Nikaah marriage for rent 16
by @hanaady
NIKAAH
(Marriage for Rent)
By
HANAADY
Rahama Aminu Bal
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
Page 16
____bai yi mamakin rashin ganin Alia a falon ba sabida haka bedroom d'insa ya nufa ,sosai lokaci yaja after ya gama shiryawa ficewa yayi zuwa masjid domin gabatar da sallar Azhar, Hjy Karime kuwa da murmushi tabi bayan sa tuwana da maganar sa tayi akan wai tafi Alia kyau saurin rufe fuskar ta tayi da tafin hannun ta alamun kunya .
A bangaren Alia kuwa direct part d'in Momy ta nufa ,zaune ta tarar da Momy karatun Qur'an mai girma,a cikin phone d'inta "
domin tunda December ta doso sam bata da walwala ko sukuni akan halinda Ramadan yake samun kansa .
Fad'awa jikinta Alia tayi had'i da saka kuka ,lafiya Momy ta fad'a tana mai ajiye wayar hannun ta Momy Ramadan baya ta'ba kauna na waye ya fad'a miki cewar Momy labarin abunda ya faru Alia ta kwashe ta fad'awa Momy d'an murmushi Momy tayi sannan tace baki ji labari a hospital ta kwana ba eh Momy ai tare muka kai ta ,kin san kuwa dukan tsiya ya mata a daren jiya shine ta gudu zuwa gidan yayar ta ,bayan taje gidan yar uwar tata shine ciwon ya bigeta nice ma na nemi alfarmar ya kaita hospital, shuru Alia tayi tana mai sauraren zancen Momy , Momy yaushe Ramadan ya fara dukan mace a iya sanina shi d'in mutunen mai tsananin tausayi, murmushi Momy tayi sannan tace for sure yana da matuk'ar tausayi sai dai me baya d'aukar shashanci and ita Karime babu abunda ta iya sai shashen ci ,
Murmushi Alia tayi sannan tace wow Momy gaskiya naji dad'in wannan labari naki d'an murmushi Momy tayi domin tuni ta gane weakness d'in Alia and yanzu da Karime take d'auke da cikin Ramadan dole tayi duk yanda za tayi domin tayi protecting babyn da kuma mahaifiyar sa that's why a yanzu dole ta san hanyoyin da za tabi domin canza tunanin Alia duba Alia shashace, unlike mahaifiyar ta wato Hjy Maria she is very smart.
Kin ga kuwa da dan tana fama da rashin lafiya ai da tuni na kirata tayi mun aikin gida,aikin gida kuma Momy cewar Alia da mamaki eh mana bata fad'a miki cewa tana cikin masu mana hidima a gida,shuru Alia tayi na wasu y'an sec sannan tace but Momy naga fa ya damu da ita matuk'a, murmushi Momy tayi sannan tace har yanzu baki gane inda ya dosa ba ai duk abunda Ramadan zai yiwa Karime a gaban ki yana yine dan ya hukunta ki akan rashin amince masa da baki yiba daga farko , Momy kina tunanin zaya soni kuwa ?
Sosai ma Alia ke dai biki komai a hankali, murmushi Alia tayi sannan tace dama gobe nake shirin fara zuwa aiki a company,zaro idanuwa waje Momy sannan tace haba Alia ai kya bari ki hutu kafun ki fara tunani wani aiki ,No Momy ina son kasancewa dashi ne , d'an kyaran murya Momy tayi sannan tace kice zaku na hadewa da Karime a can kaman ya Alia ta fad'a d'an yatsina fuska Momy tayi sannan tace ai acan take aiki matsayin cleaner na office d'insa ,kin san halin sa baya son kowa ya masa gyara that's why Sadiq ya d'auke ta tana share masa office da sauran goge goge ,shuru Alia tayi tana mai karantar Momy sosai Momy tasha jinin jikinta ga mamakin ta dariya Alia ta saka sannan tace zan so ganin ta ta y'an goge goge a company murmushi Momy ta saki had'i da sakin boyayyiyar ajiyar zuciya.
