THE MEETING DAY 👌
JA DA BAYA...
Book 1
Page 32 ✍️
***
Yau gidan hada-hada ake ta ko'ina, sabida meeting din da za'ayi yau din.
ita kuwa Gwanar wacce tashinta daga barci kenan, ko wanka ba ta yi ba, ta yi brush ta sauko saboda wata irin yunwa da ta tashi da ita ayau din.
Tana sakkowa falon ta samu Abbie cikin shirinsa kamar koyaushe, yana zaune a ɗaya daga cikin ƙayattattun kujerun falon. Kusa da shi ta je tare da kwantar da kanta a jikinsa.
“Abbie, ina kwana?”
Ba ta jira amsar sa ba, ta ci gaba da cewa, “Abbie, yunwa nake ji,bakaji cikina ba kamar ba hanji,yunwa tana son kashe maka ni🥺” ta faɗa cikin marairaicewa.
Shafa kanta ya yi cikin kulawa, sannan ya ce, “Gaskiya yunwa ba ta kyautawa uwar masu gida ba,inahh wace yunwa da neman ran uwar masu gida. Maza tashi ki ci abinci.”
Ya zaunar da ita sannan ya mike da kansa ya ɗauko cup mai kyau, yana ƙoƙarin haɗa mata tea.
“Ki maza ki tashi ki bar min nan wurin. Ki je ki yi wanka sannan ki sauko ki ci abincin. Wai ban hana ki fitowa haka ba dankali a kanki ba ko?”
Ammie ta faɗa tana ƙaraso wa gurin da wani babban faranti, wanda da alama breakfast ne a ciki.
Marairaicewa ta sake yi tana cewa, “Ammie, yunwa ce za ta kashe miki ni wallahi. In na tsaya yin wanka, kalli cikina ki gani Ammie, har tsalle yake.”
Ta faɗa tana ɗaga rigarta, za ta nunawa Ammie cikinta.
Ammie wacce jinjina kai kawai ta yi, tare da cewa, “Allah ya shirye ki. Ba zan iya da shirmenki ba.”
“Abbie, Bismillah,” ta faɗa tana miƙawa Abbie tea ɗinsa da ta haɗa masa.
Amsa ya yi yana cewa, “Allah ya miki albarka, sarauniyata.”
Murmushi Ammie ta yi cikin jin daɗi, domin kuwa ɗabi'ar mijin nata ce; duk abin da ta yi masa na kyautatawa, sai ya sa mata albarka tare da kalamai masu daɗi.
Inarah ta dago daga shan tea ɗin da take yi, wanda Abbie ya haɗa mata, ta kalle shi ta ce,
“Abbie, wai tsakanin ni da Ammie, to waye sarauniyarka ne?”
Ta ƙarasa maganar tana turo baki.
Dariya Abbie ya yi, saboda ya riga ya saba da shiririta irin ta 'yar tasa.
Kafin ya bata amsa, Ammie ta harare ta cikin sigar wasa ta ce,
“Waye kuwa sarauniyar sa in ba ni ba? Ni ce gimbiyar, ka ko Abbie?”
Ita ma Ammie ta faɗa cikin sigar tambaya da irin salon da Inarah ta yi.
"To wai Abbien ki ne ko nawa?inarah ta fada tana turo Baki cikin shagwaba.
"Abbie na ne mana ko?"ita ma Ammie ta fada tana turo Baki kamar yadda inarah tayi.
Abbie wanda ke kallonsu cike da ƙauna, murmushi ne a saman kyakkyawar fuskarsa, sai da ya yi dariya jin Inarah na cewa,
“Abbie, kaji abinda Ammie tace, wai ita ce sarauniya kuma gimbiya. Ina laifin ta ɗau ɗaya ta bar mini ɗaya ko, don Allah Abbie?”
Ta faɗa da irin sigar a tausaya mata ɗinnan, har tana langwabar da wuya.
Dariya sosai Abbie da Ammie suke yi, wanda ita Inarah kuwa da gaske jira take Abbie ya ce ita ce sarauniya.
