9
by @mahmazee1
A cikin gida kuma Aunty ta sanya fahima daki tayi mata bayanin duk abinda ake ciki, tare da tabbatar mata alheri da ita ta ke hangowa a cikin lamarin.
A ran Fahima itama bata so wannan aikin ba, ba don komai ba sai don Adam din da ta San ba zai ji dadin aikin ba.
Sai dai daga ita har Adam idan suka cewa baba aa lallai sun tabbata butulu ko ba komai Najmar nan fa yar cikin sa ce, wannan Farouk din kuma mijin ta ne.
Da zasu wuce Aunty ta da da jaddadamata "lallabasa zakiyi Fahima, Raina yana bani akwai alkhairi a cikin wannan abun"
A Napep ba wanda ya furta wa dan uwan sa a, kowanne da bukin zuciyar sa, sai hannun ta kawai da ta dora kan nasa domin support, kadan ya dago kai ya kalle ta kana ya cigaba da kallon titi.
Har weekend ya zo sati ya zagayo, bakin su bai hadu ba a kan zancen, ranar Monday karfe 8am na safe ya shirya tsab cikin corporate wears dogon Wando da shirt, sai covers da ya sanya, tana bacci ya tayar da ita, ita bata ko san tashin sa ba.
Zaunawa tayi kan gadon sosai ta na kallon sa da mamaki "ina zaka je da sassafe haka"
Murmushi yayi yana kawar da damuwar da ke ran sa yace "baba yace inje FW holdings yau Monday so am going there"
Ciki tayi da en idanun ta tana mikar bacci tace "ina ne FW holdings kuma"
"Kamfanin FAROUK WAZIRI mijin najma, kinsan baba ya nema min aiki a can"
Jinjina kai tayi tace "Allah ya bada sa'a, yayi muna zabi na alkhairi Zawj"
Ruwan tea kawai ya sha, ba yanda ba ta yi ba ko indomie ce ta hada masa yace kar ta damu he will get something on his way ta koma baccin ta kawai.
Har waje ta rako sa, side kiss ya bata kana yace "go back to sleep wifey kar ki sa damuwa a ranki kinji"
Gyada masa kai kawai tayi tana tsaye har ya bude kofar gidan ya fita ta rufe kana ta koma ciki, baccin da yace tayi ta ke kokarin komawa sai dai har tara ta wuce sai juyi kawai ta ke kan gado ta kasa komawa baccin.
Ganin haka sai ta mike kawai ta shiga gyaran gidan, sunyi waya da Aunty ta sa ke nuna mata ta karfafa masa guiwa, tana mmakin wannan nacin na aunty a kan aikin nan, which is so unlike her.
Around 12pm sai ga Salma da Furera sun zo mata har da auta sadik, a nan suka yini har suka Taya ta shirya abinci, tuwon semo suka yi miyar egusi da ganda zaqo zaqo, suka hada zobo aka jejjera tsakiyar falo.
Har suka yini suka ci abinci suka wuce bai dawo gidan ba tun bata damu ba har ta soma damuwa ta kira ba'a daga ba, hakanan ta tura masa message shiru.
Kai sai ana kiraye kirayen magrib ya shigo gidan, zuwa lokacin kam duk ta damu tana zaune falo shiru ya shigo da sallamar sa.
"Where did you kept your phone, ina kiran ka baka daga ba, na tura message no response, you got me worried" tayi demanding kai tsaye hawaye na cika idon ta.
Shishhhhhh baby girl ya fada yana takowa falon, rungume sa tayi hawayen na saukowa
"Haba Fahima wai abin kuka baya miki wuya" ya fada yana shafa bayan ta cikin sigar lallashi
sai da suka nutsu yace "a gajiye na ke fa, yanzu haka daga zaria na ke"
Zaria kuma ta fada da mamaki
"Yeah zariya, I've been driving all day, that guy is one hell of a busy man whatttt" ya fada in exaggeration
Kallon sa tayi tace "wai wa kenan"
Nonchalantly ya amsa ta da "My boss"
Toh tayi kasake tana kallon sa
Yace "ina zuwa bari nayi alwala na je masallaci za a tayar da sallah, i will gist you"
Ciki ya shiga yayi alwala ya fito ya yi masallaci, ita dai tana ta mamaki, ya fita da bacin rai ya dawo da murna haka kamar ya taka dan mutum toh fah
Suna zaune kan center carpet tana serving din shi abinci yace "i got the job" cikin fara'a, ganin fara'ar fuskar sa itama sai ta saki ranta
"Ina zuwa building din naje HR, ba wani formalities dai da aka bi cause it was like i already got the job, na jira for a while gaskiya sai ga shi an zo nema na muka je suka yi min tambayoyi, they asked for my records, wani health record ko criminal record, i assure them ni ina ga ko police station ban taba ziyarta ba bare ma har wani ya kai ni.