Matsiyaciya har office d'ina ita zata ri'ka share mun shi d'an murmushi Momy ta saki , bankwana Alia tayiwa Momy murna fal a cikin ranta , tabbas ta gazgata maganar Momy domin farkon auren Ramadan da Sa'ada haka ya ri'ka mata sosai yake yaba Sa'ada a gabanta ko kuma ya rungume ta dan taji haushi, murmushi ta saki gaskiya Momy ta taimaka mata da ta ankarar da ita .
Alia na fita jikina kyarma Momy ta kira number Sadiq ,bai d'aga ba sake kira tayi still ba'a d'aga ba urgently take son magana dashi .
Mayafi Momy ta fizga zuwa part nasu ,bayan sun gaisa cikin inda inda Rumaisa tace aikuwa baya nan , please ki fad'a masa ya same ni sashena ok Momy, har Momy ta kai bak'in k'ofa dawowa tayi sannan tace maganar Alia ki fad'a masa idan ta tambaye shi wai Karime na aiki a office a matsayin cleaner kice nace ya ansa mata da eh ,cikin mamakin furucin Momy Rumaisa tace in sha Allah Momy ,ficewa Momy tayi,sosai abun ya daurewa Rumaisa kai.
Aikuwa Sadiq na dawowa Rumaisa ta zayyana masa sa'kon Momy, sosai yayi mamaki baiyi k'asa a kwaiwa ba ya kira Momy,bayani tayi masa akan lallai tana ya d'auki Karime aiki a company nasu cikin office d'in Ramadan ,Momy bana tunanin akwai buk'atar ta ,rufe mun baki kayi abunda nace katse kiran Momy tayi cikin fushi.
Kayi abunda take so nasan tana da manufa akan hakan ,Beb yarinyar nan fa makaranta take zuwa , please kada ka damu dole nasan suna da free time
Shuru Rumaisa tayi na wasu y'an sec sannan tace baka san cewa she is pregnant ba , dariya Sadiq ya saka da Kallon mamaki Rumaisa ta bishi ki yadda kenan sosaima kuwa Hmmm ba zan ta'ba yadda cewa Karime nada ciki why ka fad'i haka ?
Because na san waye Ramadan ,amma dai kasan ance mata da miji sai Allah, ba zan miki gaddama ba but Ramadan ba zai ta'ba kusantar macen da baya so ba kana son ce mun Ramadan baya son Karima, murmushi Sadiq yayi sannan yace yana sonta so na musamman saidai me har yanzu bai gazgata hakan ba ,Karime na d'auke da cikin Ramadan cewar Rumaisa with confidence.
maganar Ramadan ya d'auki Karime aiki matsayin cleaner menene dalilin Momy , ni a ganina tayi ne domin su kasance tare ko wane lokaci a office da kuma gida ,zan aikata abunda take so .
Ina mamaki akan wai baya ta'ba kusantar macen da baya so, da Kallo Sadiq yabi Rumaisa sosai ya bata dukkan natsuwar sa, abunda nake nufi shine let's say baya ta'ba jin soyayyar Karime and the were destined to be together a haka za suyi ta rayuwa ,shuru Sadiq yayi na wasu y'an da'ki'kai sannan yace , maganar ki maganar dubawa ce saida me bana tunanin zai aikata hakan, Ramadan bai ta'ba son wata ba kaman Alia , but soyayyar da yake wa Sa'ada akwai abubuwan mamaki a cikin ta sometimes i used to wonder akan irin haukan da yake kan Sa'ada and abun mamakin shine ba suyi 18 month tare ba , ajiyar zuciya Rumaisa tayi sannan tace koma dai menene Allah yayi mana jagora, Ameen cewar Sadiq.
