RAYUWAR DAN ADAM

1

by @mahmazee1

BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM

      INDEED ALLAH IS THE BEST OF PLANNERS 



     Yinin yau na ranar juma'a ya zo da yanayi mai dadi da weather mai sanya nutsuwa a jihar Kaduna.

  Yini ne da ya zo da tarin farin ciki da exceptional moments a Gidan Alh Sanusi Chiroma, wanda ya ke cike da dan mutum, ba maza ba, ba mata ba, ba yara kanana ba, Ana ta kai kawo a harabar gidan, sai ko manya manyan luxurious motoci da ke saukewa da daukar guests, da kuma daidaiku da suke a kafa.


   Duk fadi da girman harabar gidan an cinye sa da decoration mai daukar hankali da burgewa in traditional setting, wanda aka yi in preparation for hidimar da za'ayi ta lunch.


A yau aka daura auren yar sa Kareema a katon masallacin da ke gaban gidan sa hakanan kuma a yau din mata ke ta kai da kawon yini da ake yi da kuma lunch da za'ayi zuwa anjima kadan.

    Decoration din mai burgewa ne wanda kai ba sai ka tambaya ba kasan ba kananan kudi ya lashe ba, masu aikin catering na ta kai kawo da abinci da Kayan shaye shaye wato drinks.


    A cikin gidan kuma, a dai dai wannan lokacin wata dattijuwar mace in her 40's, itama cikin adon ta mai burgewa ta ratso katon falon Haj Umaimah wato Mami kamar yanda 'ya'ya da yaran gidan ke kiranta.


   Mami ta kasance uwargidan Alh Sanusi kuma uwar amarya kareema da ake hidimar ta, ta na zaune tsakiyar yan uwa da ma mutanen ta na arziki da suka zo taya ta murnar auren autar ta.

   Mami ta sha ado har ta gode Allah cikin wani Hkg Guipure lace tana ta baza iko kamar yanda ya kasance dabi'ar ta.


   Dattijuwar matar da ta shigo falon ta gaida mutanen falon tare da nufar Mami kai tsaye Tana fadin "wai ina amaryar ta shige ne Mami, su Uncle Bashir na ta neman ta falon Alhaji zasu yi hotuna, kinsan zasu juya Bauchi yau"


   Mami ta kalli abokiyar zaman ta Ramatu, wacce kusan kowa ya fi sani da Aunty, Aunty matar Alh Sanusi Ciroma ta uku, amarya kuma wace a kan ta ya rufe kofa, hakanan mowa a gurin sa kamar yanda sauran mata, 'yaya da yan uwan sa suke gani.


    Mami ta dan yi yake kadan tace "a'ahh uncle Bashir har zasu juya haka da wuri, ai kuwa tana ciki da sauran yan uwanta, ina ga sai kin Sanyo ta gaba kar su bata musu lokaci"

  

   Aunty ta gyada kai ta nufi corridor Mami tunda sashen ba bakon ta ba ne, hakanan tsari da ginin part din Mami daya ya ke da nata, hakanan daya ya ke da na Mumny matar Alh Sanusi ta biyu.

   

    Aunty tayi knocking daya daga cikin dakuna uku da ke jere corridor din, kafin ta turo kofar dakin da yake mallakin kareema a sashen.

    Amarya kareema na zaune tsakiyar yan uwanta mata da kuma daidaiku daga cikin in-laws din gidan wato matan ya'yan Alh maza, ta yi kyau na kin Kari cikin wani magenta material da akayiwa bridal dinki, tayi kyau sosai domin dai Alh Sanusi Allah yayi masa arzikin kyawawan 'ya'ya both matan har mazan.


  

Shawarwari yan uwanta ke bata, kamar kowace amarya a daidai irin wannan lokacin, da dubaru na daukar hankali da nutsuwar da namiji.


