JA DA BAYA...

THE BAD DREAM 😲

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 45 ✍️*

***

Ya ƙwashe tsawon lokaci yana wannan ɓaccin nasa, wanda yake cike da mafarkai kala-kala, dakyar ya iya yaƙi da abubuwan da suke zo masa a baccin nasa sannan ya tashi cikin matuƙar kasalar da baccin ya saukar masa.

Ya ɗan jima a haka kafin natsuwarsa ta fara dawowa.

Ya jima zaune yana tuna wasu abubuwan da ya gani a mafarkin nasa wasu kuma ya kasa tunasu, addu'a ya ke yi sosai a zuciyarsa idanuwansa suna rufe ba tare da ya buɗe su ba.

Tashi ya yi ya shige ɓandaki kuma har zuwa lokacin addu'a ya ke yi a zuciyarsa.

Ya jima sosai a ɓandakin ƙafin ya fito, sanye da rigar wanka, fatarsa me matuƙar haske har wani ɗauƙar ido ta ke yi, kai kana kallon yanayin tsarinsa bazaka  so ka ɗauƙe ido a kansa ba.

Gurin mirror ya nufa, ya fara shirya kansa, cikin ƙasaita yadda kasan bazai gama ba, ko mace bazata tsaya wannan iyayin ba. Kitson da yake kansa wanda kamar yanzu a ka yi masa sabida kyan da ya yi akan nasa.

Bayan ya gama shiryawa ya gyara komai ya mayar inda yake,ya ɗaƙƙo kayan shan iska ya Saka sannan ya fita daga bedroom ɗin ya nufi babban falon gidan.

Da Ammie ya haɗu wacce ta fito daga kitchen riƙe da food flasks ya nufi ɓangaren dining. Tana ganinsa ta saki murmushi tace "zakin Ammie da Abbie an tashi a baccin kenan? Na shiga na ga kana ta bacci, nace bari na barka ka huta da kyau ko ka samu sassaucin gajiyar tafiya, zo ka ci abinci na san yunwa ka ke ji" Ammie ta faɗa hakan tana janyo plate tana yin serving ɗinsa.

Ai kuwa bai yi musu ba ya nemi guri ya zauna yana faɗin Ammie yunwa na ke ji sosai, kamar ban taɓa cin abinci ba" ya faɗa hakan a shagwaɓe. Yana Bismillah zai fara cin abincin ya tsinkayi muryar Mahbub na faɗin "ohhh ni Mahbubu,abu ɓanɓaraƙwai namiji da suna Hajara, yi yadda ka ke turo Baki kamar wancan me bakin tsuntsun 🤔 dama wuce gado ai wuya gare sa, hausawa sun yi gaskiya, inda saniyar gaba ta sha ruwa, ta baya ma in ta zo anan zata sha" Mahbub ya faɗa haƙan yana zama shima a ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin.

Ko kallonsa Ayzaan bai yi ba ya fara cin abincin sa,domin yasan mahbub din so yake kawai yaga yasashi surutu. Ammi kuwa tana ta ma Mahbub tsiya cewar ya cika surutu da yawa yana matsawa Ayzaan ɗin, haka dai Ammie ta bar dining ɗin ta bar su suna cin abincin, dama kuma shi Ayzaan in ya na cin abinci baya magana har se ya gama.

Suna gama cin abincin gaba ɗayan su suka miƙe zuwa ɓangaren Hajja da Innah, domin dai Ayzaan zai shiga yi mata sallama haka Mahbub zai kai mata magani.

Daga nan zasu yi ɓangaren Innah itama Dan duba ta da yi mata sallama. Gaba ɗaya Mahbub baya son tafiyar ta Ayzaan ba yanzu ba duk wani lokaci da Ayzaan zai bar ƙasar domin buga wasa, haka zai ta jin kewa sosai, haɗuwa goma se sun yi faɗa, amma kuma Mahbub baya ƙaunar su yi nesa da juna, haka kuma shima Ayzaan ɗin.

