16
by @mahmazee1
Washegari yana sane ko gurin aiki bai fita ba, yayi zaman sa gida duka domin lallashin uwargidan sa.
Sai karfe tara yau ta tashi daga bacci saboda isashshen baccin da basu yi ba daren jiya, a hankali ta mike daga kan gadon ta zuro kafafun ta kasa.
Dogon gashin ta da ya warware yana saukowa kafadun ta, ta tattare guri daya da hairband din ta da ta dauko kan bedside drawer.
Fuskar ta fayau alamar baccin da ta tashi, ta zura bedroom slippers da ke gefen gadon ta nufi hanyar bathroom.
Brush ta soma yi kafin tayi wanka ta fito daga toilet din, ta soma shirin ta wanda ba wani wahala ne da shi ba.
Doguwar rigar atamfa ta sanya dinkin flare gown, sai gashin ta da ta gyara tana raya ya kamata tayi kitson shi hakanan, ta feshe jikin ta da turare ta fito falo.
Sam ba tayi tsammanin ganin sa a gidan ba a daidai wannan lokacin, a tunanin ta ya fice gurin aiki, sai ta dan yi turus tana jifan sa da kallon mamaki a lokacin da ya ke fitowa daga kofar kitchen.
Murmushi mai kyau ya sakar mata yayin da ya ke dora madaidaicin tray din da ke hannun sa kan dinning table, wanda ke shake da breakfast
Hannayen sa ya dora a kugu "kinyi ruining breakfast in bed din" ya fada yana watsi da dayan hannun sa na dama.
Martanin murmushin shi ta mayar mishi, ta tako a hankali cikin salon tafiyar ta mai daukar hankali da ya kasance dabi'ar ta.
"Good morning" ta fada yayin da ya janyo ta jikin shi shi, yana manna mata kiss a goshi.
Ta zauna kan daya daga cikin kujerun dinning din, shi ma ya zauna yana kokarin serving mata breakfast din da ya bata awanni gurin hadawa.
"Yau ba aiki ne" tace tana kai spoonful na oats da ya ji madara bakin ta, tana kallon bangaren sa.
Ba tare da ya daina aikin hada tea da ya ke yi ba ya amsa ta "akwai, but I want to spend today with you"
Dan bakin ta ta turo gaba, tayi ciki da idanun ta in Awwnn, wanda hakan ya da da fito da natural kyaun ta da kurciyar ta tace "Nagode"
Duka sauran yinin anan gida ya karashe shi tare da ita, ba tare da leka ko kofar gidan ba, sai ma da aka kira magrib ne ta matsa mishi ya je masallaci.
Washegari yayi resuming aikin shi, inda dawowar boss ta sanya ayyuka suka da da yi masa yawa a kwanakin da suka biyo baya.
*******
Duk wani abu da duk wata hanyar da ya san zai faranta mata shi ya ke yi, ba ita kawai ba shi kan shi mamakin kan shi ya ke na yanda aka yi ya iya yiwa fahimar shi wannan laifin.
Sai dai abinda ya faru ya Riga ya faru, kuma abu ne da ya tabbatar ba zai sa ke faruwa ba hakan ya sanya, duk wata hanya ta faranta mata shi yake yi.
Watan Ramadana ya shigo, bayin Allah suka shiga gabatar da wannan watan cikin ibada da bautar ubangiji.
Yau dai kam ya shigo mata gidan da labarin da ya san ba dadi ba har farin ciki sai ya sanya ta na wucin gadi.
Sai dai ita ta riga shi ta hanyar fadawa jikin shi cikin murna ta ke sanar da shi lifting strike din su da aka yi, yau dai kam ASUU ta cire yajin aikin da suke ciki.
"Ahhh finally, yar semester nan da tayi muna saura za a gama ta" Adam ya fada.