Ina matu'kar tausayin Karime Rumaisa ta fad'a tana mai kallon Sadiq akan me kenan halinda Ramadan zai shiga kwana goma masu zuwa,da kuma yanayin da zaya jefa ta let's hope for cigaba Rumaisa cewar Sadiq bana tunanin Ramadan zaya aikata abunda yake tun bayan mutuwar Sa'ada a kowane month of December duba da akwai hope akan soyayyar Karime cikin ransa,Allah yasa hakan Rumaisa ta fad'a.
A bangaren Ramadan kuwa bai dawo gida ba sai around 4:00 sosai ya kwaso gajiya kasancewar daga duba wani site yake wanda ana bukatar sa a wajen and ya kira phone d'in Sadiq not reachable bedroom d'insa ya nufa bai bi ta kan Karime ba because ta kira shi akan zata shashen Dada,a can ya shirya , after ya shirya kitchen ya nufa kaman yanda ta fad'a yau tayi masa girki , murmushi yayi after ya bud'e food flask d'in abincin ya dauka zuwa dining,after ya kammala cin abunci bedroom ya nufa domin daukar phone d'insa tafiya yake yana mai tuna shirmen Karimen sa
after ya dauki wayar kokarin fita yake yana son zuwa shashen Dada wajen Karimen sa'karar wani sauti ne yaja hankalin sa kallon wajen yake tareda jan legs d'insa zuwa inda sound d'in yake ,rage tsawonsa yayi tareda bud'e bedside table kaman mai tsoron wani abu wani box ya dauko bud'e box d'in yayi had'i da fiddo wata kyakykyawar agogo white colour, Sa'ada ya furta tareda saurin zama saman carpet ,,dafe saitin zuciyar sa yayi had'i da lumshe idanuwan sa ,kina raina Sa'ada bakya mantuwa, promise me ba zaka kuma tayarda hankalin ka akan jarabawar da Allah ya maka ba , maganar Mahaifin sa ce ke masa yawo a brain saurin tashi yayi tareda nufar bathroom fuskar sa ya wanke had'i da ficewa zuwa islamiyya a canne yake samun peace if ya zauna gida tabbas dole ya shiga damuwa mai tsanani.
A bangaren Karime kuwa, sashen Dada ta yini ,mi'kewa tayi tana Shirin fita , ina zuwa Karima d'an murmushi tayi sannan tace Dada ina son zuwa islamiyya ne , kina buk'atar ki hutu Karime kinga ba lafiya ne dake ba , zan iya Dada , a dawo lafiya amma ban da sauri kinga yanzu bake kad'ai bace k'asa tayi da kanta tareda ce in sha Allah zan kiyaye.
Yana cikin koyarwa phone d'insa ta kawo haske alamun kira ko sa'ko kasancewar silent ya saka ta,idanuwa Zuby ta saka masa sosai yau yayi mata kyau cikin kananu Kaya blue black shirt da brown trouser, bai bita kan wayar ba har saida ya kai aya, ajiyar zuciya Alia tayi sannan tace finally, kana ina gani a cikin Islamiyya, ina ina class,ok on my way katse kiran yayi had'i da tattara kayan sa ficewa yayi zuwa office nasa , yayi kyau matuk'a cewar Zuby kije ki fad'a masa hakan mana Mimi na fad'a a hasale,dan ta fara gajiya da haukan kawarta akan wanda bai san tana yi ba.
Cikin office d'insa ya tarar da ita k'okarin rungume shi take da hannu yayi mata alama akan ta tsaya sofa ya nuna masa sosai ranta ya sosu akan dizga ta da yayi ,shi kuwa ko a jikin sa ,zama yayi nesa da ita I'm so sorry Alia ta fad'a, k'afa d'aya kan d'aya yace about?
Abunda ya faru ta'be baki yayi sannan yace ban gane ba sosai take jin shakkar sa yanzu tabbas ta lura wannan ba Ramadan d'in da tayi tarayya ada bane even though ada d'inma yana da wuyar sha'ani but yanzu komai nasa ya canza kyawunsa ya fito had'i da haibar sa .
