MATAR GIDA PAGE 59
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P59
Bayan ya gama cin abinci tea ya haɗa ya zauna nan cikin parlour ya sha,bai bar parlourn ba sai karfe sha ɗaya da wasu mintina na dare,bacci cike idanunsa ya kashe TV,daga haka ya wuce ɓangaren Unaisa bayan shigarsa wormer dake daure kan daining ya kallah,taɓe baki ya yi kafin ya wuce ya buɗe wormer,farar shinkafa ce mai da yaji rufe wormer ya yi, parlourn tsaf babu datti ba kamar jiya ba,wutar parlour da daining ya kashe daga ya wuce kitchen ya kashe wutar kitchen,daga haka ya wuce ɗakinsa ya kwanta,misalin ƙarfe ɗaya na dare Unaisa ce zaune cikin ɗakinta ta riƙe ciki idanunta cike da bacci wani irin yunwa ne ke ɗawainiya da ita,ta ci abinci kafin ta kwanta amma yanzu jin kanta take kamar wacce ta uni da yunwa,bathroom ta shiga ta yi tsarki,bayan fitarta daga bathroom kitchen ta nufa dan samarwa kanta abinda za ta ci,wutar kitchen ta kunna ta dauki plate da niyya sa abinci sai ta ji gaba ɗaya abinci ya fita kanta wannan dalilin yasa ta ajiye plate ɗin ta buɗe firiji ta dauki yogurt da buscuit,nan cikin kitchen ta zauna ta sha yogurt da buscuit kafin ta kashe wutar kitchen ta fita ta koma ɗakinta ta kwanta,bayan ta kwanta ne bacci ya yi kaura a idonta wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki,a hankali ta tashi zaune ta cusa duka hannayenta biyu cikin sumar sosai take buƙatar kasancewa da Ɗalha tun da take bata taɓa tsintar kanta cikin wannan yanayi ba ta dauki a ƙallah mintina goma zaune kafin can ta kwanta tare da rintsa idanunta,bayan wasu ƴan mintina taji bazata iya jurewa ba kawai ta tashi ta nufi ɗakin Ɗalha,bayan shigarta tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa baccinsa yake hankali kwance yadda ya rufa jikinsa da bargo,ƙhamshin air freshner da ɗakin Ɗalha ke yi duk sanda ta shigo ɗakin haka take jin ɗakin da wannan ƙhamshin Unaisa na jin daɗin ƙhamshin ɗakin Ɗalha amma yau ta ji gaba ɗaya ƙhamshin ya riƙiɗa ya koma wari,tana nan tsaye bakin kofa ta kai hannu ta rufe hanci cikinta ne ya fara haustine mata amai na taso mata da wani irin sauri ta fita daga ɗakin zuwa nata Allah ya taimake ta bata yi amai ba,zama ta yi bakin gado tana mayar da numfashi, tana nan zaune Ɗalha ya shigo bakinsa dauke da sallama ganin yanayin da take cikin yasa ya samu waje gefen ta ya zauna yana tambayarta lafiya ƙasa magana Unaisa ta yi har sannan bata dawowa dai dai ba ''me ke damunki?me yasa ki ka fita da gudu?" a hankali Unaisa ta mayar da gajiyayyun idanunta fuskar Ɗalha ta ce ''daman ba bacci ka ke ba?" a hankali Ɗalha ya kai hannu ya kwantar da kanta kafaɗarsa ya ce ''lokacin da ki ka buɗe kofa na farka,ba ki da lafiya ne?'' girgiza kai Unaisa ta yi alamar a'a ta ce ''lafiya ta ƙlau wari ɗakinka ke yi'' fuskarsa dauke da mamaki ya ce ''wari kuma?" Unaisa ta gyaɗa masa kai alamar eh tana ƙara ƙara manne jikinsa tare da shigewa jikinsa,tun Ɗalha yana basarwa har ya ƙasa riƙe kansa Ɗalha ya rinƙa mamakin Unaisa yadda ta sakar masa jiki ya yi yadda yake so da ita,ita da take zaginsa duk sanda ya kusance ta yau ita ce ta sakar masa jiki haka haka dai ya yi