RAYUWAR DAN ADAM

20

by @mahmazee1

Cikin shock sosai suka kalli juna, domin ba wanda yayi expecting wannan news din, hannun ta da ke cikin na shi yayi squeezing yana dora idanun shi kan lafaffen cikin ta, kai bata zaka ce akwai baby a cikin sa ba.


   "Wifey wifey" ya kira ta cikin tsantsan farin ciki yana rungume hannun ta a kirjin shi, fara'ar da yake ciki na bayyana kan fuskar sa mai dauke da annuri.


Fahima ma rasa tayi emotion daya da ta ke cikin sa, after 4 years of there marriage ko batan wata bata taba yi ba, yau Allah ya ba su wannan babbar kyautar a saukake, wasu hawayen farin ciki ne suka taru idanun ta.

   Ta kalli mijin ta tana yunkurawa zaune

"Careful" ya fada yana Taya ta tare da zama gefen gadon ya rungumo ta jikin sa kai tsaye, ba tare da damuwa da basu kadai ba je a dakin, itama din bata yi kasa a guiwa ba gurin zagayo da hannayen ta bayan shi.


   "Alhamdulillah" suka furta a tare kafin suka zubawa juna ido da wani irin kayataccen murmushi kan fuskokin su.


   "Thank you Dr, irin wannan good news, oh Allah Alhamdulillah" Adam ya fada idanun sa a kan likitan da shima idanun shi ke kan su.

   Bayan fitar Dr sake rungumo matar shi yayi, suna murnar wannan kyautar da Allah yayi musu.


   "Ba Kya Jin komai yanzu, babyn mu ma lafiya ya ke" ya fada yana shafa cikin ta

   bata taba sanin Adam na son haihuwa har haka ba ashe sai yau, sai yanzu da ta ke ganin tsantsar farin cikin sa da ya kasa boyuwa, amma bai taba yi mata complain ko maganar rashin haihuwar su ba.

  

   Murmushi ta saki, wanda ya sake kawata kyakkyawar fuskar ta, hawayen da ta ke makale wa na saukowa, ta dora hannun ta kan na shi da ke kan cikin ta tana fadin 


"Thank you for you Zawj"

"And thank you for you wifey" 


   Basu kwana a asibitin ba Dr ya sallame su suka yo gida bayan ya dora ta a kan ka'idojin da suke so ta bi.


   *****

Ko a gurin aiki duk wanda ya ga Adam ya San yana cikin farin ciki.

   A karo na ba adadi ya sake kiran ta a yinin yau a lokacin da yake kishingide da seat din motar Escalade da ke pake farfajiyar epitome hotel yana jiran fitowar Sir Farouk da Najib da ke ciki suna da meeting.


   "Sexy mahma" ya fada cikin shauki yana wasa da kan sitiyarin motar

  Murmushi ta saki tana sake dukunkunewa a quilt din da ta ke lullube da shi

"sunan da na samu kuma kenan"


   "Yes now, ai you're the most sexiest mama out there, kin San baby bump zai yi miki kyau, har na soma ganin ki kina daga kafa da kyar"

  "Haba dai tun yanzu"

"Ehen ai har sunan da zamu saka idan mace ne ko namiji, duka ina da nayi tunanin wannan"

Dariya ma ya bata, ta dara tana fadin "Allah ya bamu masu albarka"

   "Ka koma kan aikin ka, kar in rike ka"

"Ki rike ni ma, ni ban damu ba" ya karashe yana sakin siririn murmushi.


   A daidai lokacin ya ji karar rufe kofar baya ta motar, da sauri ya dago da idanun shi, suna hada ido da Farouk Waziri ta mirror din gaba.

   Wanda har yayiwa kan sa mazauni, Samson da ya bude masa kofar ya rufe.


    Wani irin nauyin Farouk din ya kama shi ya Sosa kai yana sauke wayar daga kunnen sa, Najib da ya bude gidan gaba ya shigo ya dan sunkuyo gefen shi, murya kasa kasa yace "da wa kake waya haka har baka ji zuwan mu ba"

   Ta jiyo muryar Najib din da abinda ya fada kafin Adam ya dakile call din, yana fadin "sorry sir, sorry sir"


  "sannu da fitowa"

Dan girgiza kan shi kawai yayi kadan ba tare da yace komai ba, da siririn murmushin kan fuskar sa da bai yi nisa ba, yana duba planner book din hannun shi.

