FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Ya Allah ka bani ikon aiki da baiwar da ka bani ta rubutu yanda ya dace, Allah ka amfanar dani da al'ummar Annabi Muhammad da wannan baiwa. Ameen.
Sample · CHAPTER 1.
ZAWARAH.NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 1.Wani irin gudu motar su ke shararawa a saman titi kamar za ta tashi sama. A daidai wannan lokacin kuwa Yunus dake zaune a bayan mota yana buga tsaki ya ɗaga hannunsa ya sake duba agogon hannunsa tare da jan wani dogon tsakin a karo na babu adadi. Cikin ransa yake jin kamar ya karɓi tuƙin motar ya ratsa ta lunguna ko Allah zai sa ya yi saurin isa gida da wuri domin ya samu sallar juma'a akan lokaci. A ƙagauce ya kalli Malam Sadi direba ya ce."Man Sadi ko za mu yanki wannan layin ne mu tsaya kawai mu yi sallahr mu a masallacin Shaikh Shu'aib; domin na kula idan muka ce sai mun je gida lokaci zai ƙure mu rasa sallar juma'ar gaba ɗayanta."Jinjina kai direban ya yi ya ce."To Alhaji duk yanda ka ce ayi ai haka za a yi."Cikin abinda bai fi mintuna biyar ba Malam Sadi ya kutsa kan motarsu cikin babban layin dake unguwar Gadon Ƙaya yan...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.