NIKAAH (Marriage for rent)

23 Nikaah marriage for rent

by @hanaady


NIKAAH
(Rental Marriage)
By
Rahama Aminu Bala

HE HAD THE COURAGE TO REMARRY!
WILL HE FIND THE COURAGE TO LOVE AGAIN???

Oum Hamim

Sunday
28 June 2026

WhatsApp
***

BOOK TWO

Page 23

Bismillah

Wayar na ci gaba da ringing.
Karime kuwa sai kallonta take yi tamkar ba tata ba ce.
"Mijin Sa'ada..."
Sunan da tayi saving number sa har yanzu.
Numfashinta ya tsaya na wasu sakanni.
Zuciyarta na ta raya mata abubuwa iri-iri.
"Pick the call..."
wani sashe na zuciyarta ya rada.
"No... Don't. Protect your heart."
wani sashe kuma ya bata amsa.
Wayar ta kusa yankewa.
A hankali ta miƙa hannu...
ta ɗaga.
Ba ta yi magana ba.
Shima bai yi magana ba.
Shiru.
Wani irin shiru mai nauyi.
Shiru da yake ɗauke da abubuwan da ba za a iya furtawa ba.
Ramadan ya lumshe idanuwan sa
Hakan yake fata...
ta ɗaga.
Amma yanzu da ta ɗaga... ya rasa abin cewa.
"...Hello?"
muryarta ta fito ƙasa-ƙasa.
Kamar wacce ta yi kuka har ta gaji.
Ji yayi kaman zuciyarsa zata fito.
"Karime..."
Ya kira sunanta a hankali.
Wani irin electric current ne ya ratsa jikinta.
Tsawon kwanakin nan...
bai taɓa kiranta da irin wannan softness ba.
Ta haɗiye ƙwallarta.
"Na'am."
Again...
Shiru.
Ramadan ya dafe goshinsa.
"Say something..."
ya gaya wa kansa.
Amma duk kalmomin sun ƙi fitowa.
A ƙarshe ya sauke numfashi.
"...How are you feeling?"
Tambayar data fito bakin sa.
Karime ta yi murmushin takaici.
"Alhamdulillah."
Iya fever ne nake dan ji
"Da sau'ki ya fada kasa kasa?"
"Yes."
"Are you taking your medications?"
"Yes."
Ya sake yin shiru.
Karime ta rufe idanu.
Wannan ba irin kiran da take tsammani ba ne.
Ta yi zaton zai ce...
"I'm sorry..."
ko kuma...
"Come back home."
Amma babu komai.
Sai tambayoyi kamar baƙi.
Siririyar ajiyar zuciya tayi sannan tace .
"Anything else?".
Ramadan ya lumshe idanu.
Actually...
akwai abubuwa dubu da yake son faɗa.
Yana son tambayarta me yasa ta tafi.
Yana son tambayarta me yasa gidan yake empty bayan tafiyar ta.
Yana son tambayarta me yasa tun jiya yake jin kamar akwai wani missing piece a rayuwarsa.
Amma...
girman kai.
Tsoro.
Confusion.
Su ne suka hana shi.
A ƙarshe ya ce,
"...Take care of yourself."
Karime ta ji wani abu ya karye a zuciyarta.
Kenan...
shi ke nan?
Ta yi murmushi mai ciwo.
"You too."
Kat!
Ta kashe wayar.
Nan take ta riƙe ƙirjinta.
Numfashinta ya fara nauyi.
"What was I expecting..."
ta furta wa kanta.
"Hakuri Karime..."
ta share hawayenta.
"If he wanted you...
he wouldn't let you go."
...
A ɗaya ɓangaren kuwa...
Ramadan ya ci gaba da kallon screen ɗin wayarsa.
Call Ended.
Ya sake kiran kansa da wawa.
"Why didn't you stop her?"
"Why didn't you ask her to come back?"
Ya jefa wayar saman bed.
Ya shafa fuskarsa.
"This doesn't make any sense..."
ya faɗa cikin rauni.
Ko aikin office bai taɓa da munsa irin haka ba.
Mutuwar Sa'ada...
Ce zai ce taɓa rikita tunaninsa irin wannan .
Me yake faruwa da shi?
...
Washegari da safe.
Karime ta shirya zuwa C.A.
Doguwar hijab mai launin navy blue ta saka.
Fuskarta babu makeup.
Amma duk da haka...
kyawunta bai ragu ba.
Mama ta tsaya tana kallonta.
"Allah ya tsare."
"Ameen."
"Ki dawo da wuri."
"In sha Allah."
Karime ta fito.
A ƙofar gida kuwa...
ta tsaya cak.
Sabuwar mota ce a ajiye.
Driver ya fito cikin girmamawa.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikum salam."
"Mahaifiyar Ramadan ce ta aiko ni."
Karime ta ɗan yi mamaki.
"Ni?"
"Eh."
"Ta ce bata son ki shiga public transport saboda baki da lafiya."
Ajiya nazo domin tafiya dake akace kin wuce
ajiyar zuciya Karime tayi sannan tace
"Allah ya saka mata da alheri."

