RAYUWAR DAN ADAM

11

by @mahmazee1

Baba yace "Faruku ya aiki ya kuma dawainiya da mutane" 

     Ya sanya murmushin nan na sa yace "Alhamdulillah Baba mun same ku lafiya"


   "Duka muna lafiya ya Nairobi din" 

   "Good, am just coming back" ya amsa

"A'a shi ne baka tsaya ka huta ba, ai ba wani uzuri ba ne, gaskiya ban ji dadin haka ba" Baba ya fada da yar damuwa kan fuskar shi.


   Yayin da Farouk waziri bai ce komai ba, domin shi a rayuwa irin ta shi ba abinda ya ke girmamawa irin time, to him time is money, time is of the essence, shiyasa ya ke mamaki sosai idan ya ga mutane suna wasting na shi.


   Komai na shi a tsare ya ke, idan bai zo ya ga Baba yanzu ba, baya tunanin zai iya managing ya dawo a yan kwanakin da zai yi a nan kaduna.


   Baba yana jin Nauyin kiran da yayi wa Farouk, sai dai kuma ya ga gwara kawai yayi magana da shi da kan shi, domin bai ji komai daga gare su ba, ya gani a news har anyi launching sabon kamfanin da najma ke magana a kai tuni a Abuja, wata daya kenan har da dori.


    "Dama Faruku kan zancen mijin yar uwar matar ka ne nayi kiran ka" cewar Baba

     Farouk waziri ya dan gyara zaman sa kan kujerar yana baiwa baba dukkanin nutsuwar shi.


     "mijin FAHIMA" Baba ya sake fada


     Dan dago da fararen idanun sa yayi ya sauke su kan Baba, cikin daurewa kai sunan yayi escaping bakin shi 


"FAHIMA" ya rada more in a question tone, cikin wata irin tsadaddiyar muryar da a gurin FAROUK WAZIRI kawai zaka ji ta, expression din da ke fuskar sa kawai na nuni da ko fahimar bai gane ba bare mijin ta.


   Baba ya gyada kai yace "Adam nake nufi, yaron guri na da mukayi maganar sa da maidakin ka kwanaki, Toh kasan yanda yanayin kasar ta mu yake he lost his job with the ministry of education saboda chanjen gwamnati da akayi""

 

     Dan shiru yayi cikin tunani, kafin sunan sabon direban sa Adam ya fado masa saboda connection din shi da matar shi Najma, da ta kawo proposal din Adam din, da kuma yanda nutsuwar yaron ya kwanta masa kai tsaye, domin shi mutum ne mai matukar son nutsuwa abinda duk ba nutsuwa a cikin shi ba zaka gan shi ba.


    Ya shafa lallausar sidebox din shi baka sidik da ta kwanta kan farar fatar sa yace 

    "ohh yes Adam, yana aiki da mu for a while yanzu, kuma muna jin dadin aikin shi"


     Baba yace "Alhamdulillah, ai Adam yaro ne mai hankali, Toh kan aikin shi ne, na san dai abubuwa sun yi yawa, probably ka sha'afa" nan dai Baba yayi masa dan bayani kan yanda suka yi da Najma.



     Kan FAROUK WAZIRI ya daure hakanan ya rasa in da zantuttukan Baba suka nufa, baya da mantuwa, bai yiwa Najma wani alkawarin sabon aiki ba, all he knows is she insisted tana so a baiwa Adam wani yaron gidan su da ta yadda da hankalin shi aikin Driver.


    Sosai ya ji ran shi ya baci, me yasa bata gaya masa Baba ne ke nemawa Adam aiki ba, why didn't she tell him Adam mijin yar uwar ta ne, the biggest question here is me yasa tayi insisting a baiwa Adam aikin direba bayan da qualifications din sa mai kyau, hakan ya sanya shi yin shiru kawai ba tare da yace komai ba.

   

    Baba ya danyi nazarin sa kadan ganin kamar Farouk din bai fahimci inda ya dosa ba, ran baba ya soma baci, shi dama tunda najma ta do ta gaya masa wai Farouk yace ba za a samu aiki yanzu ba ya san akwai wata a kasa, Farouk din da ya sani ba zai mishi haka ba, ko da ba kamfanin sa ba ya Sani Farouk yana da ikon Samar wa Adam aiki a gurare da dama a fadin Nigeria nan.