Akan bedroom d'in matarka dana shiga without permission, d'an ta'be baki yayi sannan yace idan da sabo kin saba hakan Alia,kasa cewa komai tayi ,cikin sanyin murya yace it's against our religion and morals mutum ya fad'a muhallin mutane without permissions and the worst part of it gidan aure, sosai take mamakin furucin sa ,duba da bayan auren sa da Sa'ada bata da shamaki da gidan sa including bedroom d'insa,maganar Momy ta tuna akan duk abunda Ramadan keyi yana yine domin ta because yana son ganin kishin sa a eyes d'inta , ajiyar zuciya ta saki had'i da cewa zan kiyaye.
Dafe kansa yayi ,are you ok?
Alia ta fad'a tana mai daura hannun ta saman nasa ,janye hannun sa yayi had'i da resting kansa saman sofa , kasancewar kujeru ne masu matu'kar kyau a office nasu,lumshe idanuwan sa yayi zubama fuskar sa eyes tayi ,ya gane tana kallon sa hakanne yasa ya bud'e idanunsa tareda kyara zaman sa Sam baya son kallo, d'an murmushi Alia tayi tareda fara masa fira .
A bangaren Hjy Karime kuwa yau Sadiq ne a class nasu bayani yake musu akan ahadhari hukunce hukuncen tsarki da abubuwan dake karya alawala bayan ya idar ficewa yayi da gudu tabi bayan sa, daf da zai bud'e k'ofar office nasa ta iso ,cikin sakin fuska yace matar Yaya k'asa tayi da kanta sannan tace Allah abubuwan daka koya mana su nada wahalar ganewa bayan haka duk na zama confused
,littafin hannun ta ya ansa Page's d'in da su kayi yayi folding,idan kin koma Ramadan ya miki bayani ya iya ne Karime ta fad'a dariya Sadiq ya shiga yi daga office nasa ya fara jiyo dariya Sadiq had'i da muryar mace duk da ita ba'a jin muryar tata sosai, iya sanin sa da Sadiq duk son matan sa baya kula na islamiyya toh yau kuma ya hakan ta faru,
yanzu abunda za'ayi kin ga a gajiye nake duba da na sha hayani mu shiga ciki sai nayi miki bayani tunda baki yadda mijin naki ya iya ba bin bayan sa tayi kujera ya nuna mata zama tayi had'i da bin office d'in da Kallo fridge ya bud'e had'i da d'aukar ruwan roba ,fira Alia ke masa but hankalin sa ya rabu gida biyu,, kasa samun natsuwa yayi ina zuwa ya fad'a had'i da ficewa ,
jikinsa har kyarma yake office d'in Sadiq ya nufa babu sallama ya fad'a kasancewar k'ofar ba a rufe take ba ,arba yayi da fuskar Karime,wani malalacin murmushi Sadiq yayi sannan yace aa Sadiq ashe ka shugo harara Ramadan ya banka masa saurin k'arasowa Sadiq yayi sannan yace Karime kin gaishe da Sadiq kuwa d'aga kai tayi tana kallon su ta fahimci Sadiq tsokanar Ramadan yake , kallon Ramadan tayi sannan tace ina wuni sosai mamaki ya bayyana akan fuskar sa iya sanin sa Karime tana gane su ko dan suturar jikinsu ta d'an yi shige .