..
A can gidan Ramadan kuwa...
Alia ce ta iso da breakfast.
Ta same shi yana zaune a dining table.
Coffee kawai yake sha.

"Good morning."
"Morning."
Ya amsa a taƙaice.
Zaunawa tayi kusa da shi.
"You don't look okay."
"I'm fine."
"No... you're not."
Bai ce komai ba.
Ta miƙa hannu ta riƙe nasa.
Ya janye hannunsa a hankali.
"Please..."
"I can take care of myself."
Kalmar ta fito cikin ladabi.
Amma tana ɗauke da distance.
Alia ta cije lips ɗinta.
Tun bayan proposal ɗin nan...
wani abu ya canza.
Ba ta san menene ba.
Amma.

Suits d'in ya dauke dake ajiye saman dining table chair ficewa yayi ba tareda yace mata komai ba!
Baki ta saki tana binsa da kallo ganin ya nufi hanyar fita yasa tayi saurin bin bayan sa "har suka isa Company nasu babu wanda yayi wa wani magana Alia ta kama bakinta ne because ta fahimci his not in the mood and bata son dizgi a yanda ta lura da yanayin sa tsaf zai iya yarfa ta a gaban driver.

Few minutes later

Ramadan ne zaune cikin office nasa sosai ya fada duniyar tunani me yasa yake jin kamar wani ya cire masa wani ɓangare na zuciyarsa?

He couldn't explain it.

Ba soyayyar Karime bace haka wani sashe na zuciyar sa yake ta faman fad'a masa.

At least...

Hakan yake ƙoƙarin gaskatawa kansa.

"It's just because I'm used to her..."

Ya faɗa cikin zuciyarsa.

"But why does it hurt?"

Ya rasa amsa.

...

Knock.

"Come in."

Alia ce ta shigo.

Coffee ta ajiye a gabansa.

"You skipped breakfast."

"I'm not hungry."

Ta zauna kusa da shi.

"You've changed..."

Ya ɗago ya kalleta.

"What do you mean?"

"You're here..."

Ta taɓa ƙirjinsa da yatsa.

"...but your mind is somewhere else."

Ya janye jikinsa yana mai hade fuskar.

"I'm just tired."

Alia ta yi murmushi.

Murmushin da bai kai zuciyarta ba.

"Are you thinking about... her?"

Tambayar data jefo masa kai tsaye.

Dago kai yayi yana mai binta da kallo.

Ba tareda yace komai ba.

Shirunsa ya ba Alia amsar da take tsoro.

Ajiyar zuciya ta sauke.

"You still love me..."

Ta faɗa da ƙyar.

"...Right?"

Ya kalleta.

Na wasu daƙiƙu.

Sai ya kawar da kansa.

"I don't know."

Kalmar ta fito ba tare da ya shirya ba.

Idanun Alia suka cika da hawaye.

"Then who are you trying to convince..."

"Me..."

"...or yourself?"

Ba ta jira amsarsa ba.

Ta fice.

Ƙofar ta rufe a hankali.

Ramadan ya dafe kansa.

Komai ya fara rikice masa.

