NIKAAH (Marriage for rent)

20 Nikaah marriage for rent

by @hanaady

*NIKAAH* 
                      *Rental*marriage* 

                          *By** 
                     *AUTHOR* 
                    *HANAADY* 
     

*Rahama Aminu Bala* 

HE HAD THE COURAGE 
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?

*BOOK TWO* 

*Page 3* 

*Not edited* 

Ganin yanda duk suka buga uban tagumi yasa ya shiga  tambayar maike faruwa because time d'in da Momy ta kira shi ta fad'a masa cewa wani abu ya faru gidan su Karime,yazo ya kaita ,Maman Jummai tace tayi saurin fashewa da kuka Baban Jummai ne ya b'ata, b'ata Sadiq ya maimaita,Eh cewar Mama ,kunje police station kuwa ansa masa su kayi da aaa then mu kuke jira ku taso muje station d'in,mayafi Jummai ta yafa had'i da daukar akwatin Karime room d'insu tun suna ya'mmata ta kai mata shi .
Tuni su Jummai sun fice ,Mama ce mai fad'in Maman Jummai keya kamata ki bisu ni na tsaya domin masu zuwa jaje ,aradu babu inda zani kawai ki tafi kinsan duk abunda zai had'i ni da ya'n sanda ba sonsa nake ba ,yanzu d'an jarina ya kare a banza ,shuru Mama tayi tana nazarin Maman Jummai,ki wuce suna jira nina zauna gida domin tarbar masu jajanta mana ...
Bin bayan su tayi a gurguje,duk abunda ya kamata ayi anyi Amma babu alamun nasara hakan yasa Karime fad'awa Sadiq sa'kon Hjy Mariya ,sosai yayi mamaki aikuwa baiyi k'asa a kwuiwa ba wajen gayawa ya'n sanda.

"Hjy Mariya na zaune police suka mata sallama tashin hankali ba'a sa masa rana aikuwa tuni suka bankata bayan kanta ,wayar ta aka ansa domin tracking dukkan calls d'in,a iya bincike bayan kiran da tayi wa Baban Jummai babu wani kiran da aka samu dake alaka da bacewar sa ,hakuri aka basu akan su koma gida , ya'n sanda zasu cigaba da bincike ,Sadiq ne yayi bail na Hjy Mariya,akan duk lokacin suke bukatar zaya kawo ta ,koba komai ba ita d'in kawar Momy ce .
Basu dawo gida ba sai 8:00 na dare iya gajiya Karime ta gaji sosai abubuwa suka mata yawa gani irin ciwo da take fama dashi iya daurewa ta daure, bakin biya suka tarar da Maman Jummai,zaune take ta tusa abinci gaba sai uwar loma take kaiwa ,babu wanda ya damu da ita because hali irinna Maman Jummai babu wanda bai san shi cikin su ba 

Sadiq dake bakin kofa ,magana yake wa Karime akan kwana nawa za tayi cikin yanayin dauriya tace baya son ganina ,zan zauna gidanmu har zuwa lokacin da zaya aiko mun da takardar sakina .
Kada kiyi haka Karima ,banida zab'i Abban Adil ,idan na koma gida da zama menene matsatina ,matar Ramadan Sadiq ya fad'a,. murmushin takaici tayi sannan tace,ban kai wannan matsayin ba tukun ,kin riga da kin kai shi a daren jiya k'asa tayi da kanta sosai taji kunyar furucin Sadiq ,sun san komai fa ,karawa yayi da tun ranar da aka daura auren ku kike matarsa ,saidai me a daren diya kika ansa sunan matar Ramadan ko anaso ko ba'a so ,ko yana so ko baya so ke dashi kun rigada kun zama d'aya and aure ke dashi yanzu aka fara,saidai idan ked'in ce ba kya ra'ayi 