ta mamaki,washe gari da wuri Amirah ta gama yiwa yara shirin zuwa makaranta,a can wajen Unaisa da Ɗalha kuwa da kyar Ɗalha ya samu Unaisa ta tashi ta yi wanka ta yi sallah lokacin karfe bakwai dai dai zama ya yi cikin ɗakin ya jira ta fita daga bathroom,bayan fitar ne ya dauki kuɗi dubu bakwai ya bata ya ce mata kuɗin motan zuwa islamiyya karɓar kudin ta yi ta ajiye kan gado ta dauke wata doguwar riga ta zura kafin ta shimfiɗa darduma,sallama Ɗalha ya yi mata daga haka ya fita daga ɗakin,bayan fitarsa bangare Amirah ya wuce ya tarar da ita zaune tare da yara suna breakfast,Amirah ta rinƙa binsa da ido duk yaran suka gaishi shi ya amsa masu ba tare da kallon inda Amirah ke zaune ba ya sawa kansa abinci,Amirah ta girgiza kai kawai ta yi murmushi can ta ce ''barka da safiya'' kansa ƙasa yana cin abinci ya ce ''kin tashi lafiya?" a takaice Amirah ta ce ''ƙlau'' daga haka babu wanda ya sake magana,yau ma kamar jiya Ɗalha ne ya kai yara makaranta ya kai Amirah ofis kafin ya wuce nasa ofis,yana zaune cikin ofis yana duba wani file Muhsin ya yi nocking daga ciki Ɗalha ya bada izinin shigowa bayan shigowar Muhsin Ɗalha ya tsaki a tunanin sa wani ne ke nocking,Muhsin bai kula sa ba ya samu waje ya zauna idanunsa kan file dake gaban Ɗalha ya ce ''mallam ba ka ganni ne bane ban son wulakanci fa na yi sallama baka amsa ba'' sai a sannan Ɗalha ya ɗago ya kalle Muhsin na wasu ƴan sakanni kamar yadda shima yake kallonsa ya ce ''yaushe ka dawo?"taɓe baki Muhsin ya yi kafin ya ce "ban sani ba sai yau ka ke tambaya ta yaushe na dawo?" kallon sa Ɗalha ya yi kafin ya tashi ya je inda photo copy machine yake ya kunna ya buɗe yasa wata paper ciki ya rufe kafin ya danna number copy da yake so,mayar da dubansa ya yi ga Muhsin ya ce ''ni na ce ka kashe waya'' gyara zama Muhsin ya yi kafin ya ce ''sai kuma ka yi, kawai dan ka kira waya bata shiga sai ya zama na kashe,bafa kashewa na yi ba,wanda ya fini so ne ya dauka ranar da muka dauka garin ranar aka dauke min waya,har yanzu ban siya wata ba ina jiran sai wata ta ƙare zan siya wata'' Ɗalha ya buɗe machine ya ciro paper da yasa ya yi photo copy ya ce ''Allah ya kiyaye gaba'' daga haka ya koma kujerar sa ya zauna,wayarsa ce ta fara ƙara alamar shigar kira a hankali ya kai hannu ya dauki wayar gani Maman Unaisa ke kira yasa ya saita nitsuwar sa tare da gyaran murya kafin ya amsa kiran,bayan ya amsa kiran ne cike da girmamawa ya gaishi Mama,Mama ta amsa masa daga haka ta tambaye suna lafiya Ɗalha ya ce duk suna lafiya daga haka Mama ta ce daman ta kira ne kawai su gaisa cike da girmama Ɗalha ya ce ''to Mama mungode'' daga haka ta yi masa sallama, bayan Mama ta kashe waya,mayar da dubanta ta yi ga Anty Aisha dake zaune kan tafurma gefen kofar ɗakin Mama hannunta riƙe matangaɗi tana tsintar shinkafa,idanuwan Anty Aisha kan Mama ta ce ''me ya ce?" ɓude hannu Mama ta yi kafin ta ce "cewa ya yi duk suna lafiya'' ''ba ki tambaye sa Unaisa ba?" cewar Anty Aisha numfawa Mama ta yi kafin ta ce ''ban tambaye sa kawai mun gaisa ne,kunya nake ji Aisha wai a ce tun da aka kai Unaisa ɗaki bata taɓa kirana ba har ke ƴar uwarta,ko har yanzu