Yah Hadiza, babba gabakidaya daga cikin 'yayan Mami mata ta kalli yar uwarta tana dorawa da

 "Sai kinyi hankali da tarkacen kawayen nan naki domin ba abin yadda ba ne kareema, before you know it sai ki ji wani labari daban"


  Duka yan dakin suka gasgata zancen Yah Hadiza domin duk wanda ke gidan ya kwana da sanin tarin tarkacen kawaye irin na kareema 

    Kareema ta turo baki gaba jin yanda suka yo mata chaaa, tunda aka soma shirye shiryen auren ta Yah Hadiza bata da zance sai na kawayen ta, aka ce musu ita bata San abinda take yi ba, ko kuwa shikenan saboda tayi aure sai ta watsar da mutanen ta na arziki, ta ga dai itama fa tayi yawon gidan kawayen ta da sukayi aure a lokacin. 


   Tace "toh ni ina ruwan su da miji na yah Hadiza, tunda ko sunzo ba wai ganin sa zasu yi ba" ta fada tana dauke kai 

    Hadiza taji haushin abinda ta fada tace "toh shikenan ke kika sani, tunda ke kin fi karfin shawara"


    Aunty da ta shigo dakin, ta sauke kallon ta akan ya yan mijin ta mata da suka cika dakin wanda wasu daga cikin su zasuyi kusan sa'anni da ita duk da dai babu wacce tayi sa'ar ta, duka ya yan Mami da na Mummy (wato matar Alh ta biyu) da in-laws din su suna dakin, kowa yana nan idan ka cire yaran dakin ta, Aunty tayi kwafa kawai yin wannan tunani.



    Aunty Ta kalli Hadiza tace "aa ba zaayi haka ba Hadiza, hakuri zaayi tayi Ana tsawatar wa"

    Hadiza tace "bar ni da ita kawai Aunty, rashin kunyar yarinyar nan yawa ne da shi"


     Aunty dai ta bar zancen a ranta tana raya ita kuwa tasan rashin kunyar Karima, domin ko a cikin ya yan mijin ta Karima na daga cikin wadanda basa raga mata, musamman Kareema din, sai ta kawar da zancen kawai tana fadar

 "Alh na neman Amarya falon sa, zaayi hotuna da su uncle Bashir"


   Jin haka duka yan uwanta suka ce zasuyi mata rakiya zuwa Falon Alh, tare suka rankaya falon har Aunty zuwa sashen Alh wanda ya fita daban da na matan sa.


    A falon sa suka tarar da mahaifin su da uncles din su


     Alh sanusi ciroma dattijon tsohon da zai yi kusan saba'in a duniya, kamilallen mutum da mutane ke girmamawa saboda kawaici da mutuncin sa, wanda ya nutsu cikin ilimi both na muhammadiya da na malam bature, cikakken bafulatanin Bauchi, kamar yanda uwargidan sa da matar sa ta biyu suka kasancen duka yan gari daya wato fulanin Bauchi.



    Mami yar Asalin Bauchi ce, a can Alh ciroma ya ganta a gidan Aminin sa Moyijo wato yayan mami har aure ya kullu a Tsakanin su.

 A Bauchi suka soma zama suka kuma hayayyafa har zuwa lokacin da Alhaji ya qara aure da yar uwar sa Maimunatu wato mummy, a lokacin ne ya tare a garin kaduna da iyalin sa, mummy ta kasance yar uwar Alh wacce suka taso gida daya domin yar gurin baffan sa ce, hakan ya sanya ko hidima ake a gidan most of yan uwan sa a bangaren ta suke sauka.



      Aunty kuwa zamu iya cewa da girman sa ya aure ta, domin kuwa har manyanci ya soma kama sa a lokacin, hakan ya sanya itace da kananan yara a gidan, domin ko Karima da take autar mami ta girmi Salma wacce itace 'yar ta ta farko da Alh, sai dai kafin nan ta taba Aure Allah yayiwa mijin ta rasuwa, a lokacin ne Alh ya ganta ya aura.

