22 Nikaah marriage for rent
by @hanaady
NIKAAH
(Rental marriage)
By*
*AUTHOR*
*HANAADY*
*Rahama Aminu Bala
HE HAD THE COURAGE TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
BOOK TWO
Page 22
Bata kula da Rumaisa a d'akin ba,zaune take da hadekai da kwuiwa, maganar zuci take,in sha Allah na bar rayuwar sa ar abadan abidina, fuska shabe shawaye tace dama na sani am not his type ,and beginning nice na yaudari kaina y'ar kyautawar da yake mun ce tasa nayi tunanin d'in wata abace a rayuwar sa.
We still have chance ni a ganina cewar Rumaisa,saurin dago fuskar ta tayi tana mai kallon Rumaisa murmushi da yafi kuka ciwo Karime tayi sannan tace ku daina wahalar da kanku akan matsala ta ,ina godiya matu'ka da soyayyar ku had'i da kulawar ku a gareni amma batun saka rai akan Mijin Sa'ada babu shi,nayi rayuwa ba tareda dashi ba, banma san da Allah yayi halittar saba in sha Allah zan cigaba da rayuwa babu shi fatana Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyuba.
,Hmm Anty kenan from the moments dana gane na fad'a soyayyar sa ban ta'ba tunanin giving up on him ba but now i give up,we still have chance tunda ba auren aka daura ba , d'an murmushi Karime tayi sannan tace,ta ina zan fara?
How do i compete with! Kada ki manta Anty he once loved her and there's possibility he still does,tayi proposing nasa a cikin mutane baya son kunyatata ne shine abunda nake tunani cewar Rumaisa.
I want him for myself,Anty da alama hakan ba mai faruwa bane , don't lose hope Karima , ajiyar Karime tayi sannan tace zan jira zuwa lokacin da zaya sauwake mun ,p ,ido ya zubawa wayar bai ta'ba tunanin ganin koda sako ne daga wajen ta ,,,shi a tunanin sa ba zata ta'ba koda kallon sa ba, because a yanzu ya gane irin rashin kyautawar da yayi akan abunda ya aikata mata and sosai yake jin ba dadi' idan ya tuna dukan daya mata ya rasa gane abunda ya hau kansa daya sauke fushinsa akan ta and the worst part of it shine yanda ya saki jiki yayi mata lagalaga ajiyar zuciya ya saki had'i da ajiye wayar jikinsa a mace .
Shugowar sa'ko yaji ,hakan yasa ya d'an duba wayar ,dogon sa'ko ne Sadiq ya turo masa inda yake shiga bata nan yake fita ba, abun ya sosa masa rai because irin haka bata ta'ba faruwa tsakanin su ba ,ace wai Sadiq zai turo masa sa'kon rashin kunya da rashin mutunci,muryar Alia ce ta dawo dashi daga duniyar tunani.
Daf dashi ta zauna d'an muskutawa yayi because a yanda ta zauna jikinta na gugar nasa shi kuwa baya son irin haka bai kamata yana biye mata ba da hankalin sa da tunanin sa are you ok ta fad'a cikin yanayin concern yes ya bata ansa atakaice,wayar sa ya dauka had'i da nufar dining area number Sadiq ya kira bai daga ba , kuma kiransa yayi still bai daga ba karshe ma switched off aka ke masa , saukar numfashin ta yaji saman bayan sa ,rungume shi tayi ta baya , kokarin juyowa yake please tace cikin wani yanayi let's stay like this for a while.
Tsaye yayi mata kaman yanda ta bukata after some minutes zare ta daga jikinsa yayi he's restless yana bukatar sharing problem d'insa tafiya yake kaman wanda egg ya fashe masa a stomach lol ,jagwab ya zauna had'i da lumshe idanuwan sa ,meke damun ka ta tambaya banza yayi mata ,meke damun ka ta kuma tambaya, ajiyar zuciya ya saki sannan yace,na tambaye ki please?Yes yes ta fad'a cikin yanayin kaguwa, because wani farinciki ta samu kanta after the proposal bai kuma sakar mata fuska ba and now yana son tambayar ta she's thrilled.
Baki ya bud'e kaman mai shirin magana,he wants to share his pain akan abunda Sadiq ya masa and he needs shoulder to cry for abunda yake ji tun kafun shugowar sa'kon Sadiq , he's missing her like crazy,Amma karyata hakan yake duk da yasan tabbas the whole of him is missing Karime,but for sure yasan kawai sabo ne tsakanin su because of how funny she is ,ya sani dole yayi missing jokes d'inta had'i da shirmen ta.
