7
by @mahmazee1
Sai da ta tashi ne ta shiga sashen baba suka gaisa daga nan sashen mummy suka nufa, Sadik da yayi mata rakiya na makale da hannun ta.
Mummy bata nan sai mai aikin ta suka tarar da ke ta kakkamce kakkamce zata rufe sashen, ita ke gaya musu Mummy ta wuce Lagos gurin Aunty Jamila, dazu jirgin su ya daga ita da Naseer Autan mummy kenan.
Itama din rufe sashen zata yi, za ta je gidan Ya Mairo wato yar mummy dake aure nan kaduna har mummyn ta dawo.
Bata tunanin Aunty ta san da wannan tafiyar da ta sani da ba zata ce ta shiga su gaisa ba, a ranta ta raya Allah ya kyauta.
Sashen mami suka nufa, wacce ke hakimce kan gadon ta yayin da Karima ke zaune kan stool da ke gaban dresser suna magana kasa kasa.
Ta ji kadan daga zancen su sa'adda Karima ke fadar "lagos din tsiyar me mami da har zaayi muna barazana da ita, kiyiwa ya najma magana kawai ayi miki ticket, ki je Saudi naji su OUMMAH ma zasu je Hajj as usual"
Jin motsin shigowar su sai sukayi shiru, suka karaso dakin, kan carpet ta zauna tana gaida mami, mami ta amsa a gatsine, Karima bata kalli sashen ta ba bare ta samu albarkacin gaisuwa sai ma Sadik da ta kalla ta kama hannun sa tana fadin
"Auta Sadik ja ja manya" shi kuma sai yayi dan murmushi
Fahima tace "Karima ya gida, kin shigo kenan"
Kafin ta amsa ta mami tace "yoh agola ma ya zo ya zauna bare dan masu gida"
ita sai bata ce komai ba ta ja hannun Sadik suka fice a ranta tana raya wai sai yaushe ne su mami zasu sassautawa ransu wannan bakin kishin, ita gani ta ke girma na kama su al'amuran su na da da lalacewa, Allah ya dai kyauta.
A sashen Aunty take gaya mata tafiyar mummy, Aunty bata ce komai ba, ta taba baki kawai
A ran fahima ta ji ba dadi domin hakan na nufin Aunty kawai za a bari cikin gida kamar yanda suka saba kenan, idan wannan tayi tafiya wannan ma sai ta tsiri ta ta tafiyar.
Sai dai ai lokacin sallar layya ne wato Eid Kabir, ta ya Aunty zata iya aikin gidannan ita kadai, sai ta kalli sashen mahaifiyar ta wanda ya fita banbanta da na sauran matan gidan, saboda gyara da suka fi na ta samu.
Tana jin tausayin Auntyn ta, dukkanin matan Baba sun fi ta karfi don ma dai bata da saka abu a raine, ai da sun kassara ta da bakin ciki, don da gangan za a tsiri abinda aka San ba zata iya ba.
Sai after magrib Adam ya shigo gidan, Bai wani jima a gidan ba suka wuce a keke napep.
A bangaren Aunty kuwa shiru tayi tare da buga uban tagumi tsayin wani lokaci bayan fitar su, sallama ake ta dokawa dakin na ta amma gabakidaya tayi nisa a cikin duniyar tunani har ya samu guri ya zauna gefen ta bakin gado.
"Amarya ya ya dai ina ta sallama bakya ji"
Dan zabura kadan tayi "Alhaji kai da kan ka, ai da ka kira idan wani abu kake so sai a kawo"
Murmushi yayi yace "ba abinda na ke buqata yau dai nace bari nayi tattaki na kawo wa mata na gaisuwa"
Murmushi tayi itama tace "mun kuwa gode Alh"
"Akwai wata matsala ne Ramatu ya na tarar da ke cikin tagumi"
Girgiza kai tayi alamar ba komai tace "ba komai Alh"
kallon ta yayi da kyau yace "da komai Ramatu sai dai ko baki fada ba na san ko meye damuwar, Nima kai na sabon yanayin nan da Fahima da maigidan ta suka samu kan su yana damu na, da shi na ke kwana na ke tashi, duk inda nake tunanin za a samu aiki na laluba, amma shiru, kasar ta mu ce ta lalace ko da karatun ka sai da connection, mu kuwa wa ke yi damu yanzu"
Ya jinjina kai kana yace "amma na san ta inda zan bullowa lamarin kuma ina sa rai insha Allah za a dace"
******
Washegari tana daki fitowar ta wanka kenan daure da madaidaicin towel ya shigo dakin.
