RU'UYAA (The dreams we never lived)

9. ... Babban darasi...🖊️

by @autum17





tsaye nake a tsakiyar gida ina mayarda numfashi idona cikin na Mama data gama alwala, nayi ƙasa da nawa '' daga ina kike?" ta tambaya tana miƙa min butar '' gulbi '' na amsa mata ina wasa da hijabina 

Asma'u ce ta fito da tabarma ta shimfiɗa ta kabbarta sallah,duk da kamar akwai Magana bakin Mama batace komai ba... ta wuce ɗaki ta ɗauko hijabi tazo ta kabbarta sallah 

kitchen na shiga na ɗebo gari na zauna nasha bayan sun gama sallah sunyi azkar,kiran mu Mama tayi ta zaunar damu tana mana nasiha me ratsa zukata,sosai nasihar ta tashige ni kuma zanyi amfani da ita insha Allah...

washegari koda muka isa makaranta munyi latti hakan yasa aka yi mana bulala biyar biyar, muka wuce aji kuma nida Asma'u bamuyi magana ba 

Jadeedah ta lura da yanayi na lokacin break ta matsa min da tambaya babu yanda na iya dole na faɗa mata abinda Asma'u ta faɗa min plus ankoreni daga aiki sannan abincin mu ya ƙare, tayi mamaki sosai da komai dana faɗa,jakarta ta jawo ta ciro kuɗi kusan dubu biyar ta bani amma ni Abeedatu bana son yama kalmar 

🍁🍁: Favours
bana son favours gani nake kamar daga baya mutum zai min gori akan hakan 

'' rance nake baki idan kin samu sai ki biyani!" tayi saurin faɗa dan tasan tsaf zanƙi amsa... kallon kuɗin nake ina saƙe saƙe a raina,hannu na ta jawo ta tura min kuɗin '' Idan ban taimake ki ba bansan wazan taimaka ba Bee me yasa har yanzu kin kasa sakin jikin ki dani ne?" girgiza kaina nayi amma nakasa cewa komai,daga ƙarshe sai canja topic nayi '' Spelling bee nake so zan shiga Jay!" riƙo hannu na tayi cike da murna kamar ita zata shiga muka doshi office ɗin'' baki san irin farin cikin da nayi da jin haka ba,awwn,Bee ta fara girma!" Ta ƙarashe tana dariya,wani irin kallon na watsa mata '' da ban girma ba?" ɗan waro idonta tayi sai tace

 '' a'a ba irin wannan girman ba,kin kuwa fahimci cewa wannan shine karo na farko da kikayi initiating babban abu irin wannan? Oh my God Bee kin fara yarda da kanki!"

ta juyo tana jijjiga kafaɗuna fararen haƙoranta a waje,ɗauke idona nayi daga kallonta..ni ban kawo duk wannan a rai ba da gaskiyar ta fa.. murmushi ne ya wanzu a fuskata kafin kuma na fashe da dariya tana taya ni naji wani irin farin ciki ya mamaye zuciya ta..da gaskiyar Jay D 

'' you know what?" Sai ta matso kusa tare da riƙon hannu na '' I'm proud of you...ina nufin ina alfahari dake!" 

Tayi saurin yimin bayani ganin ina harararta, sai kuma ta rungume ni..da sauri naja baya ina ɗan ƙaramin tsuki

 '' such a buzz kill!" ta furta fuska a haɗe...ganin kamar bata ji daɗi ba yasa nayi dariya mai sauti sannan na matso na rungume ta

 '' ni ina abinda yafi alfahari dake!" ina jin sautin ƙirjinta a nawa tsabar yanda take tayani farin ciki...


muka nufi office ɗin event master, 

saida malamin yayi min kallon sama da ƙasa ya taɓe baki kafin ya tambaye ni sunana bayan yayi min registering ya bani wata farar paper Godiya Jay tayi mashi nidai bance komai ba saboda yanda yake min wannan banzan kallon sai naji farin cikina ya ɗan ragu '' come on,kada ki bari ya ɓata maki rai..'' sai tayi ƙasa da murya ta raɗa min a kunne

 '' nan gaba zance ya kalli madubi kafin yayi fuskarshi haka,kin kuwa ga yanda yayi kama da birin da aka shafawa lip stick da eye shadow a ɗuwawu? Harda yar powder nan ta jarirai ma!"