   

      Ya dan jima a wannan yanayin kamar mai wani tunani, Baba sai karantar sa ya ke yi

   "it skipped my mind, amma dai Insha Allah za a samu position din da za a bashi"


   Baba yace "Yawwa Farouk Allah yayi maka albarka na gode sosai"


    Da haka sukayi sallama da baba ya mike domin barin falon, wanda hakan ya bayyanar da tsayin sa mai ban mamaki, domin ya tafi sambal har dorewa yayi.  


   Yana kokarin barin falon Mami ta da taji zuwan sa ta fado falon, bata ko jira ya je gaishe ta ba shi, hankalin ta ya gaza kwanciya, Tana son sanin me ke faruwa falon.


     Ya dakata suka gaisa da Mami tana tambayar shi yar uwar ta, kafin ya fice.

    Baba ya kalle ta bayan fitar Farouk cikin tuhuma, sai kawai ta dauke kan ta, ta juya ta bar falon itama.

********

   Tun last week Najib yayi mishi message kan dawowar Boss this week, hakan ya sanya yau Friday yayi shirin fita gurin aiki, sai after 11am ma ya bar gidan, sanin Boss baya shiga office da wuri on fridays sai bayan sallar juma'a zai shiga ya ga ayyuka ya fice.


    FW holdings wani irin katon kamfani ne mai girman ban mamaki da ke dauke da bangarora da dama da departments daban daban.

   Wani irin gini aka yiwa gurin mai tafe da modern architecting na glass da concrete.

  Kai tsaye office din su ya nufa ya karbi key din motar da yake kyautata zaton Boss zai shiga.

   

    Wacce ke pake Packing space din Farouk, musamman aka tanadar da gurin domin motocin shi kawai, cikin jerin motocin da ke nan, ya tayar da Farar Mercedes Maybach S680, yayi warming din ta, ya kashe ya fito ya nufi masallacin da ke nan cikin kamfani, domin samun jam'in sallar juma'a, wanda kusan dukkanin ma'aikatan gurin ke halarta.


     Bayan huduba Imam ya ja sallah suka bi, har zuwa lokacin da aka sallame sallar wanda nan take masallacin ya dauki yar hayaniya na isowar Farouk Waziri, wanda yayi wa masallacin dirar mikiya bayan har an tayar da sallah.


     Fitowa ake tayi daga masallacin yayin da hanya ta tunkushe kokarin kowa ya samu damar fitowa tare da ubangayyar.


     Sai da guguwar Farouk waziri ta fice daga masallacin kafin Adam ya samu sararin fitowa, shi bai ma yi attempting isa gurin ba, domin bai zama dole ayi noticing din sa ba, duk da kuwa dakatawa da Ogan yayi yana amsa gaisuwar da mutane ke ta kawo masa.



   Shi kam da sauri ya nufi packing space, ya tayar da motar ya janyo ya zo daidai in da su Samuel suka yi packing nasu motocin kusa da masallaci.


    Yayi shiru jingine da kofar direba yana kallon maigidan sa da ke taku kamar baya son taka kasa, doguwar kafar sa da ke rufe cikin bakaken covers din Berluti na bayyanar da sautin takun sa a kan interlocks din da ke lailaye da kamfanin.


    Securities din shi na biye da shi da wasu daga cikin manyan ma'aikatan kamfanin, inda kowanne ke kokarin ya ga ya fi wani a gurin maigidan.


    Cikin sauri Adam yayi unlocking motar da yake jingine da ita ganin tawagar ta nufo nan da alama mai dai fita zasu yi.

    

    Najib ya bude masa bayan motar, ya rufe ya fada gaba yana baiwa Adam umarnin gidan iyayen boss zasu je.


    Tunda ya shigo fitinannen kamshin shi ya karade motar gabakidaya, wani tsadadden kamshin da ya cakude da Ac motar yana bayar da iska mai dadin Shaka.


