RAYUWAR DAN ADAM

8

by @mahmazee1

Kwana daya Kwana biyu, kwana uku baba ya ji shiru, he was becoming impatient amma dai bai daga waya ya kira ta ba.


Kusan sati biyu da haka sai ga ta har falon sa da murmushi kan fuskar ta amma dai tana ta dar dar din yanda baba zai dauki zancen.


Ido Baba ya zuba mata tsayin wani lokaci bayan ta gama koro bayanin ta, ya ma rasa mai zai ce

Da kyar ya furta tsabar takaici "Adam ne zai yi labour work a kamfanin mijinki, da qualifications din sa ma su kyau"


Najma tayi kasa da kai tace "kayi hakuri baba yace ba wani vacancy ne at the moment, akwai sabon kamfanin sa da zai buda Insha Allah idan anyi launching za a samu ayukka sai wanda aka zaba ma, all the constructions are done, launching kawai ya rage"


Baba ya jinjina yace "ba komai an gode, Allah ya nuna muna anyi launching din amma Adam dai ba zai yi labour work ba"


Najma ta murmusa kasan mayafin ta dadi ga ni kashe ni, ta mike tana fadin zan shiga mu gaisa da su mami.


Baba yace "toh shikenan, next you're coming ki zo min da Amarya ta if not tun a bakin gate zan kora ki" tayi murmushi ta fice daga falon.


Baba ya jima bayan fitar najma yana ta nazarin abinda ta fada yana kuma dora sa a sikeli na fahimta, ba ya tunanin zai iya neman alfarma shi da kan sa a gurin mijin najma ya kasa yi masa ita, at the same time kuma baya tunanin zai sanya najma abu ta kasa yi masa shi, a ganin sa she has nothing to loose don ta taimakawa Adam ya samu aiki a karkashin mijin ta.


Wayar sa ya daga ya lalubo Aunty "ki same ni daki na"

Ba jimawa kuwa sai ga ta ta shigo dakin na sa

"Ga ni Alh" ta fada fuskar ta da yar damuwa, ganin yanayin kiran da yayi mata.


Murmushi yayi yace "zauna mana" ya nuna mata gefen sa, zaman tayi sai dai duk hankalin ta bai kwanta ba

Baba yace "yanzu najma ta bar nan"

"Toh Allah ya sa dai lafiya"

Baba yace "ba wata damuwa, dama kwanaki nayi mata zancen aikin Adam ta tuntuba muna gefen mijin ta ko Allah zai sa a dace"


Da mamaki Aunty ta dago ta kalle sa full of hope kuma domin ta san da yardar Allah ba za a rasa aiki a gurin mijin najma ba, sai dai ba tayi tsammanin baba zai tuntubi mijin Najma ba, kai ko wani daga cikin surukan sa ma.


Nan baba ya juye mata yanda sukayi da najma da kuma outcome din da aka samu.

Shiru aunty tayi bata ce komai ba, tabbas da lauje cikin nadi, baban kuwa ya shiga nuna yanda najma tayi iyakacin kokarin ta.


sai dai ita kam ta san wannan tsarin na najma ne da mahaifiyar ta idan ma shi Alhajin bai fahimta ba.


Bata tunanin baba zai nemi alfarma a gurin Farouk ya kasa yi masa ita, duba da mutunci da girmamawar da ke tsakanin su, Farouk din yana matukar girmama mahaifin Najma da dukkanin al'amuran sa, musamman da ya fahimci abin hannun sa bai tsolewa baban ido ba.


Ko ita da take matar uban ta Allah ne kadai ya san tarin alkhairan da ita da ya yan ta suka samu a gurin mijin najma, domin idan dai zaiyi kyauta a gidan tabbas baya mantawa da ita hakanan baya mantawa da mummy sai dai zata ce ba wata hulda tsakanin su, infact ma zata iya kirge adadin ganin da ta taba yi masa.


Ita kam me ta tarewa wadannna bayin Allah da suka sanya ta a gaba haka, ina ruwan Fahima da mijin ta da kishin da suke yi, mamin ta yi da ita mana ita da ta ke kishiyar ta, ta kyale yar ta, yar marainiyar ra


Baba yace "sai dai na gaya mata Adam ba zaiyi labour work ba, idan an buda kamfanin an samu aikin toh Alhamdulillah idan kuma ba a samu ba ba komai Allah ya bashi gurin da yafi nan"


Murmushi Aunty tayi mai ciwo a ranta ta raya "in kin san wata Ai baki san wata ba Umaima"


A sarari kuma sai tace "aa ba za'ayi haka ba Alh, idan akayi haka kamar ba a yi appreciating kokarin najma ba hakanan shima mijin na ta zai ji babu dadi, zai ga kamar ba a gode ba, ni da kai fa duka mun san ko waye FAROUK tunda har kaga ya kasa yi maka wannan alfarmar to abin bai samu ba ne, labour work fa is not that so bad Alh, tunda ba mu San wane labour work din ne za a bashi ba, a gani na ko ya ya ne yafi masa zaman banzan da yake yi, ni a gani na ya je kawai Allah ya sawa abin albarka Ai ko don surukutar da ke tsakanin mu da FAROUK ba zamuyi wannan keke da qeqen ba, idan an dace da sabon aikin toh ka ga walillahil Hamd"