 Kafin in iya hana kaina na fara ɓaɓɓakar dariya...samun Jay d kusa dani babban magani ne 

lokacin da aka koma aji wasu mutane..yan mata dai kamar likitoci suka sa aka taro masu yan matan ss3 dukan mu,suka zaunar damu aji ɗaya suna mana Magana akan menturechon 

🍁🍁: Menstruation!

Ke Oti ɗin nan kin cika iyayi 🙄🙄

🍁🍁: Autumn 

koma menene, ,yan da zamu kula da kan mu lokacin jinin haila,yan mata da yawa sunji kunya akan wannan topic ɗin,amma nidai na ƙaru..daga baya suka bamu audugar mata..ni nama manta da sunan masana'antar tasu abu me muhimmanci shine nasamu pad dama wanda nake amfani dashi ya kusa ƙarewa 

idona ne ya haɗu dana wani malami shima dai danginsu macijin sari ka noƙe..ɗauke idona nayi suka sauka akan Macijin sari ka noken shima kallo na yake..mamaki nayi wannan ai abinda ya shafi mata ne to me maza sukeyi a wurin? tsuki naja Batareda nasan danayi hakan ba..duk aka wani juyo ana kallo na fuskewa nayi kamar bansan ni ake kallo ba...

bayan an kammala wannan bayane bayanen muka koma aji,kowa sai maganganu suke

'' wai a canja pad duk bayan awa huɗu hauka ake?" Muhsina ta faɗa, A'ishah ta taya ta faɗin

'' sun raina ma kansu wayo kuɗin haƙo su ake ko kyauta zasu bamu?"

'' hmm..Ni wallahi idan nasa wannan abu wuni nake dashi ina naga kuɗin canjawa duk bayan awa huɗu?" Hafsa ta ƙara 

'' ku gara kuma kuna da kuɗin siya,nidai idan ba kyauta aka bamu ba saidai inyi amfani da tsumma ato '' inji Labeebah

'' Amma dai kunsan kasancewa da wannan abun a jiki na tsawon lokaci yana da illa ko?" 
'' pftt!! To illa ta nawa kuma? ai saidai ɗan baƙari!" muhsina taba Fateema amsa nida Jay D muka bisu da ido bamu ce komai ba 

ana tashi daga makaranta motar su jay d tazo ɗaukar ta,duk yanda tayi in shigo su rage min hanya naƙi dole ta barni 
.shagon su Saleh na tafi har yanzu baiji sauƙi ba dan haka bai dawo duty ba
.shinkafa tiya huɗu na auno mana na haɗa da wake da taliya sai kuma garin kwaki duk da yanda bana sonshi amma yana iya? Daga nan na haɗo da magunguna da kuma kayan miya sannan na bar wurin raina a sake..kuma har yanzu Ban biya buba mai kayan masarufi kuɗinshi ba

da Mama ta tambaye ni inda na samu kuɗin ban ɓoye mata ba..gyaɗa kanta tayi fuska ba walwala.. Asma'u tayi mana shinkafa dafe duka da wake ta kumayi mugun daɗi 

bayan mun gama cin abincin wanka nayi na shirya cikin kayan aiki na nayi masu sallama na fita... zuciya ta cike da nauyi na fara zageye zagayen gari ina neman aiki ido rufe amma har lokacin tashi daga aiki na yayi ban samu ba 

kusan kullum haka nake abun ya zame min jiki harna ma manta da wata rana za'a iya kamani..a ɗayan ɓangeren kuma ina nan ina koyon wannan mugun spelling Bee ɗin,a gida Mama ke koya min dan dama tayi daga primary zuwa secondary a makaranta Jay D, Asma'u bata da aikin yi sai gwale ni amma bana bi takanta.. oh itama ashe harda ita cikin masu yin spelling bee ɗin...