A karo na farko...

Ya fara tsoron zuciyarsa.

...
A bangaren Karime kuwa...

After sun kammala C.A wani lecture su kayi ,idan ta Fadi abunda lecturer ke koyarwa koda guda one wallahi tayi karya because baki daya hankalin ta baya jikinta.
Hayaniyar data kaurene yasa ta gane lecturer ya fice.

Students tuni suka fara fita ɗaya bayan ɗaya.

Ita kuwa har yanzu tana zaune.

Notebook ɗinta buɗe.

Pen a hannunta.

Ba darasi take rubutawa ba.

Sai kalma guda.

"Healing..."

Ta sake rubutawa.

"Moving on..."

Sai kuma ta ƙara.

"Why is it so hard?"

Ƙwalla guda ta sauko kan takardar.

Ta goge rubutun.

Amma zuciyarta...

Ba za ta iya gogewa ba.

Outside the classroom...

Wata mota baƙa ta tsaya.

Sadiq ne ya fito.

Ya hango Karime ta cikin gilashin classroom.

Murmushi yayi a hankali.

"This girl is breaking..."

"And Ramadan doesn't even know."

Numfashi ya sauke sannan yace

"In sha Allah..."

"I'll fix this."

Amma bai san cewa...
Ba abu bane mai sau'ki..

Because sometimes...

Love doesn't need distance to hurt.

Sometimes...

It hurts the most...

When two hearts love each other...

But neither of them has the courage to admit it.

Karime ta fito daga classroom ɗin a hankali, notebook ɗinta rungume a ƙirji.

Idanuwanta sun nuna alamun rashin bacci, amma ta yi iya ƙoƙarinta wajen boye hakan.

"Karima..."

Muryar Sadiq ta dakatar da ita.

Ta ɗago kai.

"Abban Adil..."

Ta faɗa tana ƙoƙarin murmushi.

Sadiq ya lura da murmushin.

It wasn't real.

Ya san Karime sosai.

Idan tana farin ciki, idanuwanta ne suke fara murmushi.

Amma yau...

Idanuwan nata sun gaji.

"You didn't sleep, did you?"

Ya tambaya cikin tausasawa.

Ta girgiza kai.

"I'm fine."

Sadiq ya ɗan yi dariya.

"One thing I've learnt about women..."

"When they say 'I'm fine'..."

"...they're usually not."

Karime ta sunkuyar da kai.

"Let's go. Zan kai ki gida."

Ba ta musa ba.

Ta bi bayansa cikin nutsuwa.

...

Cikin mota kuwa...

Shiru ne ya mamaye su.

Sadiq bai matsa mata da magana ba.

Ya san wani lokacin...

Silence heals more than words.

Bayan tafiya na kusan mintuna goma...

Karime ta kalli window.

"Abban Adil..."

"Hmm?"

"Ya na lafiya?"

Sadiq ya san ba sai ta faɗi suna ba.

Ramadan take nufi.

Ya murmusa.

"He's alive."

Ta lumshe ido.

Alive...

Amma ba lafiya ba.

Ta fahimci hakan daga amsar.

"Yana shan magani?"

"Eh."

"Yana cin abinci?"

Sadiq ya yi ajiyar zuciya.

"A little."

Ta ƙara kallon titi.

"Good..."

Sai ta yi shiru.

Sadiq ya saci kallonta.

"Kin yi missing ɗinsa, ko?"

Da sauri ta juya ta kalle shi.

Idanuwanta suka cika da ƙwalla.

"But I don't want to."

Ta furta cikin rauni.

"I really don't want to..."

Sadiq ya taɓa steering da ƙarfi.

Ya ji tausayinta.

"Karime..."

"Love isn't something you switch off."

"You heal from it."

"You don't kill it overnight."

Ta share hawayenta.

"I'll try."

"No..."

Ya gyara.

"You'll succeed."

...

A wannan lokacin kuwa...

Ramadan na tsaye gaban babban glass window na office.

Hannunsa cikin aljihun wando.

Idanuwansa suna kallon city.

Amma ba abin da yake gani.

Knock.

