15
by @mahmazee1
Cikin rashin kwarin guiwa ya shigo sashen Aunty, suka gaisa a mutunce kamar ko yaushe ta tambaye shi mutanen Saminaka.
Ya amsa da duka suna lafiya ba don ya fahimci ainahin inda zancen ta ya nufa ba, ya mike ya fice yayin da Aunty tayi kiran Fahima kan ta fito su tafi.
Bata musa ba ta fito din, tayi musu sallama suka fi ce, ba wanda yace da dan uwan sa kala har suka iso gida, kai tsaye ta nufi bedroom din su, wanda hakan ya sanya shi saurin kamo tsintsiyar hannun ta domin dakatar da ita.
Ba tare da ta kalli fuskar sa ba ta zubawa hannayen su da ke sarke ido, kafin ta kwace hannun ta a hankali ta nufi daki.
Kasage yayi shi kadai a falon cikin tunani, har ta sake fitowa daga dakin, rike da kayan bacci pajamas a hannu, ta nufi dayan dakin, wanda sai su jima basu yi amfani da shi ba.
Kayan baccin da ta shigo da su ta dora kan gado da yake bata da wasu kaya a dakin, kai tsaye bathroom din dakin ta nufa.
Ta dan jima kafin ta fito daure da katon farin towel jikin ta da alama wanka ta yo, ta nufi dresser Tana shafe jikin ta da man vaseline da ke kan madubin.
Da sallama ya turo kofar dakin, wanda da ba don musulunci ba, ba abinda zai sanya ta amsa sallamar sa, ta amsa kasa kasa, har ya ta ko cikin dakin yana kallon ta da madaukakin mamaki, na ganin ta dakin da kuma abinda ta ke yi.
Sai dai kamar Allah bai yi ruwan sa ba a gurin, ta mike ta nufi kayan baccin ta, ta shiga kokarin sanyawa.
"What's wrong Fahima, why the cold treatment, ya kina yi kamar ba na existing, ko wani laifi nayi ne" ya fada yana takowa gaban gadon.
Nan ma shiru bata tanka shi ba har ya kamo kafadun ta a lokacin da ta ke kokarin kwanciya, ya juyo da ita suna fuskantar juna.
"Wifey menene, ki gayamin meye damuwar, tunda na fita gurin aiki na ke kiran layin ki ba kya dagawa, na dawo gidan tun tuni na tarar ba kya nan, why would you go out without informing me, kuma ina magana kina banza da ni" ya karashe da damuwa sosai kan fuskar shi.
"Please ina so zan kwanta" ta fada tana kallon cikin idanun shi
Shima din ita yake kallo cikin mamaki kamar ma bata ji korafin sa ba kenan
Yace "kina nufin a nan zaki kwana"
Da sauri ta gyada mishi kan ta kuwa cikin tabbaci Tana kawar da idanun ta daga kallon shi, domin ko ganin fuskar sa bata son yi, abubuwan da idon ta suka gane mata su ne kawai ta ke gani a fuskar sa.
"don't take me for a fool Fahima, a kan wane dalili zaki kwana nan" ya fada yana sunkutar ta gabakidaya kamar wata baby ya dora kan kafadun sa, suka fice daga dakin.
Hanyar bedroom din su ya nufa da ita, sai dukan bayan sa ta ke Tana fadin ya sauke ta
Bai sauke ta a ko'ina ba sai kan gadon su, wanda almost immediately ta soma kokarin mikewa, biyo ta yayi kan gadon yana mayar da ita kwance.
"Ka kyale ni don Allah, leave me alone yah Adam, bana son gayamaka maganganun da ba su da amfani"
"Ai gwara ma ki zage ni wifey da wannan shariyar da ki ke min, da wannna yayan da kike kira na da shi, bayan kin San bana so"
Kallon kar ka raina min hankali tayi mishi Tana fadin "idan ma na share ka, ai kana da wacce ta fi ni" ta shiga kokawa da kakkausar rikon da yayi mata.
Jiki a mace ya cika ta yana jifan ta da kallon tuhuma, me maganganun ta ke nufi, kar dai ta gano abinda ke faruwa tsakanin shi da Rashida.
"Fahima" ya kira sunan ta a tausashe
"Don't, please don't Fahima me" ta yi saurin katse masa hanzari, yayin da ta juya cikin sauri ta koma dakin da suka fito.
Ta fada kan gado tare da fashewa da sabon kuka mai cin rai, ya jima shikadai a dakin kafin ya Mara mata baya, Tana kwance kan gadon ruf da ciki.
Ko tun daga daga sautin sheshshekar ta ya fahimci kuka ta ke yi
"ta ya zakiyi tunanin akwai wata ya mace a rayuwa ta bayan ke, har ma wai wacce ta fiki a guri na, babu Fahima, babu, ke kin sani you're the only one in my heart and in my life"
Ta mike zaune sosai kan gadon tana miko masa wayar ta
"Ka daina gayamin maganganun da ba gaskiya ba, kar ka kara da karya a kan laifin ka, don Allah ka daina domin bana so girman ka ya zube a ido na" ta karashe tana dora masa wayar a jikin sa yayin da ita kuma ta juya ta cigaba da kukan ta.
Wata irin faduwar gaba ce ta riske shi a lokacin da yayi tozali da WhatsApp messages din da aka turo mata a safiyar yau.
Wasu irin messages da shi kan sa da ya rubuta su yana Jin kunyar sake duba su bare ita matar shi, tun daga profile picture (dp) din ta ya gane ko wacece da wannan danyen aikin.