Jay D dai Saida ta ƙara nanata min cewa Asma'u kishi take dani amma har lokacin banyarda ba kuma bazan taɓa yarda ba..duk bata da wani uzuri nayimin abin da take min 

lokacin da wata ya ƙare Mama nata zuba ido inkawo albashi sai nuƙu nuƙu nake..turnuƙe ni tayi akan saina faɗa mata gaskiya,cikin hawaye na sanar da ita an kore ni aiki 

bata ji daɗin ɓoye matan da nayi ba... Daga nan itama ta shiga neman aiki haka ma Asma'u na tsawon lokaci babu wanda yazo neman kitso da lalle wurinta...

gaba ɗaya sai abubuwan ƙunci suka ƙara yimin yawa, Mama na matuƙar ban tausayi ina kuma baƙin cikin ganin ta tana yawo gida gida neman aiki ban ƙarajin cewa niɗin mara amfani bace sai da na farko da daddare naji Mama na kuka saman sallaya tana koro addu'oi... ji nayi wani sabon ƙunci da baƙin ciki sun mamaye ni dama na lura kwanakin nan kamar ƙasan idonta yayi duhu sannan idonta sunyi ja,na ɗauka rashin baccine ashe ba haka ba...

da safe ma da muka tashi ɗan abincin dana kawo ya ƙare babu komai har gari, muka koma talakawa talaf talaf kullum sai Mama ta bamu haƙuri akan gazawarta amma ni a ganina nice na gaza... da wannan dalilin ɗan iska Macijin sari ka noƙe yayi ƙoƙarin lalata Asma'u da alƙawarin zai biyata Alhamdulillah kafin yayi mata illa na ganoshi har office ɗin principal nakai ƙarar shi duk da nasan ba wani abu za'a yi ba dan baban shi ƙaramin ƙwaro ne a gomnati...

na ƙara shiga tashin hankali bayan na fahimci abinda Asma'u ke shirin yi kenan.. rayuwar mu ta wani irin ƙuntata musamman ni...damuwar su itace damuwa ta,farin cikin su shine nawa naga nawar ayi ayi wannan spelling bee ɗin in samu kuɗin da gidan in fitardamu daga wannan ƙangin rayuwar... wata rana aka tara mu ake faɗa mana anfasa spelling bee ɗin..ji nayi duniyata ta faɗo ta ruguje duhu ya sake mamaye ni..ɗan spelling bee ɗin dana ƙwallafa rai akai... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ranar nasha kuka kamar raina zai fita amma duk da haka ban dena karatun spelling bee ɗin ba sannan mu dukan mu bamu dena neman aiki ba

har na tsawon wata uku rayuwar mu ta cigaba da gudana cikin ciwon rashi..da ƙyar muke samu muna ci muna sha,ba sau guda ba ina kama Mama tana kuka hakan ba ƙaramin karya zuciya ta yake ba..kuma yakan ƙara tunamin dacewa na kasa sharema ƙanwata da mamata hawaye...gefe ɗaya kuma ga self esteem ɗina dake ƙara raunana ƙila ma ya ƙate tass yanzu dan kamar idon kowa ya dawo akaina ne ko a makaranta haka idan ana bada misali sai ayi dani,,,harda ji nayi wata me suna Saddiqa tana faɗin '' abuna kamar na ƙananan yara..ita ta kasa ganewa koni macece ko akasin hakan...'' kasa tsayawa nayi inji ta har ƙarshe dan kuka ne yaci ƙarfi na meyasa bazan iya jurewa ba in basar kamar ban damu ba? ko faɗa muke daga sanda aka zagi halitta ta shike nan an gama wannan faɗan sai kuka 


 da misalin ƙarfe huɗu ina zaune a ƙarƙashin bishiyar mangoron nan na kusa da gida saman benci.. hannu na riƙe da spelling bee ina karantawa saye da uniforms ɗina Dan banso in koma gida, jinginar da kaina nayi na jawo jakata ina duba pen dan inyi ticking kalmomin da ban iyaba,

 na ɗauki pen ina maki har na gama mayarwa nayi na sake jinginar da kaina ina tunanin yauma haka zamu kwana ciki rabbana? ƙamshin turaren shi ne kamar kullum ya shiga hancina kafin naji zaman shi kusa dani idanun shi akaina..zuciya ta tashiga bugu da ƙarfi... wani irin zafi ya turnuƙe ni daga ciki har waje,na rasa dalilin dayasa nake jin haka a duk sanda yake kusa dani,ƙila saboda yana da kyau ne kuma ni ga yarda nake

