10
by @mahmazee1
A filin tashi da saukar jirage da ke nan cikin jihar kaduna wato Kaduna International Airport, jirage ne ke ta tashi da sauka, wasu na ajiye passengers yayin da wasu ke daukar passengers
A bangaren FBO na airport din wato Fixed based operators na DAN wanda ke da alhakin operation na private jets da handling, a daidai lokacin executive Jet din Lesus da ya taso daga Jomi kenyatta Airport da ke Nairobi Kenya ya sauka ya kuma yi packing.
Kofar wannan chartered flight ko in ce Private jet da ke dauke da FAROUK WAZIRI da mutanen sa ta budu, wanda ya baiwa mutanen ciki damar soma fitowa.
Dan dakatawa yayi daga bakin kofar jirgin ba tare da ya sauko matattakalar ba, wanda hakan ya sanya dukkanin mutanen da ke bayan sa dakatawa suma, domin ba zai yiwu su riga shi fita ba.
A hankali ya rungume dukkanin hannayen sa biyu baya, ya lumshe idanun sa tare da shakar daddadar iskar da ke tashi da kamshin turaren Boss the Scent din Hugo boss da ke fitowa daga jikin shi.
Ya ware manyan idanun sa, masu matukar kwarjini da bayyanar da Aura din sa kai tsaye a kan mutanen da suka jeru gaban jirgin domin tarbon sa, suna jiran fitowar sa, akwai MD na sa da ke managing da handling komai a nan Nigeria, akwai CFO na FW holdings shima cikin corporate wears din black Suit, da wasu biyu daga cikin manyan ma'aikatan sa.
Sai ma'aikatan Lesus da kuma na Airport din da ke tsaye bakin jirgin, bai San sai yaushe zasu daina yi mishi irin wannan taron ba, he thought he warned Najib wato personal assistant nashi a kan haka, but no sai sun zo.
Ya zuro doguwar kafar sa ya tako almost da hanzari yana saukowa matattakalar jirgin cikin takun sa mai daukar hankali, har izuwa sa'adda ya ajiye kafar sa da ke cikin rufaffun bakaken takalman Salvatore Ferragamo a last step din sa.
Da hanzari MD da sauran wadanda suka zo tarbon sa suka karaso suna mika mishi hannun su cikin matukar girmamawa domi yin musabaha yayin da ma'aikatan da ke jere ke ta faman yi masa sannu da zuwa, the whole appearance na FAROUK WAZIRI mai cika ido ne, ba wanda ke iya tsaurin idon hada kallo da shi.
Ya gaisa da su daya bayan daya, yayin da Samuel Okeke of the Okeke Enterprise da suka sauko jirgin tare ya mika mishi hannu suka yi sallama.
Tun da Samuel din yaji labarin zuwan shi Nairobi Kenya ya yi tattaki daga United Kingdom ya same shi can, domin yayi tayi su hadu da Farouk din basu samu haduwa ba.
Ko a Nairobi din he couldn't squeeze him into his tight schedules, shiyasa kawai yace suyi having meeting din onboard, hakan ya sa Samuel din ya biyo Jirgin Farouk suka zo, yayin da suka tattauna proposal din samuel a jirgi.
Samuel yace "I'll definitely come meet you kafin in bar kaduna, think about what we discuss please Farouk" domin ya San halin Farouk din ko tun daga expressionless fuskar da ya sake masa tun da jirgin su ya ta so har suka sauka ya fahimci Farouk was not impressed or rather not interested.
Murmushi ya sakar masa wanda duk kulewar abu, murmushin nan dai shi zaka gani kan fuskar sa, wanda ya sanya annurin da ke kwance kan fuskar da da fitowa.
Da Sir ya San yanda murmushi ke yi masa kyau, da ya kasance cikin shi a ko da yaushe, Najib ya raya a ran sa a lokacin da yake kafe kallon sa kan ubangidan sa, wata halitta kwaya daya da tunda ya ke ganin dan ADAM bai taba ganin mutum mai kwarjinin FAROUK waziri ba, har yau har gobe duk tarin shekarun da suka yi yana gefen sa as his P.A baya iya hada ido da shi, baya iya zama kan shi domin girman Farouk waziri da kwarjinin sa is damn intimidating, da zai sa ka rudewa next to him.
Samuel ya nufi motar da ta zo tarbon sa yayin da Farouk ma ya nufi bakaken motocin Escalade biyu yan gidan Cadillac da suka tsufa harabar domin daukar sa, sai nishi motocin ke yi in slow.
Mutanen sa na ta ke masa baya, Samson his most trusted security ya bude masa kofar baya, kafin ya shiga ya waiwayo kadan yana kallon su MD wanda ke son briefing din sa a kan wasu abubuwa, sai dai baya Jin yana da wannan time din. Rest shine abinda ya fi bukata a daidai wannan lokacin.
Ya soke dayan hannun sa aljihun Grey suit din brook brothers da ke jikin shi, yayin da ya mikawa MD dayan hannun sa suka da da yin musabaha.
"Thank you" shi ne kawai abinda ya fada, ya fada bayan motar, Najib ya fada gidan gaba, securities din shi na dayar motar, suka ja motocin suka fice daga Airport din, duk inda suka gifta suna daukar hankalin mutane domin motoci ne da kafin ka ga irin su suna yawo on a regular haka da wuya.
Kai tsaye Najib yace su nufi Malali domin amsa kiran da surukin sa Alh Sanusi Ciroma yayi mishi tun yana Nairobi.
Tun da motocin suka nufato kofar gidan, Salis ya fito daga masallaci da hanzari ya wangale gates din domin sanin ko motocin waye.
Motocin suka paka harabar gidan Alh Sanusi Ciroma, securities din shi suka soma fitowa su uku har Samson da ke tsaye bakin kofar sa yana jiran umarnin budewa.
Tsayin wani dan lokaci kafin Samson ya bude masa kofa da hanzari, ya zuro kafar sa ya fito, Samson ya bashi hanya yana rufe kofar.
Da sauri securities biyun da ke nan suka tare Salis da ya zo gaida Farouk, hannu Farouk ya daga musu alamar su bar shi ya karaso, shi da kan shi ya mikawa Salis hannun shi suka gaisa wanda har jikin shi ke bari.
Girgiza kan shi kawai Farouk yayi ya saki dan siririn murmushi ganin yanda jikin Salis ke rawa gaban shi, kafin ya taka cikin zafin nama, Samson na bayan shi suka nufi falon Baba domin gidan ba bakon shi ba ne.
Daga bakin kofa Samson ya dakata yayin shi kuma ya fada falon
"Aahhh Farouk" baba ya fada a lokacin da Farouk yayi gracing falon domin bai San da zuwan sa ba, ya dai San sunyi waya ya kuma tabbatar masa yana Nairobi amma idan ya dawo zai shigo.
Ya Lawal ma da ke tare da Baba shima ya mike yana kallon cousin din na shi kuma mijin kanwar sa.
Farouk ya tako a hankali ya mika musu hannu suka gaisa daya bayan daya.
Lawal ya dan zauna suka gaisa sosai ya tambaye shi mutanen gida ya fice ya bar musu falon ganin da magana bakin baba.