6
by @mahmazee1
After an hour sai gashi ya dawo dauke da wata bakar leda karama da murmushi kan fuskar shi.
Kan kujerar ya zauna gefen ta yana zaro take away, sai ga shinkafa fried rice with beef gefe daya kuma har da albarkar salad.
"A Ina ka samo abinci haka" ta fada tana masa kallon tuhuma
"Don't worry kici kawai" ya fada yana mika mata disposable spoon da ke hade da take away din, bata fuska tayi tana kafa masa manyan idanun ta masu hana shi yi mata gardama
"Why would you waste so much money on this, I hope ba bashi ka karbo ba" ta fada sanin yanda ya tsani karbar bashi, duk yanda yake cikin tsanani ya fi so ya baiwa kan sa hakuri da ya ci bashi a wani guri
But we are talking about Fahima here, matar sa, the most closest person to him a rayuwar nan, ta ya zai yi folding arms yana kallo yunwa ta kassara masa ita
"No no no, kudi na da nake bin mal buhari ne na karbo and got you something to eat, bismillah oya eat"
Ta bude baki da niyar magana yayi saurin taron hanzari ta "FAHIMA please mana"
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta Karbi spoon din da ya miko mata, spoon daya tayi ta kai na biyu bakin sa, yayi Saurin kawar da kai yana shafa cikin sa yace "kici kawai ni am full"
Kallon tuhuma tayi masa, da kyar ta lallabasa ya karbi abincin, idan ta ci sai ta basa a haka har suka cinye shinkafar da dama ko mutum daya ba zata kosar ba bare biyu.
Daren ranar kam haka suka kwana ba tare da sun sanyawa cikin su wani abu ba, sai ruwa da su ke korawa da sauran kayan bukin kareema.
Washegari haka ta fice gurin aiki saukin ta naira dubu da ya bata jiya, haka tayi transport fee ta tafi.
Sa suka tashi Nafisa ta sauke ta as usual, Kan hanya ta ce ta sauke ta, haka ta tsaya wani karamin shago nan kusa da su, ta auno man hannu wato Man kuli kuli da maggi da sauran chanjin hannun ta ta yo gida.
Farar shinkafa da mai tayi musu ita suka ci, wani abu da duk rashin karfin Adam basu taba cin shi ba a gidan.
Tura shinkafar kawai yake yi ba don yana fahimtar abinda ke shiga bakin shi ba, ya cira kai ya kalli FAHIMA da kan ta ke kasa, tana cin abincin ta a natse, baya ji tana jin tafasar zuciyar da shi yake ji.
Zare hannun sa yayi daga plate din, ya mike ya nufi bedroom din su, da ido ta bi shi, idanun tab da hawaye.
Ta dan jima zaune sunkuye da kan ta a kasa kafin ta mike ta bi bayan shi.
Yana zaune bakin gado ya dafe kai da dukkanin hannayen sa, a sanyaye ta karaso ta zauna gefen sa tare da dora dayan hannun ta kan kafadun sa.
"Why me Fahima, me yasa suka yi choosing di na out of the thousand people there" ya fada da kyar ba tare da ya ciro kan sa ba.
Gaban shi ta dawo tayi durkuso tana lekon fuskar sa
"Zawj gardama zamu yi da hukuncin ubangiji" ta karashe a tausashe.
Ya ciro kai yana sanya idanun shi da suka kada sosai cikin na ta, ba zata yi karya ba idan tace ta hango hawaye a idanun Adam, wani mutum da ta ke kallo as one of the most strongest person on this earth.
Adam namiji ne mai tsananin dakiya da dauriya, bata yi karya ba idan tace tunda ta ke da shi bata taba ganin hawayen shi ba, a gida daya kuwa suka tashi, suka kuma girma, a halin yanzu kuma su ke zaune a matsayin ma'aurata.
