21 Nikaah marriage for rent
by @hanaady
NIKAAH
(Rental marriage)
By*
*AUTHOR*
*HANAADY*
*Rahama Aminu Bala*
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
Page 21
A bangaren Karime kuwa,cikin shirts d'in Ramadan ta saka kwanciya tayi tareda lumshe idanuwa kaman mai bacci,in each and every breath nata Ramadan take ji ,she remembers his touch his smile and the way the yake romancing nata ,saurin tashi zaune tayi because she's already arouse ,lafiya cewar Jummai wacce ke zaune tana breastfeeding baby Ayra.
Hmmm ba komai , hankali kwance a yanzu sai ki idasa yi mun bayani akan abunda ya faru , ajiyar zuciya Karime ta saki had'i da idasa yiwa Jummai bayani because d'azu basu samu suka kammala firar suba ,why would he do that to you , hawaye Karime ta fara please stop crying,cikin zubar hawaye tace the worst part of it shine my heart still love him ,even now da muke magana i want to be with him ,i hate him and love love him at the same time,what should i do Jummai ,try your best to control your feelings for him shine abu na farko da zan iya ce miki by tomorrow masan abun yi.
Kiyi bacci please ,bazan iya ba Jummai i want him besides me ,boye mamakin ta tayi sannan yace na fahimce Karima amma a yanzu bamu da mafita da wuce hakuri ,yanda taga rana haka taga dare,kukan zakaru had'i da sauran dabbobi ne ya tayar da ita daga d'an baccin daya fara fizgar ta .
Komai dawo mata yayi sabo ,ta saba tozali da kyakykyawar fuskar sa , ajiyar zuciya ta saki had'i da saukowa daga saman bed ,ficewa tayi zuwa toilet alwala ta d'auro tareda tayar da salla , kallon ta ta mayar kan Jummai dake ta sharbar bacci,ki tashi kiyi sallah Karime ta fad'a tana mai bubbuga Jummai.
Bangaren Momy kuwa number Karime ta kira ,bayan ta ansa hannun Rumaisa ,bayan sun gaisa ne take fad'a mata ta kara ha'kuri akan komai watarana sai labari,yana lafiya Karime ta fad'a cikin jin kunyar Momy, murmushi Momy tayi wanda saida Karime taji sautin sa ,har yanzu bai dawo gida ba Momy ta bata ansa yana ina cewar Karime cikin yanayin tashin hankali?
Kada ki damu yana gidan sa acan yake tarewa duk lokacin da abun ya motsa matsa ,amma zan turo miki address in case,,bana son zaman ki a gida ya wuce sati d'aya zuwa biyu because of Dada ,bana son tasan ta yanda auren ki ya kasance,ko kin fad'a mata?
Aaa Momy ban ta'ba fad'a mata komai ba akan aurena,Allah miki albarka cewar Momy bayan sun yi bankwana karar shugowar sako taji a wayar ta , address d'in ne Mummy ta turo mata , kallon address d'in ta shiga yi , maganar Jummai ce tasa tayi saurin ajiye wayar lafiya kika saka waya a gaba ,ko kiran sane ya shugowa wayar ki?
D'an ta'be baki tayi sannan tace ko d'aya hankalina ba baya jikina ,i can see that Jummai ta fad'a tana mai zama daf da Karime,asha zaman gidan Baba lafiya Karime domin ni dai yau a gidan mijina zan kwana,tafiya za kiyi Jummai cikin yanayin mamaki Karime tayi maganar, tabbas gidana zan koma ina dalili na baro rayuwar ya'nci na dawo ta takura ,kina ganin har mun fara samun sabani da Mama ,akan kawai nace akwai alamomin tambaya akan b'atan Baban Jummai shine fa ta rufe ni da zagi wai idan bazan iya zaman tarbar masu jaje na kama gabana.
Maimuna ta kwalawa kira akan ta kawo mata baby,baki bud'e Karime tabi Jummai da kallon tabbas da gaske take because gani tayi taja bag d'inta had'i da goya baby a bayan ta fuuu ta fice daga d'akin, ajiyar zuciya Karime tayi bata da karfi ko jarumtar bin bayan ta ,ta sani tunda tace tafiya za tayi toh fa ba fashi,kwanciya ta gyara cikin yanayin kad'aici zaman su waje d'aya da Jummai ba k'aramin taimaka mata zai yiba Saida me tunda tayi zuciya ta gudu dole ta sabawa kanta ,and address da Momy ta tura mata bata tunanin zata iya kai kanta inda yake ajiyar zuciya ta tayi tareda lumshe idanuwan ta ,bacci ne sosai cikin idanuwan ta.
