12
by @mahmazee1
Duk wata marasa abin yi ta ke Jin kan ta, saboda zaman gidan da ta ke yi yanzu, ta Saba da fita school atleast yana cire mata kewa, amma yanzu da Adam yake 9-6, ko yaushe ita kadai a gida ba dadi.
Sai dai tayi girki da aikace aikacen gida, sai dai aikin gidan ba mai yawa ba ne, tunda ba girma ne da shi ba, kuma su biyu kawai ba yara da ke batawa.
Gashi yanzu wata biyu suna cikin strike, babu wani labari daga Asuu.
A wannan tsakanin ne tunanin su fadada family su ke ta zuwa mata, tun auren su har kawo yanzu ko batan wata bata taba yi ba, tun Aunty na takura mata da zancen zuwa asibiti har ta bar zancen ganin kamar Fahimar bata damu ba.
Sai dai a kwanakin nan damuwar da ke damun ta kenan, da tana da yaro a cikin gidan, ai da ba zata yi wannan zaman kadaicin ba, ta ji Tana son haihuwa, Tana son ganin na ta itama.
Yau ma kamar sauran kwanakin Tana kammala ayyukan ta ta fada bayi, wanka ta yo ta fito ta shirya cikin wata kyakkayawar English dress da ke matukar yi mata kyau kalar burgundy.
Gashin ta da ta wanke yau da safe ta warware, ta shafe shi da mayukan ta na gashi, kana tayi drying din shi, ta pake in low bun, tayi twist daya a gaba wanda ya sauko sosai kan fuskar ta.
Ta feshe jikin ta da turare da body oil, kana ta kunna charcoal Tana turare gidan ta.
Tana cikin aikin ya shigo gidan cikin gajiyar aiki da ya kwaso
"I have a surprise" ya rada mata a kunne yana raba rungumar da tayi mishi.
"Tohhhh" Fahima ta fada Tana rolling (juya) fararen idanun ta da suka ja hankalin shi sosai, ya kafe su da kallo yana sake janyo ta jikin shi sosai, yayi kissing idanun a tausashe kana yace
"Kinsan you're seductive ko, wannan abin da gangan kike yin shi" ya fada cikin narkewar murya yana kallon idanun na ta.
Yan idanun ta fitar waje da wani murmushi kan fuskar ta na musamman, wanda idan suna tare kawai ka ke ganin ta da shi.
"Hmmmm" ta fada tana kokarin mayar da dariyar da ke zuwa mata
"Ni kuma me nayi, me na iya ma na seduction" ta karashe Tana yawo da farcen ta kan kirjin shi, hannun da ke kan kirjin shi ya bi da ido, kafin ya daga ta sama gabadaya yana nufar bedroom din shi da ita
"Yarinya ta girma, tell me wa ya koya miki wadannan abubuwan, hmmmm, ni ne ko" ya fada teasingly, yana tuna sanda aka kawo mishi Fahimar, sai kauyanci sai kunya, komai yayi mata sai kuka.
Dariya ta ke tayi a lokacin da ya sauke ta kan gadon yana bin bayan ta, tare da sakar mata nauyin shi
"Je kayi wanka you stink"
Wani kallo yayi mata "ni ko, ni, zaki ga stink kuwa" ya karashe yana zare rigar jikin shi kafin ya shiga kokawa da zip din rigar ta, daga nan labari ya chanja, tuni ya ba ta mata yar kwalliyar da tayi, dole ya sa ta sake jika gashin da ba ta jima da drying ba.
Daren ranar suna kwance kan gadon su, yayin da ta ke barin shi na dama, tana wasa da hannun ta kan kirjin shi
"Zawj ina so muyi wata magana"
Ya juyo da fuskar shi kadan bangaren ta, da idanun shi ya ke tambayar me ye
Ta nisa Tana gyara kwanciyar ta kan jikin shi "baka ganin ya kamata mu fara ganin Doctor"
Cikin daurewar kai ya kalle ta sosai "why baki da lafiya ne, me ke damun ki" ya tambaya cikin rawar murya
"Relax ba komai fa, kawai dai kan zancen haihuwa ne, ina son babies Zawj, why not mu je asibiti, may be ko akwai abinda zasu iya ba ni"
Ya dan yi shiru jim, shima din rashin haihuwar nan na damun shi, ya jima da abin a ran sa, sai dai abubuwa da suka yi mishi yawa a kai ne ya sanya bai maida hankali ba.