    Sai lokacin Adam ya samu damar gaishe shi "welcome back Sir, sannu da zuwa" ya fada, baya ji Farouk ya amsa gaisuwar shi, hakanan bai damu da sai an amsa din ba domin tuni ya fahimci ba dabi'ar sa ba ce.  


    A hankali ya dago daga jinginar da yayi da seat din motar, Babbar rigar da ke jikin sa na wani Cream Voyel lace din da ya saka mai taushi kalar Beige ya zare yana ajiye ta gefe domin tuni ta dame shi.


    Ya cira kanshi kadan ya kalli bangaren Najib  wanda ya waiwayo da hanzari yana jiran umarni.


   "My pad" ya bukata kai tsaye 

Najib ya dauko iPad din ya miko mishi, yayin da shi kuma yayi unlocking wayar ya kira video call a FaceTime. 


     Kyakkyawar fuskar yar sa Aneesa ne ya cike screen din shi, wacce mahaifiyar ta bata yi kasa a guiwa ba gurin kara masa ita Kai tsaye a lokacin da ta ga kiran sa, zuwa yanzu ba abinda Aneesar bata iya fada hakanan tana takawa ko ina.


    "Aneesa" muryar sa ta Kira sunan ta a tausashe, cikin wata irin muryar da shi bai taba Sanin yana da ita ba sai a kan Aneesa, bai taba sanin yana da ita ba sai ranar da Dr James ya dora mishi ita a asibitin John's Hopkins Baltimore da ke United States, bayan cesarean section wato CS da aka yiwa mahaifiyar ta.


    A ranar ya San babu soyayyar da ta kai ko ta fi wannan dadi a kab fadin duniyar nan.


   Jinginawa yayi da seat tare da langwabar da kai yana kallon kyakkyawar fuskar Aneesa wacce yake jin soyayyar ta kamar ya huda zuciyar sa ya fito da ita kowa ma ya gani.


   Wadanda suke tunanin baya da son 'ya'ya saboda kawaicin sa a kan lamarin Aneesa su karyata kan su da kan su, su sani ba halittar da ta kai ko ta fi Aneesa muhimmannci a rayuwar sa.


     A America ya rabu da su ita da mahaifiyar ta shi ya wuce Kenya yayin da su kuma suka wuce Paris din France, a cewar Najmar zata chanja wardrobe din Aneesa saboda duk tayi outgrowing kayan ta.


    Bai san me yasa Najmar ta ke haka ba, bai sani ba ko akwai wani abu da shi yake yi da ke nuna mata tayi hakan, bai san me yasa a duk ire iren wadannan lokutan idan ya kira ta ke hada shi da yar shi direct ba tare da damuwa da ita din ta tsaya su gaisa ba.


     Aneesa ta soma zuba zance cikin muryar ta ta yara wacce bata jima da budewa ba, da ido kawai ya ke bin kyakkyawar babyn ta sa har ya kashe wayar bayan Najmar ta karba sun gaisa briefly ta ke gaya masa suna sauri zasu fita Golden triangle.


    Wayar ya ajiye gefen sa tare da gyaran murya ya kalli Adam ta rear mirror din motar, fuskar sa a hade yace 


      "me yasa baka gayamin you have a degree ba" yayi demanding kai tsaye, rashin jin dadi na bayyana a muryar sa, domin a ganin sa akwai cutassuwa, ta ya Adam din da karatun sa mai kyau amma ya ajiye sa a karkashin sa yana yi masa aikin direba


    Shima Adam din da mamaki ya yi shiru, ya kasa hada ido da maigidan shi da ya kakkafe sa da idanun tuhuma ta madubin motar.


   A iya tunanin sa boss na da resume din sa, yayi choosing ba shi aikin driver ne kawai, amma tambayar Farouk din na nuni da bai san qualifications din sa ba ma gabakidaya ba, shi kam ya jima yana mamakin yanda basu karbi CV din shi ba, basu bukaci komai ba, kai tsaye suka bashi aikin direba, kamar dama rubuce take a goshin sa, direba ya zo nema.


    "Anyways ka zo da Resume din ka and meet Mamuda" Farouk din ya fada kai tsaye, ya cigaba da duba wayar hannun shi, kamar bai fahimci bombshell din da yayiwa Adam dropping ba.


