RAYUWAR DAN ADAM

4

by @mahmazee1

Ranar da najma ta gaji da dukan banzan da take sha islamiyya sai tayi shirin nemawa kanta mafita, suna zuwa kuwa aka tare su cikin yan latti, ya muallim Ali ya zo kamar ko yaushe domin hukunta yan latti, ana zuwa kan najma kawai sai ta fadi tana juye juye kasa wai aljanu ne da ita, kamar yanda ta ga en manyan aji keyi.


     Tsab ya mu'allim ya gano ta tun a tashin farko, akayi akayi ta tashi najma ta murdewar ta, sai yace a Nemo masa ruwa a kofi yayi mata addu'a.


   Ya mu'allim yayi en tofe tofen sa ya watsawa najma Ai kuwa ta ke ta mike ras a tunanin ta karatu ne yayi a ruwan, Ashe ya muallim tofin Abcd ne kawai yayi, Ai kuwa kamar an aiko sa duka biyu yayi mata ga na latti ga na karyan aljannu, ranar kam duk soyayyar da take wa fahima itama sai da taji ba dadi domin kwana uku sukayi basa magana.


      Al'amin ya tsagaita dariyar sa yace "najma me aljanun karya, kinsan sunan da en aji daya suka sanya mata kenan"

     A haka dai suka ci gaba da tafiya suna ta tuna baya da tayi dadi, Al'amin na ta da da tunasar da fahima Alherin najma a gare ta, domin Sam baya jin dadin yanda abotar su ta koma yanzu.


    Shiru tayi ta rasa me yasa a ko yaushe suka hadu da Al'amin aikin sa kenan tuna alherin najma a kan ta, at first kam ta dauka tuna baya ne kawai ake yi ayi nishadi, amma a yanzu ta fahimci yana tuna mata hakan ne kawai saboda kanwar sa Najma, saboda kar ta kalli najmar da halin da take nuna mata a yanzu, face ta dinga tunata a Najmar da suka ta so tare, mai son ta.


    Allah sarki her sweet najma, her best friend najma, da a kab gidan na su idan ka cire Aunty da ta haife ta bata da mai son ta kamar najmar, ko da kuwa baba ne.


    Sai dai sannu a hankali girma na kama su, ana da da cusawa najma maganganu a kan ta, musamman akan bata kishin mahaifiyar ta, da kuma ganin da suke baba ya fifita amaryar sa akan sauran matan sa.


     Gidan Alh Ciroma gida ne da ya Tara mata uku da kuma tarin 'ya'yan su, gida ne da kishi yayi yawa, ba zaman lafiya ko kadan a tsakanin matan sa.


   Kafin zuwan Aunty mami da mummy kam kishi suke mai zafi, domin a yadda labari ya zo musu a lokacin kuruciyar su har dambe sun sha yiwa baba a cikin gida.


    Saidai bayan zuwan Aunty duka sukayi channeling kishin su a kanta ganin soyayyar da maigidan yake nuna mata, duk fa kuwa basu fasa fadan na su ba yau da gobe amma dai dukan su sunfi kishin aunty tun a lokacin har kawo yanzu.

    Hakan ya sanya 'ya'yan gidan suka taso da wata irin kiyayyar aunty a zukatan su musamman matan saboda hudubar iyayen su kenan akoda yaushe.


      Mummy irin matan nan ne da ake kira munafukan mata, Sam bata son miji ya ga laifin ta, duk yanda zasuyi fitina da mami sai tasan yanda tayi ta fidda kan ta, hakanan idan mami da Aunty suka samu sabani, taje gurin mami tace wannan, taje gurin aunty tace wannan, idan  kuma baba yazo she will tell a complete different story, toh ita haka take.


    Mami kuwa kaifi daya ce, tana yin ka tana yin ka, idan kuwa bata yin ka bata yin ka, hakanan bata iya boye kishin ta ba, Aunty kuwa da ta zo gidan bata shiga harkar su, amma fa idan suka taba ta bata yafewa, daga baya ne dai da tayi nazari taga dai duka suna so su zama daya, tunda lokuta da dama haka kawai zasu takalo ta don ayi rigima, hakan ya sanya sai ta soma daga musu kafa, koda a kan idon ta ne suka kyetace ta ko 'yayan ta duk sai ta kawo ido ta sanya kamar bata gani ba don a samu zaman lafiya.

   dalili kenan da ya sake daukaka darajar ta a idon mai gidan, hadi da tsananin biyayyar da ta ke masa domin duk cikin matan sa ta fisu kawaici da hakuri ta kuma fisu kyautata masa da tausayin sa



     Su kuwa sai suke ganin hakan a rashin adalci musamman idan kayi duba da itace ta zo ta same su a gidan, yara kuwa tunda ba mahaukata ba ne ba kuma makafi ba ne, sun ga yanda Baban ke fifita lamarin Aunty akan na iyayen sa, dalili kenan da suka ta so basu da da ra'ayin ta ko kadan idan ka cire mazan, matan ma akwai wadan da ba za a rasa ba masu hankali.