Abbie bayan ya tsagaita da dariyar, ya ce,
“Duk ku biyun aikune sarauniyoyina kuma gimbiyoyi. Ke kuma gashi kin ƙara samun wani, kece mamanah gaba ɗaya.”
Ma ya faɗa da sigar wayau ga Inarah.
Aikuwa harda ihunta tana cewa,
“Yeehhhh! Nice dai gimbiyar Abbie, sannan kuma sarauniyar Zaki na.”
Ta faɗa tana ƙara murmushi sosai, wanda iyayen nata suke kallonta cike da ƙauna mai girma, wacce suke fata farin ciki ya dawwama har abada a rayuwarta.
Abbie ne ya ce,
“Hakane, ai ke sarauniya ce a ko'ina, Mamana, kuma tauraruwa mai haskaka ko'ina. Don haka kece sarauniyar wannan gidan gaba ɗaya.”
Ya faɗa yana jinjina mata kai, alamar ya Sara mata.
Aikuwa dariya take yi tana cewa,
“Inasonka sosai Abbie.”
“Inasonki sosai, rabin ran Abbie. Maza yi sauri ki gama shan shayinki ki je ki yi wanka, kin ga yau akwai meeting. Karki ɓata lokaci, kin ji.”
Abbie ya faɗa yayinda ya gama cin abincin.
Ammie ce ta ce,
“Ai inaga ba za ta yi ta gama ba, ta tsaya suturu.”
Mikewa ta yi zaram ta aje cup ɗin da ragowar tea ɗin wanda ba ta gama shanyewa ba, ta ce,
“Na koshi ma. Ni dai Ammie, ni gurin Ummee na ma zan tafi. Zaki yana can gurin shi, zan tafi.”
Ta faɗa tana ƙoƙarin fita.
Ammie ta kalleta ta ce,
“A haka ne Zaki fita saboda hankali ya miki yawa? Maza zo ki wuce ki yi wanka ki shirya, in anso in kin tafi ki kwana, ko ba komai bakina ya huta,ita Kam ummeen taki kije can kuyi ta fama.”
Kuka ta fara tana cewa,
“Ammie, don Allah ki barni na tafi, sai na yi wanka a can.”
“To na ji, Allah ya miki albarka. Amma je ki ɗauki hijab ki tafi.”
Aikuwa da gudu ta yi sama ta ɗauko hijab ɗinta, tare da zuwa ta rungume Ammie tare da sumbatar goshinta ta ce,
“I love you Ammie. Yau Yayah yana gun aiki, gani sakat, ba a takuramin ba.”
Abinda take faɗa kenan tana yin hanyar barin babban falon, wanda har ta ci karo da Mahbub, wanda shigowarsa kenan. Aikam tsarabar rankwashi ta samu, yana cewa,
“To na ji duk abinda kika faɗa, gani na dawo ai fitinanniya”
Rikewa gurin ta yi tana sosawa, tare da wucewa ta ce,
“Yaya, sannu da dawowa,Kuma se na gayawa Zaki ka rankwasheni”
Sannan ta fita cikin sauri.
Wanda shi kuwa ya daga murya yace"ki gayawa damisa inkina iyawa.
Tsakanin bangaren nasu da na su Ummee akwai ɗan tazara, amma kaɗan. Hakan ya sa ta fita tana tafiyarta cikin natsuwa, duk da akwai yawaitar mutane suna fitowa daga bangarori daban-daban a cikin estate ɗin.
Da sallama ta shiga falon, wanda yake ta kamshin room freshener mai daɗi.
Shiru falon, babu hayaniya, sai motsin da ta ji a kitchen. Tasan ko Ummee ce a ciki ko kuma mai aikin Ummee.
Dakinta da yake a wannan bangaren ta shiga, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet. Ta jima tana wanka kafin ta fito.
