NIKAAH (Marriage for rent)

19 Nikaah marriage for rent

by @hanaady

NIKAAH
     Rental marriage

                          By
               
                    HANAADY
     

Rahama Aminu Bala

HE HAD THE COURAGE 
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?

Page 19

Kiran number Sadiq Alia tayi please Sadiq ina Ramadan gani a Company ina bukatar ganin sa d'an ta'be baki Sadiq yayi sannan yace bana tunanin yana bukatar ganin ki a yanzu ,cikin rashin fahimta Alia tace ban gane ba ,katse kiran yayi had'i da sakin tsaki.

  "After 9 o'clock Karime ta tashi sosai idanuwan ta suka mata nauyi,kin tashi Karima maganar Momy ta daki kunnen ta,ansa mata tayi da eh Momy ,ya jikin naki?

Alhamdulillah,da sauki sosai,Masha Allah Momy ta ansa tana mai tashi tsaye kasancewar a zaune take tana tasbihi,ki masu kiyi wanka ,toh Momy,cikin yanayin dauriya ta sauka daga Saman bed d'in ,saurin nufar bathroom d'in Momy tayi domin had'awa Karime ruwan wanka,Momy zan iya had'awa da kaina cewar Karime cikin yanayin ladabi ,Aaaa Karima keda ba lafiya ne dake ba,ai ruwan ya zama ready ki kasa jikin ki da kyau , breakfast na hanya ansawa da toh Karime tayi tana mai shigewa bathroom,ficewa Momy tayi cikin yanayin sauri.

Ta dad'e tana mamakin kulawar Momy a gare ta ,ganin lokaci naja yasa ta fara gasa jikinta"hope kinyi komai yanda na bukatar cewar Momy wacce shugowar su kenan dakin ita da mai aikinta ,ajiye katon farantin dake hannun ta tayi cikin ladabi ta ansawa Momy da eh , bud'e food flask d'in Momy ta shiga yi peppersoup d'in kayan cikine daya sha curry,yauwa yanzu abunda nake so dake Samira ki d'auki jakar nan ki tafi da kayan gidan ku and koda wasa kada Ramadan ya san cewa ke aka bawa kayan Sa'ada bance ki sanar kowa ba .

Saida Momy ta tabbatar da Karime taci abinci sannan ta fice bayan ta umarci Rumaisa ta zauna da ita na d'an wani lokaci, number Sadiq Momy ta kira akan ya taimaka ya koma wajen Ramadan, ansar daya bata bata mata dadi' ba because cewa yayi baya bukatar ganin Ramadan a yanzu and he's still angry with him ,bayan haka ai Ramadan d'in ba yaro bane da za'ai ta faman tarairayarsa .

Tagumi Momy ta buga sosai take jin damuwa akan halinda Ramadan yake ,ciki,Allah sarki soyayyar uwa ga d'anta,duk da tana fushi dashi akan abunda yayi ma Karime hakan bai hata jin tausayin yaron taba dafe kanta tayi gashi kamal baya gari, someone must be there with him, number Alia Momy ta kira ,saurin d'aga kiran Alia tayi Momy ina Ramadan ya shiga ?
Cewar Alia ,shine dalilin kiran ki,zan turo miki address d'in inda yake please take good care of him in sha Allah Momy,katse kiran Momy tayi had'i da saurin turawa Alia address d'in inda Ramadan yake .

Tasan cewa Ramadan yayi laifi saidai me bata ta'ba samun kwanciyar hankali akan barin shi all by himself a halin damuwa , she's certain Alia zata rage masa kad'aici she's not sure whether abunda tayi dai dai ne,ta wata mahangar dai daine ta wata mahangar kuwa ba dai dai bane abunda yafi shine bari ta d'auro alwala domin gabatar da nafila akan Allah ya tsare Ramadan daga fad'awa halaka ko makamancin ta.

