Fuska Biyu: Angel & Boss

Fuska biyu angel and Boss

by @angelbossauthor

CHAPTER 15️⃣
SABREEN

Daren ya yi shiru.

Amma shiru ne irin wanda yake sa zuciya ta kasa samun nutsuwa.

Sabreen tana zaune kusa da Sheikh Muhammad Kabir, kanta a kafaɗarsa, yayin da shi yake shafa kanta a hankali.

“Ki yi barci, 'yata.”

“Ba na jin barci.”

“Me ya sa?”

“Saboda ina jin kamar idan na rufe idona, zan sake farkawa ne a lokacin da ba ka nan.”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi murmushi mai cike da tausayi.

“Ba zan tafi ko'ina ba.”

Sabreen ta ɗago kai.

“Ka yi alkawari?”“Na yi.”

Ta sake jingina kanta a kafaɗarsa.

“Na gode“Sabreen…”Na'am?”

“Kin san na yi kewarki?”Ta yi murmushi.

“Ni ma.”

Ya yi shiru.

Sai ya ce,

“Kin yi kama da mahaifiyarki.”

Sabreen ta ɗago kai da sauri.

“Mommy?”

Fuskarsa ta sauya kaɗan.

“Eh.”

“Yaya take?”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi shiru.

Sabreen ta lura.

“Daddy?”

“Ki yi barci.”

“Ba zan yi ba.”

“Sabreen.”

“Na dai tambaya ne.”

Ya kalleta.

“Wata rana zan gaya miki.”

Ta yi ɗan murmushi.

“Ka fara koyon wannan daga Zayyad?”

“Wane abu?”

“‘Wata rana zan gaya miki.’”

Sheikh Muhammad Kabir ya fashe da dariya.

“Kin fara gane shi kenan.”

Sabreen ta yi murmushi.

“Shi mutum ne mai ɓoye komai.”

“Amma yana kare ki.”

“Na sani.”

Ta yi shiru na ɗan lokaci.

“Daddy?”

“Na'am?”

“Shin ka amince da shi sosai?”

Sheikh Muhammad Kabir ya kalli ƙofar ɗakin.

“Fiye da yadda kike tunani.”

Sabreen ta yi murmushi.

“Hmm.”

“Me kika ce?”

“Babu komai.”

“Na san wannan ‘babu komai’ ɗin naki.”

Ta yi dariya.

“Daddy!”

---

A PARLOUR 

Zayyad yana zaune shi kaɗai.

Wayarsa har yanzu tana hannunsa.

Saƙon bai daina yawo a cikin kansa ba.

“Muna da hoton Sabreen.”

Ya sake kallon hoton.

Hoton Sabreen ne da aka ɗauka a lokacin da suke fita daga gidan.

Amma akwai wani abu da ya fi damunsa.

Mutumin da ya aiko masa saƙon bai ce “mun gan ku” ba.

Ya ce:

“Muna da hoton Sabreen.”

Wato…

sun riga sun kasance suna bibiyarta tun kafin su san cewa Sheikh Muhammad Kabir yana raye.

Zayyad ya tashi.

Ya fara duba kofofin gidan.

Ya tabbatar an kulle su.

Tagogin ma.

Sai ya nufi corridor.

A lokacin da ya kusa ɗakin Sabreen, sai ya ji ƙaramar ƙara.

Krrrr…

Ya tsaya.

Ya saurara.

Babu komai.

Ya sake matsawa.

Krrrr…

A wannan karon ya fahimci cewa sautin yana fitowa ne daga ɗakin da yake gefen ɗakin Sheikh Muhammad Kabir.

Zayyad ya ɗaure fuska.

A hankali ya shiga.

Babu kowa.

Sai dai tagar ɗakin a buɗe.

Ya tsaya cak.

“Wannan taga ba a buɗe take ba lokacin da muka shigo.”

Ya matsa kusa da ita.

Iskar dare tana shigowa.

A ƙasa, kusa da taga, ya ga wani abu.

Ƙaramar takarda ce.

Ya ɗauka.

A jikin takardar akwai rubutu guda ɗaya:

“Kada ka yarda da mutumin da ke cikin gidan.”

Zayyad ya daɗe yana kallon takardar.

Sai ya ɗaga kai.

“Wane mutum?”

Ya juya.

A ƙofar ɗakin…

wani inuwa ta wuce.

Zayyad ya fita da sauri.

“Hey!”

Ya bi ta corridor.

Amma babu kowa.

Ya buɗe ƙofar gidan.

Babu kowa a waje.

Sai iska.

Zayyad ya rufe ƙofar a hankali.

Fuskarsa ta yi tsauri.

“Wani yana cikin gidan.”

---

A ƊAKIN SABREEN

Sabreen ta ji ƙarar ƙofa.

Ta ɗago kai.

“Daddy?”

Sheikh Muhammad Kabir yana zaune yana karanta wani abu a wayarsa.

“Me ya faru?”

“Na ji kamar an buɗe ƙofa.”

“Ki zauna.”

Sabreen ta tashi.

“Zan duba.”

“Sabreen.”

Ta tsaya.

“Na'am?”

“Kada ki fita.”

Ta dawo ta zauna.

“Amma Zayyad yana waje.”

“Zayyad zai iya kare kansa.”

Sabreen ta yi murmushi.

“Shi dai yana ganin kansa jarumi.”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi dariya.

“Yana da ƙarfin hali.”

“Wani lokaci har ya wuce kima.”

“Amma kina yarda da shi.”

Sabreen ta yi shiru.

Sai ta ce,

“Eh.”