A bakin mirror ya tarar da ita tana shafa, jikakken gashin ta da ke digar ruwa ya kalla kana yayi siririn murmushi, murmushi ta sakar mishi itama ta madubi tana kallon yanda yayi tsaye rike da qugu yana kallon ta
"Ya akayi" ta furta
Durkusawa yayi gaban ta yana dora hannu kan knees din ta yace "wata shawara ce Na zo muyi"
Gyara zaman ta tayi tana fadin "Toh Ina sauraren ka"
"Mashin di na nake so na siyar fahima"
Kallon sa tayi da kyau tace "mashin kuma"
Ya gyada kai "eh, ba shida amfani a gurina yanzu, tunda kina gani ya fi sati uku ajiye bana amfani da shi, Toh ni yanzu idan na samu kudi ta man mashin nake yi ko ta abinda zamu ci, shine na yanke shawara kawai na siyar da shi na kama sana'ar hannu tunda dai ban da wani source na kudi bayan shi, kuma aikin nan ya ki samuwa"
Shiru tayi na tsayin wani lokaci tana nazari, shi abin hawa fa duk yanda yake gwara kana da shi da akasin sa, kan a zo a siyar da babur dinnan a zo ba a dace ba a sana'ar ayi 2 zero tunda dai haka business ya gada baka da guarantee baka da certainty.
"Kana ganin hakan is a good idea"
"Am not sure shiyasa na ce ai nazo muyi shawara, my POV kenan amma ban sani ba ya kika gani" ya fada yana safe hannu sama
Fahima tace "Allah ya sa hakan shi yafi zama alheri, ya sa kuma a dace a duk abinda aka saka hannu"
"Ameen Ameen mata ta, a ko da yaushe ina alfahari da ke, ni na sani it's your prayers that are keeping me going" ya fada yana kissing tafin hannun ta ya zarce zuwa ga wuyan ta.
Tunda wannan rashin aikin ya same shi the only aiki she knows suna yi constantly ba fashi shine sex, sometimes har tsarguwar ta ya ke wai me yafi broke sex dadi
Washegari kuwa sai ga shi ya shigo gidan da fara'ar sa dauke da bakar leda, kudin da ke cikin ledar ya zube gaban ta.
150k ne kudin da mashin din yayi
"Toh yanzu yaya Adam wace sana'a za'ayi, do you have anything in mind"
"First of all waye yayan ki" ya fada yana mintsinin ta a ciki
Wata irin dariya ta sanya "kai mana, kai yaya na ne, ko ba haka ba"
Dariyar mugun ta ya sanya yana da da mintsinin ta "Don't ever Bro zone me Allah, yayan ki zai yi miki wannan din da nake miki" ya karashe yana zuge zip din rigar ta.
Ya zura hannun ciki shi yana yawo da shi bayan ta, kan bare skin di ta
*****************
Karar horn din motar GMC Yukon bugun 2024 mai tashi da isar da sakon zuwan ta ne ya karade gidan Alh Sanusi Ciroma.
Salis wani matashin saurayi da ke zama gidan ya zo da hanzari ya wangale gate din wanda ya baiwa motar kalar Onyx Black damar ratso harabar gidan.
Akwai security kwaya daya da ke gaban motar wanda tunda motar ta tsaya sai nishi ta ke, yayi hanzari fitowa ya tsaya kofar baya yana jiran a bashi umarnin budewa.
Sai da ta sake feshe jikin ta da signature perfume din ta wato Dahlia by Versace kana tayi knocking window, da hanzari security da ke tsaye ya bude mata
Tsininin takalman ta yan gidan jimmy choo su suka fara bayyana kafin fitowar Najma wacce ta sha ado kamar ko yaushe sai zuba kamshi ta ke yi, hannun ta makale da yar handbag da ta dace da abayar jikinta.
Da sauri Salis da samari biyu da ke zaune harabar gidan a daidai wannan lokacin suka karaso suna kawo gaisuwa.
Kamar ko yaushe bata iya amsa su da fatar baki ba sai hannu kawai da ta daga musu, Tana yiwa security ta alama da hannu wanda ko bata fada ba ya fahimci abinda ta ke nufi.
