RAYUWAR DAN ADAM

22

by @mahmazee1

Ya cigaba da wasa da gashin ta yana fadin "yes, zamu je  gaida sarkin zazzau, jiya Najib ke gayamin"

   Fahima ta dan shagwabe fuska tana tightening rungumar da yayi mata

"Ni kam i will miss my zawj" ta fada

   "Nan da zariya, yau zamu je, yau zamu dawo insha Allah"


  "Allah ya yarda"

Bacci suka koma na awa daya kafin ta riga shi tashi, ta tayar da shi sanin a duk sanda zasu je zariya tafiyar safe su ke yi.


    Ya zauna sosai bakin gadon ya kamo kugun ta ya janyo ta yana sanya ta tsakankanin kafafun shi, tare da dora kan shi cikin ta.

    "I'll miss my baby yinin yau" ya fada ya dago da kanshi yana zubawa dan cikin ta ido

   Hannun ta ta dora kan sumar shi tana fadin "yau kana Abu kamar sabon ango, zaka yi latti fa"

   "Ai ko da yaushe ni sabon angon fahima ne"

"But seriously lemme get ready" ya fada ya nufi bathroom, yayin da ita kuma ta koma kitchen domin duba girkin ta.


    Ya shirya tsab cikin kaftan white na wani tattausan fabric ya murza hula ya fito falo yana jiran ta, sassaukan breakfast tayi chips da egg sauce sai spicy black tea.

  A agurguje ya yi breakfast din ya kama hannun ta suka fice domin tayi masa rakiya, bayan ta dora dogon hijabi kan kayan jikin ta, sanin ba su kadai ne a gidan ba.


    Har motar sa ta raka sa, ya tayar da motar, har lokacin hannun shi na cikin na ta yana murzawa a hankali.

  Ta fahimci kamar baya son tafiyar yau duk da yanda duk wani Abu da ya shafi Farouk waziri a gurin Adam shaukin sa ya ke, hakanan mai muhimmanci ne a gare shi, amma yau ta ga sabanin haka a idanun shi.


   "Zawj Allah ya tsare, I'll make your favorite dish kafin ka dawo"


   Ya kalle ta da kyau yana tsawaita kallon shi kan ta "i love you so much Fahima, words cannot describe, Allah yayi wa rayuwar ki albarka"

    Tace "Ameen, Allah yayi maka albarka kai ma" ta fada a lokacin da ta dan sunkuyo kadan tayi kissing kumatun shi.

   Ya cika hannun ta da ke cikin na shi yace "sai na dawo"


   Har buzu maigadin su ya bude mishi gate tana tsaye da murmushi sosai kan fuskar ta taba daga mishi hannu, sai da ya fice kafin ta juya ta koma cikin gida, duk kuma sai ta ji jikin ta ya sanyaye, kamar na shi, sai kace yau ya fara zuwa Zariyar nan fahima ta raya a ranta.

   Kasa komawa bacci tayi, har zuwa lokacin da ya kira ta, ga su har sun iso zariya suna fadar mai girma sarkin zazzau.


     Tun da ya kira ya gayamata suna kan hanyar dawowa, ta tashi ta soma shirin dawowar sa, hadiza mai taya ta aiki ta shigo ta soma gyaran gida yayin da ita kuma ta fada kitchen.

   Favorite dish din shi semo da vegetable soup da ta ji kala kalan protein ta hada, da pepper soup sai fruity zobo, ta hada fruit salad kana ta nufi dakin ta domin watsa ruwa.


   Wanka tayi ta shirya cikin kananan kaya, flare jeans da wata hot red sequence top, da sukayi mata kyau sosai, ta gyara gashin ta da tayi drying ta pake shi gurin daya, tare da sanya earrings masu kyau da suka dace da shigar ta.

   Sosai tayi kyau ta fito falo ta zauna kan kujera tana kallon show din big brother naija 

 da ake haskawa.


    Ta dan duba time din wayar ta, by now kam ta San sun isa isowa kaduna watakila dai sun tsaya gidan Sir Farouk ta raya a ranta ta cigaba da kallon ta har Hadiza ta gama aikace aikacen ta tayi mata sallama ta fice.