 

     Najma na da kishi, tun tana yar kanknuwar ta  ta fahimci Allah yayi ta a cikin jerin matan nan ma su tsananin kishi, domin ko a cikin yara yan uwanta, idan wane yayi abu ko ya zo da wani abu sai ta ji hankalin ta ba zai kwanta ba face itama ta mallaki wannan abun.

    

 Dalili kenan da tana girma da wayo tana da da fahimtar fifikon da baba ke yiwa Aunty kan mahaifiyar ta, sannu a hankali har mami da sauran yan uwanta suka soma cusa mata irin kalar na su ra'ayin, hakanan a duniya mami na kishi da Aunty fiye da tunanin mai karatu hakan ya sanya sometimes tana iya dagawa mummy kafa amma banda Aunty, hakan ya sanya lokuta da dama sai ta San yanda tayi ta takalo Aunty ta biye mata.


     Ana haka wata rana shaidan ya buga gangar sa tsakanin mami da Aunty, akayi rigima ba yar kadan ba a gidan, tashin hankali har makota, yara kuwa sai kuka suke, kanana kenan daga cikin su.


    Wannan fadan da akayi kowa ya San Mami ce bata da gaskiya, aka yi ta yar neman rigima har baba ya dawo, a dalilin haka baba yayiwa mami saki daya, wacce sai da ta kusan shekarewa a gida da girmanta kafin baba ya maida ta dakin ta.


    Wannan abun yayiwa Najma ciwo fiye da yanda zan misalta muku, hakanan tun daga ranar ta ji ba halittar da ta tsana sama da Aunty domin idan adalci baba zai yi kamar yanda ya saki mamin ta toh itama Aunty kamata yayi ya sallame ta, amma sai ya saki mami kawai ya bar Aunty tana murza ikon ta.


     A lokacin suna jss3, girma ya kama su hakanan ta San meye kishi, sai ta ji ba Aunty kawai ba har fahimar ta fita ranta, sannu a hankalin har kawancen na su ya lalace, aka koma ko ga maciji ba ayi, tun Fahimar tana biyar najma tana disgata har ta dangana ta bar ta dole, abu daya ta sani ba zata taba manta alherin Najma a gareta ba hakanan ba zata taba iya kallon ta da halin da take nuna mata ba yanzu bare har ta biye mata, domin ita kuwa Fahima akwai lafiya, bata da fada, bata da hayaniya hakanan bata da fushi, abinda duk zai bata ranta har ya fito sarari fuskar ta to tabbata ba karamin abu ba ne bare har ka ga fadan ta.


     Wannan kenan, Al'amin yayi parking a daidai kofar gidan Fahima, mai dauke da yar karamar kofar da madaidaicin bakin gate.

     Sallama sukayi kana ya juya ita kuma ta shige cikin gida, gurin da ya ke pake machine din sa ta soma sauke idanun ta, rashin ganin babur din sa kirar roba roba a gurin ya tabbatar mata bai dawo ba, ta taka a hankali zuwa doguwar verandar su, ta janyo keys din ta a jaka, tana bude kofar da zata sa da ka da ainahin cikin gidan wato dakunan gidan.

     A kan kujerar 3 seater ta watsar da tarkacen hannun ta ta nufi bedroom din su kai tsaye, madaidaicin gida ne mai dauke da palo daya, kitchen sai 2 bedrooms ko wanne da bandakin sa.


     A mugun gajiye ta ke domin tun safe ta bar gidan, tana gidan su Aunty, kayan jikin ta ta soma zarewa ta fada bandaki kai tsaye, cause she's in a serious need of a shower.

    Ta dan jima a bandakin kafin ta fito daure da madaidaicin towel light ash da ya bayyanar da sassalkar fatar ta, mai kyau da tsantsin da ke zuwa naturally.

     Wata silk nightgown ta janyo ta sanya kalar red mai dogon hannu, ta dawo falon tana duba kayan da ta shigo da su daya bayan daya.


  Tana nan zaune shiru shiru, every now and then ta duba agogon wayar ta, sai after 9pm ta jiyo karar Babur din sa, da hasken headlight din mashin din, wan da ya haske tsakar gidan su, har hasken na ratso window falon.

    Cikin zumudi ta mike daga kan kujerar da ta ke kai ta nufi kofar shigowa falon, cikakken gashin ta mai tsayin gaske da ya mummurde na yawo tsakiyar bayan ta.

    A kofar falon suka hade a lokacin da ya ke kokarin shigowa, ita kuma tana shirin fita tarbon shi, har kirjin su na gugar na juna.


  Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ya dan ja da baya kadan yana soke hannayen sa aljihun wandon jeans da ke jikin shi, idanun sa cikin na ta da ke biyar sa da kallon so da kauna.

   Lokaci daya suka sakarwa juna kyakkyawan murmushi mai dauke da shauki da kaunar da ke dawainiya a tsakanin su.