Ta taka a hankali kamar hawainiya ta nufi cikin gidan, yayin da Security din ta ya bude dashboard din gaban motar ya fitar da sababbin notes din naira dubu dubu ya basu.
Kai tsaye falon Baba ta nufa domin amsa kiran da yayi mata tun shekaranjiya tana garin Abuja, dawowar ta kaduna kenan jiya da yamma, yau ta iso gidan domin amsa Kiran sa.
Yana zaune falon sa tare da su sadik da Salma, sai Humairan Ya Lawal da ta zo gidan itama Tana tare da salma.
Sallamar su baba yayi bayan shigowar ta, suka gaisa sosai yana tambayar ina amaryar sa cewa da Anisa kafin ya nisa yace
"Akwai alfarma daya da ta sanya nayi kiran ki yau Najma"
Najma ta dago da kan ta kadan ta kalli baban wanda ya cigaba da
"Am very sure ba zaki rasa jin labarin rasa aikin sa da mijin Fahima ya yi ba a yan kwanakin nan"
Cikin matukar daurewar kai ta kalli Baba, of course kwanakin baya sunyi waya da Mami ta ke bata labarin halin da su fahima suke ciki, har Mami na tsokanar ta da yanzu ita ce fa
A lokacin kuwa she was on inflight call with Mami, Tana zaune kan daya daga cikin kujerun Private Jet din da sukayi chattering da sister in-laws din ta, zasu je kai yara hutu Marrakech.
A lokacin kuwa har jirgin su ya sauka Morocco tunanin da yanzu itace a gidan Adam cikin wannan kangin bai bar ta ba.
Ta tuna yanda ta kwana raya "Allah ya kiyaye" a ranta.
Sai dai me, bata dauka dalilin kiran da baba yayi mata ba kenan, domin she's very sure ya san abinda duk ya danganci Fahima da mijin ta ba abinda take shiga ba ne.
Baba bai da da shayar da ita mamaki ba sai sa'adda ya umurce ta da janyo drawer din da ke gefen ta.
Kamar yanda yace tayi, ta janyo wasu takardu da ke hade cikin wata folder blue
"Ki bude mana, Cv din Adam ne, wata alfarma nake nema gurin maigidan ki idan za a dace, ya samarwa Adam dan abin yi ko a nan kamfanin sa ne ko a cikin mutanen sa ne nasan ba za'a rasa ba, yana da resume mai kyau with a second class upper degree in Computer science, yanayi ne kawai irin na kasar mu da komai ya lalace"
Shiru najma tayi tsayin wani lokaci ta kasa amsa baba hakanan ta kasa dauke idon ta kan takardun da ta zubawa ido tun bayan kalaman Baba na karshe da suka daki kunnuwan ta.
Ta ya baba zai yi mata haka, ta ya zai sanya ita nemarwa Adam Aiki, mijin Fahima, surukin Aunty, matar da bata tunanin a duk duniyar nan akwai macen da ta ke kishi sama da ita
Da kyar ta iya ciro kanta tana yiwa baba kallon mamaki, bata taba tunanin akwai rana mai zuwa da Baba zai nemi wani abu a gurin mijin ta ba, ko da zai yi din bata taba tsammanin zai soma a kan Adam ba, duk tarin arziki, dukiya, kudi da alfarma da Allah ya wadata mijin ta da iyayen sa da su baba bai taba Neman wani abu a gurin sa ba, sai abinda shi own his own ya dauka ya bashi.
Sai dai meye abin mamaki najma, ta gayawa kan ta da kan ta a zuciyar ta, we're talking about Aunty fa a nan, even the unthinkable baba zai iya yi a kan wannan matar, ita kuwa a duk duniyar nan akwai macen da tayi mata karan tsaye a rayuwa irin Aunty.
Ta ina zata soma, ta yaya tana ji tana gani da taimakon ta rayuwar Aunty da iyalin ta ta inganta, domin a duk duniya kowa Shaida ne da irin so da bautar da Adam ke yiwa fahima, dukkanin abinda ya samo a rayuwa fahima ce, Fahima dai Fahima dai, ita kuwa fahima wa ta ke da shi sama da Auntyn, lamarin da ke ciwa Mami tuwo a kwarya kenan, a ganin ta idan aka cire dukiya toh fahimar duk ta fi yaran gidan samun kwanciyar hankali da soyayyya a gidan auren ta, domin soyayyar Adam gare ta a bayyane ta ke.