Ta shirya jikinta cikin wata black abaya mai kyau. Ta yi matuƙar yin kyau a cikin kayan. Ta ɗauko turare ta sa ka jikinta ta ko'ina, da yake gwanar turare ce, duk inda ta gitta sai an ji ƙamshin nan.
Tana fitowa daga bedroom ɗin nata, ta tafi ɗakin Jauhar. Ko da ta leka, bacci take sosai, kasantuwar cikin nata yana sa ta bacci. Hakan yasa yanzu ɗin ma ba ta tashi ba.
Hakan yasa ta nufo falo, inda take jin hayaniyar Afeef.
Kusa da Ummee ta ƙarasa ta zauna ta ce,
“Ummee, ina kwana?”
“Lafiya ƙalau, rabin rai. Kin tashi lafiya? Ya jikin naki?”
Ummee ta faɗa tana janyo ta jikinta tare da shafa bayanta.
“Lafiya lau na tashi. Ummee na, na shigo banganki ba dazu, shine na fara tafiya na yi wanka. Ummee, ina Zaki? Bai dawo daga motsa jiki ba ne? Sannan ban ga Abbah ba, ko baya nan?”
“Ayzaan bai dawo ba. Yanzu nake so na kira sa ma. Kun san yau meeting, kusan ko wane lokaci sai kun makara wurin zuwa. Kuna cikin gidan nan ɗin, dan haka nace ku yi maza ki shirya, indai ba faɗan kuma babanku kuke so ba, kun san halinsa.
“Abbanku kuma yana gurin Hajja. Jauhar ma yanzu tashi za ki yi, ki taso ta ta tashi a baccin nan, ta zo ta ci abinci ta shirya. Ga wannan sarkin kaye-kayen ya tasani gaba da banna, tun dazu nake bari-bari.”
Ta faɗa tana dungure kan Afeef, wanda yake kwance jikin Inarah tun shigowarta ya ƙaraso da gudu ya rungumeta.
Shafa kanshi Inarah ta yi ta ce,
“Ummee, aiki yake, tayaki. Shiyasa da ya barki shiru ke kaɗai. Gara ya sa ki busy ai ko.”
Ta faɗa tana ƙara kwantar da yaron a jikinta.
Suna zaune nan gurin, Ammie ta kira Ummee a waya. Sun ɗan jima suna waya kafin ta aje wayar, ta kalli Inarah ta ce,
“Tashi kije, Hajja na kiran ki. Kuma ban sa ki yin tsokana a hanya ba. Kin je kin gaida Hajja ma kuwa?”
“A'a, ban je ba Ummee. Ni ban son zuwa ni kaɗai. Zaki na nake jira ya zo mu tafi.”
“Ke, rabani da wani Zaki nan. Ko damisa ne? Tashi ki tafi. Inyaso in ya gama, iyayinsa ya biyo ki. Kun fi kusa.”
“Ummee, ni bana so ya je bangaren Hajja. Haka sam nake jin faɗuwar gaba. Kuma Ummee, haka waccen Maryar Aunty Farhah ɗin ta wani dinga yin iyayi tana kallonsa. Ai naga alamar sonshi take yi, kuma ba za ta aure shi ba, Allah.”
Ta faɗa tana goge ƙwallar da ta cika mata idanu, har cikin zuciyarta take jin kishin sa, da wata irin ƙaunar sa mai zafi. Hakan duk sanda wata mace ta nuna soyayya a gare shi sai ta ji kamar za ta yi hauka.
Ummee ce ta kalle ta, wani irin rauni ya rufe ta ganin yanayin da Inarah ta shiga. Za ta yi fatan ace aure zai yiwu a tsakaninsu, sedai ina, ƙaddara ta riga fata. Amma tana fatan ace wata rana wannan ƙaddarar za ta iya sauyawa.
Murmushi ne a saman fuskarta yayin da take jin ba daɗi a zuciyarta. Baki ta buɗe ta ce,
“To rabin rai, ke ba ki son Zakin naki ya auri kowa, to wa kike so ya aure shi? Ko ke Zaki aureshi ne?”