A daidai lokacin…

aka ji ƙwanƙwasa ƙofa.

Knock… knock…

Sabreen ta kalli mahaifinta.

Sheikh Muhammad Kabir ya ɗaga hannu.

“Kada ki motsa.”

An sake ƙwanƙwasawa.

Knock… knock…

Sai aka ji muryar Zayyad.

“Sabreen.”

Sabreen ta numfasa.

“Zayyad ne.”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi mata alamar ta jira.

Sai ya tashi ya buɗe ƙofar.

Zayyad ya shiga.

“Komai lafiya?”

“Me ya faru?” Sabreen ta tambaya.

Zayyad ya kalli Sheikh Muhammad Kabir.

“Za mu yi magana.”

Sabreen ta ɗaga gira.

“Ni ba na ciki?”

Zayyad ya kalleta.

“Ke ki zauna.”

“Na san magana za ku yi a kaina.”

“Sabreen.”

“Na zauna mana.”

Zayyad ya girgiza kai.

“Kin fi ni yawan magana.”

“Ni ce?”

“Eh.”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi murmushi.

“Ku biyu kuna kama da yara.”

Sabreen ta nuna Zayyad.

“Shi ne ya fara.”

Zayyad ya nuna kanta.

“Ita ce.”

Sheikh Muhammad Kabir ya girgiza kai.

“Allah ya shirye ku.”

Sai ya kalli Zayyad.

“Me ya faru?”

Zayyad ya fitar da takardar daga aljihunsa.

Ya miƙa masa.

Sheikh Muhammad Kabir ya karanta.

Fuskarsa ta sauya.

Sabreen ta lura.

“Daddy?”

Ya ninka takardar.

“Babu komai.”

Zayyad ya kalle shi.

“Ka tabbata?”

“Eh.”

Sabreen ta fusata.

“Don Allah kada ku fara ‘babu komai’ ɗin nan.”

Zayyad ya kasa hana murmushi.

“Na faɗa miki.”

“Me?”

“Daddy ya fara koyon salonki.”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi murmushi.

Sabreen ta kalli su.

“Ku haɗa kai kenan?”

“Ba mu haɗa kai ba.”

“Na gani.”

Sai Zayyad ya zauna.

“Sabreen, ki yi wa Daddy ɗin ki ɗan shayi.”

Ta kalleshi.

“Me ya sa?”

“Saboda ni ma ina so.”

“Ba kai na ce ka zauna ba?”

“Amma shayi na so.”

“Ka yi da kanka.”

“Ni baƙo ne.”

“Ba ka yi kama da baƙo ba.”

“Me nake kama da shi?”

Sabreen ta yi tunani.

“Wani matsala.”

Sheikh Muhammad Kabir ya fashe da dariya.

Zayyad ya riƙe ƙirjinsa.

“Wannan ciwo ne.”

“Allah ya ba ka haƙuri.”

“Na gode.”

Sabreen ta tashi tana murmushi.

Amma kafin ta fita…

Zayyad ya kama hannunta a hankali.

“Ki kula.”

Ta kalleshi.

“Da me?”

“Da kanki.”

Muryarsa ta sauya.

“Kar ki yi tafiya ita kaɗai.”

Sabreen ta fahimci cewa barkwancin ya ƙare.

Ta gyada kai.

“Okay.”

Ya sake hannunta.

Ta fita.

Sheikh Muhammad Kabir ya kalli Zayyad.

“Ta fara son ka.”

Zayyad ya yi shiru.

Sai ya ce,

“Ni ma…”

Ya dakata.

Sheikh Muhammad Kabir ya ɗaga gira.

“Me?”

Zayyad ya gyara zama.

“Ni ma ina son yadda take da ƙarfi.”

Sheikh Muhammad Kabir ya yi murmushi.

“Na fahimta.”

---

Sabreen tana cikin kitchen tana shirya shayi.

Ta buɗe cupboard.

Sai ta ji wani sauti a bayanta.

Ta tsaya.

Ta juya.

Babu kowa.

Ta koma kan aikin.

Sai ta ji kamar wani ya wuce a bayan ta.

Ta juya da sauri.

“Waye?”

Babu amsa.

Zuciyarta ta fara bugawa.

Ta ɗauki wayarta.

Kafin ta kira Zayyad…

an kashe hasken kitchen ɗin.

KASH!

Sabreen ta daskare.

“Zayyad…”

Ta ji motsin wani a cikin duhu.

Sai muryar wani mutum ta fito a hankali:

“Sabreen…”

Ta rike wayarta sosai.

Muryar ta sake cewa,

“Ki yi shiru.”

Sabreen ta ja baya.

Amma kafin ta iya yin ihu…

hasken ya dawo.

Sai ta ga…

Zayyad yana tsaye a gabanta.

“Ke kina tsoratar da ni ne?”

Sabreen ta dafe kirjinta.

“Zayyad!”

Ya yi dariya.

“Me kika gani?”

“Na yi tunanin wani ne!Ni ne.”

“Ka kusa kashe ni!Ba zan iya kashe ki ba.”

“Me ya sa?”

Ya yi murmushi.

“Saboda Daddy zai kashe ni.”

Sabreen ta buga masa hannu.

Kade na!”

Ya yi dariya.

Amma bayan murmushinsa…

idanunsa suka koma kan ƙarshen corridor.

Sabreen ba ta gani ba.

A can cikin duhu…

wani mutum yana tsaye yana kallonsu.

Kuma a hannunsa…

akwai hoton Sabreen.
 
To be counted…

MISS NASIR ♥️✍️