A bangaren Rumaisa sa kuwa kasa bama Karime wasi'kar Sa'ada tayi duba da halinda take cikin , because tun zuwan ta bayan gaisuwa babu maganar data  kara had'a su  ,sun dau wasu lokutta a haka daga bisani bacci Karime tayi hakan yasa Rumaisa komawa sashen su bayan fitar Rumaisa ta wasu minutes ta bud'e idanuwan ta sauka tayi daga saman bed d'in ,cikin daurewa ta nufi downstairs, inda ta bar wayar ta anan ta tarar da ita dauka phone d'in tayi tareda saurin dubawa ganin 10 missed calls from Jummai yasa jiki na kyarma ta kira number Jummai,saida Jummai ta d'an saisaita muryar ta sannan tace dafatan kina lafiya?
Tun safe nake faman kiran wayar ki,,daga tsayen da take na nufi bed cije lips d'inta tayi cikin dauriya ta zauna , numfashi taja sannan tace ina lafiya Jummai,amma lafiya naga kin mun missed da yawa haka ,bazan boye miki ba Karima muna cikin tsananin tashin hankali akan me cewar Karime cikin tashin hankali saidai kin zo ,yanzu haka ina gida kiyi kokarin shugo yanzu idan babu damuwa ,katse kiran Karima tayi tareda nufar trolly d'in data had'a jiya domin ficewa gida , suturar jikinta ta canza kasancewar rigar bacci ce duk da ba data tsaraici.
Trolly taja juwa living room Momy ce ta fad'o mata arai ji tayi ba zata iya tafiya ba tareda sanin Momy ba because of irin yanda ta nuna mata kulawa had'i da kauna abunda bata ta'ba tunani daga Momyn ba ,ajiye Trolly d'in tayi zuwa sashen Momy,a hanyar tane ta canza tunanin akan taje ta fara ganin Dada .

Tarba ta musamman Dada ta baiwar Allah daurewa kawai take because of irin zafin da take ji ,ganin Dada had'i da Little Sa'ada sosai ya gare mata rad'ad'in dake damun ta ,bankwana tayi wa Dada akan zata school ba tareda tunanin komai ba su kayi sallama,sashen Momy ta nufa ,zaune ta tarar da Momy ta buga uban tagumi hannu biyu biyu ,ganin arba da fuskar Karime ne yasa Momy tayi saurin tashi had'i da nufo to saurin sadda kanta k'asa tayi sosai take jin kunyar Momy ga wani girman tada take gani lafiya Karime ?
Momy ta jefo mata tambaya ke ya kama ta ace kina hutawa meya fito dake?labartawa Momy Karime tayi akan kiran da Jummai tayi mata ajiyar zuciya Momy ta saki had'i da cewa Allah yasa dai ba wani babban abu bane ,yanzu abunda za'ayi kije sashen naku zan kira Sadiq ya kaiki,cikin yanayin girmamawa tace ba damuwa Momy zan hau keke napep 

kiyi abunda nace kinji Karime cikin yanayin lallashi Momy tayi maganar,ansa mata tayi da toh ,ficewa tayi cikin dauriya because dakyal dake taka kafarta , d'aya daga cikin kujerun falon nasu ta nufa zama tayi tana mai kwarewa babban falon nasu kallo 

sauka idonta tayi Saman dining table kujerar da yake yawan zama ta kalla ,jiki a mace ta nufi dining table d'in shafa kujerar ta shiga yi slowly ta rungume kujerar wasu marayun hawaye ne suka silalo daga idanuwan ta ,ji take kaman shi Ramadan d'in numfashin tane ta dad'e rungume da kujerar,daga bisani Bedroom d'insa ta nufa 
ido ta baza tana bin bedroom d'in da kallo,komai a tsare yake kaman kullun,takawa tayi zuwa bed kwanciya side d'in yake kwana a kullun tayi rungume pillow tayi tareda dauke numfashin ta ,tana matuk'ar kaunar Ramadan sai dai me sosai take jin haushin kanta akan me zata kai kanta wajen sa half nake,ita a ganinta laifin tane ,yanda yabi da ita babu tausayi yasa taji wani irin haushin sa saidai me wani sashen na zuciyar ta still fad'a mata yake ita ce mai laifi 

sauka tayi tareda nufar wardrobe d'insa ,kayansa ta shaga shafawa wata shirts tasa da dauka tareda shakar kamshin sa ,zare ta tayi daga hancin ta rungume ta jikinta tayi tareda lumshe idanuwan ta a daidai wannan lokacin wasu zafafan hawaye suka gangaro saman kuncin ta .