    Wanda tsabar murna kamar kan steering wheel din hannun sa zai kwace masa, bai san sa'adda ya soma zuba godiya ba Najib na taya sa wanda ke murmushi cikin alfahari da ubangidan sa wanda alkhairan sa ba sa karewa.


    A kan Farouk waziri ya gasgata zancen nan na malam bature da ke cewa "Money, the more you give the more they come"  Farouk waziri kuwa kyauta yake kamar bai san ciwon abin hannun sa ba.

    Basu kyale shi da godiya ba har sai da yayi gyaran murya tare da daga musu hannu, alamar ya isa, ta ke motar tayi tsit.


    Adam driving ya ke amma ji ya ke kamar ya paka ya rungume Farouk waziri har suka iso gidan iyayen sa da ke unguwar Sarki.

***********


     Da murna ya isa gidan sa, ya dauki matar sa ya shiga juyi da ita tsakiyar bedroom, dariya ta ke ta kyalkyatawa ba tare da ta san ainahin murnar me yake ba.


     "Fahima Allah yayi wa Farouk Waziri albarka" sauke ta yayi a ranta tana raya Farouk waziri again.


    Amma zancen da mijin ta ya zo mata da shi ita kan ta bata san sa'adda ta kai goshin ta kasa ta yiwa Allah godiya tare da bin Farouk waziri da addu'ar gamawa da duniya lafiya ba.

  

   "Wifey me zance da Boss, ya gama min komai, ban ma San ya zan kwatanta miki farin ciki na ba"


"He's a rare Gem" fahima ta fada idanun ta na glittering with respect to maigidan mijin ta, wani mutumi da bata taba gani ba, amma labaran sa babu wanda bata sani ba a gurin maigidan ta, Kama daga Nursery school din da yayi, har izuwa journey din sa to success, wani mutumin da babu komai tsakanin su da shi face addu'a.


  

     Ko da weekend ya kare Monday ta zo, daga Adam har matar sa a kagauce su ke.

   Ranar Monday kamar yanda Farouk ya umurce shi kai tsaye office din Mr Mamuda ya nufa kafin ma ya isa office din su, Cv din shi ya bukata, ya duba ya ga aikin da zai kama ce shi yace mishi ya dawo gobe.


    Goben ya koma, ba tare da wani dogon zance ba, HR suka sada shi da sabon office din sa as daya daga cikin Administrative Assistants na FW.


     Bai san sa'adda idanun sa suka cika da kwalla ba, a duniyar nan bai taba tunanin wai shi ne zai yi office irin wannan ba.


    Shi kuwa me zai yiwa Farouk waziri ya saka masa da alheran sa a gare sa, saboda haka ya kudiri aniyar yi masa aiki tsakani da Allah babu gajiyawa ko kyeta.


    Kai tsaye Office din President/COE na FW holdings ya nufa wanda ya ke a last building na kamfanin, domin yi masa godiya

    Sai dai a nan Secretary ke gaya masa FAROUK din is out of the country, tafiyar gaggawa ta kama shi to Cairo da mahaifin sa, sai addu'ar Allah ya tsare hanya kawai yayi masa ya juyo.


   Ko da ya tashi aiki gidan baba ya nufa, ya samu Baba a harabar gidan kan kujerar rubber yana Shan iska.


    Godiya sosai yayi wa Baba, bai san me zaice da baba ba a duniyar nan, sai Allah ya kara girma, ya bashi ikon gamawa da duniya lafiya. 

     Da ana gane mutanen aljanna tun a nan duniya da ya ce baba kam dan aljannah ne.

*********


   Kudin wardrobe kawai da FW ta bashi as allowances da suke baiwa manyan ma'aikata sun bashi mamaki, domin bai taba rika kudi masu nauyin su ba lokaci daya.

  

      Ba tare da sanin Fahima ba ya soma nema musu chanjin haya, domin baya son wannan unguwar da su ke zaune, saboda yanayin ta.

   Dama yana da dan savings din da yake yi a asusun bankin shi, sai ya fitar duka ya hada da allowance din da aka ba shi ya kama sabon Rent