ansa ba illa speed daya k'ara ,cikin lokaci kan kane ya isa k'ofar gidan Jummai, wayarsa ya d'auka sosai yayi mamaki da yaga missed calls d'in Karime , kiran number ta yayi Jummai ce ta d'aga tareda fad'a masa Karime bata lafiya ba zata iya fitowa ba , cikin tashin hankali ya fice ,Alia kuwa bud'e mota tayi tareda........,.....
Mu had'u next page