Wata shirt d'in ta kuma daukar rungume ta ta kuma yi still kara daukar wata tayi rufe marfin wardrobe d'in tayi tareda ficewa , kujerar data bari ta nufa zama tayi tareda janyo trolly d'in shirts d'insa ta saka cikin kayan ta ,lumshe idanuwan ta tayi kaman mai bacci jin ana knocking kofa ne yasa slowly ta tashi ,kofar ta bude ba tareda ta tambayi waye ba ,arba da fuskar sa yasa gaban ta wani irin fad'awa murmushin da ya saki ne yasa ta gabe ba Ramadan d'inta bane ,sosai yau taga kamar su ,ya karfin jikinsa Sadiq ya fad'a cikin yanayin sakin fuska, k'asa tayi da kanta cikin jin kunyar sa tace Alhamdulillah,,tare nake da Dr Fadil idan ba damuwa zai iya shugowa cewar Sadiq da kai ta bashi ansa ,komawa tayi domin ta basu damar shugowa.

Gaishe da su tayi bayan sun zauna ya karfin jikin cewar Dr Fadil Alhamdulillah ta fad'a atakaice babu abunda ke miki ciwo babu ta fad'a, please ki kwantar da hankalin ta ki Karima wannan da kike gani shine best friend d'in Ramadan cewar Sadiq jin an ambaci Ramadan yasa Karime saurin kallon guy d'in, murmushi ya saki had'i da cewa Sadiq ya fad'a mun komai akan aurenku da kuma abunda ya faru jiya iya mai baki hakuri on behalf of Ramadan ,and a yanda na fahimta ke d'in jajirtacciya ,keep it up , thanks ta fad'a cikin yanayin muryar lashin lafiya.
Zan yi iya kokarina wajen taimaka masa akan matsalar dake damun sa ,dama yana da wata matsala? Karime ta fad'a,saida tayi maganar sannan taji kunya had'i da haushin kanta , y'ar dariya Dr Fadil yayi wajen Sadiq ma hakan take domin baki ya saki yana ta dariya abunsa because sosai maganar Karime ta bashi dariya .

Gyaran murya Dr Fadil yayi sanann yace it's just a trauma akan mutuwar Sa'ada and it's normal akan wasu mutanen, thank God ba kowane lokacin abun ke dawo masa ba ,bangane ba cewar Karime? Bayanin Dr Fadil ya fara kaman haka,wani yanayine where by some people struggles to forget traumatic or horrible incidents ,su kan masu kansu stock in the past, hakan yakan faru da mutanen da suka rasa loved ones nasu ,for example death of a baby ,rape, death of the parents, death of a wife da dai sauransu, ajiyar zuciya tayi sannan tace a haka zaita rayuwar sa ?
D'an murmushi Dr Fadil yayi sanann yace by having you on his side in sha Allah komai zai zama labari,baya son ganina ya fad'a mun, zai so ya ganin ki duk lokacin da abun ya d'an lafa masa cewar Sadiq, because ked'in ta musamman ce a wajen sa, mi'kewa Sadiq yayi shima Dr Fadil muje koh Sadiq ya fad'a yana mai kallon ta ,ganin bata da niyyar tashi yasa yace ko kin fasa zuwa gidan naku ,saurin tashi tayi runtse idanuwan ta tayi domin wani irin zafine ya ziyarce ta zanje ta fad'a kanta a k'asa gaba su Dr Fadil su kayi hakanne ya bata damar jan trolly d'in ta zuwa wajen.
Aaaa yana ganki da kaya cewar Sadiq, d'an susar kanta tayi sannan tace ina son na d'an huta a gida ,Momy tasan da kaya zaki ?
Rasa ansar da zata bashi tayi waya ya dauka domin kiran Momy saurin katse s shi tayi ta hanyar cewa Dan Allah ka taimaka mun ina son na d'an zauna gida ne na wani lokaci,fasa kiran Momyn yayi ba tareda ya kuma magana ba, trolly d'in ya dauka mota ya bud'e tareda saka shi ,matsawa yayi wajen Dr Fadil wasu ya'n maganganu su kayi had'i da bankwana ko wanen su motarsa ya nufa .