Bayan nan fahima i met FAROUK WAZIRI, FAROUK WAZIRI da kan sa, the first thing he asked me was "ka iya driving" ya fada yana koikoyon bossiness din ogan na shi
"Gabakidaya kamar cat got my tongue, sai na ji ni kamar wani yaro karami a gaban shi, kwarjinin shi Fahima is top notch.
Nace eh na iya, shikenan fa i drove him myself, securities din shi suna bayan mu in the other car, muka je yayi wasu en ayyuka kana yace mu wuce Zaria kawai
A zaria ma fa he was having meeting upon meetings ba mu nan ba mu can kinsan na iya zaria sosai (da yake a can ya hada degree din sa a jamiar ABU), so aikin bai yi min wahala ba, daga karshe dai muka kai wa sarkin zazzau ziyara Ashe uncle din shi ne, and finally muka dawo kaduna.
Daganan kawai P.A din sa ya kira ni daban, ya gayamin sun bani aikin driver, office driver kawai, idan ya zo office duk in da zaije i will be the one taking him"
"Fahima kinga yanda ake ba ni amana, ana jaddadamin in rike Amana"
Lallai, ita kam sai jinjina kai ta ke tace "Masha Allah he sounds like a great guy"
"Not only great Fahima, idan kika ganshi ba zaki ce shi ne behind FW holdings ba, a very simple and outgoing person, ba ya da girman kai, tarin dukiyar sa bai sa shi wulakanta na kasa da shi ba, yana da kirki beyond what words can say"
Fahima ta murmusa tace "duk a haduwan farko har ka gane kirkin sa haka"
Ya gyara zama yana kai kofin zobo bakin sa "shiyasa nace miki yana da kirki domin tun a haduwar farko zaki gane FAROUK WAZIRI is a great person, babban abinda ya burge ni da shi shine saukin kan sa, kai ba zaka ce shine mijin najma ba"
Hada ido suka yi suka kyalkyale da dariya a tare, domin ko yau ka soma haduwa da najma toh tabbas ba zaku rabu ba face kasan arzikin mijin ta, ga girman kai da daukar kai, a ganin ta kowa ba sa'an ta ba ne.
Fahima tace "Ai ya huta"
"Kuma kin san wani abu, salary na 100k, that's not bad considering abinda na ke karba gurin tsohon aiki na, from the looks of it dai ta mu zata zo daya"
Fahima tace "congratulations, am so so happy for us"
Daga haka Adam ya soma aiki a karkashin mijin najma, a FW holdings, tun fahima tana jin dadin labarukan Faruk WAZIRI da ta ke ji a gurin mijin ta har ta soma kosawa, domin Safiya duk farouk din ba zai rasa yin abinda zai burge Adam ba, haka shi kuma ba zai fasa fada ba, ko da yaushe my boss this my boss that, boss yace kaza boss yayi kaza, ta fahimci yana ganin Farouk din like he is surreal, yana ganin shi with such high standards, hakanan yana jin dadin aiki da shi and from all indications shi ma Farouk din yana jin dadin aiki da Adam din.
A bangaren samun sa kuwa zai ce haduwar sa da Farouk has been nothing but blessing upon blessings to him, fita batun albashin sa kawai, wato mai gidan na su wani irin mutum ne mai yawan kyauta, kamar wanda bai san ciwon abin hannun sa ba, ga tarin alkhairan da yake samu a gurin associates din maigidan na sa, abu ne mai wuya suje wani gurin bai samu wanda yayi masa dan alkhairi ba.
Idan yana bata labarin tarin kudin boss sai ta ga bata ga laifin najma ba idan ta ji da kan ta, mijin ta na da tarin arzikin da ko kasa idan ta ga dama ba zata sake takawa ba
Ranar dai cikin tsarguwa tace "wai wannan boss din na ka Zawj, anya ba dan yankan kai ba ne, irin wannan tarin dukiya da ake fada sun soma saba hankali"
Zancen ta ya sanya shi dariya sosai domin da ta san ko waye Farouk waziri da ko kusa bata furta haka ba.