Ehun Maman Jummai ne ya tayar da ita bud'e idanuwan ta tayi had'i dafe kanta dake mata ciwo maza tashi ki hura mana wuta tunda dai Maimuna ba lafiya ne da ita ba ,nishi Karime ta saki had'i da cewa yaushe ciwon ya kamata nasan dai garas take kafun na kwanta bacci ,bata bata ansa ba illa ficewa da tayi kara ta jawo had'i da nufar d'akin da Karime take ,maza tashi tunda dai auren naki ya mutu dole kiyi mana moriya , zunburo baki Karime ta shiga yi kafun ta sauko daga saman katifar da take , d'akin Maman ta ,ta nufa zaune ta tarar da ita tana faman gyaran wake , Sa'ada ce gefenta rubutu take ,ina Hauwa cewar Karime bayan ta zauna ,ta tafi talla?
Sa'ada ce mai bata ansa Mama fisabibillah yaushe zaki daina daurawa Hauwa talla , kinsa fa ba wayau ne da ita ba ,kayan Maman Jummai ne Sa'ada ta bata ansa baki Karime ta turo sannan tace wallahi Mama a shirye nake na gyarawa Maman Jummai zama dan wallahi bazan kuma daukar iskancin taba , ajiyar Mama ta saki sannan tace me kike boye mun Karime,cikin rashin fahimta Karime tace ban gane ba ,ina takardar sakin cewar Mama wacce ke kokarin boye damuwar ta , d'an murmushi Karime tayi sannan tace ki yadda da magana ta ,yayi tafiya , k'asar turawa akan lafiyar itace iya gaskiya ta Mama ajiyar zuciya Mama tayi tareda cewa tunda kika zab'i zaman gida dole ki yiwa Maman Jummai abunda take so da haka ficewa Mama tayi siririn tsoki Karime taja tana mai bankawa kofar d'akin Maman Jummai harara .
Yunwa take ji and still tana jin jikinta ba dadi',gadon Maman ta nufa , kwanciya tayi Karima kada Maman Jummai ta shugo fa ,ke yaushe za kiyi hankali da kunya ,bakya jin kunyar kiran sunana gatsau kaman wata tsararki ,dariya Sa'ada ta saka tareda cewa ai abunda muka saba kiran ki kenan Amma duk lokacin da kika haihu zan koma kiran ki da Maman sunan yaron ki harara ta bankawa Sa'ada dadi' na dake baki cika kunya ba Mama duk tabi da daure miki bakya ganin kowa da gashin arziki, shugowar Maimuna d'akin nasu da gudun gaske yasa Karime tamke fuska,lafiya zaki fad'owa mutane d'aki ba sallama,wayar ta ta bata cikin haki tace kiran ki ake tayi ansar wayar Karime tayi cikin sauri ,Maman Adil , picking tayi tareda cewa Anty kina lafiya ?
Ajiyar zuciya Rumaisa ta saki sannan tace dafatan kina lafiya? Alhamdulillah ina samun sau'ki,sosai Rumaisa ta jajanta mata akan abunda ya faru had'i kwantar mata da hankalin akan komai yayi farko akwai karshen sa sallama su kayi akan gobe zata zo Jangefe duba Karimen.
Jin ta take a takure because tunda tazo garin nasu bata fita waje ba da sunan ziyara koh yawo Mama ta kasa ta tsare ,zunbur ta mike had'i da jawo mayafi hanyar fita ta nufa cikin sand'o ina zuwa cewar Mama cikin yanayin daure fuska ,baki Karime ta washe ,zan je gidan su Aisha ne,ki nemi izinin mijinki kafun ki fita magana Mama take hankalin ta kan wutar da take hurawa , number sa ta laluba sosai gabanta ke fad'awa,ba kira zanyi ba ta fad'a cikin zuciyar ta ,danna kira tayi ba tareda sanin taba zaro idanuwa waje tayi had'i da saurin katse kiran.
Wayar ta kanga a kunne magana ta fara kaman haka eh ina lafiya , d'an murmushi tayi sannan tace dama Mama ce tace na tambaye ka akan zan d'an fita makota ,toh in sha Allah,katse kiran tayi tareda kallon Mama yace a gaishe ki da haka ficewa tayi abunta, addu'a take Allah yasa kada ya kula da kiran data masa .