Ummee ta ce hakan cikin sigar wasa.
“Ummee, nifa Zaki zai aura, ni kaɗai a duniya. Ba zai auri kowa ba Saini. Ummee, ni ku aura min shi kawai. Allah, in Abbah ya dawo zan gaya masa haka. In aka mana aure, in ga shegiyar da za ta sake ko kallon shi. Allah, boye shi ma zan yi, ba wanda zai sake ganin sa.”
Ta faɗa hakan tana turo baki, wanda ita hakikanin gaskiyarta take faɗa.
Dariya sosai Ummee take yi sannan ta ce,
“To ke da shi, ban san wanda yafi kishi ba, tunda shi ya cire wa wani haƙori a kanki...”
Inarah ba ta bari Ummee ta ƙarasa ba, ta katse ta tana cewa,
“Ummee, ni ido zan cire ma wata ai,muddin suna kallon sa. Shiyasa kawai nace gara ya daina fita. Kin ga shikenan ko?”
Ta faɗa da sigar tambaya.
Wanda Ummee dariya kawai take yi.
Sai da ta tsagaita sannan ta ce,
“Inarah, zan yi fatan ace ku kasance a ƙarƙashin inuwar aure, ke da Ayzaan. Zan fi kowa farin cikin hakan, saidai kuma ƙaddara ta riga fata. A yanzu aure ba zai yiwu tsakaninku ba, ba ma gake ba, ko wacce mace yanzu ba za ta yiwu ga Ayzaan ba.”
Cikin matuƙar damuwa take maganar, wacce Inarah ta ji ta tamkar an daura mata aradu a saman kanta. Har wani jiri-jiri take gani a idanunta. Da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce,
“Ummee, a yau ina roƙonki domin Allah ki gaya min menene yasa aure ba zai yiwu ga rayuwar Yaa Zaaan dina ba?”
“Zan gaya miki Inarah, domin ba yarinya ba ce ke yanzu, kin san menene rayuwa ta ƙunsa"ummee ta Fadi hakan fuskar ta na sauyawa.
“Shekara uku baya da suka wuce, kin san hatsarin da Ayzaan ya yi, wanda ya ɗauke kusan shekara ɗaya yana jinya ko?”
Da sauri Inarah ta daga mata kai, domin ba ta taɓa mantawa da wannan lokacin ba, lokacin da kaɗan ya rage ba ta bar duniya ba saboda tashin hankalin da ta shiga sanadiyyar ciwon nasa.
“To a wannan lokacin ne ya samu mummunan rauni a gabansa, wanda sai da aka yi masa aiki. Kuma likita ya tabbatar cewa ya riga ya naƙasa, ba zai iya tarayya da mace ba, haka ba zai taɓa iya haihuwa ba, saboda wannan bugun da ya yi.
“Wanda duk wata ƙasa da kika sani a faɗin duniya mun je, amma magana ɗaya ce. In fact ma, Ayzaan ba zai iya jin sha'awar mace ba ma, bare kuma a kai ga wata alaƙa ta shiga tsakaninsu. Wanda duk sanda na tuna da hakan ina shiga wani hali, amma kuma Allah ya fi mu sanin dalilin yin hakan.”
Ummee ta ƙarasa maganar tana goge hawayen da ya zubo mata.
Inarah wacce ta yi kasake tana kallonta ne ta ce,
“Ummee, dama akan wannan ‘yar matsalar ake faɗin Zaki na ba zai iya aure ba?”
Kallon ta Ummee ke yi cikin mamaki ta furta,
“‘Yar matsala kika ce fa? Kalle ni nan , rabin rai, kin san menene aure kuwa?”
Ummee ta faɗa cikin mamaki akan abinda Inarah ta ce.
“Ummee, nasani mana. Tarayya tsakanin miji da mata, a taƙaice dai kwanciyar aure ko? Wacce ake samun ciki har a haihu, ko ba shi kike nufi ba Ummee?”