Plus fahimar kan ta her mind was not there, amma it's high time da ya kamata su fara Neman taimako tunda sun gwada natural shiru
"It's a good idea, amma bari weekend sai in raka ki" yace da murmushi fuskar sa
"Da gaske, thank youuu" ta nisa " I love you Zawj"
"I love you too wifey, you're the best thing that has ever happened to me, kin sani ko"
"Sosai ma na sani" ta karashe tana sanya dariyar abinda ta fada.
*********
Sun je asibiti an duba ta hakanan likitan ya bukaci ganin Adam din shima suka yi masa wasu tests.
The following day Dr ya bukaci ta dawo sanda ta fara period cause akwai abinda ya ke son tabbatarwa, jikin fahima ya soma sanyi tun a nan, ganin questions din da Dr ke yi musu wanda direct duka kan ta ne.
Shiyasa fa tuntuni ta ki zuwa asibitin nan saboda irin haka, saboda gudun zullumi.
To cheer her up washegari yace ta shirya zasu fita ganin yanda duk tayi wani suku suku, duk da ba yanzu ya so bata surprise din ba.
Sun fito tare yana cikin farar kaftani yayin da ita kuma ta ke shirye cikin Atamfa dinkin boubou da siririn mayafi suka fice.
Hanyar Hadeija Road suka dauka tana ta mamakin ina suka nufa kuma.
Gaban wani madaidaicin estate suka tsaya, compound mai dauke da flat house hudu duka ginin kala daya, dattijon tsohon da ke gadi gurin ya zo yana gaishe su.
"Maigida Adamu barka da zuwa"
"Yawwa Mal Boubakar kana lafiya" Adam ya tambaya yana mika masa hannun shi su ka gaisa.
Dan karamin dakin sa ya koma ya dauko mishi keys ya mika masa, ya ja hannun ta suka nufi ciki, har zuwa part din da yake nasu a compound din.
Madaidaicin flat house ne mai dauke da 2 bedrooms, 2 living rooms wato falo, babban falon madaidaici ne mai dauke da dinning section din shi, sai karamin mini falo wanda ya ke na matar gidan.
Gidan yayi kyau sosai domin tsarin shi ginin Zamani ne, ga wadataccen kitchen da store, ta kalle shi cikin daurewar kai ta ke fadin
"Gidan waye wannan"
Dan ja da baya yayi kadan ya ware hannuwa yana fadin "welcome to your Newhouse wifey"
Wani irin kallon tayi mishi, mai dauke da tsantsar mamaki da shock
"New house kuma" ta sake fada
"Yes yes yes"
Idanun Fahima suka ciko da kwalla nan ta ke ta kalli mijin ta "Zawj whyyyyyy"
Saurin dora farcen sa yayi kan labatan ta "no Fahima duk abinda nayi miki ban biya ki ba, just enjoy the house pls"
Hannun ta ta zagayo wuyan shi in hug, tare da saukowar siraran hawayen da suka samu damar sauko mata, shiyasa soyayyar sa a koda yaushe da da ninkuwa ta ke a zuciyar ta, ba don komai ba sai ta yanda shi ko ta kan shi baya yi, komai Adam ya samu a duniyar nan na ta ne.
"Nagode sosai Zawj, Allah ya bar mu tare" ta karashe tana sake cusa fuskar ta wuyan shi
A hankali ya raba rungumar da tayi mishi, ya kamo hannayen ta duka ya sanya cikin na shi, ya zubawa hannayen su da ke sarke ido yana murzawa a hankali.
"Idan ban yi miki ba Fahima a duniyar nan wa zanyiwa, ba ni da kowa face ke sai yar uwarta, ba ni da uwa ba ni da uba, you're all I have, idan ban faranta miki ba wa zan yiwa ehmmm"
"Oya share hawayen" ya karashe yana dauke hawayen fuskar ta, ya kama hannun ta suka shiga zagayawa cikin gidan.
Gida kam yayi kyau sosai duk da ba abinda aka saka, amma tsarin gidan kadai ya burgeta, har suka dawo tana ta yaba tsarin gidan.
Da murna ta kira Aunty ta sanar da ita, ai kuwa Aunty da yaran ta suka shiga murna.
Ba ba ta lokaci suka soma gyaran gidan su wanda mama zuhra tayi kokari sosai gurin gyara mata babban falon ta, ta yi mata new set na kujeru masu saukin kudi hade da dinning table din su.