Koda taje gidan su Aisha cikin ta ta gyara kasancewar akwai sabo tsananin su yasa bata ji kunyar tambaya ba bayan ta gyara cikin ta kwanciya tayi tareda lulawa duniyar bacci, kiran Rumaisa ya tayar da ita ,takalmi ta zura tareda saurin ficewa ba sallama ,motar da tayi parking d'an nesa da gidansu ta nufa ,fuska dauke da murmushi Rumaisa ta fito daga motar rungume ta Karime tayi cikin tsananin farincikin ganin Antyn tata ,mu shiga ciki Karime ta fad'a,tare muke Rumaisa ta bata ansa tana mai nuna mota ,Abban Adil Karime ta fad'a cikin gare sautin muryar ta.
Kai Rumaisa ta gyada alamun eh , knocking kofar motar Rumaisa tayi kofar ya turo had'i da fito gaishe shi Karime ta shiga yi ,cikin sakin fuska ya ansa mata kaman yanda ya saba d'an susar kanta tayi sannan tace ina Mijin Sa'ada?Siririn tsoki Sadiq yaja hararar wasa Rumaisa tayi masa , d'an gyaran murya yayi had'i da fito da wayar sa daga aljihun jeans d'insa , d'an daddanna wayar yayi na wasu ya'n sec Karime ya nufa da wayar ,ansa tayi jikina na kyarma kokarin kanga wayar take a kunne a tunanin ta wai Ramadan d'inne akan layin ,kallo za kiyi Sadiq ya fad'a yana mai jin tausayin sa a bangaren Rumaisa ma hakan take sosai take tausayawa Karime .
Ba'a gani sosai ta fad'a haske yayi yawa cewar Rumaisa,mota ya nuna ma Rumaisa da hannun sa hakan yasa tace wa Karime muje cikin mota kya kalla acan zaifi baki washe tabi bayan Rumaisa zuwa cikin mota Sadiq kuwa jingina yayi motar ,video d'in Rumaisa ta mayar daka farko had'i da kai hasken wayar karshe,wani kayataccen wurin shakatawa ne zata iya cewa bata ta'ba ganin mai tsananin tsari da kyawo kaman wannan waje , fuska dauke da murmushi take kallon video d'in,Ramadan ne zaune hankali sana kan tsadaddiyar wayar sa murmushin ta kara fad'ad'a yayi gani tayi fara dago fuskar sa d'an murmushi ya saki ,alamu sun nuna magana ake masa ,ajiye wayar yayi tareda kallon k'asa Alia yace cikin shiga ta alfarma,rage tsawon ta tayi ta hanyar yin kneeling,box ne a hannun ta sosai mamaki ya bayyana akan fuskar sa , bud'e box d'in tayi tareda fito da ring d'in dake ciki marry me ta fad'a kaman mai shirin kuka please don't say no, please Ramadan I love you! please marry me ,kasa magana yayi sai ido daya ke binta dashi please ta kuma murtawa this time around hada hawaye ajiyar zuciya yayi had'i da dafata ..
Tsaye ya tayar da ita cikin alamun rarrashi yace why are you doing this , please ta kuma fad'a wasu hawayen na kuma silalowa daga idanuwan ta ,ok ya furta can cikin makoshi, murmushi ta saki had'i da saurin saka masa ring d'in hugging d'insa tayi tightly,I love you, take furta tana mai kara matse shi cikin jikinta.
Numfashi ta tsayawa yayi cak, jikinta kyarma ya shigayi ganin hakanne yasa Rumaisa saurin dafa kafadar ta,kuka ta saka had'i da hade kanta da kwuiwa sun dau wasu mintuna haka ,idanuwa Rumaisa ta zuba mata sosai take tausaya mata, bud'e kofar motar tayi ,fuuu ta nufi gidan su hannayen ta saman kuncinta , hawayen fuskar ta take faman sharewa , thank God tsakar gidan nasu babu kowa , direct room d'in Maimunatu ta nufa fad'awa tayi saman katifa had'i da saka wani marayan kuka.
Ki mace Rumaisa ta fito daga cikin mota ,Sadiq ta nufa ,ina tsananin tausayin Karime ta fad'a cikin yanayin nuna damuwar ta , ajiyar zuciya yayi hannayen sa cikin aljihun jeans d'insa, after some sec cewa yayi nayi tsammanin hakan and to be honest with you abun ya fara bani tsoro , because Ramadan da kansa ya turo mun video d'in nan on WhatsApp,bana tunanin hakan Rumaisa ta katse shi ,ni dai a ganina Ramadan bazai turo maka video ba ,are you sure?
Cewar Sadiq gaskiya ina tunanin Alia and tayi ne domin tasan tabbas dole Karime tayi arba da ita ,kibi bayan ta please ki kwantar mata da hankali and ki fad'a mata bazan ta'ba sakawa Ramadan ko Alia ido su wulakantata ba ,in sha Allah cewar Rumaisa tana mai nufar gidan su Karime.
Rahama Aminu Bala.