CHAPTER 1.
by @1239900
ZAWARAH.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️
PAGE 1.
Wani irin gudu motar su ke shararawa a saman titi kamar za ta tashi sama. A daidai wannan lokacin kuwa Yunus dake zaune a bayan mota yana buga tsaki ya ɗaga hannunsa ya sake duba agogon hannunsa tare da jan wani dogon tsakin a karo na babu adadi. Cikin ransa yake jin kamar ya karɓi tuƙin motar ya ratsa ta lunguna ko Allah zai sa ya yi saurin isa gida da wuri domin ya samu sallar juma'a akan lokaci. A ƙagauce ya kalli Malam Sadi direba ya ce.
"Man Sadi ko za mu yanki wannan layin ne mu tsaya kawai mu yi sallahr mu a masallacin Shaikh Shu'aib; domin na kula idan muka ce sai mun je gida lokaci zai ƙure mu rasa sallar juma'ar gaba ɗayanta."
Jinjina kai direban ya yi ya ce.
"To Alhaji duk yanda ka ce ayi ai haka za a yi."
Cikin abinda bai fi mintuna biyar ba Malam Sadi ya kutsa kan motarsu cikin babban layin dake unguwar Gadon Ƙaya yana fatan su isa da wuri dan su samu sallah akan lokaci. Sun yi nisa da tafiya ya hango cincirindon mutane a gabansu wanda da damar mutanen wajen yara ne suka fi yawa a wajen. Tsaki direban ya ja ya ce.
"Nan kuma ko taron me ake yi haka suka tare wa mutane hanya oho?"
A ƙagauce ya hau danna horn ɗin motar dan taron ya watse su samu su wuce,amma ga mamakinsa ko gezau yaran nan basu yi ba ballantana su basu hanya,wasu yaran ya hango daga lunguna da saƙon unguwar suna sake fitowa suna leƙen tsakiyar taron. Kafin ya ce wani abu Yunus da ya gaji da jira ya ce.
"Je ka ka leƙa ka ga me yake faruwa Please dan na ji har an gama khudba."
Da sauri Malam Sadi ya kashe motar ya buɗe ƙofa ya fita har yana haɗa wa da gudu. Yana isa wajen taron sai ya dinga leƙa wa yana janye yaran dake ta leƙe suna faɗin.
"Ku casu arna ku casu,ku casu ba mai raba ku,duk wanda ya raba faɗan Nansy Ƙaya tamkar ya raba auren tsohonsa da tsohuwarsa ne."
Yana isa tsakiyar filin ya ci karo da wata yarinya fara wadda ba za ta wuce shekaru sha uku zuwa sha huɗu ba a duniya,yarinyar tana da matsakaicin tsawo da girman jiki. Zaune take a saman wani bokiti tana zane a ƙasa kamar babu abinda ya dame ta a gidan duniya. A gefenta na hagu kuwa wata ƙatuwar yarinya ce wadda za ta girme mata tsaye tana cika tana batsewa tare da faɗin.
"Kin ga dai na ce miki ki ɗaga min bokitina na tafi gida jirana ake yi ko?"
Kai yarinyar dake zaune a saman bokitin ta ɗaga tana zabga wa ƙatuwar dake girgiza ƙugu harara ta ce.
"Ai na faɗa miki idan kina da ƙarfi to ki yi amfani da shi ki ɗaga ni sama ki ɗauki bokitinki. Sai dai da dikkan alamu kurin banza da cika baki kawai kika iya."
Malam Sadi na shirin yiwa yaran magana Yunus da ya gaji da jiransa ya biyo bayansa sai ya kama hannunsa tare da girgiza masa kai. Kafin su juya su bar wajen yarinyar nan dake zaune saman bokiti ta yi kukan kura ta kwashe ƙafar ƙatuwar nan ta zubar da ita a ƙasa;sannan ta bi ta ta zauna a ruwan cikinta tana duka kamar an aiko ta. Nan take yaran dake wajen suka kaure da ihu da sowa suna faɗin.
"Da kyau Nansy Ƙaya sa ƙato kuka;mata da sun ganki su ɓuya a bayan uwarsu."