  Ya kame bayan motar cikin wata arniyar bakar suit din Armani, Fuskar sa da tayi wani irin fresh na tsananin hutu dauke da annuri mai kayatarwa, ya dan shafa cikkakiyar beard din shi baka sidik da ke ta shekin hutu da tsantsar kulawar da ta ke samu yana going through schedules din shi na yau.

  

   A bangaren fahima kuwa, ta dan tashi da karfin jiki ba kamar jiya ba duk da akwai amai da dan zazzabi kadan.

   Yau ma shi ya shigo musu da dinner, Chinese food din da ya san tana so.


   "Yarinyar nan kadan ki sani abin kunya yau koma in ce nayi" ya fada a lokacin da yake kai dumpling bakin shi

Fahima ta murmusa tace "me nayi" nan ya bata labarin abinda ya faru gurin aikin shi "kinsan har suka iso suka shiga motar nan ban sani ba, ina waya da ke


Ai kuwa dariya ta sanya har da kyalkyalawa 

"Don't blame me, Little baby na ne ya dauke min hankali, har na kosa"

***********


   Fahima ta shiga rainon cikin ta wanda yake cikin wata uku yanzu har ya soma nuna kan shi, hakanan har sunyi exams, ta gama degree din ta gabakidaya sai zaman jiran notification.

   

"Wifey hurry up please, ke kadai na ke jira" Adam da ke tsaye tsakiyar falon ya fada yana gyara zaman cufflinks din sa, cikin wata light blue shadda da tayi kyau sosai a jikin shi, ya murza hular kube sai zuba kamshi ya ke yi.

    Fahima ta fito daga kitchen din cikin dan hanzari, itama ta yi kyau sosai cikin wani lilac purple Swiss lace dinkin boubou, ta sanya madaidaitan fashion earrings da mesh veil.


    Raffia Basket ne hannun ta da ta jere abincin da ta shafe awanni suna yi, da yake yanzu ta samu yarinya da ke shigowa makotan su tana kama mata aikace aikacen gida.

"Let me help you" ya fada yana karbar basket din hannun ta, wanda aka jere abinci cikin sa a manyan takeaway packs.

   "Akwai daya a kitchen"

"Me ye"


"Basket da na saka abincin Baba"

"Ohhh okay"


   Ta kalle shi da kyau ganin how excited he is for yinin yau tace cikin kokwanto "are you sure zai ji dadin abincin nan, zai ci kuwa" 

   Adam yace "I know he will enjoy it, baby na tayi abinci da kan ta da hannun nan na ta mai albarka, ai duk wanda ya ci zai nemi Kari"


   Dukan kirjin sa tayi Tana fadin "jokes apart"

"Na sani, zai ji dadin shi, I know am not the only one da zai kawo masa sallah treats, amma am confident"


   Fahima ta gyada kai tace "okay"

"Kai da boss din ka ne ai kun fi kusa"

"Har da ke ma haka zaki ce, kinsan mutane da yawa suna gaya min jinin mu ya hadu da na boss, har fa Najib ya sha gayamin haka"


   Fahima tace "hadin jini ne kawai, Allah ya hada jinin ku"

"Yes you can say that"

      Ya fice da basket din ya dawo ya dauki dayan da ke kitchen Ya ja hannun ta suka fice daga gidan, a motar sa suka fita, wata sabuwar motar da bai jima da siya ba, saboda alherin da ya samu a gurin aiki mai nauyin gaske, har ya siye fili yana son fara gini.


   Farar Kia picanto mai saukin kudi, ya ja suka tafi, a gida ya sauke ta ya wuce.

  Yayin da ita kuma ta nufi cikin gidan su, wanda ya cika da hayaniyar 'ya'ya da jikokin Alh Ciroma, kowa ka gani cikin ado da kwalliya mai kyau saboda hidimar Sallar layya (Eid ul kabir).


   Da salma ta soma cin karo a falon Aunty, itama ta yi kyau cikin kwalliyar ta.

 Da sauri salma ta karaso "Bama son maman baby tana wani aiki fa" salma tace tana karbar mata basket din hannun ta