Had'e kira yayi ba tareda yace komai ba,robar ruwan da Sadiq ke sha ya bama Karime ansa tayi tareda cewa na gode mijin Sa'ada, ganin tana k'okarin kai robar a bakinta yasa Ramadan saurin anshe robar ruwan jifar Sadiq yayi da ita had'i da banka masa harara, dariya Sadiq ya saka tareda kallon Karime
muje koh tashi tayi tana mai k'okarin bin Sadiq wanda ya nufi k'ofar fita ,kasa hak'uri Ramadan yayi hannun yasa had'i da tura Sadiq waje rufe k'ofar office d'insa yayi had'i da banka mata wata uwar harara , fuskewa tayi tana mai nufar k'ofa , please ka bani key na fita kai wane irin kannen Mijin ne
ohhoo so you are still pretending d'ago kai tayi tana kallon sa ,baki ta bud'e da zimmar magana, jawota jikinsa yayi had'i zare hijab d'in jikinta, tsit tayi tana kallon sa zare hairband d'in kanta yayi had'i da saka fuskar sa yana mai shinshinar gashin kanta zuwa wuyan ta , hakan bai masa ba janta yayi zuwa sofa kwantar da ita yayi had'i fara yi mata wasu abubuwa, kasancewar yanzu kome zaya mata hani romance nasu yayi nisa saurin janye jikinsa yayi kaman wanda ya tuna wani abu ko wanda ke tsoron wani abu.
Toilet ya shige ,da kallon mamaki ta bishi a bangaren Ramadan kuwa lumshe idanuwan sa yayi tareda dafe kansa dake masa mugun ciwo,kimtsa jikinta tayi tareda jiran fitowar sa , after like 10 minutes fitowa yayi had'i da cewa muje koh ?
Kai ta gyada tareda saurin bin bayan sa , lokacin ta suka fito tuni an tashi , office d'insa ya nufa ,baiyi mamakin ganin k'ofar a rufe ba domin yasan aikin Sadiq ne, hanya suka d'auka zuwa gida ,alwala ya d'aura tareda fucewa domin gabatar da sallar magrib, a nata bangaren alwala ta d'auro tareda fara gabatar da sallah.
A bangaren Alia kuwa zaman jiran Ramadan take shugowar Sadiq office d'in yasa tace ina Ramadan ,saida ya boye dariyar sa sannan yace he's busy ,busy a office d'inka cikin mamaki tayi maganar,yes he's busy on ibada , ibada ta maimaita yes Sadiq ya bata ansa then ina nan har ya idar ,babu lokacin kammala ibadar nan just mu wuce gida sai ki jira shi acan ,bin bayan Sadiq tayi mamakin fal aranta akan wace ibada Ramadan keyi.
Daf da zai shiga gida yaji muryar ta tsayawa yayi ba tareda ya juyo ba, finally ta furta juyowa yayi had'i da binta da kallo ,baki tafi ba?
Muna tsaka da fira ka fice bud'e baki yayi da niyyar magana saurin katse shi tayi ta hanyar cewa Sadiq ya fad'a mun ibada kake,naso na jira but yace bai san time d'in da zaka idar ba Sadiq ya furta yana mai mamakin hali irinna Sadiq wai ibada yake, you should get going dare nayi magana yake yana mai duba agogon hannunsa, takowa tayi daf dashi saurin jada baya yayi ,can kiss you ta fad'a tana mai nuna kuncin ta,
kallon ta yayi she's not happy nor sad,yanayin ta ya nuna kaman tana cikin damuwa,yes ya furta can cikin makoshi, takowa tayi slowly ta dafa shi ya fita tsawo nesa ba kusa ba sabida haka saida d'an rage tsawonsa yayi kissing d'in kumatun sa tayi had'i da cewa good night love , night ya furta tareda shigewa cikin gida.
Da ido ta bishi har ya bace mata da gani ajiyar zuciya ta saki tareda saurin nufar motar ta ,da tayi parking gaban gidan Sadiq, after ta zaune resting kanta tayi tana mai tuna beautiful moments nasu,ada baya ta'ba barin ta tayi driving da kanta most especially a cikin dare , murmushi tayi tareda shafa lips d'inta rabonda lips d'inta ya ta'ba fatarsa tun ranar data dawo gida Nigeria,kauda tunanin tayi tareda fara driving..
Oum Hamim