  


   Aunty yan Asalin kasar nijer ne da kakannin su sukayo balaguro Nigeria, tun zamanin da da ake zuwa saudiya by road (wato a manyan motoci), sai dai tun a Nigeria Kakan su Ali, buzun jihar Niger dan garin Diffa yayi masauki a Kano, tafiyar da bai yi ba saudia kenan saboda harkar kasuwanci da ya samu a nan jihar Kano, kafin daga baya ya dawo kaduna gabakidaya. wannan ya sanya lokuta da dama idan sabani ya shiga tsakanin Aunty da matan Alh sukan yi mata gorin asali.


     Alh ciroma ya kalli ya yan sa cikin alfahari da kuma godewa ubangiji da yayi masa arzikin ganin ya wanke dukkanin ya yan sa mata da ransa, idan ka cire Salma wacce ta kasance auta a cikin mata, hakanan yanzu ta ke a SS1 na babban sakandiri.

      

Sautin takun Christian louboutin high heels din ta ne ya cike falon kafin bayyanar ta cikin kyakkyawan ado mai tafe da class da daukar hankali, kyakkyawa ce sosai domin komai kushen ka ba zaka Kira ta da mummuna ba.


   Daga gani ita ma din tana daga cikin 'ya'yan Alh Sanusi ko don kamanceceniyar da ke tsakanin ta da mahaifin ta da ma sauran yan uwanta mata, hakanan tana cikin ankon atamfar Embroidery Sheraton da 'yayan gidan suka yi a yinin yau.


Ta dauki hankalin mutanen falon musamman yan uwanta da ke kallon ta full of admiration, NAJMA kenan yarinyar mami, hakanan wacce amarya kareema ke biwa.



     Tasha ado cikin dinkin ta mai daukar hankali wanda ya zauna das a dan karamin jikin ta kasancewar ta siririya sai dai tana da tsayi, tayi accessorizing kayan ta da asalin jewelries din English gold, ta ke falon ya kama da fitinannen kamshin turaren Dahlia by Versace da ke fitowa daga jikin ta.



     Ta tako cikin yauki kamar wacce bata son ta ka qasa, Kana ganin NAJMA zaka fahimci ta fita daban ko a cikin sauran yan uwanta, aji da kudi sun zauna a jikin daram sun samu masauki, da gani zaka fahimci wata ce, idan na ce wata ina nufin masu abin hannu da shuni domin duk wani abu na jikin ta is screaming luxury and money.

   


    Mata biyu ne biye bayan ta, dayar security ce cikin uniform din ta dauke da brown Birkin handbag din Najma, dayar kuma wata Singaporean mace ce wato yar kasar Singapore cikin light blue uniform din ta na Nanny, dauke da kyakkyawar baby girl din NAJMA wato Aneesa, yarinyar da ba zata wuce 2years ba itama kyakkyawa kamar mahaifiyar ta.


    Aneesa tayi kyau cikin wata Pink sequence dress na yara, gashin kanta ya sha gyara mai kyau sai yan baby pink socks da aka saka mata, yarinyar kan ta sai kamshin turaren yara na baby Dior ta ke.

     Fara'ar fuskar Jamila ta da da fadada tana kallon yar uwar ta da suke Uba daya, da yake Jamila yarinyar Mummy ce tace


    "Gaskiya Najma anyi fushi da ke sai yanzu kike zuwa" 


     Najma ta tako tsakiyar falon tace "daga Airport muke fa, sai da muka jira Daddyn Anisa ya dawo daga daurin aure, wai sai Aneesa tayi masa rakiya Airport tukunna"

  Jinjina kai kawai Jamila tayi cikin dacin rai jin abinda najmar ta fada

    Hadiza tayi saurin cewa "Allah sarki har ya wuce kenan, Toh Allah ya kai su lafiya" 


    Najma ta gyada kai tana nufar mahaifin ta, har kasa ta zube ta gaida mahaifin ta da sauran yan uwan sa kamar yanda ya kasance al'adar Alh Sam yaran sa ba sa gaishe shi daga tsaye.