Bata iya sake cewa komai ba face rungumo shi kawai da tayi jikin ta, ta zagayo da dukkanin hannayen ta wuyan shi, sai iska ya ke furzarwa wanda ta ke jin saukar shi a wuyan ta,
The next day kam bata iya fita gurin IT ba, haka tayi zaman ta gida, yayin da a gurin Adam tun safe ya fice daga gidan, bashi da wata sauran dubara face aikin karfi, irin ayyukan nan da ake sallama daily.
*********
A kwanakin da suka biyo baya duk inda suke tunanin tsanani ashe rayuwa ta wuce hakanan, domin zasu iya tashi abinda zasu ci ma ya gagare su, za kuma su iya yini a hakan.
Tayi kuka a boye, tayi a bayyane ta kuma yi a sarari, ta kuma yi iyakar nata kokari na kwantar da hankalin mijin ta, domin ta san sanda yake da shi bai kyetace ta ba, infact ma Adam is the type da duk abinda ya samo a duniyar nan sai ya kawo mata sunyi shawarar yanda ya kamata ayi, sometimes abokanan sa kan tsokane shi da mai bin shawarar mace ko mijin tace, kai har mutanen gidan su kan yi mishi wannan sharrin.
Tuni ya rarraba CV din shi gurare da dama, Baba ma ya karba, da fatar za a dace, haka ma Alh Balarabe gidan da yake ba da extra lesson.
Wata daya kenan suna cikin wannan tashin hankalin, a karo na ba adadi Nafisa ta sake gwada layin Fahima, wacce bata zo gurin aiki ba yau kwana uku kenan.
Har wayar ta gama ringing ba a daga ba sai kawai tayi deciding zuwa gidan ta ta duba tunda dai ta san gidan.
Daga nan chan ta wuce direct tayi packing gaban gidan kafin ta fito motar ta ta tura kofar gate din su.
Gidan shiru, harabar gidan da ke dauke da zallar siminti a tsabtace ko kare wannan babu, sai mashin din Adam da ke pake chan daga nesa.
Ta karasa tayi knocking kofar da ta ke da tabbacin zata sada ta da cikin gidan, knocking biyu kafin aka zo aka bude mata.
"Nafisa" Fahima ta Kira sunan ta in disbelief domin bata yi tsammanin ganin ta a gidan ba, duba da bata taba attempting shigowa ba tun da take ajiye ta, ita kuma da rashin hausa irin na ta bata taba yi mata tayin shigowa ba.
"Yes ni ce Fahima" Nafisa ta fada cikin rashin dadin rai tana kallon wayar Fahima da ke rike hannun ta, which means ta ga kiran ta ko da kuwa missed calls ne, ta kuma ki dagawa.
"Shigo mana" suka karasa cikin falon, Nafisa ta zauna tana bin dan falon na Fahima da kallo wanda ko girman dakin ta ba zai yi ba.
Sam fahimar bata yi kalar irin wannan gidan ba, amma who is she to judge, suma din da su ke da ba su suka ba kan su ba, Allah ne mai bai wa wanda ya ga dama a kuma sanda ya so.
Fahima ta zauna kawai shiru ta rasa me zata kawo wa Nafisa, first time din ta gidan ta amma ko ruwan pure water bata da wanda zata ba ta.
Sai da gaban Nafisa ya fadi a lokacin da ta ankare da wata irin rama da Fahima tayi, da damuwa ta musamman da ke kwance kan fuskar ta.
Suka gaisa a mutunce, Nafisar na tambayar ta ko lafiya kwana biyu bata shigo ba.
"Ba komai Nafisa, kawai dai I have something da na ke handling"
"Shi zai hana ki zuwa aiki Faheema, suma last days na karewa, kar su janyo miki matsala a makaranta kin San dai basu da imani mutanen nan"
Fahima tayi yake ba tare da tace komai ba
"Fahima kina da damuwa, me ke faruwa ne"
"Ba komai Nafisa"
duk yanda Nafisa ta so jin damuwar fahima sai nuna mata ta ke ba komai.
Nafisa ta dan bata rai "I thought mun wuce haka Fahima, amma ba komai thank you, Allah ya sawwaka" ta mike tana tattara jakar ta.