Fasa sharing matsalar sa yayi he can't fad'a mata sirrin sa after duk sanaiyar dake tsakanin su had'i da sabo baya iya sharing komai wa Alia ,why baya jin komai wajen bayyanawa Karime matsalar sa ,oh i miss her ya furta cikin ransa ,am all ears Alia ta fad'a ganin ya fad'a DUNIYA tunani, gyaran murya yayi sannan yace why do you love me so much? murmushi ta saki had'i da shiga jikinsa sannan tace, Allah ne ya saka mun sonka had'i da kaunar ka from the first moment dana fara haduwa da kai a Airport,and a kullun soyayyar ka dad'a karuwa take , ajiyar zuciya tayi tareda d'agowa daga jikinsa, fuskar sa ta tallafo da tafin hannun ta sannan tace please kayi mun afuwa akan abunda na maka a baya yarinta ce tareda kishin,sune su kayi tasiri akai na but a yanzu na shirya kasa ka farinciki for the rest of my life, d'an murmushi tayi ba tareda yace komai ba murmushi tayi itama tareda kwantar da kanta saman jikinsa.
After few hours da tafiya Alia ya dad'e zaune ya saka wancan ya kwance wance daga karfe ,ficewa yayi cikin sauri,mota ya fad'a tareda nufar office nasu , direct Office d'in Sadiq ya nufa banka kofar yayi ba tareda sallama ba ,kallo d'aya Sadiq yayi masa mayarda kansa yayi akan system da yake faman dannawa....
Zama Ramadan d'in yayi had'i da cewa yaushe raini ya shiga tsakanin mu?
Bai bashi ansa ba illa mi'kewa da yayi ,hanyar fita ya nufa , don't you dare walk out on me Ramadan ya fad'a cikin fushi,ficewa Sadiq yayi had'i da banko kofa,dafe kansa yayi what's happening ya tambayi kansa, wayar sa ya laluba tareda saurin kiran number Momy harta kare ringing d'inta ba'a d'aga ba ,fuuu ya fice zuwa parking space,mota yaja sai gidan Momy .
Zaune ya tarar da Momy kallo d'aya tayi masa dauke kanta tayi had'i da tamke fuska,gaishe da ita yayi had'i da zama d'an nesa da ita,sosai gaban sake dukan uku uku because ya sani Momy tana d'aga masa fiye da dukkan yaranta and wannan fushin tana yana da alaqa da abunda ya aikatawa Karime ,sosai take jin tausayin sa saida me tuni tayi kanta fad'a akan yanda take zuba masa ido yana ta'bara akan mutuwar matarsa for sure ta sani abun da ciwo and tana masa uzurin hakan but yanda yayi wa Karime rashin tausayi had'i da rashin imani tuni ta yanke hukuncin hukun tasa ,bayan haka sai a yanzu take gane wasu abubuwan akan Ramadan d'in ma'ana kaman tana nuna tsoron sa that's why abubuwan nasa suke yawa .
When are you going divorce her?
Tambayar data jefo masa kenan,ban gane ba ya fad'a yana mai d'ago kansa wanda yake ta faman sunnewa , your rental wife Momy ta fad'a cikin dakiya, k'asa yayi da kansa tabbas abunda ya aikata ya batawa Momy rai matu'ka ,bai ta'ba tunanin akwai ranar da Momy zata iya bayyana sirrin auren sa da Karima ba because yasan yanda take son boye duk wani plan da kuma sirrin ta most especially akan Hjy Mariya.
Duk wani role daya kamata tayi playing is over ,Alia is back and a baya na roke,akan ka bud'e zuciyar ka for her ,cikin ikon Allah kayi abunda nake so ,she proposed to you and kayi accepting so yanzu it's time for Karime to walk out of the picture ,kafi kowa sanin Alia ita ce daughter-in-law dana ke mafarkin samu , d'an murmushi Momy tayi sannan tace finally ka kusa cika mun gurina ,zan jira divorce paper na Karime by ending of this month Momy i don't want to divorce her ya fad'a kai tsaye, d'an kankance idanuwa Momy tayi sannan tace don't tell ka fara kaunar ta? ajiyar zuciya yayi had'i da shuru na wasu ya'n sec tambayar ka nake ....No Momy babu wata soyayyar ta cikin raina ,sam ba taji dadi'n ansar daya bata ba, then zan jira divorce paper nata da haka bedroom ta nufa ranta a bace she thought zai ce he love her ne that's why baya iya divorcing nata,she clearly understands har yanzu haukan soyayyar Sa'ada nan daram cikin ransa,Sadiq ya fad'a mata komai akan proposal d'in Alia she's not happy about it at all,babu macen da zata so Ramadan kaman Karime ta gama fahimtar hakan daga gareta ita Karimen.