'' Kitten...'' ya kira ƙasan maƙoshi,matse ƙafafuna nayi da idona kafin na shiga buɗe su ahankali ganin shi nayi zaune kusa dani dama kuma nasan yana kusa dani ɗin '' Meye kuma wani kichin can?" na tambaya gira ɗage

batareda ya dena kallona ba murmushin shi a faɗaɗe yace '' kitten..na nufin jinjirar mage...'' wani irin tashi zaune nayi da kyau ina hararar shi a ƙufule nace '' oh,wato ni kake haɗawa da mage ko? nayi maka kama da mage ne?" wani irin lumshe idanunsa yayi tareda tallafo gefe da gefen fuskarshi da hannayen shi
yana bina da kallon ƙasan ido da yasa zuciya ta neman fitowa ta baki yace '' Eh mana, musamman idanun ki... da yanda kike min tsiwa kullum idan mun haɗu..i like your eyes.. they're beautiful!" 

Ƙifta idona nayi cike da jin haushi nace '' na faɗa maka ban jin turanci ka dena min turanci amma baka ji!" dariya kaɗan yayi sannan yace '' Allah ya gafarci ranki ya daɗe..bazan sake ba!" ɗauke kaina nayi daga kallon shi 

'' Abeedah...'' ya kira irin yanayi da ban fahimta ba, juyowa nayi idona suka shiga cikin nashi a wani irin kasalance yace
'' ina son Idanun ki... suna da kyau sosai!"  

Naji  kamar shock ya ziyarci ilahirin gangar jikina,kamar yanda mutum zaiji idan ya taɓa wayar nepa...banan kaɗai ba harda wani wurin da bazan iya faɗa ba...'' a'udhu billahi '' na faɗa cikin raina ina ɗauke kaina daga kallonshi,wanda shi a wurin shi a bune me wuyar aiwatar wa dan dai ya cigaba da kallo na '' toh ko cirewa zanyi in baka?" Yana wani shu'umin murmushi ya jinginar da bayanshi ga bishiyar '' gashi ban zo da kayan aiki ba da mun gwada...'' sakin baki nayi da abinda ya faɗa...na ɗauke ido na daga kallon shi...


 '' muzama ƙawaye mana!" ya sake furtawa a kasalance to ko bacci yake ji? Ko dai shegantaka ce irin ta maza yake ƙoƙarin gwadawa a kaina? Na kalle shi da takaici a fuskata kafin na maƙe kafaɗa '' Pls!" ya furta da murya me zurfi ya cigaba da faɗin '' ko nawa ne zan biya just pls ''

miƙewa nayi na ɗauki jakata shima ya miƙe batareda na kalleshi ba nace '' matsalar masu kuɗi gani suke kamar zasu iya sayen kowa...'' 

kallo na yake da damuwa jin abinda na faɗa shiba haka yake nufi ba sam '' ki fahimce ni..''

'' shhh..!" na katse shi ta hanyar ɗaura hannu na a baki na,ragema idona girma nayi sannan na ƙara da faɗin ''bakada kuɗin da zaka saye ni KHALIL!" na juya na tafi 

Yabi bayanta da kallo'' hmm fiesty little kitten! we're tangled" ya furta word by word sai ya juya yabar wurin

dana koma gida ganin Mama da Asma'u nayi suna dawowa daga inda ban sani ba na matsa na gaida Mama ta amsa da tambayar ina nake..kawai na faɗa mata ina zaune ƙasan bishiyar mangoro.... 

washegari da muka tafi makaranta a mugun mugun bazata aka kwashe mu yan spelling bee muka tafi kwampetishon..babu wanda ya shirya cikin mu sai Zufa muke 

wasu harda hawayen tsoro Asma'u taso ta dizgani gaban mutane amma hakan bai yiyu ba
lokacin da muka isa mun ɗauka round round ne abun idan an zubar daku wannan round ɗin zaku iya shiga a wani round a wani sati amma ba haka bane, round guda ne makarantu biyar harda tamu... Sannan kowa kanshi zai amsa mawa ba kamar yanda muka tsamma ta ba 

tashin hankali mun shige shi, musamman ni, ganin anata zubar da mutane masu kwanya ina gani danake daƙiƙiya? lokacin da aka kawo kaina jikina ya hau ɓari dole aka tsallake ni aka yima wa'yanda suka shirya...

mafiyawancin su ko point guda basu samu. da aka kawo kan Asma'u harda wani ɗan iskan kallo tayimin irin na ki kalla ki koya

amma sai Asma'u tayi dumkun kum da aka tambaye ta sai rarrabar ido take, tama ƙasa magana ko tsoro take ji ne?..

nice ta ƙarshe kuma Alhamdulillah na samu point uku cikin biyar... ba ƙaramin mamaki kowa da kowa yayi ba harni kaina 

daga ƙarshe akayi announcing result,gidan nan dai da nayi burin samar mana na sameshi harda ƙarin dubu ɗari biyu...