Fahima ta saki murmushi cikin farin cikin da ta ke cikin shi tun dazu
Sai da suna yin iftar ne ya ke gayamata na shi good news din
"Da gaske zawj, Umrah, how" ta fada da matukar mamaki, da farin cikin da ya bayyana a fuskar ta har ma fararen idanun ta nan ta ke
Ya kalle ta cikin farin cikin faranta mata shi kan shi yace "yes, zamuje Umrah last ten days Insha Allah"
Hannun ta ta dora tana toshe bakin ta alamar mamakin da ta ke ciki, she just can't believe it, Umrah, Saudi, what a surprise
"Thank youuuuuuu" ta fada ta sanya hannun ta cikin na shi, ta shiga murzawa a hankali, kafin ta mike gabakidaya ta fada jikin shi, ta kankame shi tana sakin dariyar da ta kasa rike wa.
Shi kan shi dariyar ta ya rika yi, ganin farin cikin da ya ki barin fuskar ta, har sai da ya janyo ta shi da kan shi ya mayar kan kujera.
"Amma zawj ya aka yi, don't tell me savings din ka ne kayi using"
Girgiza mata kan shi yayi a hankali yace "ko kusa" ya gyara zaman sa.
"It's all thanks to our Boss, mutumin nan dan aljannah ne Fahima, ni kam da Ana gane mutanen aljannah tun a nan duniya da na ce Baba da Farouk Waziri kam yan aljannah ne"
"He has this habit na biyawa ma'aikatan sa Umrah and hajj, so luckily enough for me kinsan muna tare da shi duk sa'adda ya ke gari, shine Najib ke gayamin suna nan na cikin wadanda zasu je Umrah this year"
Fahima ta tallabe fuskar ta da dayan hannun ta ta dakata da cikin abincin da take yi tare da langwabar da kai tace "Masha Allah, Allah ya biya shi"
"So kawai I've been thinking, since zasuyi mana covering komai har accomodation, na ga bari nayi seizing opportunity din mu je tare kawai, ticket kawai zan nema miki"
Wannan news din kam ba karamin dadi yayiwa Fahima ba har ma da iyaye da yan uwan ta, idan ka cire su Mami da wannan labarin ko kusa bai yi musu dadi ba kai har da Mummy ma.
Salma ce ke bata labarin kalaman da Mami ke jifar su da shi wai na cin arzikin suruki kuma dan ta, a wani yini da suka kawo mata, ita sadik furera har ma da yaran Mama zuhra su biyu.
Ba bata lokaci suka je aka yi renewing passport din ta, ya nema mata visa da ticket, komai ya kammala sai zuwan ranar tafiyar su.
Azumi na goma sha takwas su Adam suka daga da ya ke ba jirgin su daya ba, washegari ita kuma nasu jirgin na Ethiopian airline ya daga da su.
Karfe goma sha daya na dare suka sauka a Prince Mohammed international airport da ke Madina Saudi Arabia, wata kasa da rabon ta da ita ko ba'ayi ba she's sure za'ayi shekara 8, tun wani zuwa da suka yi last tun kafin kariyar arzikin da ya samu Baba.
Sun kwaso uwar gajiya kam, tun da sai da suka tsaya Ethiopia suka yi chanjen jirgi, ga azumin da suka kamo hanya da shi wanda akan hanya suka yi iftar.
Tuni ya tsufa a airport din yana jiran isowar su, a WhatsApp call su ke communicating har ta gano gurin da ya ke.
"Baby na tayi kokari, long flight haka ita kadai" ya fada a lokacin da ya rungumo ta jikin shi, yayi hugging din ta da kyau, yayi kissing kumatun yana karbar akwatin ta "welcome"
"Thank you zawj, na gaji" ta karashe Tana shagwabe mishi fuska
"Let's go, mu je ki huta"
Ya tsayar musu mai taxi da ya dauke su zuwa Al'andalus Diamond hotel, wani hotel din da FW holding ta kama musu, daga shi har ma sauran ma'aikatan da aka biyawa, dakin da aka bashi yana second floor.
Ya barta domin ta watsa ruwa yayin da shi kuma ya sauka domin nema mata abinda zata ci.