Ɓangaren Inarah kuwa tana can ta gama aikin da ya Saka ta, tana ta jiran dawowarsa amma shiru ba shi ba alamar sa, tana ta tinanin to ko ya dawo ne ya biya wani guri, haka ta yita duba lokaci har ta gaji ta kwanta a kujera tana kallo bacci ya ɗauƙe ta.

*_**_**_**_**

Yanayin da ake ciki yasa kowa ya ke ɗari-ɗari akan fita zuwa babban titin bypass, domin kuwa in ka fita kana fargabar zaka dawo da ranka ko kuwa gawarka za'a dawo da ita. Haka suma ƴan uwanka ko yayan ka suna cikin taraddadin abinda zai faru da kai, domin kuwa babu rana ta duniya da zata fito ta faɗi ba tare da ance an yi hatsari mutun kaza sun mutu ba, to hanyar ba ta da kyau, gyara a ke yi, kuma wannan titi shine hanyar wucewar masu manyan motocin, masu mashina masu Keke da masu ƙananan motoci, haƙa kuma wanda zai tsallaka shi ma ta hanyar zai bi.
Sannan hanyar ta hada manyan anguwanni Wanda dole sai anbi, Hakan yasa kullin al'ummar wannan yankuna suna cikin taraddaɗi.

Sai dai haƙan yasa gaba ɗaya mutane sun rage yawan zirga-zirga.

yanzu kuwa kasantuwar abin yayi sauƙi sosai tunda an ɗau satittika komai bai faru ba yasa kowa ya cigaba da harkokinsa.

To kamar nan yadda aka Saba,anan  ɓangaren ma haka, wasu yara ne na gani su biyu, suna ta shiri da alama fita zasu yi.

Muryar maman na jiyo daga falo tana faɗin "Maryam wai baza ku yi sauri ku zo ku yi ku tafi ba! Baku ga rana ta riga ta yi ba in yamma ta yi babu inda zaku je se kuma wata ran" ai kuwa da sauri yaran sun fito kowacce na faɗin" mama yi haƙuri yanzu zamu wuce".

Kuɗin mota ta ɗaƙƙo ta ba su tare da musu gargaɗi akan su kula da hanya, sannan su gai da ƙanwar tata wacce gurin ta suka shirya ranar suka ce zasu je domin gaishe ta. Cikin farin ciki su biyun sun fita daga gidan Maryam da ƙanwarta Khadija, ƴanmata ne dukkansu babbar sheƙarar ta sha bakwai ƙanwar kuma sheƙara sha biyar.

Suna fita kuwa har zasu je baƙin babban titi su hau mota ƙaramar tace ma yayar ta kawai su hau mashin yafi musu sauƙi ya sauke su har ƙofar gida, hakan yasa su samu mashin suka hau su biyun domin zuwa inda suka yi niya.

Tafe suke akan mashin ɗin cikin yaƙini na cewar zasu je lafiya su dawo lafiya, suna tafe suna hira suna dariya ƙanwar tana tsokanar yayar tata cikin ɓarƙwanci kamar yadda suka saba.

Cikin matukar farin ciki suke da ziyarar da zasuje yi,haka cikin nishadi suke tafe a mashin din.

Babu zato Babu tsammani, ba gudu suke na wuce ƙa'ida ba, amma haka ƙatuwar mota ta tayi kansu, wanda kafin ma me mashin ɗin ya Ankara ya kauce, me afkuwa ta afku, wannan mota ta take waɗannan yara guda biyu wanda take a gurin sun mutu ko shurawa basu yi ba, me mashin ɗin kuwa shine akwai sauran rai a tare da shi, sai dai shima Babu yaƙinin cewa zai iya rayuwa shima.

Kamar kuma yadda masu aikata ɓarnar wato masu manyan motocin kafin mutane su sukai ga ƙarasowa tuni wannan mai babbar mota ya gudu ya bar gurin, domin kuwa dira ya yi a motar ya gudu ya bar gurin.

