RAYUWAR DAN ADAM

13

by @mahmazee1

"Adam Sit" Farouk ya sake fada yana jinjina kan shi, a natse ya zauna kan kujerar suna fuskantar juna.


   ""I wanted to come personally and thank you Sir, Nagode sosai, Allah ya sa ka da mafificin alheri"

    Dan siririn pen din da ke hannun sa ya shiga jujjuyawa kamar bai ji godiyar da Adam ke yi masa ba, har ya karasa jero masa addu'oin.


    Ya ciro kan sa kadan ya kalle shi, ya jinjina kai yace "just do your work okay, Allah ya ba da sa'a"


Adam ya dan yi jim yana jujjuya yanda Farouk zai dauke maganganun da ke bakin shi, sai dai shi yana Jin dadin aiki next to Farouk, yana son aiki next to him.


    Farouk is a mentor, a go-getter, a motivator, abin kwaikwayo wanda matukar kana tare da shi zaka karu sosai a ilimi na rayuwa ko tun daga yanda yake gudunar da rayuwar sa.

   "Sir ina neman alfarma daya" Adam ya fada cikin karfin hali.


Ya dan dago ya kalle shi kadan, a idanun shi ya fahimci go ahead din da ya bashi, alamar ya fadi ko ma meye.


    "Sir in da hali, ina son cigaba da zama direban ka, please"

   Da mamaki sosai ya ke kallon shi wannan karon, yayi folding hannayen sa a kirji, yana kakkafe sa da kallo cikin karantar sa.

   "Why" Farouk ya bukata yana dage masa girar sa


Adam ya dan yi shiru, haka kawai ya ji ya fi sabo da aikin direban kan aikin office din da yake yi yanzu, ba wai ya fi son aikin direba kan Wanda yake yi ba, aa kawai dai yana Jin dadin tsohon aikin shi.


   Duk da kwarjinin da yayi masa haka ya dake yace "I just like driving you Sir, zan iya aikin duka biyu, don Allah ka ba ni wannan damar"


"Shikenan ka je, Najib will discuss with you" (wato Najib zai neme shi) 

   Da fara'a sosai kan fuskar shi ya shiga yi mishi godiya har Farouk na mamakin fara'ar da ke fuskar yaron, bayan fitar Adam ya zubawa kofar ido sosai cikin nazari kafin ya daga kafadun shi kadan ya mike ya koma kan kujerar aikin sa.

**************


Bai yi tsammanin zai samu aikin ba, wanda sati daya ma da zancen kafin Najib ya kira shi ya sanar da shi yanda suka yi da Farouk, akan zai cigaba da tuka sa, domin shima Farouk din yana son tukin Adam, tun daga nutsuwar sa da yanda yake tsare ka'idar tuki.


   Sai dai ko da Najib ya sanar da shi za'a cigaba da biyan shi tsohon salary shi, ya tabbatar masa baya da bukata, wannan din ya ishe shi, shi kawai dai yana son aiki tare da Boss ne, domin a nan gurin da ya ke yanzu ganin Farouk din ma wahala ya ke mishi, shi kuwa ya Saba da yanda matukar yana kaduna suna tare.


    Yau dai kam tun bayan fitar sa itama ta so ma shirin fita asibiti, ta shirya cikin doguwar abaya, ta yane kan ta da gyalen Abayar ta rufe gida ta fito.


    Bata wani jima ba ta samu ganin Dr din da su ke gani, wanda kai tsaye suka soma yi mata gwaji da ultrasound.


Sai da ya gama duba takardun da ke gaban shi, kafin ya mayar da hankalin shi kan Fahima da ta bashi dukkanin hankalin ta, tana jiran bayanan shi.

    "Mun jira period din ki ne domin yi miki wannan test din, ina son ganin ya kwayoyin haihuwar ki su ke wato eggs din ki, which kuma Alhamdulillah everything is looking good"


    Ya nisa "but we still have to run more tests, cause ina tunanin issue din daga fallopian tubes din ki ne, zamuyi HSG test next week and see me zamu samu"


    "Amma Dr kana ganin ba babban issue ba ne" ta karashe da damuwa sosai kan fuskar ta

   "Don't panic please, Insha Allah ba wata matsala ba ce da ba zamu iya magani ba, ki je gida kawai ki huta, next week zamuyi HSG insha Allah"

   Ta gyada kai cikin rashin kwarin guiwa "toh Dr, Nagode"


   Haka dai ta dawo gida jiki duk sukuku, duk kwanakin da suka biyo baya binciken wannan fallopian tubes din kawai ta ke tayi, ganin dai duk results din da research ke bata ba mai dadi ba ne, sai ta tattara ta ajiye.


