5
by @mahmazee1
Ajiye wayar yayi kan table ya janyo mug ya hada tea, itama ta hada na ta suka shiga karyawa in silence, har suka kammala ya koma ciki ya chanja daga three quarter da shirt din jikin shi zuwa kaftan ya fito.
"Are you going out" ta tambaya idanun ta na kalar puppy eyes, domin ta dauka zasu karasar da sauran yinin a tare kamar yanda suka saba almost every weekend.
Sunkuyawa yayi yayi kissing forehead din ta "ba jimawa zan yi ba, akwai abinda dole zan je in duba"
Ta mike daga kan carpet din yana taya ta da dayan hannun shi, yayin da dayan ke aljihun kaftanin sa, ya janyo ta yana sanya ta barin jikin shi na dama, iya tayi mishi rakiya har gurin Babur din shi, ya tayar ya fice yayin da ita kuma ta koma cikin gida.
Duk gidan yayi mata shiru ba dadi domin ta saba on weekends suna tare, weekends ne ranakaun da suke samu for themselves tunda during the weekdays kowanne yana fita, ita school shi kuma gurin aiki, shiyasa suka maida weekends ranakun da suke Samarwa junan su time.
Guraren karfe daya aka yi knocking gidan, cikin mamaki ta nufi bedroom din ta ta janyo hijab ta dora kan kananan kayan jikin da ke jikin ta, ta dawo falon tana tambayar "waye"
"Ni ne Aunty" Salis ya fada daga chan waje, ta gane muryar Salis, wani yaron makotan su da Adam ke sanyawa aike.
Ta bude kofar da ke locked da murmushi kan fuskar ta.
"Ina yini Aunty Fahima"
"Lafiya kalau Salis" ta amsa gaisuwar yaron
"Gashi Uncle Adam ne yace a kawo" ya fada yana miko mata bakar ledar da ke hannun shi.
Ta karba ta juya ciki tana fadin Ina zuwa, tarkacen kayan bukin kareema su chin chin da Dublan ta diba a Leda ta bashi "ka kaiwa maman ka" ya karba yana ta godiya ya juya.
Kayan Miya ne a cikin ledar wadanda basu da a gidan, ta dora white rice and stew duk da kayan miyan ba yawa amma ta sani abincin zai ishe su.
Bai dawo gidan ba sai after 9pm kamar jiya sai da ya fito daga gurin tutoring (extra lesson) din da yake yi, sai complain din jimawar sa ta ke mishi kamar zata yi kuka.
Haka weekend din ya kare babu armashi a gurin FAHIMA unlike sauran weekends din da ta ke spending din shi tare da mijin ta.
Yau Monday karfe takwas saura ta kammala yan aikacen ta, ta shirya tsab domin fita gurin attachment din ta, cikin wata doguwar riga emerald green da siririn mayafi milk, ta ratayo tote handbag.
A karo na ba adadi ta sauke kallon ta kan Adam wanda baya da alamar ta shi daga kan gadon bare har yayi shirin fita gurin aiki.
Karasowa tayi gaban gadon cikin mutuwar jiki ta zauna gefen shi, ta zuba mishi ido yayin da ya ke baccin shi, sai lokacin ta da da lura da karamar ramar da yayi a yan kwanakin.
Ta dora hannayen ta duka kan kirjin shi, ta sunkuyo tana daidai ta fuskar ta da tashi.
"ZAWJ, ZAWJ" ta shiga kiran shi a tausashe, cikin sunan da ta ke addressing din sa da shi.
"Zawj wake up" ta sake furtawa a sanyaye, cikin siririyar muryar ta, idanun shi ya soma budewa a hankali kan ta, kafin ya bude su sosai for a moment yana kafe ta da shanyayyun idanun shi.
"Zawj kana yin latti fa" muryar ta mai cike da nutsuwa ta sake fada.
Dan mikewa yayi zaune ya jingina da pillow yana sakin murmushin yake
Yace yana murza hannun shi da ke cikin na ta "har kin shirya"
Da kai ta amsa shi da eh
"Ba zan fita da wuri ba yau, ki je kawai Allah ya tsare" domin sometimes tare su ke fita ya ajiye ta kafin ya wuce gurin aikin shi tukunna.
