RAYUWAR DAN ADAM

2

by @mahmazee1

"Assalamu alaikum" aka yi sallama dakin Aunty cikin wata karamar murya mai tafe da tsantsar nutsuwa kai ba zaka ce ta matashiyar budurwa ba ce, kana ta turo kofar dakin ta shigo.


  Daga bakin kofa ta tsaya tana kafe Aunty da manyan idanun ta masu dauke da wata irin koyar ido wato eye balls irin idanun nan da ake Kira da Hazel eyes, ganin fitinar da ke kwance fuskar Auntyn ta ta.

"Ki karaso mana, zaki tsaya daga bakin kofa FAHIMA tunda ko yaushe ba zaki daina dauko min abin magana ba"


  Gaban ta ne ya sake dokawa a karo na biyu domin tun bayan da Furera ta zo Neman ta ta San wani laifin ne ta aikatawa Aunty.

   Ta lumshe idanun ta kadan ta bude tana fadin "me aka ce nayi Aunty"


"Ba cewa aka yi kinyi ba, gani nayi da ido na, me yasa baki je sashen Mami cikin sauran yan uwan ki ba, ke ko yaushe rabe rabe ana fadar ba kya son su"

   Fahima ta dan sunkuyar da kan ta ba tare da ta ce komai ba, domin ta sani ita mai laifi ce a gurin Aunty, hakanan indai akan wannan ne laifin ta ba zai taba gogewa ba.


  Shiru tayi bata amsa ba, sai jujjuya awarwayen hannayen ta na danyen azurfa da take yi, Mama zuhra sister Aunty ce tayi intervening 

  "Ni kam ban San fadan me kike yi ba Ramatu, sai kace baki San halin mutanen gidan ku ba, bayan duk kin san ba dadin su take ji ba"


   Aunty ta girgiza kai tana zama gefen gadon ta "ki fahimce ni Zuhra, ai zaman gidan ne yanzu ya koma haka, kowa shaida ne da fitinar da yan dakin Umaimah da yan dakin Maimuna ke yi, amma ga su chan sashen Mami har surukan su ana ta yake, kai ma ai sai ka shiga ayi da kai, haka din da take yi, har yan uwan Alh yanzu gani suke Fahima ce bata son hulda da sauran yaran gidan kuma haka ne"


  Mama zuhra tace "aa zuciya ba daya ba, what's the point of kana zaune da dan uwanka kana masa yake amma da shi a zuciyar ka, wannan ai mugun zama ne, irin wannan zaman ma baya da amfani" 



    Aunty ta motsa baki da niyar magana, mama zuhra ta yi saurin katse ta a karo na biyu "zaman gidan na ku ai ya Ida lalacewa Ramatu, yanzu yara sun kawo, duk sun bata muku gida, gabakidaya zaman gidan na ku bashi da dadi, Allah dai ya sawwaka"


   Aunty tace "ni dama ba don su nakeyi ba saboda Alh ne, kar ki so kiga yanda duk ya damu dazu da bai ganta ba falon sa"

    

Mama zuhra tana nadiye abin sallah tace "ai sai yayi hakuri"

   Aunty tace "toh ai shikenan, amma duk da haka ki dan sake lekawa, idan ma zaki wuce ki shiga kuyi sallama"


    FAHIMA ta jinjina kai tana amsawa da

"Toh Aunty" tare da sakin dan siririn murmushi Wanda ya kawata kyakkyawar fuskar ta mai dauke da zallar kyau har kumatun ta na lotsawa.


Ta tako a sanyaye ta nufi toilet din Aunty, itama tana cikin ankon Sheraton Embroidery din da aka yi wanda Najma ce ta dauki wannan nauyi, su dai sai kawo musu Atamfa kawai aka yi.

  

 Dinkin Atamfar yayi wa dan murmurarren jikin ta kyau, sai dai sabanin sauran yayan Alhaji da suka kasance farare, FAHIMA kam wankan tarwada ce, duk da kasancewar Aunty fara kal, kalar fatar FAHIMA ta sirka da ta buzayen Niger republic da kuma hausa fulani wato jinsin mahaifin ta, hakan ya sanya skin din ta yake da kyau, tana dan da duhun fata mai haske sosai, domin ba zaka Kira ta da baka ba Sam, irin skin dinnan da mal bature ke Kira da pecan skin tone.

    Alwala ta yo ta fito ta kabbarta sallar Zuhr a nan dakin Aunty


    Haka taron yinin buki ya cigaba da gudana cikin tsari da ban sha'awa, Sosai 'ya'yan Mami suka bude bakin jakar su suka shiga yiwa shahararren makidin nan falasfa liki, wanda aka dauko tun daga jihar katsina domin taron yau.