   Har sati ya zagayo ta koma asibitin, suka yi mata wannan HSG test din, wata simple procedure amma sai azabar tsiya.

   Sai da suka bar ta ta dan huta kafin Dr ya shiga yi mata bayanin result din ta


"I don't have good news, am afraid"

"Amma kar ki tayar da hankalin ki please" yayi saurin fada ganin tsoron da ya bayyana kan fuskar ta nan ta ke.


    "Kina da what we call fallopian tubes blockage, su wadannan tubes din biyu su ke baiwa kwayoyin halitta na diya mace damar haduwa da kwayoyin halitta na da namiji har yayi resulting to Pregnancy"


   "In your case, tubes din ki are blocked a rufe su ke, amma wannan procedure din da muka yi an dan buda su kadan, with magungunan da zan dora ki a kai, Insha Allah muna fatar za a dace, domin mata da dama anyi musu din kuma Alhamdulillah an dace"


   "Ke ma Insha Allah it will work, sai kuma a dage da addu'a, we do our best, amma komai yana a hannun ubangiji"

   Ya ba ta magungunnan yace ta soma shan su a yau din.

 Ta dawo gidan jikin duk a sanyaye har ya dawo ya tarar da ita a hakan.


     "Insha Allah, Allah bai manta da mu ba, zai bamu namu too kin ji" ya fada cikin sigar lallashi yana shafar sumar kan ta.

********


     Rayuwa ta dan ja sosai cikin tarin alkhairori da dama a rayukan wadannan bayin Allah.

    Watan Ramadan na kokarin shigowa suna ta shirye shiryen tarbon wannan watan mai dunbin albarka.


  Yau kam babbar bakuwa ta ke da a gidan ta, Nafisa ta kira ta tun jiya ta sanar da ita zata shigo gurin ta yau, dama kwana biyu bata gari.


  Sosai ta ji dadin zuwan Nafisa wacce suka rungume juna cikin murna, sun jima ba su hadu ba, tayi missing Nafisar sosai wata kawa kwaya daya da ta ke da ita a halin yanzu.

   Ba karamin dadi Nafisa ta ji ba, ganin sauyin rayuwa da cigaban da ta tarar da Fahimar a ciki, gidan ta ba laifi yayi kyau, tana ta yaba kyaun gidan.


   "Nafisa sai kika manta da ni kawai"

Wani Harare Nafisa ta jefe ta da shi "hmmm bana son tsokana, ke din da ma da ina biye ta ki ai da yanzu kawancen mu ya lalace"

   "Kinsan last week na dawo, tunda muka gama da school ina Lagos gurin yaya ta, ita tana aure a chan"


Fahima tace "Allah sarki ya kika baro su"

"Alhamdulillah, su na gaishe ki, kinsan sun San ki, tun daga labaran ki da na ke ba su, na wata kawata ta mai mugun zurfin ciki da wulakanci, sai dai akwai hakuri"


   "Lahhh yanzu nafisa kema kallon da kike yi min kenan"

Nafisa ta sanya dariya sosai tace "wasa na ke miki, amma dai na gaya musu kina da tsananin hakuri"


   Tayi murmushi kawai 

Nafisar ta cigaba "Toh mummy ma dai har cewa tayi ita kam wannan yar ta ta har yau ba ta zo ta gaishe ta ba" 


"baki taba zuwa gidan mu ba kallon ki kawai na ke yi" Nafisa ta karashe tana munching on kayan marmarin da Fahima ta jere mata shake da center table din.


   "Zan zo in gaida mummy Insha Allah" daga nan dai suka dauko zancen school, Nafisa kam har sun kammala gabakidaya sai jiran notification da ya ke school din su ba under Asuu ya ke ba, so su strike din bai shafe su ba.


   Fahima tayi ta jininin wannan semester daya da tayi mata saura, yau wata biyar kenan suna cikin strike Asuu ba su dawo ba.

   Seven ya shigo gidan, zuwa lokacin tuni Nafisa ta wuce, kai tsaye ta Taya shi zare kayan jikin shi, yayin da shi kuma ya nufi fada toilet domin watso ruwa.


    A karo na biyu ta sake kai kallon ta kan wayar shi da ke kan gado, wacce ke chiming tun dazu alamar shigowar sakonni a WhatsApp, ta kawar da kan ta kawai ba tare da ta duba wayar ba, har ya fito daga bayin, kai tsaye wayar sa ya nufa yayi unlocking yana duba sakon da ya shigo.


   Kadan ya kalli bangaren ta, wacce itama idanun ta ke kan shi sai dai hada idon da suka yi, ta kawar da kan ta ta mike tana fadin "I'll serve dinner"

   Bata jira amsar shi ba ta fice daga dakin, cikin sauri ya soma shiri domin samun jam'in sallar Isha da ake kira.