Jinjina kai kawai matashin nan ya yi suka koma wajen da motar su take suka yi parking a gefe sannan suka ratse taron yaran suka nufi masallacin a ƙafa. Suna isa liman na tada kabbara,dan haka babu ɓata lokaci suka shige masallaci suka shiga cikin sahu.
Bayan sun idar da sallah sai suka zauna suka yi azkar sannan Yunus ya fito waje domin ya saka takalminsa su wuce. Ta gabansa Nansy Ƙaya ta zo za ta wuce ita da ƙawayenta tana basu labarin yanda ta yi wa Nabila Bultuƙa dukan tsiya. Yaran sai yaba mata suke yi suna jin daɗin yanda ta zane yarinyar da kowa ke jin matsanancin tsoronta a kaf layin da ma sauran unguwannin dake kusa da su. Babu zato babu tsammani ya ji muryar Nansy tana faɗin.
"Ke dalla wannan ɗin ne kyakkyawa? Ba dan kar na rantse Allah ya saka ni a wuta ba da sai na ce Luƙman ɗina ya fi sa kyau."
Dariya sauran yaran suka fashe da ita,cikin dariya ɗaya daga cikinsu ta ce.
"Ashe dai kin san ƙarya kika yi,shi yasa kike tsoron kada Allah Ya saka ki a wuta."
Juyawa ta yi cikin sa'a idanuwanta suka shiga cikin na Yunus dake kallonsu yana murmushi. Cikin sauri Nansy ta ɗauke idanuwanta daga nashi tana haki tare da tattare zaninta ta kwasa da gudu ta sha kwanar layin dake kusa da inda suke. Nan take Yunus ya fashe da dariya mai sauti ya kalli Malam Sadi ya ce.
"Mu je ko?"
Gaba ya yi Malam Sadi na biye da shi yana mamakin sauyawar uban gidan nasa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Ko da suka isa wajen motarsu sai suka ga an yi rubutu a jikin motarsu cikin salon haɗe manyan baƙi cikin ƙananan baƙi an rubuta.
"MoTar NaNSy ƙAyA."
Ran Malam Sadi a ɓace ya kalli mai gidan nasa ya ce.
"In Allah Ya yarda wannan ja'irar yarinyar ce da suka yi dambe ɗazu ta yi wannan aika-aikar."
Murmushi Yunus ya yi ya shafi jikin rubutun ya furta.
"Nansy Ƙaya."
A hankali,sannan Ya kalli Malam Sadi ya ce.
"Mu je ko?"
Ba tare da Malam Sadi ya sake furta komai ba ya shiga motar yana cin alwashin ko a hanya ya sake ganin yarinyar,sai ya yi mata shegen duka. Motar su na barin layin fuskar Yunus ta sauya daga farinciki zuwa ƙunci da damuwa. Ta madubi Malam Sadi ya hango uban gidan nasa,cikin sanyin murya ya ce.
"Ranka ya daɗe ko dai na kai ka gidanka kawai ka huta?"
Murmushin yaƙe Yunus ya yi ya ce.
"Ah ah,kai ni gida na gana da ƴan'uwana."
Kai kawai Malam Sadi ya jinjina ya ɗauki hanyar gidan Gwani Ibrahim Yunus Gombe.
*****************
A guje Nansy ta shiga gidansu kamar wadda aka koro ta da makamai. Tana zuwa tsakar gidan ta ci karo da bokiti cike da ruwa,ba tare da tunanin komai ba ta ɗauki bokitin tare da ƙarasawa ƙofar ɗakinsu ta ɗauki kwandon wanka ta faɗa. Tun tana cire tufafinta take jin wani irin sululin azaba a wuyanta. Tana gama tuɓe kaya ta duƙa ta kindimi ruwa da kofin wanka ta kwara tun daga saman fuskarta ya sauka har zuwa ƙafafuwanta da suka yi fururu. Ƙara ta saki saboda azabar zafin da ta ji a lokacin da ruwan ya sauka a dokin wuyanta da ya sha yaƙushi. Ƙwafa ta yi tare da cin alwashin wannan faɗa babu mai kashe shi har sai ta daki Bultuƙa dukan da zai wanke mata zafin ciwon da ta ji mata a wuya. A gaggauce ta gama wankanta ta fito tsakar gida tana sheƙa dariya kamar mahaukaciya. Babu abinda take tuna wa sai lokacin da ta cika bakin abokiyar dambenta da ƙasa,ga kuma jini yana zuba da yawu mai yauƙi. Da ta kai mata sabon naushi sai ta ce.