   Hakanan a bangaren mummy yah Jamila ce ta bude jakar ta tayi barin naira, da yake a dakin mummy itace gwana, domin mijin ta na da rufin asirin sa, Aunty ma tayi liki ba laifi haka ma Mummy.

    Sai uwar amarya Mami, ita kam karshe domin a cewar ta wannan shine bukin autar ta, kuma bukin ta na karshe.



     Zuwa magrib gidan ya rage hayaniya sosai ya rage yan kai amarya kawai, a daidai wannan lokacin kuma FAHIMA ta fito tare da rakiyar kanwar ta Salma zuwa sassan matan gidan.

     Da sashen Mami suka soma, sashen ya rage hayaniya ba kamar dazu ba, ba kowa falon sai kananan yara da ke kallon Peppa pig a tashar Nick Jr.

    Da sallama suka shigo dakin Mami, suka gaishe ta da sauran matan da ke dakin


   FAHIMA tace "ni zan wuce Mami Allah ya sanya alheri ya ba su zaman lafiya"


     Mami ta murmusa irin murmushin nan da take  mata idan ta ga yan uwan Alhaji kusa, wannan Karon ma shi tayi tace "Fahima dai manya, tunda kika shigo gidan nan ni so daya ma na gan ki, duka sauran yan uwan ki suna nan sashen tun dazu" Mami ta karashe cikin iyawa


    Fahima batayi mamaki ba domin ta saba da wannan halin hawainiya da mami ke nuna mata

 idan da mutane kusa ta kan nuna mata so, amma idan daga ita sai ita ne sometimes ko gaisuwar ta ba ta amsawa.

      Adda Rabi kanwar Alh kamar yanda suka ji iyayen su suna kiran ta wato Adda meaning yaya a fulatance da yake ta girmi duka matan Alh, sai suma yaran suke ce mata haka, Adda Rabi tace cikin gatsine "mugun halin ta ne dai yarinyar nan ba zata daina ba, ya yan masu gida ma basu guje ka ba, Sai Kai agola zaka nunawa mutane girman kai"


    Fahima tayi kasa da kanta bata ce komai ba, chan ta ja hannun Salma da ta cika fam suka nufi dakin da su ke jiyo hayaniyar su Karima.


    Wannan Karon ya yan mami ne kawai a dakin suna taya yar uwar su shiri domin sada ta da dakin mijin ta, dakin yayi shiru bayan shigowar su.

     

"Karima ni zan wuce Allah ya tabbatar da alheri, may yours be among the best"

   Karima ta amsa da "Ameen thank you"


Sai kuma aka sake shiru a karo na biyu, hakan ya sanya sai ta nufi yarinyar Najma da ke hannun yah Amina a kokarin ta na kawar da zargin da ake mata na nisantar yaran gidan.


Ta sunkuya da murmushi kan fuskar ta ta karbi Aneesa, baby Aneesa na burge ta sosai tana son yarinyar, ko don kusancin da suke da shi da mahaifiyar yarinyar ne tun inda aka fito oho.


    An chanza mata kaya zuwa wata sassaukar riga white mai polka dots, da yar pacifier (ruma ruma) bakin ta tana tsotsa kyakkyawa da ita kamar mahaifiyar ta, kyau a gurin Aneesa ai bata baki ne domin daga uwar har uban kyawawane, tayo gado ta kowane bangare.


    "Aneesa how're you" ta fada tana yiwa yarinyar wasa, ita din tana son yara, musamman Aneesa da dole ta burge ka sai idan baka dora ido kan ta ba, ko don kyau da kwalliyar da ta ke cikin ta koda yaushe.


  "na jima ban ga Aneesa ba Najma, ta girma sosai, hope you're all good" Fahima ta fada tana sauke kallon ta kan Najma da ke zaune tsakiyar gado, tana ta basu labarai, ko na meye oho


 musamman zaka lura da added attention din da mutanen dakin suka bata duk da labarin ba wani mai armashi ba ne, sai dai zuwan fahima ya katse yar hirar ta su.


    Itama Najma ta chanza zuwa wata doguwar rigar boubou na wani tsadadden material red mai manyan duwatsu da ya karbi farar fatar ta sosai.

     Dan murmushi tayi da bai kai zuci ba, cikin alfahari tace "ai kam itama ta jima bata gan ki ba, kinsan we are always out of the country, Aneesa bata zama"


    jinjina kai Fahima tayi, a ranta kuma tana jin dariyar abinda Najma ta fada, ta San ba komai ya sanya ta fadar haka ba sai don ta nuna mata irin rayuwar hutun da ta ke ciki, tayi rubbing din shi on her face.


    sai dai abinda bata sani ba, ita din dadi ta ke ji mata ta sani kalar rayuwar da Najma ke so kenan kuma ta samu, Allah ya sani har a zuciyar ta bata kyashin wannan cigaban da ta samu a rayuwa.