    Ta sake kallon time for the umpteenth time, dama idan yana tare da Farouk ko an kira baya dagawa, ta raya a lokacin da ta kira number sa har sau biyu ba a daga ba.


    Cikin zumudi ta lalubo wayar da ta dauki ringing, sai dai sabanin kiran da ta ke expecting sai ta ga number Al'amin tana yawo kan screen din.


    Daga wayar ta yi jiki a sanyaye tana karawa a kunnen ta

  "Hello fahima kina gida" abinda ya fada kawai kai tsaye

    Cikin nauyin baki ta furta eh

Yace

"Okay ina kan hanyar zuwa baba yace in zo in dauke ki" 

   bai jira Jin ta bakin ta ba ya dakile kiran, sororo ta bi wayar da ido, Toh ko lafiya baba ke neman ta haka, taba baki kawai tayi jiki a sanyaye ta wuce bedroom din su.


  Abaya ta dora kalar ruwan zuma kan kwalliyar da ta sha ta tarbon miji, tayi wrap around da gyalen abayar.


     Ta dawo falo jiran Al'amin, a gefe daya kuma tana tunanin kar kuma ya dawo bata nan, Bai wani jima ba sai ga Al'amin ya iso har tana mamakin saurin da yayi.


    Ta rufe gidan ta riko yar handbag din ta fito, yana zaune mazaunin driver ya hada kai da steering wheel, sai da gaban ta ya doka a lokacin da sukayi ido biyu da Al'amin tsabar yanda ta ga idanun sa sun kada.


    Duk da yawan barkwanci irin na Alamin musamman a kan ta, yau duk babu, kai tsaye ya ke driving din sa, idanun shi a kan titi, har suka iso gida.



       Bugun zuciyar ta ya tsananta a lokacin da suka tunkaro gate din gidan wadda ta soma cika da mutane tun daga waje har zuwa harabar cikin gidan na su, Al'amin ya samu guri yayi parking.


     Ba zata iya cewa ga yanayin da ta ke ciki ba domin komai ya kunce mata, dandazon mutanen da ta tarar harabar gidan na su ya bata tsoro, irin tsoron da bata taba shiga kwatankwacin sa ba kab rayuwar ta.


Duk wasu ya yan Alh maza da k zaune cikin garin kaduna sun hallara a harabar gidan, idon ta ya sauka kan farar motar hilux kwaya biyu ta yan sanda da ke pake harabar gidan na su, yayin da yan sandan suke zagaye da motocin su da wata mota da ta fi mata kama da Ambulance.


   Can ta hango baba tsaye gaban Ambulance din tare da wani dattijon da ko bai yi ba ya kusa sa'ar baban, sai kuma Lawal din mami tare da wani wanda zai yi sa a da shi suna tattaunawa, akwai damuwa mai tarin yawa kwance kan fuskokin ko wannen su.


    Kallon Al'amin tayi wanda ya kasa cewa komai sai idanu da ya zura mata, a hankali ya sanya hannu ya dauke kwallar da ta sauko masa wacce yake ta rike wa tun dazu, tausayin kanwar sa na cika duk wani gurbi na zuciyar sa.


   Hannu ta Mika ta balla murfin motar ba tare da ta damu da wayar ta ko jakar ta ba, bata san abinda ke shirin faruwa da ita ba, bata san abinda ke fizgar ta zuwa ga baba ba, amma ko ma meye she has a feeling it's huge.


     hakanan kiran da baba yayi mata ba lafiya ba, cira kafar ta tayi da kyar tana takawa zuwa inda baba yake tsaye wanda ya zuba mata ido daga shi har Lawal har mutanen da suke tsaye tare da su da bata san ko su waye ba, kai gabakidaya sai ta ji idanun mutanen da ke gurin ya dawo kan ta

    "Allah sarki ita ce iyalin sa" shine abinda kunnuwan ta suka jiye mata a lokacin da ta ke gota gungun wasu dattijai.


     Da kyar ta ga ta iso gurin baba saboda nauyin da kafafun ta suka da da yi hadi da wani irin jiri da ya kwashe ta har yana dusasa ganin ta jin abin da mutanen nan suka fada, a daidai lokacin aka fitar da gawar da ke kwance bayan ambulance lullube da farin kyalle.