Ta dan bata fuska cikin rashin jin dadi kafin tace "okay, breakfast yana falo" ta mike daga kan gadon.
Saurin kamo tsintsiyar hannun ta yayi, ya dakatar da ita, suka zubawa juna ido for a while, kafin ya murmusa yana janyo side drawer da ke gefen gadon, ya ciro 1k da ke nan yana mika mata.
Dan kallon shi tayi kadan, a yan kwanakin ta fahimci babu kudi hannun shi ko tun daga cefanen gidan ta da ya chanja, hakanan da yawan fitar da yake yi sometimes ba da abin hawan shi ba saboda rashin mai.
Ta girgiza mishi kai tana fadin "ina da sauran transport fee din da ka bani last week, zanyi amfani da shi"
Girgiza kan shi yayi ba tare da ya saki hannun ta ba yace "no, bana so ki takura, just take it please" ya karashe yana da da murza hannun ta da ke cikin ka shi.
Dan jim tayi kafin ta karbi kudin "thank you Allah ya kara rufa asiri"
"Ameen"
Ta dan sunkuya tayi kissing forehead din shi ta fice da sauri saboda tana latti.
Sai bakin titi ta samu napep din da ta dauke ta zuwa gurin aikin ta.
Ta nufi HR tayi signing attendance tafin ta wuce department din su, gurin da aka kai ta
Kusan su biyar ne IT students a gurin , akwai Nafisa Jalal wata student din FBIU wato Franco British international university kaduna da jinin su ya hadu sosai da Fahima.
Fahimar na burge Nafisa tun da suka soma haduwa ranar da suka yi reporting, itace tayi initiating friendship din na su domin kyau da nutsuwar fahimar da ke burge ta, yanayin ta na shiru shiru da kamewa ma burge Nafisa wanda mutane da yawa a gurin ke gani a matsayin girman kai ko wulakanci, wanda a gurin FAHIMAR Sam ba haka ba ne, ita dai haka Allah yayi rayuwar ta da rashin hayaniya sai mutane da yawa suke ganin hakan a matsayin girman kai, a gidan su ma bata tsira ba kallon da suke mata kenan, bare duk wani guri.
Nafisa ta karaso da murmushi kan fuskar ta cikin kulawa ta dafa kafadun, tare da tambayar fahimar how she's doing ganin yanayin da ke kan fuskar ta.
"Lafiya qlw Nafisa, ya kike"
Ta zauna kan kujerar da ke gefen ta "am good, kin tabbata fahima, you look down"
Ta da da fadada fara'ar fuskar ta hadi da sauke wata ajiyar zuciya, ita kan ta bata San damuwar da ta ke ciki ta bayyana kan fuskar ta ba.
Tayi yake kawai ba tare da ta amsa ta ba, aikin da ke gaban su suka soma har zuwa lokacin tashin su wanda ya ke karfe daya.
Tare suka fito da Nafisa wacce kana gani zaka fahimci tsantsar wayewa, gaye da aji da ta ke tattare da ita, tana sanye cikin wata Turkish gown da vintage scarf da ta daura sai handbag din Lv da ke hannun ta.
Duk yanda fahima ta so ta bar ta ta bi napep Nafisa ta ki
"Bana son irin haka Fahima, ta ya zamu fito tare ina da ride kuma ki ce zaki hau adaidaita, please mu je kawai, sai idan mijin ki ne baya so, wannan kam ba zan takura ki ba"
Fahima ta dan jinjina kan ta tare da kallon nafisa a natse tace "shikenan mu je"
Suka nufi farar Range Rover evogue din da Nafisa ke hawa, tun da suka kamo hanya Nafisar ta Kure motar da music tare da vibing to it.
Sai dai a gurin fahima kamar ma, ba ta cikin motar, domin hankalin ta ya tafi chan gurin mijin ta, da ta rasa me ke faruwa da shi a yan kwanakin.
Nafisa ta ajiye ta har kofar gida kafin ita kuma ta juya.
Kai tsaye dakin ta ta nufa, ta fara yin wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt din atamfa, tayi sallar zuhr ta dan sake gyara gidan, ta saka turare ta fito falo.
