14
by @mahmazee1
Yanayin yanda muryar sa ke fita kawai ya tabbatar mata da mace ake wayar.
Bata da bukatar Jin ko ma meye ke fita daga bakin shi, hakanan ta tabbata bai ji motsin ta ba duba da wayar sa da ya cigaba da yi.
Sai ta juya cikin tashin hankali ta koma daki, tayi tsaye gaban madubi, ta rungume hannayen ta a kirji Tana kallon kan ta a mirror, Neman abinda ta rasa a jikin ta, da Adam ke nema a wani gurin ta ke yi.
Wasu hawayen bakin ciki suka samu sararin saukowa kan fuskar ta, tayi saurin toshe bakin ta ta fada bayi.
Ta jima sosai a bayin kafin ta fito dauke da alwala, kyakkyawar fuskar ta ta dan ta sa kadan alamar kuka, zuwa lokacin ya dawo dakin yana zaune kan bedside drawer ya zubawa kofar toilet din ido.
"Kin tashi kin ga ba na nan ko, I was in the kitchen naje Neman ruwa ne" ya shiga yi mata bayanin da bata tambaye shi ba, ganin yanda ko bangaren sa ba ta kalla ba, ta nufi sallayar carpet da ke dakin.
"Okay" kawai ta fada lokacin da ta ke sanya jilbab din ta, ta tayar da sallar ta.
Bai dauke idanun sa kan ta ba har ta kammala sallolin ta ta janyo alqur'ani Tana Karantawa domin samun saukin abinda ta ke ji.
Ita kan ta bata taba sanin tana da kishi kwatankwacin wannan ba sai a daren yau, ta buda suratul Arrahman ta na tilawa.
Tun yana kishingide yana jiran ta har bacci yayi awon gaba da shi.
Har aka kira sallar asuba a kunnen ta, tayi raka'atainil fajr kafin ta isa gaban gadon ta shiga tashin shi a hankali.
"An kira sallah Zawj" kawai tace ta koma kan carpet din ta.
Shima alwala yayi ya fice masallaci, har ya dawo tana nan inda ya bar ta, duk da kuwa tuni ta gama azkar din ta.
Ganin dai bata da alamar dawowa kan gadon, ya sanya ya nufe ta, ya tayar da ita yana fadin "addu'ar ya isa hakanan, Insha Allah Allah ya karba, zo mu je mu kwanta"
Bata yi mishi gardama ba, ya zare mata hijabin da kanshi, kana ya kwanta yana janyo ta jikin shi.
Tayi shiru a kirjin shi, tunanuka har ma wadanda bai kamata tayi ba na ta zuwa mata.
A kwanakin sosai ta sanya ido a al'amuran shi, sai dai ko kusa bata taba duba wayar sa ba ko daga kiran sa, amma tuni ta fahimci akwai wacce ta dauke hankalin mijin ta.
Ta yadda Adam din ta yana magana da wata 'ya mace sabanin ita, wata sad reality da bata taba jin abu mai daci kamar sa ba.
****
Yau ta fito daga kitchen din su da dan hanzari jin wayar sa da ke ta ringing falo da alama ya manta wayar a nan, ganin Baba ke kiran shi ya sanya ta nufi dakin su domin kai mishi wayar, nan ma baya nan sai karar saukar ruwa da ta ji bayi.
Hakan ya sanya wayar na sa ke ringing na biyu ta daga domin sanar da shi Adam din baya kusa.
"Hello Baba"
"Hello handsome" suka fada lokaci daya ita da mai kiran, wacce sabanin muryar Baba sai muryar mace ta ji na cika dodon kunnuwan ta.
Da sauri ta dago wayar daga kunnen ta Tana dubawa, Baba2 shine rubuce a number ita sai lokacin ma tunanin ta ya kawo chan, bata San baba da wata number ba face number sa kwaya daya, bare har ayi saving wannan da Baba2.
Daga dayan bangaren kuma Jin muryar wacce ta daga sai aka katse kiran, ta jima tsaye rike da wayar hannun ta in disbelief, hawayen ta wani na korar dan uwan sa.
"Why why why Zawj" fahima ta furta Tana ficewa daga dakin cikin hanzari.
Kitchen ta koma ta dafe kan ta a bango Tana fadawa dogon tunani, ya zata yi da lamarin Adam, ya zata bullowa wannan al'amari da ke kusanto rayuwar auren ta.
Tana ji yana ta faman kiran ta tayi banza da shi sai ma kofar kitchen ta baya da ta bude ta fice domin bata ma so ya leko kitchen din ya ganta.