Abinda Inarah ta faɗa kenan cikin ƙarfin gwiwa da ƙoƙarin yi wa Ummee bayani yadda za ta yarda akan ta gane abinda take nufi.
“Tirkashi, yaushe Chuchu za ta yi hankali ne?”
Shine abinda ya furta a zuciyarsa bayan tsayuwar da ya yi na ɗan lokaci yana jin tattaunawar tasu.
Ita kuwa Ummee ta riga ta saba da zancen Inarah, tasan wannan ma kaɗan ne daga cikin aikinta. Domin Inarah akwai sakewa sosai tsakaninta da Ummee, ba ta iya ɓoye mata komai.
Ba ta bari Ummee ta yi magana ba ta ci gaba da cewa,
“Ummee, ni dan tani bamu da matsala, sai mu yi zamanmu tare da Zaki. Ba dai zai ci gaba da goya ni ba?ai yanzu ya hallata in anmana aure zamu kwana guri daya ya Goya I tunda kiri kiri aka Hana ni ko rike hannun yaa zaaan dina yanzu kuwa in aka mana aure ai shikenan mu yi wasanmu, mu yi ƙwallonmu, mu yi girkinmu tare. Ni hakan ya wadatar da ni. Didi ita kuma za ta haifa mana yara kawai, ayi mana aurenmu Ummee. Didi in ta haihu sai ta bamu yaran, shikenan fa, muma muna da yara.”
Cikin hakikanin gaskiyarta take faɗin maganar.
Ummee ce kawai ta sauke numfashi tana cewa,
“Ba ki da hankali ke kam. Dan haka maza, ni tashi ki tafi. Kiran da Hajja take Miki.
To ummee Zaki ai yadawo bari yazo mu tafi".
Ta faɗa tana juyawa ta kalli hanyar da take jin takunsa.
Aikuwa shine ya ƙaraso falon cikin shigar ƙananun kaya milk color. Sun yi matuƙar yi masa kyau, wandon iyakarsa gwiwarsa, inda rigar ta kasance T-shirt ce. Sai gashinsa da ya daure a gurin keyarsa, wanda har ya kwanto a wuyansa zuwa bayansa sai ɗaukar ido yake. Fuskarsa akwai saje mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Kafafuwansa sanye da takalma masu matukar taushi da gashi,Shima milk color.
Kallonsa take, ko ƙyafta ido ba ta yi. Hararar ta yi, kana ya ja kunnenta ya ce,
“Parrot, daina kallo na.”
Murmushi ta yi ta ce,
“Ka yi kyau sosai Zaki. Don Allah ka daina fita, kaji. Su yi ta kallonka kamar mayu.”
Ta faɗa tana marairaicewa tare da fatan ace hakan ta faru.
“Ummee, Sabahul Khair,” ya faɗa yana rungumar gefenta.
“Sabahunnur, Zaki,” Ummee ta faɗa tana shafa kwantaccen gashin nasa.
“Maza ku ci abinci sannan ku tashi ku je bangaren Hajja ku gaida ta,” Ummee ta faɗa tare da waigawa tana kallon Inarah wacce take ƙoƙarin gyara wa Afeef kwanciyarsa.
Tashi ta yi ta zuba musu abincin, ta dawo ta zauna a kusa da shi. Amsar abincin ya yi tare da gyara zama, hakan yasa ita ma ta gyara zamanta.
Cokalin ya ɗauka ya ɗiba, ya yi Bismillah, ya kai bakinta. Haka take buɗe baki tana amsa cikin shauƙin da take jin kanta a ciki, wanda ko sau ɗaya idanuwanta basu sauka akansa ba suna kansa, tana kallonsa.
Gefe guda kuma Ummee ke kallonsu, yayin da ta goge hawayen da ya zubo mata, tana fatan abinda take ayyanawa a zuciyarta, ya yiwu,sedai tasan ba abu bane dazai faru.
Bayan sun gama cin abincin ne ya mike tare da yi wa Ummee sallama, suka nufi bangaren Hajja.