Muje koh yace da ita ,kofar baya ta bud'e tareda shigewa baice da ita komai ba yiwa mota key sai jan gefe 😆 

A bangaren Ramadan kuwa dakyal ya samu ya kuma watsa ruwa, briefly ya shirya cikin three quarter white colour had'i da riga armless blue,wani lobby ya bi daya sada shi da wata kofa tura kofar yayi had'i da kunna kansa,wani kayataccen garden ,a yanda na lura baki d'aya gidan nasa tsarin gidan laranawa ne because of yanda tsarin gidan yake a zahiri ,hannuwan ya saka cikin pocket d'in three quarter d'insa, idanuwan sa a lumshe suke ,saukar jikinta yaji saman bayan sa rungume shi tayi ta baya tightly,ko ba'a fad'a masa ba yasan Alia ce because of kamshin perfume d'inta,kaine farinciki na ta fad'a cikin yanayin jan hankali,janye hannun ta yayi daga jikinsa,tafiya ya fara yi zuwa living room,bin bayan sa tayi ,zaune ta tarar da shi saman sofa hannun sa biyu biyu saman kuncinsa .

Hannuwan nasa ta janye had'i da zama dab dashi , fuskar sa ta tallafo sannan tace damuwar ka damuwa tace please Love ka fad'a mun damuwar ka if kuma abun bana fad'awa bane please ka cire damuwar aranka kada ta maka illa,saurin shiga jikinta yayi had'i da sakin wani marayan kuka itama biye masa tayi kukan ta shiga yi cikin yanayin tausayin sa, soyayyar had'i da makirci irin na mace ,sun dad'e aka daga bisani shiya fara shuru dago kansa yayi had'i da goge hawayen fuskar ta am hungry ya fad'a a kasalance, d'an murmushi tayi tareda cewa mezan girka maka .
D'an ta'be baki yayi tareda cewa bana da choice a yanzu sai dai bana son abu mai sugar "d'an zame jikinta tayi tareda mi'kewa kissing hannuwansa tayi tareda nufar kitchen,a iya dube duben ta bata sami abun girkawa ba hakan yasa ta kira drivern ta list d'in abunda take bukata ta tura masa , kitchen d'in ta shiga gyarawa duk da ba wani dirty yayi ba
A bangaren sa kuwa kwanciya ya gyara had'i da rufe eyes d'insa kaman mai bacci ,kukan tane ke masa yawo cikin brain had'i da caring d'inta akansa ,komai dawo masa yayi a yanda ya hau kanta had'i da wahar da ita and still she followed him a bathroom domin jin halin da yake ciki ,furzar da iska yayi daga bakinsa ,now ya amshi laifinsa akan abunda ya mata saidai me why zata je room d'insa half naked ,shine dalilin da yasa wani sashe na zuciyar sa ke za'ka masa wasi'kar jaki akan tabbas taje ne domin tayi seducing nasa .

Fitowar Alia ne yasa ya bud'e idanuwan sa iya bayan ta ya hango cikin skirt d'in kanti blue colour da light pink top mai shegen kyau ,kashin kanta a daure kasancewar kanta ba hula ajiyar zuciya ya saki had'i da runtse idanuwan sa gashin Karime ne ya fad'a masa arai , Alia jinin larawa ce because Dad d'inta balaraben Egypt ne duk da akwai laranawa masu ba'kar fata Mahaifin ta farine sol,iya kyau Allah ya horewa Alia saidai me gashin kanta sam ba irinna Karime bane because Alia Momy ta biyu gashi da dukkan alamu.

Tana gaba Jafar driver na bin bayan ta hannun sa dauke da kaya ni'ki-ni'ki , direct kitchen suka nufa ,ajiyewa yayi tareda komawa ya d'auko wasu , siyayya Alia tayi bata wasa ba ,tun wuce warta bai kuma kallon inda take ba ,yana dai jin sautin maganar su.

Girki tayi masa mai rai da lafiya time d'in da ta idar baya falon sabida haka bin sa bedroom tayi , sallah ta tarar dashi yana yi jiransa tayi har ya idar ,hannuwansa ya d'aga, addu'ar samun sukuni yake ma kansa ,shi kansa zaiso ace yana rayuwa kaman kowa, shugowar Karime a rayuwar sa ya sami canje canje bazai karyata hakan ba sai dai me he can't control kansa akan duk abunda yake yi lura da ya idar da sallar ne yasa ta nufi sa rungume shi tayi ta baya ,Alia please ya fad'a a kasalance,

janye jikinta tayi tareda cewa food is ready,ok ya fad'a can cikin makoshi ,tashi yayi had'i da ninke praying mat ,da kallon so ta bishi ,this is her chance to win him back a tunanin ta ajiyar zuciya tayi tareda ficewa, gidan ta shiga gyarawa sosai take jin gajiya tunda ba wani saba aikin wahala tayi ba