Haƙa mutane sun taru a gurin cikin cikin matuƙar tashin hankali da ƙaɗuwa ganin yadda gaba ɗaya kan yaran ya fashe ya ke zubarda jini gaba ɗaya kansu ya yi daga-daga wanda ko kamannin ɗaya a cikinsu baza a gane ba.

Da yake akwai waya a tare da su hakan yasa a ka ɗau wayar a ka kira number na ƙarshe wanda sukayi waya da ita, wato Auntynsu wacce zasu je gidanta.

Cikin wani irin matsanancin tashin hankali ta ƙaraso gurin, ko gabanta bata gani sabida wani irin kuka da ta ke yi. Yaran sun kusa zuwa gidan nata domin suna fita a babban titin kwanar da zasu shiga shine zai kai su har gidan nata.

Haka dai a ka Saka gawarwakinsu a ambulance ana nufi gidan iyayen su da su.

Babu zato Babu tsammani ambulance ta faka a ƙofar gidan, wanda mutanen gidan Dana unguwar suka taso domin leƙen shin me wannan mota ta zo yi a gidan.

Ita kuwa mahaifiyarsu tana zaune a ƙofar ɗakinta akan kujera kamar an ɗaure ta ko motsi ta ƙasa yi bare itama ta bi ayarin masu leƙen Dan ganin abinda yake faruwa.

Abu ɗaya ta tsinkaya ihun mutanen gidan wanda suka leƙa tare da jiyo sautin kukan ƴar uwar ta, bata dawo daga tunanin me yake faruwa ba, jami'an suka shigo da gawar yaran guda biyu wanda suturar jikinsu gaba ɗaya ta wanke da jini, har zuwa lokacin kuma kansu bai Dena zubar da jini ba.

Take gidan ya ɗau wani irin koke-koke da ihu, wanda tuni ƙofar gidan ba ma Saka tsinke.

Mahaifiyar yaran kuwa abinda kawai ya fito a bakinta shine "Babu abin bautawa da gaskiya se Allah, Allah duk abinda ka yi dai-dai ne, ka bani iƙon cinye wannan jarabawar" Wani irin kuka ne me tafe da ɓaƙin ciki ya kufce mata, wani irin raɗaɗi ta ke ji wanda baza ta iya misaltawa ba 😭😭.

Haka a ka yi wa yaran sallah tare da kaisu gidansu na gaskiya, mahaifiyar su kuwa bata ƙara cewa komai ba har zuwa lokacin da a ka gama yi wa yaran sutura a ka kai su gidan su na gaskiya.

Haka Kuma har a ka yi kwana uku ba tare da hukuma ko kuma wasu masu faɗa aji sun yi ƙoƙarin ɗauƙar mataki akan al'amarin ba domin kare rayukan bayin Allah.

Mahaifiyar yaran kuwa komin rashin imaninka ka ganta se ka tausaya mata,ba uhmm ba um'um bata iya cewa komai,domin irin wanna mutuwa ta yara har guda biyu lokaci ɗaya abu ne mai wuyar mantawa.

 Ita kuwa Aunty tasu wacce zasu je gurin ta har se da a ka kai ta asibiti sabida tsananin tashin hankalin da ta ke ciki.

 Haka iyayen wannan yara suka dauki dangana,domin hakan dama ya Saba faruwa, hukuma Kuma  bata iya yin komai a kai, su kuma masu manyan motocin basu fasa gudun ganganchi suna take kawunan bayin Allah ba,domin kosun aikata ma suna iya guduwa ba tare da anyi masu komai ba.

(Ya Allah ka ƙara kiyaye al'ummar musulmi a duk inda suke 😥 ya Allah duk waɗanda suka rasa ƴan uwansu ko iyayensu ko ƙannen su, ko yayan su ta hanyar hatsari 😥 ubangiji ka ƙara ba su juriya da haƙuri, ka sa aljannah ta zamo musu makomar wahalar su da mu baƙi ɗaya 😭🤲🤲)