RAYUWAR DAN ADAM

3

by @mahmazee1

Jin abinda mahaifin su ya fada ya sanya Salma tayi charab tace "Napep zan raka ta, ta hau baba" sanin yanzu baba zai taso koma waye a gidan ya zo ya ajiye yayar ta.


   Fahima tayi saurin zungurar ta domin tun kafin su shigo sai da tayi warning na ta, sanin yanzu zai iya dorawa kan sa wata damuwar.

    Baba yayi shiru tsayin wani lokaci ba tare da yace komai ba, a duniyar nan Allah ne kadai yasan yanda yake jin ciwon irin kalar rayuwar da Fahima da dan sa ADAM suke ciki, a duk cikin Yayan sa mata da ya aurar, kowace tana zaune dakin mijin ta cikin rufin asiri ko da dai ba a sarauce ba a wadace.


   Amma fahima itace kadai mijin ta yake da karamin hali domin karamin ma'aikaci ne da ke aiki da Ministry of education ta nan jihar Kaduna.

    A duk lokacin da ya ganta a ire iren wadannan yanayin ya kan tuhume kan sa da irin kalar auren da yayi mata, domin kafin auren ta da ADAM Allah ne kadai yasan adadin manyan mutane, da ya yan manyan da suka yi ta fitowa neman auren ta.



    Wani sa'in idan yana ga 'yar sa Najma sai ya ga bata yi laifi ba don bijirewa auren Adam da ya so dora mata.

     A lokacin da yar cikin sa Najma da maidakin sa (mami) suka kasa yi masa biyayya Akan auren Adam, Fahima da bai haifa ba da mahaifiyar ta su suka share masa wannan hawayen, a lokacin har guduwa najma tayi daga kaduna zuwa Bauchi gurin yar uwar mahaifiyar ta, tare da sanin Mami da tayi mata kudin mota tace tayi bauchi duk don gudun auren talaka ADAM wanda ya kasance maraya hakanan marikin sa ya kasance Alh wato mahaifin najmar da kan sa.



     Asali Adam Yaron makotansu ne Malam Ummaru da mama kulu, su biyu iyayen su suka haifa. shi sai yayar sa Meramu, Malam Ummaru malamin addini ne kuma limami da ke kula da masallacin da baba ya gina tun lokacin a nan kofar gidan su.


    Wannan dalili ne ya sanya baba mutunta Malam ummaru da iyalin sa domin an zama tamkar yan uwa, matar sa da ya yan sa sun zama en gida basu da shamaki da gidan.


    Sai dai da kananun shekarun su wato Adam da yar uwar sa meramu Allah yayiwa iyayen su rasuwa a hatsarin mota da suka hadu da shi a kan hanyar su ta saminaka domin zuwa ganin gida.

    Bayan an sallaci mal ummaru da maidakin sa, an sada su da gidan su na gaskiya sai yan uwan mal ummaru suka wuce da 'ya'yan sa saminaka, jin haka baba yayi tattaki da kan sa ya isko su, ya kuma nemi alfarmar a bashi yayan mal Ummaru ya rike, basu musa ba suka bashi Adam sanin mutuncin sa da kuma kokarin sa gurin inganta rayuwar Marayu, domin gidan Alh ciroma cike yake da 'ya'yan yan uwan sa da yake riko.


    Sai dai meramu suka bashi hakuri kan mace ce kuma har sun tsaida shawara aure zasuyi mata da yaron wan mahaifin ta da ke nan saminaka, domin a lokacin tana da shekara 15 a kauye kuwa duk yarinya sa'ar ta ta isa wanki.


    Baba bai matsa ba ya karbi Adam din da aka basa yana godiya, da auren meramu ya tashi kuma duk abinda uba ke wa yar sa na aure, baba bai yi kasa a guiwa ba yayi mata komai, aka daura aure, mijin ta ya dauke ta zuwa Ibadan inda yake nema.


     Wannan dalilin ya sanya Adam ya tashi a gidan,  kuma baba bai kyetace sa ba yayi tsaye ya samar masa ilimi mai kyau kamar sauran ya yan sa.