suna Kano ko sun dawo sai Allah'' wani irin murmushi Anty Aisha ta yi kafin ta ce ''na faɗi maki Mama ta kulle layin mu kusan kullum sai na kirata amma number bata tafiya,dan Allah ki kwantar da hankalin ki tun da ya ce suna lafiya aiy shikenan'' fuskar Mama cike da damuwa ta ce ''to shikenan Allah dai ya shiryar da Unaisa'' Anty Aisha ta taɓe baki kawai ta ce ''ameen'' tana mayar da hankali kan tsintar shinkafa da take can ta ce ''Allah dai ya kyauta amma Unaisa akwai wauta da rashin hankali ƴan uwa da dangi har makwabta kowa sai tambaya yake ko sun dawo daga Kano,duk wanda ya kirata wayarta bata shiga'' shiru Anty Aisha ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''in Allah ya kaimu gobe zan je har gidan nata na duba in ita bata nan na tabbata zan haɗu da kishiyarta'' Mama ta ce ''Allah ya kaimu goben'' shiru Anty ta yi zuciyarta na mata zafi kenan saboda Unaisa ta yi aure zata yanke alaƙa da ƴan uwa dole ne ta yi maganinta in har ta haɗu da ita gobe,daga haka ta yunkura tare da miƙewa tsaye hannunta riƙe da matangaɗi ta nufi rumfar girki,matangaɗi dake hannuta ta daura kan wata roba daga haka ta durkusa gaban murhun gawayi ta fara kunna wutar gawaye,Mama dai bata sake cewa komai ba ta faɗa duniyar tunani
Aina'u yau bata yi wahalar zuwa da wuri ba,sai karfe tara da rabi,zama ta yi compund a tana jiran fitowar Unaisa,karfe tare da mintina arba'in Unaisa ta fito cikin shirin zuwa makaranta koyan mota da sauri Aina'u ta tashi tana jero wa Unaisa gaisuwa,a takaice Unaisa ta amsa gaisuwar daga haka ta miƙawa Aina'u makullen ɓangarenta ta ce ''yau towun masara miyar kuka take sha'awar ci'' Aina'u ta amsa da to,bayan shigar Aina'u ɓangaren Unaisa idonta ne ya sauka kan daining inda ta ga wormer da ta sawa Ɗalha abinci yammacin jiya,bata yi mamaki ganin wormer wajen ba a tunanin ta Ɗalha ya ci abinci Unaisa ce bata ɗaga wormer ba,bayan ta buɗe wormer ta ga gaba ɗaya Ɗalha bai ci ba,taɓe baki ta yi kawai ta dauke wormer ta kai kitchen daga haka ta fara aikace aikace gidan,Allah ya taimake Aina'u yau bata yi aiki da yawa ba,ƴan share share da goge ta yi kafin ta yiwa Unaisa tuwo kamar yadda Unaisa ta buƙuta,bayan Unaisa ta dawo zama ta yi a parlour ta baje, sosai ta gaji kwana biyun nan bata san me ke damunta ba abu kaɗan ta yi sai ta ji gaba ɗaya ta gaji,nan parlour ta ci tuwon da Aina'u ta girka mata bayan ta gama cin tuwon ne ta tashi ta wuce ɗaki dan rage kayan jikinta,wani irin wari ta ji ɗakin ke mata ta rasa wari me,nan ta shiga dube dube ko zata ga abinda ke wari a ɗakin amma ta yi dube dubenta har ta gama bata ga komai ba,a daddafe ta canza kaya ta fita daga ɗakin lokacin karfe huɗu da wasu mintina nan cikin parlour ta yi sallar azahar da la'asar,bayan ta idar da Sallah kwanciya ta yi kan darduma tana mayar da numfashi sosai ta gaji,yau ma kamar jiya Ɗalha ya kwashe yara a makaranta ya dauki Amirah ofis sai da ya fara biya ofis ɗun Amirah ya dauko ta kafin ya wuce makarantar yara ya kwaso su,bayan dawowar su gida Amirah ta yi duk wasu abubuwan ta saba Malam ya zo ta tura masa yara,yau da wuri Aina'u ta tafi kasancewar babu aiki sosai a