Wasu yara daga wata government school sukayo na ɗaya da na biyu sai wata yarinya itama tayo na na uku ni nayi na huɗu exactly position ɗin da nake so.... kuma fa ba mata kaɗai bane akwai maza

yan makarantar mu sun tayani murna ba kaɗan ba banda Asma'u data yi kamar zatayi kuka har na tanadi maganar da zan faɗa mata amma ganin yanayin ta yasa nayi shiru 

nan gaban jama'a aka mallaka ma kowa mukullin gidan dayaci kuɗi cikin envelope 

nayi matuƙar farin ciki harda hawaye shikenan matsalar mu taƙare...

da muka koma makaranta dubu ɗari aka barni dasu, dubu ɗari kuma wa'yanda muka tafi tareda su dasu malaman dasu ka kaimu suka raba...

da gudu na isa gida na faɗa jikin Mama na fashe da kuka, lallashina ta fara duk da batasan dalilin kukan ba saida na huta daga kukan sannan na faɗa mata aiko ta faɗi tayi sujoodush shukoor bawai dan abinda naci ba, a'a karo na farko dana nuna cewa niba daƙiƙiya bace.. tayi murna sosai tamin addu'a 

Asma'u kuwa kamar xatayi kuka Mama ta ɗauka Saboda bataci bane ta dinga lallashinta amma dalilin wani abune daban...

makullin gidan na miƙa mata ta karɓa ta ajiye tareda kuɗinu

'' yaushe zamu koma gidan Mama?" jim tayi kafin tace a sanyaye '' yaushe kuke so mu koma?" '' ko ranar Lahadi haka '' na bata amsa 

'' Allah ya kaimu!" 

washegari da muka tafi makaranta harda assembly aka tara don a karramani yan ajin mu sun kasa yarda wai tuwo tayi na huɗu da addu'a suka bini, lokacin munyi sharholiya duk dan su tayani jin daɗi...

ranar da muka koma gida bayan mun gama cin abincin mun huta muka shirya muka tafi unguwar da gidan yake, unguwar masu ƙaramin hali ce dai kamar tamu amma hanyoyin wannan unguwar sunfi na tsohuwar unguwar mu kyau,daɗi da ƙari bishiyar kashuna ( cashew nut) daidai ƙofar gidan mu har tayi mashi runfa kaɗan...

sauke mu me mashin yayi daidai ƙofar gida Mama ta biyashi kafin ta buɗe ƙofar da mukullin,zauren gidan anyi cementi a ƙasa haka ma bangon anyi plaster.. tsakiyar gidan m haka,ɗakuna biyu ne suna kallon juna sai dakalin da aka sama tiles a tsakani 

Sai kitchen da baye sosai gidan ya burge Ni , Asma'u kuwa a ƙuntace take har lokacin, Mama nata yaba kyaun tsakar gidan...cikin ɗaki Munyi mamakin ganin akwai komai da muke buƙata sannan harda baye 

Akwai gado da wardrobe da dressing mirror harda TV a ɗaya daga ɗakunan, sannan tiles ne a ƙasa ɗakunan suna da faɗi sosai komai sak... saidai ɗakin da nida zamu zauna ba tv...

sosai Mama take samin albarka, bayan mungama ganin gida muka koma...

nan na gane cewa, wasu lokutan zama me ƙoƙari bai wadatar ba idan babu aiki tuƙuru sannan mutum ya zama me tawali'u sai ya fita daga kunya,girman kai da jiji da kai bashi da amfani 

kuma mafi girman darasin dana koya shine kawai mutum na zama abunda ya yardar ma kanshi ne,ni ba daƙiƙiya bace na zama hakan ne kawai dan nayarda niɗin daƙiƙiya ce da gaske...