   ADAM ya dan sosa cikakkiyar sumar kan sa, baka sidik ta cikakken malam bahaushe zuciyar sa full of contentment da godiya ga ubangijin sa da ya ba shi wannan kyakkyawar halitta a matsayin iyalin sa.


    "Saboda kin ga Aunty, shi ne throughout yau ko nema na ba kiyi ba" kakkausar muryar sa ta fada

  

   Murmushi ta sakar mishi, ta dora hannun ta kan nashi tana janyo shi cikin falon "yaushe ka zama mai korafi kuma, Auntyn da ma yau ko lokaci na bata yi ba, tana ta hidima" ta karashe tana zagayo da hannun shi kugun ta.

    "Sannu da zuwa"

Ajiyar zuciya ya sauke "Yawwa, how was your event" ya tambaya cikin kulawa

   "Alhamdulillah" ta amsa, suka nufi dakin baccin su tare tana taya shi cire kayan jikin shi.


A karo na ba adadi ta sauke idanun ta kan shi, cikin salon kallon da ya fahimci tana yi mishi a 'yan kwanakin, a lokacin da ya ke murza man Vaseline jikin shi bayan ya fito wanka.


   Tana hango damuwa sosai a fuskar Adam a 'yan kwanakin, damuwar da ta rasa ko ta me ye.

    Duk yanda ya so boye mata damuwar da ya ke ciki, hakan bai hanata fahimta ba, sai dai tunda ta tambaye shi har sau biyu yace ba komai sai kawai ta zuba masa ido, domin ita ba mutum ba ce mai tsanantawa tasan dai ko mai daren dadewa zai gayamata, watakila ba yanzu ba, domin dai tsakanin ta da Adam ba boyo, a duniyar na bata ga abinda yake boye mata ba.


    Murmushi ya sakar mata tare da dage gira daya sama cikin salon tambaya, sai ta girgiza kan ta kawai alamar ba komai.

   Falo suka dawo, wani Tv series da su ke kallo a laptop din shi the night Agent suka cigaba daga inda suka tsaya jiya, har lokacin baccin su yayi.


    Washegari baccin safe suka sosai kasancewar yau weekends, bata fita IT hakanan Adam ma baya da aiki yau Saturday hakan ya sanya basu tashi ba sai wani karfe goma na safe.

   A hankali ya sanya Hannun shi cikin sumar kan ta da ya bazu kan pillow ya shiga yawo da yatsun shi, a cikin baccin ta wani bakon lamari ya ziyarce ta, ajiyar zuciya ta sauke tana da da mirginowa gefen shi tare da yamutsa fuskar ta tana shigewa faffadan kirjin shi mai dauke da gargasara kamar wata 'yar mage.


   Murmushi Adam ya saki tare da shafar kumatun ta yana raya "Kamar wata baby" a ran shi.

  Bai tayar da ita ba ya nufi toilet kai tsaye, wankan shi mai dan ba ta lokaci ne, ya dan jima ban dakin kafin ya fito daure da farin towel iya Kugu, murdadden jikin sa a bayyane yana digar ruwa, Wanda hakan ya fitar da siffar sa ta zaratan maza duk da bashi da dabi'ar daga karfe, baki ne shi sidik kana ganin shi ka ga cikakken malam bahaushe.

   Fuskar sa mai dauke da sirrin kyau ta wadata da murmushi a lokacin da ya sauke idanun shi kan ta, tana tashi daga bacci hadi da yin mika.


   "Good morning" ta fada itama tana maida mishi martanin murmushin shi

"Morning sleepy head" ya karashe yana takowa gaban gadon, shi ya taimaka mata ta mike ta hanyar mika mata hannun shi ta kama.

  Kai tsaye itama bandakin ta nufa kamar yanda yake al'adar ta ko ma ince al'adar su su duka, wanka is the first thing out of their daily routine.


    Tayi wanka ta fito zuwa lokacin ya shirya har ya fice daga dakin, ta dan bata lokaci gurin shirin ta, ta shirya cikin wani straight skirt jeans da cream satin top mai dogon hannu.

    Ta zurawa fuskar ta ido ta madubi a lokacin da ta ke warware cikakken gashin ta da ya bazu kan kafafun ta nan ta ke, ta taje shi da man gashi na Dax, tare da pake shi tsakiyar kai, ita dai tana son gashi, bata gajiya da gyaran gashin ta, sai ga shi Allah ya ba ta wareatacciyar sumar da kullum aikin kenan gyaran ta.

   Ta feshe jikin ta da cologne din Mousuf peach ta fito falon rike wayar ta.


Kai tsaye kitchen ta nufa ta fere dankalin hausa da suke da shi a gidan, ta yi mishi yankan slice tayi frying, ta dora ruwan tea ta dafa shi da ginger and honey tea bag ta juye a flask.

    Ta jere komai a tray ta kawo falon, zuwa lokacin yana kan center carpet da waya hannun shi, da alama call ya ke yi sai dai ganin ta ya sanya shi cutting call din nan ta ke yana basarwa.


   Kamar bata ga abinda yayi ba, sai ta basar kawai tana dora breakfast din kan center table.