Ta gama fahimtar how simple and innocent Karime is ,sosai take jin tausayin ta domin tuni ta gane Karime ba tada gata,duba da yanda Mahaifin ta ya bar da auren ta akan haya,tana son taimaka mata ne but she can't force him to love her ,Sadiq ya fad'a akwai ta for sure akwai soyayyar Karime a cikin zuciyar Ramadan he's just dying it ne , ajiyar zuciya Momy tayi sannan tace dole nabi shawarar Sadiq akan sakaran yaron nan Ramadan wanda sam bai san inda ke masa ciwo ba,wace hanya za tabi domin sulewa daga tarkon Hjy Mariya ta gaji da had'a zuri'a da mace mai tsananin san kai wacce akan bukatar ta zata iya aikata komai.
Jiki a mace ya nufi Sashen sa,tura kofa yayi cikin ikon Allah kuwa a bud'e take ,shiga yayi had'i da sallama shuru yaji babu alamun motsin mutum ,sake sallama yayi this time around da d'an karfi still shuru, bedroom d'insa ya nufa ,komai a natse yake kaman yanda ya bar shi, lumshe idanuwan sa yayi he just wants to remember each and every moments nasu shida Sa'ada Mijin Sa'ada muryar Karime ta daki kunnen sa saurin bud'e idanuwan sa yayi had'i da kallon kofa.
Am I imagining things ya tambayi kansa, tabbas yaji muryar Karime maybe buya tayi bayan ta kira sunan sa , bedroom d'inta ya nufa ,komai ya nan yanda ta bar shi ,Karima ya kira sunan ta cikin taushin murya yana mai knocking kofar bathroom d'inta jin shuru yasa ya tura kofar,babu kowa a ciki ,karema bathroom d'in kallo yayi gabansa fad'uwa yayi ganin shi a bushe alamun an dad'e ba'ayi amfani dashi ba ,is that why a message d'in da Sadiq ya tura masa yace ya turawa Karima divorce papae nata a gidan su does that means ta tafi gidan su ko yaya?
Bashi da mai bashi ansar tambayar sa for now ,shifa yaji muryar ta ,ta kira shi da sunan da take kiran sa , maybe tana upstairs ya fad'a, upstairs d'in ya nufa ,acan d'in ma bata nana ,mamaki ne ya rufe masa fuska ganin room d'in wayam babu pictures d'insu da Sa'ada kaman wani sabon kamu ya nufi wardrobe d'inta,babu komai a ciki bud'e bud'e ya shiga yi duk inda yasan ya ajiye wasu memories d'in Sa'ada babu su , saurinlalubar wayar sa yayi Sadiq ya shiga kira still bai daga ba, tabbas this time around Sadiq ya gama kaishi karshe dole ya nuna masa iyakar sa.kiran daya shugo wayar sa ya dauke hankalin sa ,yes ...ok on my way ,kiran gaggwa ne daga office yayi mamaki akan yanda Sadiq ya fice ashe suna da important meeting a company nasu this boy has turning into something cewar Ramadan yana mai ficewa dole na koya masa darasi.
Troughout busy yake bai samu ya sami kansa ba sai after isha prayer, agajiye ya iso gida, surprise cewar Alia wacce ta fito hannun ta dauke da food flask,a dining table ta ajiye flask d'in tareda saurin nufar sa hugging d'insa tayi,janye ta daga jikinsa yayi ,me kike anan ?
Naje can baka nan that's why na biyo ka anan , d'an ta'be baki tayi besides matar gidan naga bata nan, ashe maganar Sadiq gaskiya ce akan Karime bata bukatar sa a rayuwar ta ,ashe dagaske takardar saki take jira,basarwa yayi ta hanyar cewa tayi tafiya ne but soon zata dawo d'an murmushi Alia tayi amma ba tace komai.bedroom d'insa ya nufa ,rufe kofar yayi because yasan halin Alia ba katsarine da ita ba .
