RAYUWAR DAN ADAM

18

by @mahmazee1

Wani irin katon hallway suka yi tozali da shi kafin matar nan tayi musu iso izuwa living room din da ke nan, da alama an San da zuwan su, wani irin babban falon da ya cinye setin kujeru biyu.

  Gabakidaya idan ba ka sani ba zaka ce mutum a gidan sa yake saboda tsananin tsaruwa da yelwa.


    Dattijuwar matar da suka zo gaidawa na kan  daya daga cikin kujerun da ke falon, farar bafulatanar Bauchi da a kallo daya zaka fahimci kamanceceniyar da ke tsakanin ta da Farouk, tun kama daga farar fatar su, izuwa kyakkyawar fuskar su ta fulanin usul.


    Tun da suka shigo ta gyara zaman ta tana zare farin medicated glasses din da ke makale kan fuskar ta, ta dora glasses din da littafin hisnul Muslim da ke hannun ta kan table.

     Ba ita kadai ba ce a falon, akwai 'ya'yan ta biyu mata da tarin jikokin ta, wasu irin kyawawan family masu kamanceceniya da juna, .


   Zaka fahimci tsantsar wayewa, gayu da ajin da ke dawainiya da su tun daga yanayin suturun jikin su, izuwa mu'amalar su.


 Akwai ma'aikata mata uku da ke ta dawainiya da kananan yaran da ke nan falon suna wasa, kowanne cikin pajamas.


    Hajiya Oummah uwa a gurin FAROUK WAZIRI ta kawata fuskar ta da yar fara'ar, idanun ta a kan Najib wanda yayi musu iso tsakiyar falon.

    "Have your seat" OUMMAH ta fada tana kallon Najib, wanda shi kuma yayi musu nuni da kujerar da ke gefen shi.


Najib yace "administrative assistant din mu ne da madam din shi"

 Cikin matukar girmamawa Adam ya gaida matar haka ma Fahima wacce girma da kwarjinin matar ya gama cika ta.

   Oummah ta kawata fuskar ta da murmushi tace "sannun ku da zuwa"

Suka gaisa da matan nan biyu da k kan kujerar wadanda suka amsa su a mutunce har suna Jan su da yar hira.


   A hankali ya sauke old fashioned glass cup din hannun shi kan dinning table, wanda ke dauke da sauran ice cubes da zallar sliced lemon daga lemonade din da ya sha.

  Ya soke hannun sa a aljihun tsadaddiyar jallabiyar jikin sa, fara kal mai taushin gaske da har wani daukar ido ta ke yi, a natse ya tako daga dinning section din zuwa falon cikin kamewa.


   Daddadan kamshin turaren Gucci Guilty Absolu da yayi amfani da shi ne ya ruda falon yana sanar da su isowar Farouk waziri, wanda ke takowa kamar baya son taka kasa, farar jallabiyar jikin sa ta matukar yi masa kyau, ta da da fitar da kyaun sa da freshness din sa wanda zallar hutu ya haddasa.


    Dukan su shi suka zubawa ido, idan ka cire Fahima da ta sake yi kasa da kan ta saboda dan rashin sakewa da ta ke ji.  

   Yar sa Aneesa rungume a hannun sa har ya karaso yana zama kan kujerar da mahaifiyar sa ke kai, wanda hakan ya sanya Adam da Najib mikewa kusan lokaci daya cikin matukar girmamawa ga ubangidan su.


   "Ina yini Sir, ya ibada, an sha ruwa lafiya" Adam ya gaishe shi

Da hannu ya amsa gaisuwar tare da dan chanja yanayin fuskar sa ya kalle su duka biyun yana furta

"Sit please"


  Dukan su suka koma kan kujera a sukwane, yayin da Farouk ya dan gyara zaman sa yana dora kafa daya kan daya, wanda hakan ya bayyanar da doguwar kafar shi da ke cikin bakaken slide slippers din Puma, Oummah ta karbi Aneesa hannun shi tana dan yi mata wasa.


     Adam ya kalli sashen boss din sa wanda kwarjinin sa kullum da da ninkuwa yake a gurin shi, yana kasa hada ido da shi yace

 "this is my wife sir" 


    wanda hakan yayi daidai da dagowar fahima wacce ta dago domin ganin wannan FAROUK WAZIRIN da ta sha labarinsa a gurin mijin ta har ta kosa.


   Siririyar muryar ta mai laushin gaske tayi echoing falon saboda dan tsit din da yayi, tun bayan isowar shi, ta gaishe shi muryar ta na fita da kyar saboda wani irin kwarjinin da fuskar tayi mata, wacce wani mahaluki bai taba yi mata ba.

   

    Kadan ya kalli sashen ta yana amsa gaisuwar ta wacce sauran ta tsaya a siraran labatan sa.

  Ya ware fararen idanun sa sosai a kan ta, cikin yanayin kallon da bai gaza na seconds goma ba, ya dauke idanun da hanzari, saboda zuwan wani irin shock da ya ziyarce shi with full force.


   Fahima ta sake furta "Ya Ibada" cikin karamar muryar ta.


   "REINA" 

   wata irin kalma tayi escaping lips din sa, a lokacin da ya ke dauke kan sa da sauri daga gare ta, yana saukar da shi kasa kan lallausar luxurious carpet din da ke shinfide, ya dan jima cikin wannan yanayin.