 

   Ganin hankali da sanin ya kamata irin na Adam sai baba yayi sha'awar hada alaka ta jini da shi, a lokacin ya kammala bautar kasar sa ana cuku cukun nema masa aiki.

   A lokacin najma ce ta fado masa a rai domin sune yan mata a gidan, sun zana SSCE din su kenan suna jiran result, ba tare da shawara da kowa ba baba ya tsaida auren Najma da Adam, domin wannan ba shine karo na farko da yake aurar da 'yayan sa ga daya daga cikin yaran da yake riko ba.


    Sai dai bai taba samun dan da ya bijire masa ba sai a kan najma, hakanan mami tayi tsayin ta kan ba za a aurar da najma ga Adam ba, domin a lokacin tana da nata buri da ta dora a kan najma.




     A bangaren najma kuwa tun da ta taso Allah yayi ta yarinya mai son kyale kyalen duniya very materialistic, tana son rayuwa hutu da jin dadi musamman da ta taso a cikin ta, a yanzu kuma da Allah yayiwa mahaifin ta kariyar arziki sai ta dauki alwashin auren miji mai kudi.


    Aka raya aka kada, ta inda duk aka buga Najma ta cije, mahaifiyar ta kuma ta goya mata baya, a cewar mami ai ko sa'adda yake hade haden auren sa, 'yayan yan uwa yake baiwa da yake riko, ba Adam da babu dangin iya babu na baba ba, gashi ba shida wani abu sai abinda baban ya yi masa.


    Ana cikin haka najma ta gudu daga gida, aka nema ta aka rasa, hankula sun tashi sosai, baba ma ya shiga damuwa a tunanin sa Najma ta shiga duniya ne, Mami ma ta nuna tashin hankalin ta, neman duniyar nan taki ta fadi ita ta yiwa najma kudin mota tana gurin yar uwar ta bauchi.


      Kai abu dai yaki ci yaki canyewa, aminin baba Alh moyijo wato yayan mami shi ya kawo karshen wannan tashin hankalin, a lokacin da ya Kai wa yar uwar sa ziyara wato kanwar mami a can Bauchi, can ya hadu da najma, tun daga gidan Aunty zuwairar yake babbaka masifa, ya hade da najmar da zuwairar har ma Mami da ke kaduna yayi musu tas, daganan ya kada kyeyar najma gidan sa, washegari ya sanyo ta mota direban sa ya tuko su sai kaduna.


    Sosai ran baba ya baci da abinda Mami tayi, wato Tana sane da irin tashin hankalin da ya shiga, da yanda bacci ya nemi gagarar sa amma baiwar Allah nan tayi shiru, hakan ya tunzura baba yace aure ba fashi, kuma ma ya dawo da auren nan da wani wata mai zuwa.


    Tashin hankali wanda ba a sa mishi rana, najma kuka mami kuka, kai haka sai akayita rigingimu har dai daga baya yan uwan baban suka shawarce sa ya hakura da wannan hadin, tunda dai najma ta soma da haka toh ko auren yayi mata ba zama zatayiba.


    Ba don baba yaso ba ya hakura, musamman da lokacin auren saura sati biyu, kuma ya gama gayawa duniya, yana ta tunanin yanda zaiyi da Adam, a lokacin Fahima ta fado masa a rai, mai yasa ma baiyi wannan hadin ba tun inda aka fito, sai sai ganin najma na gaba da fahima a shekaru ya sanya bai kawo ta a rai ba, hakanan najma yar sa ce ya so ta da wannan alheri, it's just him been human, sai dai ganin abinda ya faru yayi shakkar furta abinda k ransa.


    Kamar Aunty ta shiga zuciyar sa, ganin yanda ya shiga damuwa sosai, sai ta kawo masa shawarar mayar da auren kan Fahima.



    Fahima yar albarka wannan halaccin da tayi masa har ya kwanta dama ba zai taba mantawa ba, domin ko dago da kanta bata iya yi ba bare har ta musa masa a lokacin da ya kira ta da zancen, kai tsaye ta amince da auren.