     Alh yayi murmushi yana amsa gaisuwar ta tare da fadar "shi dai mijin nan na ki baya gajiya da yawo sararin samaniya, Allah dai ya taimaka ya yi jagora ai yana kokari" 


      Ba don Najma ta so ba ta nufi matar mahaifin ta Aunty da ke zaune can kan daya daga cikin leather seat kujerun da ke falon, gaishe ta tayi domin tasan idan bata gaishen ta ba ma Alh zai sanya ta gaisuwar dole, itama Aunty bata tsawaita gaisuwar ba ta amsa kawai, ta girgiza kai a ranta tana jinjina lamarin ta da 'ya 'yan mijin ta da ke kishi da ita, kamar ba mahaifin su ta ke aure ba.



      Najma ta nufi Yar uwar ta suna hugging juna

 "congratulations little sis, may Allah bless your new home, an shigo sahun mu kuma" 

suka sanya dariya ita da karimar wacce a duk cikin yan uwanta tasu tafi zuwa daya da najma, ko don ita ke bi mata ne, tare suka tashi oho.


     Alh ya kalli yaran sa duka da kyakkyawan murmushi kwance kan fuskar sa, ya ga yaran sa duka mata a falon idan ka cire mutum daya, mutum daya da ke missing a gurin wato Yar sa FAHIMA, domin Salma yasan suna School saboda exams watakila basu dawo ba. 

 

   Alh ya kalli Aunty yace "ya naga kowa amma  banga dayar yar hannun daman Amarya ba" 

   ko ba a fada ba kowa yasan wa ya ke nufi, take kuwa falon ya dauki wani irin tsit jin Abinda Alh ya fada, Aunty kuwa a ranta ta jinjina zancen tana raya, a da kenan Alh, a da ne FAHIMA take yar hannun daman Karima, amma a yanzu ita ta sani idan akwai mutum daya da yaran gidan har ma iya yen su suka ki jini to FAHIMAR ta ce, her innocent daughter FAHIMA, yar ta da ta zo da ita gidan, Alh kuma ya dauka ya hada da sauran ya yan sa  ya rika kamar shi ya haife ta.


    "Hmmmm Nima tunda ta zo muka gaisa ban San inda kuma ta buya ba, kasan halin yar ta ka"


    Alh ya murmusa yace "FAHIMA FAHIMA kenan yanzu haka hayaniyar nan ce ta boye ta, lalubo min ita a waya"


    Aunty ta mike daga kan kujerar tana fadar "ai kuwa na baro wayar ciki, kyale FAHIMA kawai Alh idan karimar ta shiga ciki sa yi hoton, kar a batawa su uncle Bashir lokaci suna da tafiya gaban su" 


Aunty ta karashe a kokarin ta na son shashatar da zancen, domin ita taga fuskar yaran dukan su a lokacin da aka ambaci FAHIMAR ta, Alhajin ma kawai don ba ruwan sa ne da ya Lura da kyau da zai fahimci yanda atmosphere din dakin ta chanza nan take.


    Ba don ya so ba yabar zancen, a haka akayi kiran mai hoto akayi ta daukar hotuna, a kasan zuciyar yaran kuma suna jin haushin yanda Aunty ce kawai ta samu halartar wannan photo session din ba da iyayen su mata ba.



    Ita dai Aunty ta baro Falon, ta na hadewa da securities biyu maza a nan kofar shiga sashen Alh, suna ta rarraba ido kamar su dake duk wanda ya kara musu, cikin ba da kariya da tsaro ga ma ko waye su ke guarding wanda ko ba a tambaya ba ta San securities din Najma ne, ta koma na ta sashen kai tsaye, itama part din nata ba Laifi akwai dan taro na yan uwan ta da sukayi mata Kara da kuma wasu daga yan uwan Alh da suka sauka bangaren ta.



    Dakin ta ta nufa kai tsaye, ba kowa dakin sai yar uwarta da ke zaune kan sallaya da alama sallar Zuhr ta sallame

     Kwala kiran Furera tayi, sai ga ta ta shigo dakin "gani Aunty"

    Aunty tace "ina FAHIMA"

Furera ta sosa kai tana fadar "Nima ban ganta ba aunty" 

  Aunty tayi kwafa cikin takaici tace "je ki dubo min ita"