Ta siyar da tsofaffin kujerun ta da dayan gadon ta da ya dan ji jiki, kudin aka hada aka yi mata kananan kujeru L shape na karamin falon, sai dayan gadon ta shi kam shi ta saka, dayan dakin kuma Adam ya gyara.
Gida kam yayi kyau gaskiya sai zuwa ake gani, mutanen gidan su sun zazzo sun ga gida, yan uwanta na gefen mahaifin ta ma sun zo da yake Tana da siblings da suke uba daya da su, Mummy ma ta zo amma Mami kam har yanzu da suka ci ke sati daya a cikin gidan ba su ga kafar ta ba.
A karo na biyu ya sa ke nufar office din President/CEO na su yinin yau, domin samun ganawa da FAROUK WAZIRI, tun bayan da ya samu chanjin aikin nan bai iya haduwa da boss yayi masa godiya ba.
Dama bai jima da dawowa kasar ba, hakanan schedules din sa a kaduna yawa ne da su sabo da rashin zaman sa, shiyasa duk kwanakin da ya ke zuwa bai samu ganin shi ba.
Tun da ya tunkaro counter din ta, Rashida secretary Farouk ke jifan shi da murmushi, sanin yau dai zai samu damar ganin Sir.
Tace "you can go in Adam" ta karashe tana gyada masa kan ta.
Ajiyar zuciya ya sauke na samun relief kafin ya nufi Giant Wooden door din da zata sada shi da office din, wani irin office da bai ta ba shigar shi ba, kai Floor din ma bai taba samun damar zuwa ba, sai yanzu da ya samu wannan chanjin aiki.
A hankali ya turo kofar cikin wani irin tarin nutsuwar da bai san sa'adda ta saukar masa ba, shi dai ya samu kan shi a cikin ta ne tun bayan da ya bayyana office din Sir
Wani irin katon office din da bai taba ganin makamancin sa ba, sai wani irin ni'imtaccen kamshi da ke tashi da ambience din office din mai sanya nutsuwa.
Ya sauke idanun shi kan serene furnishing din da aka yiwa ofishin da ya tafi da dukkanin hankalin shi.
Office ne da ya kawatu da wasu irin setin hadaddun kujerun leather seat dark brown da aka hada kamar falo suka zagaye wani zallar glass center table, da ke dauke da flower vase daya da tulip flowers a ciki.
Daga chan karshen office din FAROUK WAZIRI ne zaune kan office chair da takardu da yawa jere kan table din da ke gaban sa, yana aikin rubutu kan su.
Akwai Desktop din Apple kan table din da ke kunne tana aiki, da alama amfani ya ke da shi.
Ya baiwa takardun dukkanin nutsuwar shi yana signing kowanne tare da duba content din da ko wace takarda ke dauke da shi.
Da sallama Adam ya shigo, sai dai tun daga bakin kofar ya dakata rungume da dukkanin hannayen sa baya, idanun sa a kan kyakkyawar halittar Farouk mai matukar kwarjini da cike ido.
Da ba don da labatan sa da ya ga sun motsa ba da ba zai ce Farouk din ya amsa sallamar sa ba, wanda shigowar sa duk bai sanya shi dagowa daga rubuce rubucen da yake yi ba.
Sun dan jima a haka yana ta aikin shi, kafin ya mike daga kan kujerar da yake kai, cikin wata fitinanniyar slim fit suit din Emporio Armani, kalar konanniyar navy blue.
Idanun shi kan Adam ya soma takowa a hankali, kakkausar muryar sa na cike ofishin a lokacin da ya ke fadin
"Adam come in"
Cikin tafiyar sa mai cike da tsantsar nutsuwa da daukar hankali har ya iso gaban kujerun leather seat da ke office din, wanda tsakanin teburin sa da kujerun yar tafiya ce.
Sai lokacin Adam ya sauke ajiyar zuciya ya karaso, cikin matukar girmamawa ya gaida ubangidan na sa, hannaye sarkafe a bayan sa.
Kallon nan na sa yayi masa, yana karantar yanayin yaron, kafin ya balla bottoms din Suit din sa biyu ya zauna kan daya daga cikin kujerun gurin tare da dora kafa daya kan daya.
"Sit" ya Umarce shi yana nuni da kujerar da ke fuskantar sa, nan ma dan jim yayi shi bai zauna ba shi bai ce komai ba