"Nafisa" ta Kira ta a sanyaya, ta juyo tana kallon fahimar wacce tuni hawaye suka cika idanun ta, tana da bukatar wanda zata yi sharing damuwar ta da shi, she has been bottling up a lot a yan kwanakin nan.
Duk da Aunty na Kira a kai a kai tana kwantar mata da hankali, amma akwai abinda ba zata iya gayawa Aunty ba, hakanan akwai abinda ba zata iya gayawa Adam ba, tun da abin nan ya faru sai dai ta rufe kan ta daki tayi kuka ita kadai.
Ko Adam din bata so ya ga kukan ta bare Aunty da ta tabbatar ita ma din akwai tarin hidimomi a kan, bata so ta tayar musu da hankali, domin ta tabbata kukan ta babban damuwa ce ga mutanen nan biyu, zata kara ma Aunty damuwa ne kawai kan wanda ta ke ciki.
Ta dawo kan kujerar da ta ke kai ta dafa kafadun ta cikin sigar lallashi "komai yayi tsanani maganin shi Allah Fahima, I don't know what's wrong amma ina rokon Allah ya yaye miki"
Kama hannun nafisa tayi cikin na ta kafin ta fashe da kuka, suka rungume juna Nafisa na da da lallashin ta, a ranta tana raya koma meye damuwar ba zai wuce may be mijin Fahimar ba ko kuma rashin da ta ga alamar su fahimar na cikin shi.
A yanda ta ga Fahima ta rame a idanuna ta sai da abin ya tsorata ta, tun kwanaki ta fahimci chanjin yanayi a tattare da fahima amma bata dauka abin yayi worst ba.
Nafisa dai bata sake tambaya ba, fahimtar ko ma meye damuwar dagaske Fahima bata son gaya mata, watakila kusancin da ita ta ke tunanin suna da a gurin fahimar ba haka ba ne.
"Just pray for me Nafisa, Nagode sosai, thank you so much" ta fada genuinely, Ashe haka aboki ya ke da dadi, ko da bata gayawa Nafisa damuwar ta ba atleast ta saurare ta, ta bata shoulder to lean on.
Nafisa tayi mata sallama ta tafi tare da tabbatar mata da lallai gobe ta shirya zuwa aiki, zata biyo ta dauke ta.
Washegari kamar yanda Nafisa ta fada, ta kuwa zo ta dauke ta suka fice, tun daga ranar kuwa Nafisa made it her duty na ta zo ta dauke ta ta kuma mayar da ita, tun tana ce ma Nafisar a'a har ta saduda.
Fahimtar da tayi abinda ita ta ke gani wani abu ba komai ba ne a gurin Nafisa.
*****
Sati biyu suka biyo baya ba tare da wani chanji ba a gurin wadannan ma'auratan.
Yau karfe 1pm suka tashi kamar ko yaushe, tana kokarin shiga mota, Sakon sa ya shigo wayar ta.
"idan kin gama ki wuce gidan baba kawai, ina da abubuwan yi, when am done zanyi branching mu koma gida"
Dunkule wayar tayi a hannun ta ko bai fada ba tasan mai yake nufi da taje gidan baba, hakan ba zai rasa nasaba da yanda ta baro gidan ba, ta kuma tabbata bai samo komai ba a waje, shine yace ta je gidan baba ta wuni sanin a can ba zata rasa abinci ba ko da ya ya ne kowa.
Yi tayi kamar kar ta je, sai kuma kawai tace Nafisa fa ajiye ta gidan su instead. hanyar gidan su Aunty suka dauka ba don tana so ba, sai don ba ta son bijirewa umarnin sa.
Sosai Nafisa tayi mamakin gidan da suka zo, wato gidan iyayen Fahima, ta tuna gidan Fahima, ta kalli wannan katon gida mai dauke da manyan parts da dama, bata dai ce komai ba suka shiga ta gaida Aunty, ta fito tayi mata rakiya.