"Come in."

Secretary ta shigo.

"Sir, the meeting is about to start."

"I'm coming."

Ta fita.

Amma bai motsa ba.

Wayarsa ya ɗauka.

WhatsApp ya buɗe.

Chat ɗin Karime.

Ya danna.

Ya rubuta.

How are you now?

Ya tsaya.

Ya goge.

Ya sake rubutawa.

Did you eat?

Ya sake gogewa.

A ƙarshe...

Ya rufe WhatsApp ɗin.

"What is wrong with me?"

Ya furta.

A karo na farko...

Ya fara jin tsoron abin da zuciyarsa ke yi masa.

...

A can gida kuwa...

Alia na zaune tare da Hajiya Mariya.

"Momy..."

"I don't understand him anymore."

Hajiya Mariya ta ɗago.

"What happened?"

"He keeps drifting away."

"Even when he's sitting beside me..."

"...it feels like he's miles away."

Hajiya Mariya ta ɗan yi shiru.

Sai ta ce,

"Then don't give him space."

"Stay close."

"Make sure Karime never comes back."

Alia ta ciji lips ɗinta.

"But what if..."

"What if I'm already too late?"

Hajiya Mariya ta kalleta da ƙarfi.

"No."

"You don't lose."

"Karime is just a contract wife."

"The real wife..."

"...will always be you."

Sai dai...

Ko ita kanta Hajiya Mariya...

A yau zuciyarta ba ta da cikakken tabbaci.

Domin ta fara ganin canjin da Ramadan yake ƙoƙarin ɓoyewa.

...

A gefe guda...

Karime ta isa gida.

Ta shiga ɗakinta.

Ta cire hijab.

Ta zauna bakin gado.

Wayarta ta ɗauki haske.

Message ne.

Numfashinta ya tsaya.

Da sauri ta ɗauka.

Amma ba Ramadan ba ne.

Jummai ce.

"Ina kewarku sosai. Gobe zan shugo in sha Allah.

Karime ta yi murmushi na farko tun bayan kwanaki.

Ta rubuta.

"I'll be waiting."

Ta ajiye wayar.

Sai ta kalli saman ɗaki.

"Ya Allah..."

"Idan soyayyarsa ba alkhairi ba ce a gare ni..."

"Ka cire ta daga zuciyata."

"Amma idan ita ce ƙaddarata..."

"Ka haɗa zukatanmu ba tare da wani ya cutu ba."

Ta share hawayenta.

Ba ta san cewa...

A wannan lokacin...

A wani ɓangaren garin...

Ramadan ma yana ɗaga hannayensa bayan sallar Magariba.

Kalma ɗaya ce kawai ta fito daga bakinsa.

"Ya Allah... Ka shiryar da zuciyata."

Ba shi da masaniyar cewa...

At the same time suke kai kukan su wajen sarki mai duka...

...To be continued in sha Allah

OUM HAMIM CE

Comments naku
Likes naku
Sharing naku

Sune abunda muke bukata ::::

You can follow me on

Whatpad @ Rahama000
Tiktok @ hanaady
😊😊😊😊😊😊😊😊😊
Zan yi farinciki da hakan thanks

ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN NIKAAH (Marriage for Rent). ❤️

Ina mai baku haƙuri bisa shiru da aka yi na kusan shekara guda ba tare da update na Nikaah ba.

Na san da yawa daga cikinku sun yi ta jira cikin haƙuri da fatan ganin cigaban labarin. Na gode ƙwarai da ƙaunar da kuka nuna da kuma rashin gajiya da kuka yi wajen ci gaba da tambayar yaushe za a dawo.

Ina neman afuwarku bisa wannan jinkirin. In shaa Allah, na dawo, kuma zan ci gaba da kawo muku sabbin pages cikin tsari.

In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina wajen ba ku labari mai armashi da zai saka ku manta da tsawon lokacin da kuka jira.

Nagode da soyayya, addu'o'i, da goyon bayan da kuke ba ni koyaushe.

Allah Ya saka muku da alheri. ❤️

- Rahama Aminu Bala Author of Nikaah (Marriage for Rent)