cikin zubar hawaye tace ko ina ra'ayi menene amfanin hakan tunda shi wanda nake zaman auren domin shi baya ra'ayi , hakuri shine ribar duniya Karima idan kika saka ha'kuri a tsarin rayuwar duk tsanani duk wahala kice mai nasara daga karshe,sosai maganganun sa su kayi tasiri akan ta ,bazan hani ki zama gidan ku a yanzu ba because kina bukatar hakan,but don't break trust d'in da kika samu wajen Momy kiyi iya kwana kin da kike ganin zaki iya har ki samu ki warware ki dawo gidan Mijin ki , murmushin takaici tayi sannan tace Mijin Sa'ada dai , that's your problem Karime ke da karan kanki baki yadda Ramadan Mijin ki bane,shuru tayi tasan gaskiya ya fad'a mata,duk abunda kika san zaki bukata ki turo mun shi ta WhatsApp domin zaman gidan ya miki dadi',am ok a hakan ma ,sunan Jummai ya kira wacce ke d'an nesa  dasu ,cikin sec ta bayyana , please, zan jira a mota duk abunda kika san zata bukata ki rubuto mun ko Yarona ki bamawa ya kawo mun ansa masa tayi da toh ,mun gode sannu da kokari ,ficewa yayi zuwa motarsa.

Dogon  list Jummai ta rubuta da kanta ta kai masa ,kin rubuta komai cewar Sadiq yana bai bin list d'in da kallo ,sai kayan miya da kuma nama ko kifi, dariya ya saka sannan yace tunda kin rubuta fridge za'a siyo mata su da yawa sai a saka cikin fridge d'in, bankwana ya mata akan ta fad'awa Karime ko min dare zai dawo kawo mata siyayyar.
Jikin baya mata dadi' so take ta watsa amma ganin babu alamun murhu a sunne yasa ta ha'kura because gidan Mijin Sa'ada ya b'ata ta bata iya wanka da ruwan sanyi ko kad'an and koban komai ba tana bukatar ta kuma sakawa  jikinta ruwa.

zafin ciwo had'i da gajiya sun gama ji mata lugulugu ,yanzu haka kwance take tsakiyar d'akisu ko nace tsohon d'aki su ita da Jummai wanda yanzu ,Maimuna ce da Sa'ada ce amfani dashi ,saukin data samu shine Baban Jummai ya d'an kyarawa Maimuna d'aki cikin kud'in daya samu wajen Hjy Mariya, kasancewar Maimuna an fara zama ya'mmata and sosai Maman Jummai ta dora mata guri a cewar ta Maimuna sai mai mota because tafi Jummai nesa ba kusa ba shiya ,ko kad'an Maman Jummai bata wasa da kashe wa Mamaina ya'n kud'in ta .

Wanka nake son yi cewar Karime tana mai d'an cizon lips d'inta na k'asa sabida yanayin da take ji ,bari na hura miki wuta cewar Jummai,saurin rike hannun ta Karime tayi sannan tace bana son sara miki aikin had'a wuta cikin daren nan ,, ringing d'in wayar Karime ne ya katse musu fira ,ina waje,idan ba damuwa zamu iya shugowa cewar Sadiq,ba damuwa Karime ta bashi ansa,bayan kiran ya yanke ,Yayan sane wai zai shugo,cikin azama 
Jummai ta nufi waje,kayane nike nike Sadiq ya shugo dasu ,tare yake da wasu maza suma d'in kayane suka zudo, Jummai ce mai nuna musu inda zasu ajiye kayan,sannu da kokari cewar Karime d'an murmushi Sadiq yayi sannan yace kada ki damu matar Yaya kud'in Mijin kine ,muna godiya Jummai ta fad'a tana mai kallon kayan ,gyaran murya Sadiq yayi sannan yace kiyi zaman ki a gida har sai lokacin da kika ji zuciyar ki ta amince da komawa gidan Ramadan,duk abunda kika san babu anan ki fad'a mun in sha Allah gobe komai zai zama ready ,tana kusan komai ka siyo cewar Jummai saidai me d'akin da za tayi amfani dashi wutar d'akin nada matsala ,babu damuwa gobe in sha Allah zan zo da mai gyara ,godiya Jummai tayi masa ,matar Yaya zan wuce cewar Sadiq Allah ya baki lafiya ya kuma saka miki da alkairi,ina miki godiya ne on behalf of Ramadan,bata bashi ansa ba illa cewa da tayi agaishe da Anty ,za taji da haka bankwana tayi musu.