bangaren Unaisa,tun da Ɗalha ya ajiye su Amirah bata sake sa shi ido ba sai misalin ƙarfe tara nan ma ya shigo ne ya yi mata sai da safe kallo ɗaya ta yi masa ta fahimci yana cikin damuwa tana zaune kan gado tana sawa Fauziyya pampers ya shigo bakinsa dauke da sallama amsa masa sallama ta yi tana kallon sa a hankali ya tako har wajen gado ya zauna bakin gado yana kallon yadda take sawa Fauziyya pampers ya ce ''har ta yi bacci?" Amirah ta ce ''eh karfe tara fa ai duk sun yi bacci'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''kina da maganin ciwon kai?" mayar da dubanta ta yi garesa kafin ya ce 'a'a bana da shi ba aka jin dadi ne?" a takaice Ɗalha ya bata amsa ya ce ''lafiyata ƙlau Unaisa ce kai ke mata ciwo'' Amirah ta dauki wando ta fara sawa Fauziyya babu yabo babu fallasa ta ce ''Allah ya bata lafiya'' Ɗalha ya amsa da ''ameen'' shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni,can Ɗalha ya yunƙura tare da miƙewa tsaye idonsa kan Amirah dake canza kaya zuwa nigth wear,kafera da idanunsa ya yi Amirah bata ankata ba sai jinta ta yi jikinsa ya rugumeta ta baya yana manna mata kiss a wuya da wani irin sauri Amirah ta waigo suna fuskantar juna tana kallon cikin idonsa ta ce ''ka bar yarinyar ba lafiya,please ka je ka duba ta'' ta kare magana tana ƙokarin raba jikinta daga garesa kwantar da murya ya yi yana ƙokarin haɗa lips ɗinsu waje ɗaya ya ce ''ita ta ce maki bata da lafiya?" cike da hikima Amirah ta samu ta kwato kanta,da gudu ta wuce bathroom dake ɗakin ta kulle ƙofa,murmushi kawai Ɗalha ya yi ya fita daga ɗakin,bayan shigarsa ɓangaren Unaisa ganinta ya yi har sannan tana kwance inda ya baro ta tana bacci,a hankali ya kai hannu ya taɓa goshinta ya ji babu zafi sosai,a hankali ta ɓude tana kallonsa ''ciwon kan ya yi sauƙi?" gyaɗa masa kai kawai ta yi,a hankali ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta ce ''a nan zan kwana bana son ɗakin" ta ƙare magana tana kwantar da kanta kafar Ɗalha,gyara zama Ɗalha ya yi inda ya jingina bayansa da kujera ya miƙe ƙafafunsa duka biyu yadda Unaisa zata ji daɗin kwanciya,har sha biyu Ɗalha na zaune parlour a hankali ya kai hannu ya dauki karamin pillow daka kan kujera ya daura kan Unaisa a kai,daga haka ya tashi ya wuce ɗakinta ya dauki bargo da pillow tare da gidan sauro,nan parlour ya yi mata shimfiɗa,tashin ta ya yi ta shiga gidan sauro ta rufe jiki da bargo daga haka Ɗalha ya wuce kitchen ya haɗawa kansa tea bayan ya gama shan tea bathroom ya wuce ya yi wanka ya shirya kansa kafin ya dawo parlour, wutar parlour ya kashe kafin ya shiga gidan sauro ya kwanta gefen Unaisa tare da janyo ta jikinsa,misalin karfe uku Unaisa ta farka daga bacci dalilin fitsari da ya cika mata mara,bathroom ɗinta ta wuce bayan ta gama abinda zata yi ta koma parlour,Ɗalha da tun sanda ta farka ya buɗe ido bayan dawowar ta parlour kwanciya ta yi kan doguwar gaba ɗaya taji bata son kwanciyar ƙasan,ganin ta kwanta kan kujera Ɗalha ya tashi ya fita daga gidan sauro daukar ta ya yi kamar jaririya ya mayar da ita gidan sauro ya kwanta gefen ta,nan Unaisa ta rinƙa shigewa jikinsa har ta samu abinda take so
SHUUKRAN