but akan Ramadan babu abunda ba zata iya yiba ,ta rasa shi a baya because of her stupidity and selfishness but this time around baza tayi wasa ba ,saida ta jera masa komai saman dining kafun ta kuma komawa Bedroom d'insa,kicibis su kayi bikin kofa ita zata shiga shi kuwa zaya fito ,alamu sun nuna wanka yayi because ya canza suturar jikinsa zuwa jeans da shirt mai v neck , easy ya fad'a yana mai kallon ta d'an murmushi tayi tareda d'an bashi hanya wucewa yayi ba tareda ya kuma cewa komai ba .

Bin bayan sa tayi,ita tayi serving nasa kafun ta nufi upstairs da kallon mamaki yabi ta akan me kuma za tayo bedroom d'insa bayan gashi a living room, basarwa yayi tareda fara cin abincin sa.

"A bangaren Alia kuwa wanka ta watsa because jin nata yana bukatar hakan duba da zaki work d'in data sha ,a gurguje ta shirya daya daga cikin shirt d'insa ta saka , had'i da mayar da jeans d'in data cire,in a seductive way take taka stairs d'in kallo d'aya yayi mata janye idanuwan sa yayi had'i da cigaba da cin abincisa ,zama tayi tana mai kare masa kallo.

A bangaren Karime kuwa da taimakon ta Sadiq ya isa kauyen su , parking yayi bakin gidan nasu , ajiyar zuciya ta saki had'i da bud'e kofar motar ,zuwan ta girin nasu ayau ya tuna mata last time da suka zo da Mijin Sa'ada samun kanta tayi ta mugun missing Mijinta had'i da wani haushin sa , kokarin daukar kayan ta take ,aaa matar Yaya ki fara shiga gidan tukun zan biyo ki dasu idan ba damuwa ,da kai ta ansa masa tareda shigewa gida.

Zazzaune ta tarar da mutan gidan ko wanen su ta buga uban tagumi,Mamanta ta nufa had'i da tambayar lafiya ?Bata iya bata ansa ba illa Maman Jummai ta tayi caraf tace Baban Jummai ne ya b'ata,bangane ba cewar Karime mamaki dauke da fuskar ta ,takowa Jummai tayi kusada Karime,abun zama ta ajiye mata kasa zama tayi,ban gane me Maman Jummai ke nufi ba , dagaske ne Karima Baba ya b'ata tun ji bayan isah rabon da a saka shi ido ,duk inda ake tunanin ganinsa babu inda ba'a duba ba ,kin kira wayar sa kuwa ?
Wayar sa yanzu haka gata can wajen Maman Jummai because a da'kinsa ya barta ,dafe kanta tayi Maman su Alia ta aikata abunda take ikirarin zata aikata kenan cewar Karime cikin fushi,Maman Jummai ce mai fad'in bana tunanin hakan sabida ai jiya zuwa yau ta bashi kinga kuwa ai ba'a wuce ranakun ba ,kallon Maman Jummai Karime tayi , a yanda ta fahimta ba wani damuwa tayi ba janye tunanin tayi ta hanyar cewa koda yake Maman Jummai haka take bata cika nuna damuwa akan abu ba ,ba kaman Maman taba .

Sallamar Sadiq ce ta katse mata tunani,,ganin shi janye da akwati yasa Maman Jummai saki baki had'i da cewa badai har kin anso takardar sakin ba ,matse yatsun Karime Jummai tayi tareda cewa me kika aikata ,it's long story Jummai ,yanzu bata wannan muke ba fatana anan inda Baba yake ,Mama kuwa kokarin shigewa daki ta ,ganin hakan yasa Karime tace Mama bafa shi bane wannan kanin sane dakatawa Mama tayi tareda satar kallon Sadiq Allah mai ikon wannan wace irin kama ce ,ita kanta Jummai bata yadda da cancan Karime ba , murmushi Sadiq yayi tareda gaishe dasu tabbas sai yanzu Mama taga banbancin because tuni ta fahimci Mijin Karime bashi da fara'a cikin sakin fuska ya shiga gaishe dasu

*NIKAAH fans me zaku ce Baban Jummai fa ya b'ata 😂* 

*Toh Readers mu had'u next page.* 

Oum Hamim