Saurin fad'owa tsakar gidan Maman Jummai tayi kayan da Sadiq ya siyo ta fara bi da ido had'i da sakin salati yanzu Karime dan rashin imani hada su fridgeee kika sa aka kawo miki wato baki iya sam ruwa babu sanyi ,haba Babar mu wai yaushe zaki daina shiga abunda babu ruwanki a ciki ,cikin yanayin jin haushin uwar tata Jummai ke magana ,nice da kaina na rubuta duk abunda nasan zata bukata a zaman ta gidannan,Yoo auren nata baya mutu ba cewar Maman Jummai ya mutu Jummai ta bata ansa cikin gatse dariya Maman Jummai ta saka sannan tace abu yazo da sauki kenan me kike nufi da hakan cewar Jummai cikin yanayin tuhuma ,banza Maman Jummai tayi da ,kayana ta shiga dubawa ,Jummai da kanta ta fara jidar kayan zuwa d'akin Maimuna ,thank God wasu kayan dama a cikin d'akin tace su Sadiq su saka .

Kifin gwangwani Maman Jummai ta dauka roba ta samu had'i da bare guda ukku ,ci ta shiga yi tana tayi tana tand'e harshe ,Mama dake d'akin ta , addu'a ta cigaba dayi duk da kame suke cewa tana in su ,bayan Jummai ta shirya mata komai gas  ta kunna ta dafa mata ruwa kasancewar hada shi ta rubuta tashi kiyi wanka please cewar Jummai tana mai zama kusa da Karime saman carpet shima duk cikin kayan da Sadiq ya siyo ne,Jummai da kanta ta kai mata ruwa toilet,bayan ta samu ta kasa jikinta,tea tasha had'i da sauran paracetamol d'in data zo dashi daga gidan Momy , kwanciya tayi ,rufe idanuwan ta tayi kaman mai bacci ,i love your hair, maganar sace ta dawo mata saurin tashi zaune tayi tareda dafe saitin zuciyar ta lafiya cewar Jummai tana mai tsare ta da ido.

Boyayyiyar ajiyar zuciya ta saki sannan tace baki tambaye ne komai ba ,akan me kenan cewar Jummai,akan komai ma, fad'owar Sa'ada d'akin yasa Karime kame bakin ta , Karime Mama tana kiran ki , Jummai ce mai saurin kama kunnen Sa'adatu dan ubanki yaushe zaki daina kiran sunan ta haka ,bakya ganin yanzu itama matar aure ce ,yanze kunnen ta tayi had'i da cewa sai lokacin dana ganta da baby sannan zan daina kiran sunan ta ,tana idar da maganar ta fice , d'an murmushi tayi idan da sabo ta saba duk kunnen ta babu Mmai ce mata Anty ko Yaya ,ina zuwa ta fad'a tana mai nufar d'akin Mama, Jummai kuwa sauran kayan ta shiga gyarawa.
Bayan ta zauna ne Mama ta numfasa sannan tace meke faruwa? Akan me Mama cewar Karime akan auren ki Mama ta fad'a kai tsaye, d'an cizon lips d'inta tayi sannan tace bai sake ni ba zaro idanuwa waje Mama tayi tareda cewa ban gane ?

Mama Mijina bashi da lafiya a halin yanzu ,meke damun sa cewar Mama cikin tsananin tashin hankali,Mama kibi komai a hankali ,yana fama da wata lalura ce ,amma yanzu yana kan magana ko fita ma ba'a so yayi ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace toh akan me zaki dawo gida bayan kin san Mijin ki yana bukatar ki , d'an murmushin takaici Karime tayi sannan tace shine da kansa yace na dawo sabida likitocine masu kula dashi ,kodai har ya baki takardar sakin ne?
Aaaa Mama ki yadda da magana ta ,Hmmm shikenan,Allah ya kaimu gobe sai muje mu duba shi ,ai baya k'asar Karime tayi saurin cewa ,zaro na mujiya Mama tayi sannan tace kice abun bana wasa bane ,toh Allah ya bashi lafiya Ameen Karime ta ansa tana mai boye damuwar ta kije ki kwanta da alama akwai gajiya tareda ke.

Jiran bayanin ki bake Jummai ta fad'a tana mai tsare Karime da ido ,bayan ta kwanta,bayani ta shiga yiwa Jummai shugowar Maimuna d'akin yasa suka kama bakinsu ,babyn Jummai ta kawo mata ,bayan ta anshi baby cema Maimuna tayi toh ai sai ki bawa mutane waje koh?
Zunburo baki tayi sannan tace mutum da d'akin sa ,dalla malama fice bi bama mutane waje kafun na saba miki cewar Jummai cikin kuluwa.Fita tayi tana gunguni hakan yasa Jummai kwantar da babynta bin bayan Maimuna tayi da gudu boya tayi bayan Maman Jummai wacce keta faman lasar hannu ,