Aunty ta fadi hakan tana rayawa a ranta, tunda har Alh da kan shi ya bullo da wannan al'amarin ita kuwa ba zata Bari wannan opportunity din ya wuce su Fahima ba, wa ye zai rabi FAROUK bai samu alkairin sa ba, mutumin da kowa ya san shi da tarin alkhairorin sa da taimakon na kasa da shi, Mutumen da tarin abin hannun sa bai rufe masa ido ba, mutum kamar FAROUK mai tarin nagarta da dattijantaka.

   Ta sha jin labaran FAROUK da yanda yake taimakawa Youths, how he helped a lot from nothing to something 



     Idan har Adam ya je din ta tabbata FAROUK ba zai bar shi hakanan ba, kai shi da kan sa ma Adam din along the way zai iya applying for a better position idan ya gane kan wurin, ta san duk wannan abin da su mami sukayi ba komai ba ne fa ce don shi Adam din ko Alhajin suyi fushi su ki karbar aikin, daga haka maganar ta shashance.


     Baba yace "Anya ramatu anyiwa Adam adalci kuwa bana tunanin zai iya wannan aikin, more especially karkashin mijin najma mu fa maza muna da ego, ko fahima kina tunanin zata ji dadin haka"


"In don ta fahima ne ni nasan ba wata damuwa, Adam din ma lallaba sa zakayi, kai fa mahaifin sa ne ka fi shi sanin what's good for him, Ai abinda babba ya hango yaro ko ya taka tsani ba zai hango ba"


Baba yace "toh shikenan ba zan ki ta ki ba, amma zan binciki Adam din idan naga ran sa bai so ba ba zan tursasa sa ba"

Aunty tace "Adam ba zai ki ta ka ba Alh"


Baba yace "kiyi min kiran fahima ki gaya mata ina neman mijin ta"

Aunty tace toh ta tashi.


A bangaren lovebirds din kuwa, tana kitchen tana aikace aikacen ta, jollof rice ta ke hadawa da soyayyen plantain, Tana aiki tana humming wata wakar India mai taken Shehzada.


Tun bayan da Adam ya siyar da mashin din sa abubuwa suka soma yi musu sauki, domin tuni ya sanya hannun jari da kudin a nan wani shagon drinks na abokin sa, kuma ba laifi yana dan samu every week suke biyan shi.


Ya shigo gidan da madaukakiyar fara'ar sa ya same ta kitchen, ta baya ya rungumo ta gabakidayan ta ya cusha kan sa a wuyan ta yana sakin dariya.


Har ta so ta tsorata, sai dai ya san ba wanda ke da key din gidan da zai iya zuwa har ya bude mata gida ya kuma yi karfin halin rungumar ta face mijin ta.

Hannun ta ta sanya gana shafa kan sa ta baya da murmushi fuskarta tace "sannu da zuwa"


Juyo ta yayi suna fuskantar juna ya kama kugunta yace "kashe gas din ki, ki zo ki ji wani abu" tun kafin tace komai ya juya ya koma falo

 

     Ita kuma da yake shinkafar ta tayi sai kawai ta kashe ba tare da ta kwashe ba, man da ta ke suyar plantain din kuma ta tsantsame wanda ke ciki ta kashe.

Falon ta nufa tana fadin "Allah ya sa muji alkhairi"


"Alkhairin ne ma baby girl, zo ki zauna" ya nuna mata gefen sa, zama tayi tana shigewa jikin sa, ledar da ya shigo da ita, ya dauko ya warware yana nuna mata abinda ke ciki 


Ido ta fitar waje tace "zawj ina ka samo kudi da yawa haka"


"Maida yan idanun kar su fado, 200k ne kike budewa ido haka" ya fada yana dariyar ta

"Still wannan kudin yayi yawa, i can't wrap my head around inda ka samo"


Murmushi yayi yace "wato last month ganin yanayin da nake ciki sai Alh balarabe ya dan dora ni kan wasu harkokin sa, Toh sai na ce duk abinda ake samu ya rikemin chan hannun sa da nufin idan sun taru na biya rent, Toh kinga fa shine har kudin sun wuce na biyan rent din mu"


Kwalla suka tarar mata "Allah ba ka da dole, Allah ka biya bawan nan na ka da alheran sa a gare mu"


Adam ya ce "Ameen Ameen Ai Alh balarabe is a Gem, samun irin su masu taimako don Allah sai an tona"

"Gobe gobe zan biya rent dinnan Ai Alh sambo ma yayi muna kokari, kinga abinda suka rage take it kije ki chanzawa kan ki wardrobe" ya fada cikin tsarguwa yana kallon ta kasa kasa


Hararen wasa tayi masa ta daga hannu kamar zata dake sa tace "ana zancen ciki wa ya ke ta wardrobe yanzu, kawai ka kara kudin a kasuwancin ka Allah yayi musu albarka"


Ya amsa ta da "Ameen Ameen my love shi yasa nake da da son ki akwai number 6"


Murmushi Kawai tayi tana kallon sa, kai talauci bala'i ne a en kwanakin nan da abubuwa sukayi sauki wannnan ramar fa da rashin nutsuwa da kake ganin u tattare da su tuni sun kama hanyar su. 