    Farar jallabiya ya zura ya fito da bakaken slippers kafar sa, Tana gaban dinning Tana jere abincin yace "wifey zan je masallaci"

"Allah ya tsare" ta bishi da addu'a, Tana bin bayan sa da kallo har ya fice daga falon, ta dan yi jim kafin ta koma daki, itama sallar Isha din tayi, tayi shafa'i da wutiri kana ta dawo falon.


   Zuwa lokacin har ya dawo yana kan dinning yana jiran fitowar ta, ta karaso tana zare dogon jilbab din ta, wanda ya bayyanar da long sleeve top din da ke jikin ta mai shara shara, domin kana iya hango komai na jikin ta, da bakin leggings da ya lafe mata sosai yana fitar da kyakkawar zubin halittar ta, ta cikakkiyar 'ya mace da ta hada dukkanin abinda ake nema a mace.


    Idon sa kan ta har ta karaso tana kokarin zama kan kujerar gefen sa ya kamo hannun ta, ya janyo ta kamar zata fado jikin shi.


    "Zo in ji kamshin ki, you're looking sexy" ya fada yana shakar daddadan kamshin da ke fitowa daga jikin ta.


   Murmushi na musamman ne ya bayyana kan fuskar ta, cikin Jin dadin yaba kwalliyar ta da yayi, domin kwana biyu yanzu ta lura da complimenting din kwalliyar ta da baya yi koda kuwa zata bata awanni Tana gyare jikin ta, da kuwa, abu kadan idan tayi zai rika zuzuta yanda tayi kyau, ko yanda abu kaza yayi mata kyau.


    "Da gaske" ta tuhuma, muryar ta chan kasa

Adam ya zuba mata ido yana yi mata mazauni kan kafafun sa "Ofcourse kina doubting ne" 


    Dan girgiza kan ta tayi kafin tace "saboda ka rage complimenting di na ne"

   Ya dan yi shiru shima cikin tunani kafin yace "Really, ni kuma, haba sai dai idan stress din aiki ne yayi min yawa, but you're the most beautiful woman in my eyes wifey, kema kin sani ai"


   Ta zagayo da hannayen ta wuyan shi kamar wata karamar yarinya Tana makale jikin shi 

"Na yadda da kai"

   Hmmmm ya sauke wata irin ajiyar zuciya kafin ya ce "zo ki ciyar da ni" da kan ta kuwa ta rika bashi abincin, suka gama dinner, ta gyara gurin kafin suka ba je nan falon suna kallon movie 


    Washegari ma da safe kafin ya fita suna breakfast hankalin shi na ga wayar shi da ya ke dubawa, har suka gama ya fice

   Yau ma sai 7pm ya dawo kamar jiya, sabanin time din da ya Saba shigowa gidan, da tayi complain sai ce mata yayi Boss yana gari shiyasa.


    Ita kam har bacci ya dauke ta Daren yau abin a ranta, Adam din ta yana wasu dabi'u da bata San shi da su ba, obsession din shi da wayar shi a yan kwanakin shi yafi komai daga mata hankali.


    Tana ji ya janyo ta jikin shi har bacci barawo yayi awon gaba da ita, karfe biyu na dare ta tashi saboda sallar dare da ta zame mata jiki a yan kwanakin.


   A hankali ta sake laluba gefen shi Jin kamar ita kadaice a kan gadon, wanda ba kama ba ne, haka din ne.


   Ta lalubo sabuwar wayar da bai jima da chanja mata ba, farar iPhone 12, ta duba screen din wayar wanda fuskokin su ya cike screen din, hoton su ne da tayi wallpaper da shi, Tana kan kirjin shi, wadataccen gashin ta ya bazu jikin shi, yayin da shi kuma yake dauke da madaukakiyar fara'a


    Ta kalli hoton na su kafin ta sake duba time wai ko ita ne tayi saurin tashi ba tsakiyar dare ba ne, sai dai agogon ya nuna mata biyu da rabi har da yan mintuna.


   Ta zuro kafafun ta, ta sanya bedroom slippers da ke gefen gado, fuska fal bacci ta kunna bulb wanda ya wadata dakin da haske.

  Tabbas ita kadaice a dakin cikin daurewar kai ta fito ta janyo kofa, hanyar falon su ta nufa, sai dai tun bata isa ba ta soma jiyo tashin murya kasa kasa wacce ta ke da tabbacin ta Adam ce.


    Rassss gaban ta yayi wata irin muguwar faduwa, domin abu ne da bata taba experiencing ba a zaman su da shi na shekara hudu kenan yau.


   "Adam" sunan shi yayi escaping bakin ta a hankali, tare da dafa kirjin ta saboda wani irin bugawa da yake mata da sauri sauri"