17
by @mahmazee1
Hannun sa dauke da farar Leda ya dawo dakin, zuwa lokacin Tana zaune bakin gado, da alama har tayi wanka, domin bathrobe ne a jikin ta wanda ta samu a toilet din
Fuskar ta tayi shar wanda ta dan yi laushi alamar gajiyar da ta ke tattare da ita, ya zuba idanun shi cikin na ta da suma suka nuna gajiyar ta.
"Ga abinci" ya karaso gaban ta
"Thank you zawj" ta furta ta karbi abincin ta dora nan kan gado, ta bude abincin da ke cikin Aluminium foil take out, mutton biryani rice ce, ta kai abincin bakin ta Tana taunawa a hankali.
Tana kammalawa sai bacci, ya tsura mata ido kawai hadi da girgiza kan shi, ganin yanda nan ta ke bacci ya dauke ta ko abincin bata kawar ba, hakanan ko bathrobe din jikin ta bata chanja ba to kayan bacci.
Ya janyo bargo ya rufa mata da kyau yayin da shima ya fada bayi domin yin wanka.
Sai kiraye kirayen asuba ne ya tayar da su, suka shirya suka fice masallaci tare domin samun jam'in Subhi, bayan sun dawo nan ma wani baccin ta sake komawa.
Sun zazzaga garin madina hakanan sun dan yi shopping, kwanan su uku a madina suka dauki haramin sauke umrar su, suka wuce garin mecca.
Al-ebaa hotel suka sauka, kayan su kawai suka sauke suka nufi Haram domin sauke umrar su.
A sanda suka isa gaban ka'aba kowanne ya dage hannun sa cikin rokon ubangiji, addo'o'i su ke jerowa tare da kai kukan su ga mai kowa mai duka.
Bayan iyayen sa, matar sa da Baba, mutum na gaba da ya shigo jerin addu'o'in Adam, Farouk waziri ne, ya sha addu'a sosai a gurin Adam, ya roki ubangiji ya biya mishi dukkanin bukatun shi, ya bashi abinda yake nema duniya da lahira.
Duk da a iya nashi tunani, a duniyar nan dai kam bai San abinda Farouk ya rasa ba, amma kuma kowane mutum ai mai kwadaituwa ne ga rahamar ubangijin sa.
Yayi tuba ga ubangijin shi tare da neman tsari daga sharrin zina da duk abinda ya shafe ta.
A kan hanyar su ta komawa hotel ne ya ke tambayar ta me ta roka
"Ya'ya Zawj, na roke Allah ya ba mu zuri'a mai albarka"
"Ameen, Allah ya karba, amma ni fa me kika roka min, tun ma baki samu yaran ba har kin fara mantawa da ni"
"Of course zawj nayi maka, Allah ya bar mu tare cikin farin ciki har gaban eternity"
The following day ya same ta daki yake gayamata ta shirya after isha zasu je ta gaida Boss, shima yana Saudiyar da Family din sa duka
"Na yiwa Najib magana, so anjima zamu je, mu gaida mahaifiyar boss, suma din they are around"
Ta gyada kai tana fadin "Allah ya kai mu"
Yau a masallaci ma tayi iftar bata dawo ba sai da ta samu jam'in Isha da taraweeh, kana ta kamo hanyar hotel din su, dama tun dazu da suka zo masallaci suka rabu tun da gurin zaman mata daban da na maza.
Ai kuwa ya riga ta dawowa har ma ya shirya cikin jallabiya kalar ruwan kasa da irin hular nan ta mutanen saudiya wato malam ja Hadith.
Shigar tayi masa kyau sosai, yayi ta uzzura mata kan tayi sauri kar dare yayi.
Kai tsaye ta shiga bayi tayi wanka, a gurguje ta feshe jikin ta da deodorant ta shafa wata khumrah mai saukin kamshi.
Bakar abaya ta dauko daga cikin siyayyar da suka yi, abaya ce mai sasssaukan ado a jikin ta, Sam rigar bata da hayaniya.
Ta tufke cikakken gashin ta kasa a ribbon tare da yane kan ta da gyalen abayar, wanda hakan ya sanya gashin ta tasawa a cikin gyalen abayar kadan.
Tayi kyau kamar wata balarabiyar Yemen saboda yanda abayar ta dauko jikin ta, ta dauko wata madaidaiciyar paperbag din da ta yiwa mutanen da zasu je gaisuwa tsaraba.
Ya kama hannun ta yana fadin let's go, da ya ke hotel din su na dan da tazara da Haram sai suka shiga taxi kawai, wanda ya ajiye su gaban gada kadan, saboda police da ke nan suna hana wucewa.
Da Najib su ke communicating wanda ya tabbatar masa da yana nan reception din Hilton Suites hotel yana jiran su.
Sosai ta zuba ido tana kallon haduwa, kyau da tsarin hotel din.
Tun da suka nufo Najib hannu sarke da na juna ya zuba musu ido, ya kalli Adam, kafin ya sauke kallon sa kan wacce yake kyautata zaton matar Adam din ce, cikin kallon sani, wacce ya rasa ina ya San ta.
Suka karaso Adam na mika masa hannun sa, suka gaisa cikin mutunta juna.
"Ina yini" fahima ta gaida Najib a sanyaye, a ranta tana raya wannan shi ne Najib din da bayan sunan Boss ta ke Jin sunan sa sosai a gurin Adam.
"Lafiya qlw madam, ya ibadah"
Ta amsa da Alhamdulillah suka nufi elevator, Najib yayi amfani da key din shi ya danna button din last floor wanda chan zasu.
Yayi Shiru yana sauraren hirar da ke tashi tsakanin Adam da matar sa, wacce ke amsa mijin na ta murya chan kasa, cikin rashin sakewa saboda wanzuwar sa a gurin.
Yayi kasa da Kansa yana so ya tuna a ina ya San wannan fuskar.
Wata irin daukewar wuta ce ta ziyarce sa, tare da daukewar numfashin sa na wucin gadi, har yana sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciyar da da kyar yayin kokawa da numfashin sa gurin fitar da ita.
Idanun sa suka firfito waje cikin razana ya dan dago da kan sa ya kalli bangaren su kadan.
Ta ya ma za'ayi ya iya manta wannan halittar Najib ya raya a ransa, bai kamata ya manta wannan fuskar ba ko da na minti daya ne, komai tsayin shekarun da suka zo suka shude kuwa.
Bai ankare ba sai Jin karar elevator din ya yi, alamar ta kawo su last floor din.
Yaji kamar yace da Adam su juya kawai, su fasa ziyarar, sai dai a kan wace hujja bayan har sun iso, cikin sanyayewar guiwa yayi musu jagora zuwa Presidential suite din da mahaifiyar FAROUK WAZIRI tayi masauki, har Adam din na tambayar sa ko lafiya.
A daburce ya danna doorbell din, ringing biyu tayi wata mata ta zo ta bude musu, wacce a shekare zata girmi fahima, cikin shigar da ke nuni da ma'aikaciya ce ko mai hidima.