Rashida ce, wacce ta turowa Fahima screenshots na chat din shi da ita, masu dauke da pictures da kuma sakonnin da suka yi munin da bai kamata a ce ta gani ba.
Wani irin chat da bai kamata ace namiji magidanci yayi da wata mace ba sabanin matar shi ta Sunna.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya furta yana bin wayar da wani irin kallo, da ma babu fuskar shi a daya daga cikin hotunan da yace sam ba shi ba ne, amma baya da bakin kare kan shi, domin shi din ne dai a hoton, duk wanda ya San shi kai ko ba farin sani ba zai shaidi shi ne.
Ya dafe goshin sa yana kallon ta a lokacin da kukan ta ya tsanan ta, me yasa Rashida zata yi masa haka, me yasa zata zubar masa da girma a idon wacce ya San ba mai daukar shi a high standards kamar ta.
Daga chats din da ta turo akwai hoton shi shi da Rashidan a office din sa, a lokacin da ta kara waya ta dauke su tare da kwantowa kan jikin shi.
Akwai chat na hotunan da Rashida ta turo masa na ta, wasu hotunan da dai ba kyan gani domin tsiraici ne, ga replies din sa na yanda ya ke ta yaba kyaun halittar jikin ta, ga kuma chat na sexting tsakanin sa da Rashidar, Tana da receipts na kama shi da duk laifin da ta ga dama, hakanan baya tunanin akwai kalaman sa da zasu wanke sa daga abinda Allah ne kadai ya San me zuciyar ta ke raya mata.
Allah knows ba shi ya nemi Rashida ba, ita ce tayi ta bibiyar sa, yayi iyakacin kokarin sa na kaucewa sharrin ta amma tayi galaba a kan shi.
Shi dan Adam ne mai rai da tsoka a jikin shi, he got tempted ba tare da shi kan shi ya San sa'adda ya tsunduma a tarkon ta ba.
Sai dai tun da ya ga ta ci galaba a kan shi har tana Neman kai shi ga aikata sabon da bai taba yi ba kab rayuwar sa ta duniya wato Zina, ya takawa zamantakewar su burki, ya yakici abin a zuciyar sa karfi da ya ji.
Yanzu wa ya isa ya wanke shi a idon fahima, wasu kalamai zai gaya mata da zasu wanke shi a idanun ta, sai kawai ya mike ya fice daga dakin cikin zafin rai da kunar zuciya.
Sun jima a cikin wannan yanayin kafin ya iya fuskantar ta, ya dawo dakin yana jifan ta da wani irin kallo mai cike da tsantsar tausayawa da soyayyar ta da ta gama cike zuciya da kirjin sa.
"Fahima" ya kira sunan ta a tausashe
"Don't ever think I'll let you disrespect me, saboda wani chanjin yanayi da muka samu na rayuwa, I'll not take it na rantse maka" ta tabbatar masa da hakan a lokacin da ya ke takowa gaban gadon.
"Na ji na amince, amma ina so Kiyi hakuri kinji" ya fada yana hayowa gadon, tare da kamo kafadun ta ya sanya ta a kirjin shi, cikin sigar lallashi ya shiga ba da hakuri ba tare da kokarin dora dukkanin laifin a kan Rashida ba.
"Na rantse miki it's not what you think, wallahi ba abinda ya shiga tsakani na da ita, of course I got tempted har na so kaucewa hanya, amma tsoron ubangiji na and the fact that zan ci amanar auren mu bai iya bari na na kai ga aikata barna ba"
"Kiyi hakuri wifey, don Allah kiyi hakuri, for the first time ina Neman afuwar ki a kan laifin da ba ki taba kama ni da shi ba, kiyi hakuri kin ji, na rantse miki irin haka ba zata sa ke faruwa ba, please am sorry, kar kice zaki share ni, wallah ba zan iya dauka ba"
Cikin kukan da ya ci karfin ta ta shiga dukan kirjin sa "why why why zawj, me yasa zaka yi min haka, me na rage ka da shi"
Saurin dago ta daga kirjin sa yayi, yana dora farcen sa kan labatan ta"
"It's not you wifey, ni ne, baki rage ni da komai ba, ke din kin cike duk wani gurbi da ya kamata macen kirki ta cike a gurin mijin ta, you don't give me a reason to complain, laifi ne na aikata, na kuma karbi laifi na, ina kuma ba da hakuri, hakan ba zai sa ke faruwa ba"
Sun jima a cikin wannan yanayin, yana shafar bayan ta cikin sigar lallashi, kafin ya janyo wayar sa ya nuna mata
"Na daina daga wayar ta, na daina replying na ta, na gayamata I'm not in anymore, shiyasa ta turo miki wadannan chats din, am not saying laifin na ta ne, but I want you to trust me, na katse alaka ta da ita tun kwanakin baya, tun before this, kinji"
Haka dai ya rika gaya mata kalamai masu sanyaya zuciyar masoyi, har ta hakura ta yadda a zuciyar ta
Adam din ta ma dan Adam ne full of humanity, namiji ne shima da ire iren wadannan temptations din da suke gani a waje zasu iya tasiri a kan sa.
Uzuri daya tayi masa, bata taba kama shi da kwatankwacin irin wannan laifin ba, for the past 4 years of their marriage bata ta ba kama sa da laifin cin amanar ta ba, saboda haka tayi masa uzuri a yau.