"Nansy ki bariii,kin ga dai aike na aka yi bana son faɗa ban shirya baaa."
Tana tsaka da dariya ta ji an sakar mata ƙoso a tsakiyar kai. Da sauri ta dafe wajen ta juya a fusace tana huci kamar kububuwa. Cikin tsananin ɓacin rai Yah Hauwa ta ce.
"Ke dan ubanki wa ya ce ki ɗaukar min ruwan wanka na ki yi amfani da shi? Ko an faɗa miki uwarki ce ta ɗebo min ruwan?"
Baki Nansy ta murguɗa cike da tsantsar rashin kunya ta kalli babbar yayar tasu ta ce.
"Ko uwata bata ɗebo ruwa ta ajiye ba;ai a bokitinta aka ajiye ruwan,ni na ce mutum ya baro ɗakin aurensa ya zo gidan mutane yana aron kayansu?"
Baki Yah Hauwa ta saki tana kallon Nansy, domin kuwa duk gidan suna shakkarta saboda ita ce babba,daga ita sai Lawizah,Sabirah da Hanifah,sannan Rabi da Usman ƴaran ɗakin Kilishi. Nasibah wato Nansy Ƙaya ita ce babba a ɗakinsu,sai ƙannenta mata biyu Faihah da Najlah. Cike da jin takaicin rashin kunyar da Nansy ta yi mata cikin zafin nama ta yi kanta a guje za ta dake ta. Sai dai kafin ta kama ta har ta isa ɗakinsu ta rufe ƙofa ta danne tana dariya. Cike da takaici Yah Hauwa ta tsaya tana haki a tsakar gidan ta ce.
"Ai sai dai idan yau ba za ki fito tsakar gidan nan ba Nasibah. Ke har kin isa ki min laifi in yi magana ki yi min rashin kunya? To ko uwarki bata isa ba ballantana ke."
Daga can cikin ɗaki Nansy ta ɗaga murya ta ce.
"Yah Hauwa na faɗa miki idan muna abunmu ki dena sako uwata a ciki ba kya ji ko?"
"Kan uban can kayyasa! Ni kike faɗawa haka Nasibah? Na rantse da...."
"To bismillahi,me yake faruwa ne ake ta hayaniya a gidan?"
Kafin Yah Hauwa ta yi magana,Malam Sanda Uba Makaɗi;wanda mutane ke kiransa da Makaɗi ya durƙusa ya ɗauki buta ya shiga banɗaki. Nasibah kuwa na jin muryar mahaifinta sai ta buɗe ƙofa ta fito tana karkaɗa ƙugu tana kallon Yah Hauwa tana ɓaɓɓata rai. Makaɗi na fitowa daga banɗaki ya ce.
"Ke Hauwa menene haka kike wani cika kina batsewa kamar za ki fashe iye?"
Tura baki gaba Yah Hauwa ta yi,sannan ta ce.
"Baba ka shiga tsakanina da wannan yarinyar,idan ba haka ba zan karya ta na nakasa shegiya a banza."
Cikin sauri Nansy ta kalli Baban nasu ta kyaɓe baki tana wani irin kuka,kai da ka ji kukan ka san na tsantsar makirci ne. Nan take Makaɗi ya ɓata rai ya kalli Yah Hauwa ya ce.
"A gabana kike sheganta min ƴa Hauwa? Ke wai me yasa notikan kan ki ba sa aiki ne? Ki dube ki shirgegiya kamar bajimin Sa amma ki tsaya kina faɗa da ƴar cikinki,da Allah Ya kawo rabo da wuri ai da kin aje kamarta. Amma da yake ke ba cikakken hankali gare ki ba shine kika biye mata kuke faɗa. Ni bana son jin me ya haɗa faɗan ki kama gabanki ki koma ƙofar ɗakin tsohuwarki,tunda kin dage ke ba zaki rabu da wancan direban ba,to ga wajen zama nan,duk lokacin da ya gama zagaya duniyar ya dawo sai ya kwashe ki ku yi gaba."