   Salma ita ce ta ji haushin wannan gorin da aka yiwa yar uwarta, hakan ya sanya ta karbe Aneesa daga hannun Fahima ta mika ta hannun uwar ta, cikin yake tace "Aneesa har yanzu pacifier ake ba ki, ai kin girmi pacifiers"

   Duka akayi yake, Hadiza tace "kema Salma wucewa zakiyi ba zaki jira kai amaryar karima ba"


    Salma tayi kwafa tace "aa rakata kawai zan yi" a ranta tana jinjina girman son kai irin na mutanen gidan su, su Hadiza a dole sai ta fi son su a kan FAHIMA tunda su take uba daya da su, yayin da fahima take uwa daya da ita, sai dai ai tana ganin yanda zaman gidan na su ya koma, yan daki da daki kawai, so suke kamar yanda suka tsabbace Fahima daga cikin su itama tayi mata hakanan, ai ba zai yiwu ba ta raya a ranta.


       Daga haka suka baro part din, daganan part din mummy suka nufa wanda ke cike da yan uwan Alh nan ma sai da safe tayi musu kana suka rankaya falon Alh

    Zuwa lokacin yana zaune falon sa kan three seater, tashar BBC World yake kallo, inda suke hasko labarai da dumi dumin sa.


     Da ginger tea hannun sa yana kurba a kai akai, ganin su sai ya fadada fuskar sa.

    Har kasa suka zube suna gaishe shi

"Lafiya qalau, ya gajiyar hidima" Alh ya amsa gaisuwar su yana kallon Fahima 

"sai yanzu nake sanya ki a idanuna fahima ina kika boye yinin yau"

   Dan karamin murmushi tayi tana sunkuyar da kanta kasa tace "na zo da safe Baba kana gurin daurin aure, da rana kuma mutane sunyi yawa bangaren ka"

    Baba ya jinjina kai yana sakin karamin murmushi a ransa yana raya "a gaida fahima manya"


   A sarari kuma sai yace "ba dai har kin fito ba" ya fada yana kallon shirgin souvenir da ke gefen ta, kayan buki ne da Aunty ta bata wadan da tayi, ba laifi Auntyn tayi kokari tunda tayi paper bags mai dauke da hoton Karima da mijin ta, tayi tissue boxes da jotters, duk da wadanda tayi don su ba yaba kokarin ta zasu yi ba.


  Amma hakanan Aunty ta dunkule abinda take da mama zuhra ta kama mata, tayi souvenirs din, ta kuma yi musu dinkuna na fitar kunya sanin ba karamin shiri aka yiwa bukin na Karima ba, ta kuma yi abincin ta na saukar bakin ta, sanin ba isashshen abinci ko ince ba abincin kirki masu bukin zasu aiko mata ba.

    Aunty ta hada mata har da souvenirs din da Mami ta aiko, manya manyan jakunkuna sukayi da tarin souvenirs masu tsada a ciki, har abin yaso zama qazanta sbd almubazzaranci.


     Fahima ta da da yin kasa da kai tace "eh baba ana jirana a gida"


    Alh ya ce "toh ba damuwa Allah bamu alheri, ina ji dai ADAM din ne ya zo daukar ki" ya fada yana zare fararen tabaron da ke idanun sa wato medicated glasses


    Wannan Karon kam shiru tayi bata ce komai ba, domin bata da amsar ba shi, tasan abinda duk zata fada zai bata ransa ne kawai, tunda a duniyar nan baba ya tsani keke napep da take bi, to amma ya zasuyi da abinda basu da maganin sa daga ita har baban, Allah bai yiwa mijin ta wadatar da yayiwa sauran mazajen yan uwanta ba, hakanan a yanzu baba kan sa baya da irin zarahin da yake da shi a da, da da ne kam baba na da arzikin da ba ita ba har maigidan ta zai iya siyawa abin hawa.

      Alh Sanusi ciroma babban mutum ne da yayi tashen arziki da kudi a lokacin baya, a lokacin yana daga cikin attajiran da ake ji da su a kab garin kaduna.


   Sai dai Allah da ikon sa sannu a hankali girma na kama sa arzikin yana da da raguwa, komai ya kare sai abinda ba za a rasa ba


 a halin yanzu 'ya'yan sa ne dauke da shi da matan sa, most especially zamu iya cewa NAJMA ce breadwinner din gidan domin Allah yayi mata arzikin auren babban mutum dan babban gida mai ji da kudi da lokaci da POWER wanda a kab Nigeria ba inda sunan Su bai zaga ba, hakanan mijin nata baya da kyeta, sosai ya sake mata tana yanda take so, hakanan kuma bai gaza ba gurin taimakon mahaifin ta da iyalin sa.