"Alhamdulillah Allah ka kara buda muna, ka kuma tsare duk wasu iyali da shiga kwatankwacin yanayin da suka shiga a kwanakin baya" ta raya a ranta tana kallon fara'a da nutsuwar da ke kwance kan fuskar mijin ta sai ta ga bai taba yi mata kyau irin na yau ba.


Hannu ta ta kai fuskar sa tana shafar sajen sa, zuwa gefen fuskar sa to wuyan sa, cikin sabon yanayin da ya ziyarce shi nan take, ya wani irin lumshe ido yana narke mata kamar yaron goye


"What are you doing" ya fada muryar sa na narkewa, murmushi tayi tana kasa da kanta, ya ware idanun shi kan ta, yana son wannan kunyar ta fahima


"Naughty girl" ya furta yana mikewa ina zuwa, kofar falon ya rufo ya dawo, ya sunkuci kayan sa gabakidaya sai bedroom din sa ya sauke ta.


After what felt like the most exciting intercourse they ever had, bayan lafawar komai, yana tsaye gaban madubi yana goge kan sa fitowar sa daga wanka kenan yayin da ita kuma ta ke dunkule cikin bargo har lokacin tana yi masa wani irin kallon sha'awa 


Wato Adam dirarren namiji ne mai duhun fata, dogo ne shi sosai mai faffadan kirji yana dan da kaurin sa ba can ba, sai dai ba za a sanya sa cikin jerin mazajen nan masu tsananin kyawon fuska ba, sai dai duk inda ake neman namiji ya kai, not only the structure, the charisma is there has always been there, and will always be there.


A wannan lokacin a wannan yanayin sai fahima ta ke ganin duk mazan duniyar nan a bayan sa suke, ba wanda ya kai gare shi ba wanda yafi Adam din ta haduwa.


A daidai lokacin wayar ta da ke bedside ta dauki ruri, Aunty ce ke kiran ta, ta raya a ranta Toh ko lafiya duba da basu jima da gama wayar ba.


Sai da suka gaisa, aunty ta isar mata da sakon baba ga mijin na ta, ta mirror ya ke kallon ta ganin shi ta zubawa ido, sai tace "toh shikenan Aunty zan gaya masa"


Gira ya daga mata ta madubi "how far"

"Baba ne yake neman ka" ta fada tana jujjuya wayar da ke hannun ta, agogon bango da ke makale dakin ya kalla, karfe biyar na yammaci, sai ya taba baki ba tare da damuwa ba yace

     "okay Toh ki shirya mu je tare kema sai ki gaida su Aunty"


  Tare suka shirya tab shi yana cikin kaftanin bula har da hula yayin da ita kuma take sanye da doguwar Abaya baka, sai da suka ci abinci kana suka rufo gidan su, maiadaidaita ya sauke su har gate din gidan baba.

     Falon baba ya wuce kai tsaye yayin da ita kuma ta nufi na su sashen


    *********

"Kaje ka gwada aikin ka ji Adam, idan har aikin bai yi maka ba ni ba zan tursasa ka ba"


     Shiru yayi bayan ya gama jin dukkanin bayanan baba, me yasa baba zai nemar masa aiki a gurin mijin najma ba tare da ya gayamasa ba, shi fa he is contended with what he has yanzu, he rather keep hustling than ya je aiki a karkashin mijin najma

wannan zai janyo masa raini not only him but to his wife also, ita da take tare da su cikin gida, domin shi zantuttukan su ko a kwalar rigar sa.


     Shiru yayi ya kasa cewa komai, ba zai iya cewa baba aa ba, musamman yanda ya ga yana ta yaba wannan mijin najmar, at the same time kuma ba zai iya cutar kan sa ba.


      Baba ya kalle sa da kyau, ya san ba komai yake tunani ba fa ce abinda shima din yayi tunani a lokacin da najma ta zo masa da zancen


ta ya Adam zai koma aiki karkashin mijin wacce ya nemi auren ta ta ki saboda tana ganin ba shi da wani abu, yanzu kuma ya koma karkashin mijin ta yana mishi aikin masinja ko direba.


     Sai dai we're not talking about pride a nan, future sa da ta iyalin sa ya ke duba masa, a yanzu haka ma ya abubuwan suka kare bare in sun soma tara zuri'a.


     Zuciyar Adam ta soma yi masa tururi hakanan ransa ya baci sosai, dama shi mutum ne mai saurin daukar zafi amma kuma yana da saurin hucewa

     "Kaje kaji Adamu Allah ya sa a dace"

Da kyar ya iya furta "nagode baba Allah ya kara girma"