     A lokacin da yar cikin sa ta kasa yi masa biyayya ta nemi kunya ta sa Fahima ta share masa hawaye, wannan abun na daga cikin dalilin da ya sanya idan ya ganta a koda yaushe ya kanji guilty conscience.

   Baba ya nisa yana fadin "da daren nan Fahima, ina mijin ki"

    Fahima tace "yana tutoring, a wani gida nan unguwar mu yanzu, yana yiwa yaran gidan extra lesson after isha"


   Baba ya jinjina na kai lallai Adam ya gaya masa ya samu tutoring a kwanakin baya sai dai sam ya sha'afa, sai ya kalli salma yace "je ki cikin gida salma, samarin nan idan suna nan ki yi min kiran daya"

    Cikin rawar jiki salma ta tashi ta fice yayin da baba ya dinga jan Fahima da hira jefi jefi

   "Toh ya maganar karatu ana nan ana tayi ko"

Tace "eh last week muka fara IT" wato industrial attachment 


    Baba yace Masha Allah, can kuma cikin yar damuwa  yace "Toh ya kike covering expenses" 

   "Adam yana bani, aunty ma kan yi min aike sometimes"

   Baba ya dan hade rai yace "me yasa ni baki gaya min ba, sai Auntyn ki kawai, wato ni ban kai ki gayamin damuwar ki ba ko fahima, amma ba laifin ki bane laifin auntyn taki na gani"


    Da sauri tace "kayi hakuri baba ba zaa sake ba, ni ce nace kar ta gaya maka"

   Baba ya murmussa yana fadin "toh shikenan tunda bakya son laifin auntyn ki" 

     A dai dai lokacin Salma da Al'amin suka shigo falon da sallama, salma ce gaba sai Al'amin din mummy, zama yayi kan carpet shima yana fadin "gani baba"

   "Yawwa Aminullahi akwai mota hannun ka"


 "Eh baba akwai motar gida akwai kuma motar mummy hannu na"


   "Toh Fahima zaka ajiye gida, ku je ko wace aka samu da ke da mai, ko ta gida ko ta Maimunan sai a ajiye ta, kayi maza maza ka dawo kafin lokacin kai Amarya yayi"


     "Toh sai kin fito" Al'amin ya fada yana kallon sashen fahima, ya fice daga falon, itama din bayan sa ta bi  tana yiwa baba sai da safe.

    Har bakin mota salma ta raka ta, sai da ta ga wucewar su sannan ta koma cikin gida.


    Da motar mummy suka ke, wacce yaran ta suka hada kudi suka siya mata, duk matan gidan kowacce da motar ta da yaran ta suka siya mata idan ka cire Aunty.


    Motar Mummy sabuwa hul lafiyayya kirar Honda Accord EOD da ba a jima da siyen ta ba, yaran ta suka siya mata domin huce mata takaicin Motar da mami ta jima tana hawa ita kadai a cikin gidan.


Sai da suka dan yi nisa da tafiya kana Al'amin ya kalli bangaren ta kadan yace "Haj Fahima Uwargida a gidan yayana Adam"

    Dan murmushi tayi kadan tana kallon bangaren sa, itama sai tayi shirin tsokanar sa domin Al'amin mutumin ta ne, kusan sa'ar ta ne, a tare suka tashi, sukayi wasa tare, ita, shi da najma, sai dai shi yana gaba da najma da shekara daya, yayin da ita kuma najma ta ke gaba da fahimar da shekara daya, ko a islamiyya ajin su daya su duka, a boko ne dai ya wuce su da aji daya.

    "Yaya Al'amin kenan manya, mutanen Lagos"

    Al'amin ya dara har yana buga kan sitiyarin motar sanin yayan tsokana ne ta kira shi da shi, idan sun tashi iskancin su ita da najma haka suke kiran sa.