Aunty na nan falo inda suka bar ta, tana kallon tashar Arewa24 a DSTV din da mama zuhra bata yi sati biyu da hada mata ba, saboda korar da mummy ke yiwa Sadik a duk sanda yaje sashen ta kallo da yake shi Yaro ne ba ruwan sa ko an kore sa gobe ma zai koma, plus mummy tana da yara sabanin mami duk da dai sun girmi Sadik din, ranar mama zuhra ta zo gidan ta tarar aunty na rankwashin sadiq ta nemi ba'asi ta gayamata korar da ake masa kuma tayi tayi ya daina zuwa yaki, shine fa mama zuhra tace "indai akan DSTV ne Sadik ake korar ka, kai da gidan uban ka to kuwa ba za a sake ba" haka kuwa akayi wani sati ta turo yaron ta Abdulwahab da masu ha din DSTV suka setawa aunty.
Kallo daya Aunty tayi mata ta ji ranta ya baci da yanda Fahimar ta ta koma, tayi duhu tayi wata irin ramar da ko a Hijab zaka iya hango ta, sai Kashin wuya, fahimar ta da ke da kumari ce ta koma haka. Kai rashi bai yi ba.
ko fahima bata fada ba tasan rashin abin yin nan na mijin ta is affecting rayuwar su, bata taba yi mata complain na yanayin da suke ciki ba amma ko bata fada ba ai ita uwar ta ce, ko kowa bai fahimta ba ita zata fahimta, gabakidaya fahimar ta ta lalace kamar ba ita ba.
Da ido ta bita har ta samu guri ta zauna tana tambayar su Salma
"Ya maigidan na ki" Aunty ta tambaya
Alhamdulillah Ta amsa
Aunty ta kalle ta da kyau tace "ki shiga ciki ki huta hala dai daga gurin aiki kike"
Ta gyada kai "eh nace bari na biyo na duba ku kwana biyu ban shigo ba, kamar kin laluba zuciya ta Aunty wallahi a mugun gajiye nake"
Aunty tace "ai dole"
Mikewa tayi rataye da jakar ta, daki ta nufa dakin da da yake mallakin su ita da salma, wanda a yanzu ya dawo mallakin Salma da furera.
Furera a matsayin ya ta ke a gurin Aunty, daga nijer ta zo diyar tobashiyar Aunty ce wato cousin din ta, tunda suka zo auren fahima sai aka bar Furera da tace ba zata koma Nijer ba, Maman ta ma hakan yayi mata, domin ko a Diffa din a cikin wani kauyen Diffa su ke.
Da kanta Aunty ta shiga kitchen ta debo mata abinci kasancewar duka yaran na makaranta, watakila dai suna kan hanyar dawowa.
kwance ta tarar da ita ta zubawa silin ido kamar mai karantar wani abu, sai da Aunty tayi sallama so biyu kafin fahima ta ji ta.
Mikewa tayi zaune tana sakin siririn murmushi, Aunty ta zauna gefen gado "na dai san kam kin kwaso yunwa, ki tashi ki ci abinci"
Murmushi tayi tace "Da baki wahalar da kanki ba Aunty, zan zo da kaina na dauka"
Ba wanda ya sake cewa komai har ta bude plate din ta soma kai abincin bakin ta wanda ita kanta ta San ta kwana biyu bata ci abinci mai armashin wannan ba.
Jollof Rice ce da ta ji man ja da wake da zafin ta da alama yanzu aka sauke ta daga wuta, Tana kai loma daya bakin ta , sai da ya fado mata a rai, ko a wane Hali ya ke ciki oho
Aunty tayi breaking silence din tana fadin "fahima har yanzu Aiki dai shiru ko"
Da kai ta bata amsa da eh
Aunty ta girgiza kai tace "kai jama'a ace mutum da takardun sa mai kyau amma aiki ya gagara, wannan kasa ta mu Allah dai ya kawo muna dauki"
Ta Mike tana barin dakin tare da fadar " Allah ya sawwake"
Tana kammala cin abincin, sallah kawai tayi ta bi lafiyar gado, ko da su Salma suka dawo school Aunty hana su tayi su tashe ta, ba ita ta tashi ba sai wani lokaci har yammaci yayi.