Yau kam ya rasa gane kan fahimar sa, kai yan kwanakin ma ya rasa gane kan matar ta sa, wacce ya sha tambayar ta domin Jin damuwar ta sai ta ce mishi ba komai.
Washe gari kuwa ko yar rakiyar da ta saba yi mishi bata yi ba, ya fice gidan rai a cunkushe ba dadi.
Zama kawai yayi an office din shi, kiran Rashida ya shigo wayar.
Ko bai duba ba ya San mai Kira, sai yayi ignoring call din, yana kokarin sanya wayar a Do not disturb saboda calls da ke ta shigowa na ta, ta turo kofar office din hannun ta rike da wayar ta alamar kiran da ta ke ta yi mishi.
"Really" Rashida ta fada tana karasowa ciki
"Me yasa ka ke ignoring calls di na"
Da kyar ya dago da idanun shi ya kalle ta a lokacin da ta ke kokarin yiwa kan ta mazauni yace "Don't" in warning
"don Allah fice min daga office"
Ta kalle shi da kyau "wai me nayi ma ka ne"
"Rashida I told you I don't want this anymore bana so, ina da mata, ina da iyali, so please ko gani na kika yi ko a hanya ne ina so ki nuna ma kamar ba ki sanni ba"
Wani kallon raini tayi masa "ohhhhh da baka San kana da mata ba sai yanzu"
"Please Adam ni ba ruwa na da matar ka, wallahi ba ni da matsala da ita, don Allah kar kace zaka rabu da ni" ta fada Tana kokarin zagayowa kan seat din da yake kai.
"Get out of my office I said" ya fada yana dukan table, zabura tayi, ta zuba mishi ido kafin ta fice cikin bacin rai.
Duk wanda ke tare da shi a yau ya fahimci chanjin yanayin sa, domin komai ma baya mishi dadi, ran shi a cunkushe ya ke, ba abinda ya ke son gani face matar sa, wacce ya sani yayi mata laifuffuka masu tarin yawa wadanda baya tunanin ita ta ko sani, amma guilty conscience na abin na ta cin sa a kwanakin, ya ki ya bar shi.
Yayi ta kiran layin ta amma ba a dagawa
*****
Tun bayan shigowar wadannan munanan messages din da aka turo mata a WhatsApp din ta, ta ke kwance kan gado ruff da ciki tana darzar kuka.
Agogo ta duba wanda yayi nuni da karfe goma sha biyu na rana.
Cikin kunar rai ta mike daga kan gadon ta nufi bayi, wanka tayi da ruwan dumi, ta fito ta shirya cikin kaftan boubou na material da mayafin ta.
Ta sanya wayar ta a jaka, ta fito, rufe gidan tayi ta fice gabakidaya.
Mai adaidaita ta samu wanda ya ajiye ta Malali kai tsaye, bata San me zata cewa aunty ba ko duk wani, amma wallahi ba zata iya cigaba da shakar wannan abin takaicin ba.
Gidan na su Aunty da hayaniya kamar ko yaushe, ta nufi part din su kai tsaye, duk da sunyi mamakin zuwan ta, amma ba wanda yayi tunanin da wata matsala.
A gidan ta yini, wanda duk da hayaniyar su hakan bai hana abinda ya faru safiyar yau ba yi mata Karan tsaye a rai, har lokacin magrib yayi.
Aunty ta kalli bangaren Fahima wacce bata ko ga Tana shirin komawa gida ba tace "sai yaushe zaki wuce ne, ga magrib Ana yi" sanin dai Fahima bata kai dare a gidan.
Ta dan yi yake tace "ina jiran shi ne"
Aunty bata kawo komai a rai ba tace "okay"
Da mamaki sosai ya bude gidan da ya ji shi a rufe, ya shigo yana Kwala kiran sunan ta, sai dai ko'ina ya duba, babu ta a gidan.
Ya sake trying number ta nan ma kamar sauran calls din sa wannan ma ba a daga ba
"Me ke faruwa" ya raya Cikin faduwar gaba, zuciyar shi ta soma raya mishi ba lafiya ba, domin Fahima ba zata fita gidan ba tare da sanin shi ba, lafiya ba zata sa fahima ta ga kiran sa ta ki dagawa ba kuma ta ki bin bayan calls din shi
Yayi ta tunanin ina ta je har yamma shiru bata dawo ba, domin tunda 4pm tayi ya gudo daga office ya yo gida, sai dai wacce ya ke zullumin gani har zuwa lokacin idanun sa basu gan ta ba.
Baya tunanin tana da gurin zuwan da ya wuce gurin su Aunty, hakan ya sanya tun bayan da ya fito masallaci sallar magrib ya dauki hanyar Malali.