Cikin sauri Nansy ta kalli mahaifinsu ta ce.
"Kuma Baba ɗazu sai da su Lawal suka zo gidan nan,baka ga yanda suka dinga cin abinci ba har da zubarwa suka yi,da na yi musu magana Yah Hauwa ta kai min duka,ka ga inda ta ji min ciwooo a wuya na. Yiiiiiii."
Nasibah ta ƙarasa maganarta tana mai rushe wa da kukan zogi da raɗaɗin da ciwon wuyanta ke yi mata. A hasale Malam Sanda ya yi kan Yah Hauwa ya na surfa mata zagi tare da cin mutunci kamar ba shi ne ya haife ta ba. Cikin tsananin fushi ya ƙarasa maganganunsa da faɗin.
"Ah toh,kin dai ji na faɗa miki,ko ki biya abincin da shegun yaranku suka cinye min,ko kuma na ja Allah Ya isa."
Kuka mai matuƙar cin rai ne ya ƙwace wa Yah Hauwa. Cikin matsanancin kuka ta kalli Nansy ta kasa cewa komai,sannan ta juya ta kalli mahaifinta dake ci gaba da zagi da aibata mata yaranta kamar ba ƴaƴan sunnah ba. Da gudu ta bar wajen ta nufi ɗakinsu ta hau haɗa kayanta. Ta na gamawa ta zira doguwar rigarta ta saka hijabi ta fito tsakar gida. A tsaye ta tarar da Babansu yana shafa wa Nasibah rob a wuyanta,ita kuma sai wani kukan shagwaɓa take yi tana tsalle. Kilishi da takaicin su Nasibah da mahaifinta ya kai mata ko ina sai ta dinga aiki tana wurgi da kwanuka tare da habaici. Cike da takaici da baƙinciki Yah Hauwa ta kalle su ta ce.
"Baba ka yi haƙuri ka yafe wa su Lawal abincinka da suka ci yau,da yardar Allah ko bangon duniya Habu zai je neman kuɗi ba zan sake zuwa gidan nan ba. Allah Ya jiƙan Innani,da tana raye na tabbata ba za ka yi min haka ba."
Cikin matsanancin kuka ta bar gidan tana fyace majina. Jikin Malam Sanda ne ya yi mugun sanyi,sai ya sakar wa Nansy rob ɗin ya shige ɗakin Kilishi domin ita ce ke da girki a wannan ranar. Yana shiga ciki Nansy ta faɗa ɗakinsu ta samu gefen gadon da mahaifiyarta ke kwance tana baccin rana ta zauna tana ƙunshe dariya.
A can tsakar gida kuwa tuni gidan ya ci gaba da hayaniyar shige da ficen yara. Kilishi da ta cika ta yi fam saboda takaicin yanda mijin nasu yake fifita Nasibah akan duka yaran gidan,sai ta ɗauki abincinsa ta shiga ɗakin babu ko sallama ta dangwarar masa ta fito tana ƙunƙuni. Shiru Makaɗi ya yi yana tunawa da uwar gidansa da ta rasu sakamakon jinyar cancer ta mama da ta sha. Cike da jimamin abinda ya aikata wa Hauwa ya zamo bakin gado ya buɗe abincin nasa ya hau tsakura yana ci kamar baya so.
Sallamar wasu mata ne ta ja hankalin mutanen gidan gaba ɗayansu. Kallon gidan suka hau yi kafin ɗaya daga cikinsu ta buɗe baki ta ce.
"Nan ne gidan su Nansy Ƙaya?"
Kilishi dake cike da takaicin Nansy a cikin ranta,sai ta buɗi baki ta ce.
"Tunda kuka shigo har tsakiyar gida kuka kama suna ai kun san kun zo inda kuke nema ko?"
Chewing gum ɗin bakinta matar ta tauna sannan ta ce.
"Ok. Ina ita Nansyn take?"
Nansy dake ƙunshe a ɗaki a jikin labule tana leƙen matan sai ta ji hanjin cikinta na kaɗawa,nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta. Cikin ranta take ayyana.
'Me waɗannan Hajiyoyin matan suka zo yi a gidanmu ni Nasibah?'....