Sosai ya dara sai da ya tsagaita yace
"he owns the largest holding company a west Africa gabakidaya, kin kuwa ga we're talking about REAL money a nan"
Jinjina kai kawai tayi kamar ta fahimci bayanin na sa
"kinsan me ye holding company" ta girgiza ma sa kai alamar aa
"Yawwa a holding company is like a parent company to many other companies, businesses, industries and organizations, holding company yana buying shares na companies da dama, zaka iya buda kamfanin ka ko business a holding company ya zo ya siya share, ko major shares ma zai iya siya, ya zama major share holder kuma yayi owning businesses din, Toh FW Holdings has major and minor shares in over 100 small and large companies a Nigeria left alone kewayen Africa, kin ga kuwa ba karamin kudi ake magana ba"
Fahima ta gyada kai tana jinjina lamarin a ran ta, tabbas biri yayi kama da mutum, Shiyasa najma ta ke kashe kudi kamar bata san ciwon su ba, bukin Karima kawai don kusan komai ita ta dauki nauyi, zata ce millions din da Najma ta kashe sun zama kazanta saboda irin kala kalan abubuwan da aka yi a bukin.
Adam ya cigaba "kinsan kuma a yanda na ji labari lokacin da ya soma wannan Harkar, he was very young cause yana university at the time, baban sa cewa yayi waste of time ne kawai mai zaiyi da wani holding company, ya zo ya kama harkokin sa yace shi yana son building wani abu na kan shi.
Baban ya bashi jari yaje ya soma and lucky enough for him sai Gashi ya zama successful, according to Forbes, yana daga cikin top 10 youngest billionaires in Africa"
**********
Fahima tana ta karatun ta cikin tarin nasarori domin a yanzu ne hankali da nutsuwar ta suka dawo kan bokon na ta, gashi har suna batun gama first semester 400level wato final level din ta kenan
Adam kuma yana cigaba da aikin sa a FW cikin tarin nasarori shima, domin a yanzu ya fi karfin abinda zai ciyar da iyalin sa sai dai ya ba wani.
Ta bashi shawarar saving domin siyen mashin din sa da ya siyar, shi kuwa kudurin sa duk bai wuce ya chanja musu haya ba, wannan gidan da suke ciki da unguwar sun ishe sa
Karfe biyu ta dawo daga school, last exams din su kenan ta wannan semester, sai kuma shiga second semester na final year, ta shigo gidan a mugun gajiye.
Yana kwance kan doguwar kujera da wani newspaper a hannunsa yana dubawa. Ita kam Tana mamakin Adam, Toh wa ke karanta newspaper a wannan digital era da ake ciki.
"Lazy youth" ta fada cikin tsokana Tana Jan sumar shi, domin kwana biyu yanzu ba abinda yake yi face hutawa, da yake maigidan na su yayi tafiya, for a week kenan yanzu yana United States
Dariya yayi yana mikewa zaune, tare da janyo hannun ta ya yi mata mazauni kan kafafun shi, ya zagayo duka hannayen shi bayan ta, yana kallon cikin idanun ta sosai
"Ya exam din, yayi dadi" ya tambaya cikin kulawa
"Alhamdulillah, na gama da wannan stress din sai maida hankali kan project kuma"
Cikin Jan fada yace "ya na gama kamar ASUU zasu saka ku strike"
"Don Allah ma kama daina, yar semester daya dinnan da tayi min saura abeg"
"Da gaske yanzu na gani a newspaper, but basu dai kai karshe ba, just pray kinsan mutanen nan sai a hankali"
Fahima ta sarke faratan ta biyu Tana fadin "fingers crossed"
Daki ta nufa, kai tsaye ta soma da wanka ta dauro alwala, ta shirya cikin wata doguwar rigar Swiss lace, flare gown, tayi sallar Zuhr kana ta dawo falon.
Indomie kawai ta dafa suka ci, suka shiga sauraren wakokin king of R&B wato Christ brown, domin dai Adam babban fan din shi ne, ita tun bata son wakokin har ya koya mata.
Haka ta shiga hutun ta cikin kwanciyar hankali, ga mijin ta a gefen ta wanda shima yanzu fine da wata daya kenan sai hutu ya ke saboda maigidan su da bai dawo ba har zuwa lokacin.
Hakan ya sanya ya dan soma fita aikin karfi, duk da hakan bai hana a bashi albashin sa na watan ba, amma dai sai baya Jin dadin zaman gida idle
Sai gashi kuwa bakin shi ya karbu, hutun su na zancen karewa ASUU suka shiga indefinite strike wanda ba a san ranar dawowa ba kuma.