Sanin babu kayan girki a gidan sai bata ma yi attempting yin komai ba, ta zuba sauran kayan dublan da chin chin na bukin kareema kan plate ta zauna kan kujera da takardu gaban ta, da log book din ta tana kokarin cikawa.
karfe 4:30 na rana ya turo kofar falon, da sallama ya bakin sa, sai dai ko daga muryar sa zaka fahimci firgici da tsantsar damuwar da ke kwance kan fuskar sa.
Tabbas something is definitely wrong, Fahima ta raya Cikin faduwar gaba.
Ta tsura mishi ido ba tare da ta iya furta wani abu ba, bugun zuciyar ta na da da tsanan ta for some weird reasons, har ya karaso gaban ta, ya zauna kan carpet din da ta ke kai yana sanya ta gaba kamar Malama da dalibin ta
A hankali ya zare hular da ke kansa ya shiga fifita da ita duk kuwa da fankar sama da ke kunne tana basar da iska, Adam sai gumi yake yi, ya ajiye hular sa a karo na farko tun da ya shigo falon ya iya cira kai suka yi ido biyu.
"Fahima akwai damuwa"
Da ido kawai ta iya amsa shi ta hanyar fitar da yan idanun ta tare da dafa kirji, fahimtar ko wace damuwa ce wannan ba karama ba ce.
Ya sanya hannu aljihu ya zaro wata farar takarda, wata takarda da ya jima yana hawo da ita jikin shi gudun kar ma ya ijiye wata rana Allah ya nuna mata.
Wani irin dokawa kirjin ta yayi ta mika hannu cikin dauriya ta karbi takardar da yake miko mata, ta soma karanta content din ta.
"Fahima na rasa aiki na, for a month yanzu, these past few weeks I have been job hunting, but na buga na raya duk inda nake tunanin za a samu aiki ko abin yi na je amma har yanzu shiru, last hope di na was today, shima din ba a dace ba" ya fada cikin matsananciyar damuwa, muryar sa na nuna dacin da ke zuciyar sa har muryar sa na rawa
Wani irin mummunan abu da ita dai bata San sunan shi ba ta ji ya zo ya daki kirjin ta, da tana da ciwon zuciya ta sani da ba abinda zai hana zuciyar bugawa a daidai wannan lokacin.
"Innalilllahi wa inna ilaihi rajiun" ta shiga jerawa a boye kuma a sarari, kana a natse ta furta "hakika inna ma'al usri yusrah" tana jujjuya takarda da ke hannun ta, sacking letter ce da ga Ministry of education kaduna, da ke tabbatar da an Kori Adam daga gurin aikin shi.
Fahima ta samu damar fada cikin tsananin tashin hankali at the same time kuma tana kokarin boye firgicin ta.
Adam ya rasa aikin sa ta garin yaya, how, when, what exactly happened, dan aikin da suke ji da shi, ya zame musu gata daga su har yan uwan sa da yake taimakawa a gida, da aikin ma ya aka kare bare babu shi, dududu albashin nawa ne, shine suka karbe kayan su.
Cikin rawar murya tace
"Me ya faru zawj ,dama ana rasa aiki ne haka kawai"
Adam ya nisa yana jujjuya Kansa yace "kinsan an samu canjin gwamnati right, kuma party da ya sauka ba shi ya ci zabe ba wannan Karon, Toh sai sabuwar gwamnati suka Kori ma'aikata domin su samu damar dora na su mutanen, aka ciccire wasu aka dora wasu, mostly ko ince dukkan wadanda aka kora wadanda basu yi party daya ba ne da sabuwar gwamnatin, but look at me Fahima bana siyasa, ban taba yin ta ba kai ban ma San ya abubuwan suke tafiya ba, amma unfortunately for me suna na ya fito cikin list din wadan da aka kora"
Fahima tace "innama'al usri yusra, innamal usri yusrah, Allah kai ka dora mana, ya Allah see us through" cikin karfin hali, ta furta ayar da a duk lokacin da ta samu kan ta cikin tsanani ta kan karanta ta
"Ban so gaya miki na tayar miki da hankali ba, amma I have no other option domin yau ko abinda zanyi cefane da shi na rasa, ga kudin haya har an bani notice, dan tuition fee din da nake samu gidan Alh balarabe su ne na hada na baiwa Aunty meramu da ta haihu kwanaki, wane irin shuwagabanni muke da su yanzu, wane irin system muke cikin sa da rayuwar talaka ba ta zama a bakin komai ba"
Ya fada yana dora kan sa kan cinyar ta cikin zafin rai, ji yake nauyin da zuciyar shi ke yi mishi kamar zata buga
A hankali ta kai tattausan hannun ta ta dora kan sumar kansa, ta shiga yawo da hannun ta cikin sigar lallashi.