    Har sai da Oummah ta dan dafa shi kadan, ta kira sunan shi cikin tsananin kulawa "Farouk"


    Idanun shi da ke cikin wani irin yanayi ya cira ya sauke kan Oummah ba tare da ya iya furta komai ba, sai jujjuya kan sa da yake yi , da yayi masa wani irin nauyi nan ta ke. 

    "Ana gaishe ka fa" Oummah ta sake fada ganin yanda yayi kasa da kan shi kamar ma baya falon tare da su.


    "Excuse me" shi ne kawai abinda ya fada, yayin da ya mike tsam yana rungume dukkanin hannayen sa baya ya fice daga falon, duka suka bi ingarmar bayan shi da kallo har ya fice daga falon, ba ma kamar Najib da yake ji kamar ya bi bayan shi.


   Sai dai ya san ba zai ko fara ba domin boss din na su mutum ne mai tsananin son privacy, mai wuyar communicating. 


    Nannauyar ajiyar zuciya Fahima ta sauke saboda yanda mere presence din sa kawai ya sake saka ta a cikin yanayi na rashin sakewa.


  Mahaifiyar shi da ta zubawa kofar ido tun bayan fitar shi, ta mayar da kallon ta kan 'ya'yan ta mata tana fadin "Farouk baya Jin dadi ne" ta karashe da yar damuwa kan fuskar ta.


   Suma damuwar ce kan fuskokin su, kafin babbar ta amsa da "I think so, cause dazu naji yana complain na headache"

  "Toh Allah sawwaka"


       Sai lokacin Fahima ta zuba idanun ta kan Aneesa, kyakkyawar yarinyar da ita dai bata fasa burge ta, yarinyar tayi wayo sosai kan last ganin da tayi mata auren kareema, ta dan watsa idanun ta a falon, wai ko zata hango ta inda Najma zata fito, sai dai da alama bata nan.


    "Aneesa, zo" ta fada tana mikawa yarinyar hannu, wacce ta lafe jikin kakarta cikin salon kuiwa tana sanya lollipop din chupa chups a baki, da alamar yarinyar bata waye ta ba, ta ya ma Aneesa zata waye ta ta raya hakan a ranta.


   Oummah ta kalli Aneesan tana fadin "hmm wannan sarkin kuiwan" a ranta kuma tana raya ina Fahimar ta San Aneesa, domin a idanun ta ta hango kallon sanayyar da ta ke wa Aneesa, ko kusa basu San alakar su da Najma ba, suma kuma basu yi kaudin fada ba.


    Siririn murmushi kawai fahima tayi, kafin suka mike domin komawa hotel din su.


   Suka yi musu sallama, wannan matar da tayi musu iso ta fito daga wata doguwar corridor rike da madaidaiciyar paperbag ta baiwa Fahima inji Oummah.

   Sosai suka yi musu godiya suka tafi, kowanne na yaba kirki da saukin kan mutanen nan wadanda Sam basu yi tsammanin samu haka ba.


    Sai da suka tsaya Al-romansia, suka siye abinci saboda complain din yunwa da ta ke yi mishi tun da suka fito, duk da kuwa himilin abincin da ta ci lokacin Iftar.


   Sai washegari ma ne ta dauko kayan da Oumma ta bata, tana dubawa daya bayan daya, manya manyan Arabian perfumes ne in a gift box, irin wannan da ke zuwa da perfume, oil da kuma bakhoor, sai gift set kuma na mayukan jikin British rose din the bodyshop, gefe daya yar farar envelope ce, wacce sai da ta tsorata a lokacin da ta buda ta ga abinda ke ciki.


   New notes din 100 riyals ne bunch daya wato 10,000 Saudi riyal

  da mamaki sosai ta ke jujjuya kudin, duk sai ta ji ba dadi, irin wannan kyauta haka, kar dai suyi tunanin kwadayin abin hannun su ne ya kawo su.


   Shima Adam yayi mamakin yawan kudin a lokacin da ta nuna masa, sai dai bai yi wani mamakin hakan ba domin ya San mutanen zasu iya fiye da haka, ba yau ne rana ta farko da wani na Farouk yayi mishi kyautar da ta bashi mamaki ba.


   Haka dai suka cigaba da ibadodin su har ga shi anyi sallah sun kuma soma shirye shiryen komawa gida.


********

    Karfe hudu har da arba'in da wani abu na yamma ta fito daga haram, dama tun da aka sallaci sallar Asr, sai tayi zaman ta kawai tana karatun alqur'ani.

 

  Chat su ke yi da Adam, wanda yace ta same shi a hotel din su boss sai nasu hotel din tare, saboda haka kai tsaye ta nufi hotel din Hilton Suites.


    Bata da karfin bin escalator sai kawai ta nufi gurin lifts domin daukar elevator da zata kai ta lobby.

  Ta danna button ta gyara tsayuwar ta tana jiran isowar lift din.


   Counter din da ke hannun ta ta ke dannawa a natse tana ambaton khailala kafin ta soma shako wani irin ni'imtaccen kamshi da ke nufo ta, wani kamshi mai dadi da yayi mata yanayi da wanda ta taba Shaka.


   Ta dan ciro da kan ta kadan tana sauke fararen idanun ta da suka yi luuu kan doguwar hanyar, suna sauka kan Farouk da ke nufo lifts din da dan hanzarin shi.