"Najma" Baba ya kira sunan ta a tausashe, bata san ta zurawa baba ido ba Ashe all this while tayi nisa cikin tunanin ta sai da yayi kiran ta
"Kina ji na Najma"
Da kai kawai ta iya amsawa, baba yace "ki kokarta from your side too, daga Adam din har fahimar duka yan uwan ki ne, idan kika inganci rayuwar su Allah zai biya ki"
A hankali zuciyar ta na radadi ta furta "toh yayi baba Allah ya sa a dace"
Kai tsaye bangaren Mami ta nufa rike da yar folder a hannun ta.
A falo ta same su, rabi mai aiki na durkushe gaban Mami Tana hada mata ginger Tea a dan tea cup.
A rikice ta iso falon bata ko saurari gaisuwar rabi ba tace "get out"
jiki na bari kuwa rabi ta bar gurin duk da kuwa zatayi sa'ar Najmar, amma haka ta ke katsa mata tsawa, da yake ita ta sanya aka kawo wa Mami ita, domin a rayuwar nan Najma ta ci alwashin sharewa mahaifiyar ta hawayen da Baban su ya kasa share mata, tayi alkawarin baiwa Mami duk wani farin cikin duniyar nan matukar yana existing
"Najma lafiya, ya na gan ki haka a rude wani abun ne ya faru a gida" mami ta fada cikin tashin hankali tana dudduba jikin Najmar da ta fado mata.
"Mami ba lafiya ba, wallahi ba lafiya ba" ta fada tare da dora mata takardun, Mami ta dudduba da kyau ta hadiye fuska tace "ke kuwa meya hada ki da takardun Adamu"
Nan ta juye mata duk yanda sukayi da baba
"kina ina mami har kika bari irin haka ta faru, yanzu ya zanyi, ta ina zan bullowa wannan al'amarin"
Ashar mami ta lailayo domin ba wuya ta ke mata ba tace "nan fa kadai wallahi karyar su ta sha karya, Toh ina hadin kifi da kaska, ina hadin mijin ki dan asalin, dan babban gida, jinin saurauta da sadakar yallar Nijer, ai wallahi ko da bakin dodo Ramatu ke tsafi sai ta bar FARUK a inda ta gan shi, domin abin da duk ya koro ta a tsaye ya tarar da ni"
Najma ta nisa tana dan samun relief a ranta
"mami what am I going to do, ya zanyi da Baba, wallahi ba zan iya ba"
Mami tayi wata muguwar dariya mai daci tace "ehhhh lallai mutanen gidan nan sun iya cin arziki, to ina hadin su da FAROUK, da har za a dora masa lalura, na ga dai FARUK dinnan da ne, da ni da uwar sa uba daya yayi silar zuwan mu duniya, Sanda na ke fadi tashin hada auren ku ai babu wanda ya kama min, infact ma dariya ta ake ganin ba abinda zai yiwu ba ne, FAROUK ya fi karfin ki, Toh wallahi ahir din su kurwar Faruk ta fi karfin duk wasu dangin mayu"
"Toh mami ya zaayi, me zan cewa baba me zan cewa daddyn Anisa, kina tunanin baba zai iya neman alfarma a gurin FAROUK ya kasa yi masa ita, not possible"
Mami ta yi kasa da murya tace "wani lokaci dai Najma kina da abin takaici, wani labour work can zaki nemar masa ko masinja ne ko maigadi, Ai bai fi karfin su ba"
Najma ta girgiza kai ganin kamar Mami bata fahimtar ta tace "ta ya Adam zaiyi aikin masinja mami with a second class upper degree, Baba ba zai yarda ba, FAROUK ma na san ba zai bashi labour work ba, not after knowing daga gurin baba ya fito"
Mami tace "ke kam dai baki da dubara, Sai ka ce ba mace ba, Toh bari zakiyi ya san Alh ne ya turo sa, bana tunanin ko Fahima FAROUK ya sani bare wani banzan mijin ta chan, Ai lallaba sa zakiyi ki samu ko aikin masinja ne ya hada shi da shi, idan ba haka ba muna ji muna gani FAROUK zai maida Adam wata tsiyar da Kirkin nan na sa mai ban takaici" mami tayi Tsaki tana fadin wallahi dai Alh ya ci zarahi na.