Kalamai masu sanyi da ta san zasu tausasa ransa ta shiga furta masa cikin rada, ba don itama din tana cikin nutsuwar ta ba sai don faranta ran wanda ta San baya da buri a fadin duniyar nan face faranta mata.
Ta yi iya kokarin ta na danne hawayen da ke son sauko ma ta, wannan wani babban alamari ne ke kusanto rayuwar su ko ma tace rayuwar su take ciki already.
Da aikin Adam din ma ya rayuwar ta kasance musu bare babu, Allah ne kadai yasan adadin iyalan da ke cikin tashin hankali kwatankwacin wanda su ke ciki ko ma fiye da wannan chanjen aikin.
domin na su da sauki, akwai magidancin da ke da mata da ya ya birjik yanzu an karbe dan aikin ina zai samu abinda zai ciyar da iyalin sa in this harsh economy da recession da muke ciki.
Ba ta yi kuka ba sai da ta shiga kitchen din su domin sama musu abinda zasu ci ko ya ya ne, dama tun dazu shi ta zauna zaman jira ya kawo cefane.
Rike kugu tayi da dayan hannun ta tare da dafe goshi da dayan a lokacin da ta fahimci basu da wani abin arziki a kitchen din face danyar shinkafa da wata dadaddiyar doya, wadanda suma din babu abin sarrafa su ko da kuwa da mai da yaji ne suji, dama dankalin Hausan da yayi musu saura ne tayi musu dubarar shi in the morning kafin ta fita.
Wasu hawaye masu zafi suka sauko mata ba tare da ta shirya musu ba, sai ta hada kai da bangon kitchen din tana sauraron bugun zuciyar ta da ya da da tsananta.
"Kuka kike yi ko fahima" ta ji an fada daga bayan ta, kasa juyowa tayi domin bata so yaga kukan ta
Dafa kafadar ta yayi yana fadin "kiyi hakuri fahima kiyi hakuri, ni din na kasa baki farin ciki da rayuwar da kika chanchanta.
Sai ta juyo gaba daya ta fada kirjin sa tare da fashewa da kuka, kuka mai zafi, mai fitowa tun daga kasan zuciyar mai yin sa.
Bayan ta ya shiga shafawa kamar karamar yarinya yana fadin
"am sorry, I am so sorry my wife, ina rokon Allah kar ya dauki raina face na rama miki irin halaccin da kike yi min"
Da sauri ta ciro kanta daga kirjin sa tana dora tafin hannun ta kan labatan sa, ta shiga jujjuya kai alamar bata son zancen sa na mutuwa.
Wani murmushi mai ciwo yayi ganin hawayen ta da wani ke korar dan uwan sa.
Hannun ta ya kama, ya janyo ta kamar wata karamar yarinya suka dawo falon su, ya zaunar da ita kan kujera yayin da shi kuma yayi durkuso gaban ta, yana dora hannayen sa kan knees din ta yace
"Kiyi hakuri kin ji fahima, kiyi hakuri wifey" ya karashe yana shafar fuskar ta.
Hannun na sa da ke kan fuskar ta ta kama ta sanya cikin tafin hannun ta kafin ta yi kissing hannun na shi a hankali.
Sun dan jima a wannan yanayin kafin ya mike da hanzari kamar wanda aka mintsina yace "ina zuwa" ba tare da ya tsaya saurarar ta ba ya sa kai ya bar falon, shiru tayi ita kadai wondering ina kuma zaije.