A bangare Alia kuwa zaune suke sai faman fira take masa ,sam hankalin sa baya kanta ,shi kansa baya iya cewa ga ainafin abunda yake tunani,kirane ya shugo wayar ta , excuse me ta fad'a tana mai tashi in a seductive way can nesa dashi ta matsa , hello Momy ,hope yana lafiya ?
Yes Momy yana lafiya zan iya magana dashi? Bacci yake a yanzu sai dai idan ya tashi ,ok Alia , thanks baki ta d'an ta'be sannan tace ok Mom,mu kwana lafiya.Katse kiran tayi tareda nufar sa a yanda yake zaune saman sofa haka ta tarar dashi ,zama tayi tareda jinginar da kanta saman jikinsa, he's not comfortable da abunda take masa but baya son gwale tane ,tun she's trying akan sa , d'an janye jikinsa yayi hakan ya basu damar had'a idanuwa, kallon shi ta shiga yi kaman zata cinye shi ,shiya fara janye idanuwan sa had'i da tashi tsaye, kitchen ya nufa ruwan gora ya tsiyaya a cup had'i da kaiwa baki..
A bangaren Alia kuwa ajiyar zuciya ta saki ta sani ba k'aramin kokari take ba wajen controlling kanta akan Ramadan d'in ,ji yayi ta rungume shi ta baya ,janye jikinsa yayi had'i da cewa it's getting late , you should go home ,ma'ke kafadar tayi ,yau anan zan kwana ,No Alia you have to go shagwabe fuska tayi , please ina son kula da kai bana bukatar hakan besides ni d'in Mijin aure ne bana bukatar irin haka daga gareki ,ficewa yayi yana nufar upstairs sosai maganar sa tayi mata zafi you are married then why ka gudu ka bar matar taka tsayawa yayi amma bai juyo ba hakan yasa ta cigaba da magana , because baka sonta , she's not your type I'm your type,kuma am very certain kana sona har yanzu ,idan kuma baka so ka fad'a mun naji , fad'a mun da bakin ka, cigaba da tafiyar yayi cikin sauri sauri ,banko kofar room d'in yayi da karfin gaske .

Wani shu'umin murmushi Alia ta saki had'i da furta he's still in love with me ,Ramadan nawane tunda farko and ko yana so baya so saina zama matarsa da haka ,kayan ta ta tattara tareda ficewa.....
A bangaren sa kuwa he's restless,ba zai iya cewa ga abunda yake so ko abunda yake missing, totally he's brain is not working , bathroom ya nufa ,alwala da d'auro had'i da kabbara sallah koya samu sau'ki akan abunda ke damun sa .

Late night Alia ta isa gida,tayi mamakin ganin haske a room d'in Momy hakan yasa ta nufi room d'in cikin mamakin abunda ya hana Hjy Mariya bacci because tasan wacece mahaifiyar ta sam bata wasa da bacci,zaune ta tarar da ita ta buga uban tagumi,lafiya Momy cewar Alia tana mai zama daf za mahaifiyar ta?
Baki ga missed calls d'ina ba cewar Momy cikin fushi kaman zata fashe,la wallahi Momy ban kula ba,Hmm wai yau ni yaron Hjy Mariya zai kai wajen police zaro idanuwa Alia tayi sannan tace akan me ? Baban matar sa ya b'ata shine fa yasa aka damke ni yanzu haka ina under investigation ba wai sun barni ba ,kina son ce mun Mahaifin Rumaisa ya b'ata harara Momy ta bankawa Alia sannan tace Mahaifin Karima , bangane ba cewar Alia ?
Ramadan nake magana yaron nan bashi da mutunci ko miskala zarratun dariya Alia ta saka sannan tace Momy yaushe kika daina gane su , wallahi ba Ramadan bane Sadiq ne domin through out ina tareda Ramadan .
"Dafe kunci Hjy Mariya tayi sannan tace kice Sadiq ne,eh Momy because Momynsa da kanta ta turo mun address d'in inda yake ,and throughout of the day muna tare ,then me matarsa take a gida cewar Hjy Mariya tana wani murmushi it seams your plan works,Ramadan ya sake ta.

Mu had'u next page 

*Thanks for  your love and support NIKAAH RENTAL MARRIAGE FANS*

*LOVE YOU LODI LODI* ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