Saurin d'aga kiran daya shugo wayar ta tayi ,kalle- kalle ta fara kaman marsa gaskiya "hello Momy dawowar sa kenan fa ,ki tabbatar kin masa maganar engagement dinku domin this week Mahaifin sa zai shugo Katsina haka Fadila ta fad'a mun ,abunda ya kawo ni gidan nasa kenan ,oh albishirin ki cewar Alia goro Hjy Mariya ta bata ansa matar gidan bata nan ,kaman yanda kika fad'a mun ,dariya Hjy Mariya ta saka sannan tace iya takardar saki ta rage mata kaman yanda na fad'a miki,kedai kiyi masa maganar,domin next month nake son komai ya kammala....Jin takun takalmin sa yasa Alia yiwa mahaifiyar ta bankwana .
Gajiya koh Alia ta fad'a tana mai doso in da yake bai bata ansa ba illa ficewa da yayi , direct sashen Dada ya nufa ,zaune ya tarar da ita ,bai san wacce irin tarba zata masa ba ,maganar Little Sa'ada ce ta katse masa tunani , jikinsa ta fad'a had'i da kasa kukan shagwaba ,wai sun tafiyar su unguwa shida Momy sun barta .Raba na mujiya ya shiga yi sosai yake jin fad'uwar gaba ,ki barshi ya zauna mana cewar Dada cikin sakin fuska sosai yanayin Dada ya daure masa kai, he's expecting ya ganta cikin fushi , gaishe ta yayi ansawa tayi tareda jefo masa tambaya akan ya Karime ?.
Tana lafiya ya fad'a cikin kyarmar murya,kun sha Abuja koh? Cewar Dada d'an susar kansa yayi sannan yace ban gane ba , d'an murmushi Dada tayi sannan tace ai ranar da kuka tafi Sadiya ta shugo take fad'a mun wani aikine ya taso maka a garin Abuja ,baka sami yi mun bankwana ba , Allah sarki Momy ta fad'a cikin ransa , gyaran murya yayi sannan yace,hakane Dada m,Yo ina Karimen?
Shuru yayi ya rasa ta ina zai fara domin shidai Allah bai bashi baiwar karya ba ko had'a zance da dai Sadiq ne ,ai ita tana Abujar wani aikin gaggawa ne ya taso a Company namu shine dalilin dawowar, cewar Sadiq wanda shugowar sa kenan,baki ya saki yana bin d'an uwansa da kallo,Masha Allah Dada ta fad'a fuskar ta dauke da murmushi, mi'kewa Ramadan d'in yayi akan zai wuce gida bin bayan sa Little Sadiq mai bin ta da harara akan ta koma ciki ,cikin yanayin kukan shagwaba ta koma sashen Dada............
Plan d'in Momy yana maka aiki but believe me kayi kokarin sakin yarinyar nan koh kasan abu yi kafun kasaka kanka cikin rigima da ita kanta Momyn,kallon Sadiq d'in yayi amma bai ce komai ba,if baka shirya zama da ita is better ka sake ta ,zata samu wanda zai aure ta ya kuma sota kaman ransa,da haka tafiyar sa yayi ,dama ta upstairs ya hango wucewar Ramadan d'in zuwa sashen Dada,yasan tabbas dole Dada tayi masa tambayoyi wand for sure yasan Ramadan bazai iya kare kansa ba and bayan son abunda zai had'a Dada da Momy domin tuni Momy ta fad'a masa abunda ta fad'awa Dada akan tafiyar Ramadan d'in da kuma Karime .
A bangaren Karime kuwa a yanda taga rana haka taga dare,kiran sallar farko da taji ne yasa ta nufa toile alwala ta d'auro gami da gabatar da nafila ,rokon sau'ki had'i da safsaf ce take nema ,bayan haka addu'a take Allah ya cire mata duk wata soyayyar Ramadan a cikin zuciyar ta.....Bayan ta gabatar da sallah d'an kwanciya tayi bata fatan bacci ya dauke ta because tana da C.a 8:30 ,kirane ya shugo wayar ta , gaban ta wani irin fad'uwa yayi ganin Mijin Sa'ada ya bayyana a Kan screen d'in wayar ta ........Fushi take dashi at the same time missing nasa take had'i da wani jin haushin sa,kaman yanda kowane d'an adam keda abokan shawara hakan take ga Karime wani sashe na zuciyar ta yace ta d'aga d'aya kuwa ya koma kaman can...yace ba zata d'aga ba....
Mu had'u next page
Shin wane sashen za tabi ?
Why zai kirata sassafe?
Author Hanaady.
Rahama Aminu Bala.