     "Toh ya za'yi, a man has to hustle, ga yan kannen mu nan duk sun yi aure, before you know it an fara kiran ka baba, kai ko auren baka yi ba, ai dole ne mu boye Lagos mu nemi kudi"


    Da yake shi a Lagos yake zama gidan Aunty Jamila inda take aure, yana karatu a jami'ar Unilag, hakanan kuma yana yan buge bugen sa.

    Fahima tayi murmushi tace "Ai kila sai an kai ga ce muku kaka ma, don 'ya'ya kam mun kai ga enmata ma, ga Anisar najma nan Masha Allah ta girma, kuma fa naji humairan Yaya Lawal an kusa kawo kaya" (Lawal babban dan Mami ne, shine first born a gidan gabakidaya)


    "Kai girman ya mace ba wuya, duka duka fa a hannun mu aka haifi Humaira, bana tunanin zata girmi salma"

      "Haba ta ba salma almost a 2years fa, haka before you know it zaka ji Anisa an kai enmata, sai kawai kaji ana kiran ka da Kaka Al'amin"


    "Who would have thought wai Najma ce yau anyi hankali, she's a mother fa yanzu" 


"Allah kinsan me na tuna" Al'amin ya da da dorawa

Girgiza kai tayi alamar aa 

   "Na tuna da da ne fa, na tuna kiriniyar ku da najma, gashi kamar ba ayi ba wai duk kunyi aure"


     Fahima yace "abin ma wai ne kenan, ni kuma kasan me na tuna, dukan da muka sha Islamiyya na latti, wai a duniya kuwa zan iya mantawa da ya mu'allim Ali da muguntar sa"

    Al'amin ya kyalkyace da dariya domin shi abin dariya baya yi masa kadan

   "Ai wallahi ba zan manta ba, ke ce ko yaushe kike ja muku latti, ita najma tace sai ta jira ki, har na tuna sanda ta sha dukan aljannu"


    Kallon juna sukayi kamar hadin baki suna sakin wata irin dariya, domin ba ranar da wannan memory din zai daina sanya su nishadi.


   "How can I" fahima ta raya tunda sun jima suna tsokanar najma akan haka

     Allah sarki my sweet najma ta da da rayawa a ranta, a duniya idan akwai wanda zai gaya mata akwai rana mai zuwa da ita da najma zasu koma haka tabbas zata karyata, ita kanta najmar zata karyata hakan.


    A lokacin baba ya auri aunty ta zo da ita gidan, tana da shekara biyar a duniya, yayin da najma take da 6yrs da dan dori a lokacin.

   Dalili kenan da suka taso tare, a islamiyya ajin su daya hakama a boko, hakan ya sanya najma bata da wata kawar da ta wuce Fahima a lokacin haka ma itama fahimar.



   Duk da kuwa tun a lokacin mami bata son kawancen nan nasu, amma haka najma ke sato hanya tunda farar safiya tayo sashen Aunty domin aje wasa, sometimes har rufe mata kofa mami ke yi, amma da ta samu dama zata gudu gurin fahima.


   Idan za a islamiyya kuwa haka zatayi sammakon shiri ta zo sashen Aunty zaman jiran fahima, ita kuwa fahima Allah yayi ta mutum sanyi da nawa sabanin najma, kusan duk rana ta lillahi sai ta janyo musu latti har kowa ya fice ya bar su, su sha dukan lattin su tare.


    Mami na jin bakin cikin wannan duka da Najma ke sha akan fahima, tayi fada, tayi nasiha , tayi lallashi tayi lurrasuwa amma duk a banza, idan mami ta tura su islamiyya ita da karima suna fitowa harabar gida zata tura karima tace tabi sauran yaran gidan ita kuma ta jira fahima.


     Duk yanda karima ta so shiga cikin su ganin kusan dai sa'anni suke da ita tunda najmar shekara biyu ta bata yayin da fahima ta bata daya sai najma tayi ta hantarar ta a cewar ta su ba sa'anta ba ne. Wannan abin da Najma ke yi ya jima yana ciwa Mami tuwo a kwarya