ƊAURIN ZUCI

Chapter 1

by @maryamstar248

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄❤️‍🔥🔐
  𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔& 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙄𝙉𝙂

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍 ⭐

****
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



ƊAURIN ZUCI FREE BOOK.

KATSINA NIGERIA

Gaba ɗaya idanuwanta sun gama kullewa ba ta iya ganin komi face duhu, duhunta shi ya mamaye raunataciyar zuciyarta har ta makance akan abin da ba ta san makomarta ba a nan gaba.
     Sake damƙe hannun shi ta yi a ƙirjinta da ke hawa da sauka tana jin zuciyarta na gab da tarwatsewa akan mugun ɗaurin da ake neman yi mata.
    Kafin ta samu damar dawowa a hayyacinta ta sake tsinkayar muryar shi yana faɗi a kausashe.
    "Dole ki zaɓi ɗaya, zaɓin ki shi zai tabbatar da cigaba da zamanmu da ke ko akasin hakan, shin kin zaɓi mu aura maki shi da sharaɗin za ki nesanta kan ki da mu, bi ma'ana za ki fita daga rayuwarmu domin kuwa mun sallama mashi ke."
    Ba iya harshenta ba hatta da fatar jikinta karkarwa take yi, ta so ace tana da damar yin tunani wataƙila da ta hangi abin da suke ƙoƙarin nuna mata, sai de kuma lokaci ya riga da ya ƙure mata ba ta da sauran wata damar a yanzu dole ne ta tabbatar da abin da take ganin shi ne daidai.
Ba ta iya ganin kowa saboda idanuwanta a rufe suke amma tana iya hasashen yanayin da ke kan fuskarsu a sanda ta soma magana.
    "Zan bi shi zan zauna a tare da shi zamu rayu tare, na haƙura da komi nawa idan na ce komi ina nufi komi ciki harda abin da ba ku yi tunani ba."

Wani makirin ɓoyayyen murmushi  ƙasaitaciyar macen da ke hakimce akan sofa ta saki, sai kuma ta marairaice fuska tare da kallo magidancin da ke zaune ɓacin rai bayyane ƙarara akan fuskar shi, cike da kissa ta ce.

    "Haba Daddynsu tun da dai har ta kafe ina ga lokaci yayi da zamu barta ta yi rayuwarta kamar yanda ta zaɓa, mu bita da fatan alkairi kawai shi ne mafita."
    Da wani irin sauri Fari tas ɗin matashin da ke tsaye damuwa bayyane akan fuskar shi ya ce.
    "A,a Momma please kar ku yi haka a sake ba ta dama dan Allah."
Ya faɗa da alamun roƙo tsoro na bayyana akan fuskar shi.
   Wani banzan kallo me cike da gaegaɗi Mommah ta watsa ma shi sannan ta ce fusace.
  "Shin ka na so mu shiga haƙƙin marainiyar Allah ne, sau nawa zamu taure ta akan ra'ayinta gaskiya a wannan karon ina bayanta ya kamata ayi mata adalci."
    Wani irin harbawa zuciyar matashin ta yi jin abin da Mommah ta faɗa, ji yake kamar ya ɗora hannu aka ya rusa ihu dan yasan muddin aka tafi a haka shi ne a ruwa tsullum.
    Kafin ya samu zarafin cewa wani abu Daddy ya yi gyaran murya sannan ya soma faɗin.
   "Ba mu taru anan dan tattauna albarkacin bakunanku ba, hukunci ne zan zarta kuma a yanzu a karo na ƙarshe ina me sake bawa  Zunaina damar zaɓi a gaɓe da rayuwarta, na yi alƙawari ba zan sauya hukuncina ba zan aiwatar da du abin da ta zaɓa."

A wannan karon sai da ta buɗe idanuwanta, wanda suka yi jazur duda ba gani take yi sosai ba a haka takai dubanta gefenta na haggu.
   Yana nan a yadda yake tun farkon fara zaman, kan shi duƙe a ƙasa yayinda hannunshi ɗaya da ta riƙe har lokacin na rungume a ƙirjinta.
    "Daddy na amince, na amince ka aura min shi zan rayu tare da shi kamar kuma yanda na faɗa zan sake maimaitawa zan bar komi zan manta da komi ba zan taɓa karya alƙawarina ba."
    A can wani ƙaramin yanki na ɗaurarriyar zuciyarta faɗi take.
   'Anya za ki iya kuwa Zunainah za ki iya jurewa me yasa za ki yi hakan?.'
 Yayinda kaso mafi rinjaye ke azalzalarta akan hakan shi ne daidai.

A cikin abin da bai rufe mintuna biyu ba ta yankewa rayuwarta hukunci ta hanyar binne umarnin zuciyarta, ba ta yi tunanin hakan zai isa sauya rayuwarta ba, kuma ba ta yi tunani akan abin da zai je ya zo ba, ta buɗe ƙofofin ƙaddararta da hannayenta, ta bawa ƙalubalen rayuwa damar kusantar inda take.

*****
Ba iya abin da ya faru kaɗai ke kai komo a ruhi da kwanyarta ba harda wanda ke shirin faruwa da ita nan gaba.
   Tafe ta suke ita da shi ba tare da sun san inda suke jefa ƙafafuwansu ba kawai sun fuskanci gabansu ne ba tare da waiwayen baya ba.
    Tasan ƙaddara ta ɗauki tsayin shekaru tana buɗe mata sababin shafuka amma ba ta hasaso buɗewar wannan shafin ba, tuna abin da ya faru kawai na sake ruɗar da ruɗaɗen tunaninta sai kawai ta zaɓi tafiya ba da iya ƙafaguwa da gangar jikinta ba, harda kwanyarta ta hanyar soma nazartar inda za su dosa.

 SHINKAFI
Tabi round about ɗin da aka yi rubutu ɓaro-ɓaro da manyan haruffa aka rubuta Shinkafi, yayinda kwanyarta ta ci gaba da lalubo mata wata rana.
        
          *****
   "Anty Zunaina kin san wani abu, yau a makarantar mu Shugaba ya ce za'a buɗe sabon reshe a Shinkafi."

Aje wayar da take dannawa ta yi tare da maida hankalinta akan yarinyar da ke bata labari, sai da ta ware manyan idanuwanta calmly ta ce cikin sweet voice ɗinta.

   "Shinkafi kuma Afnan ina ne hakan?."  Ta yi tambayar tana jiran amsar yarinyar.

Sai da ta kyalkyale da dariya sannan ta ce.
    "Bafa wani waje me nisa da yawa ba ne can gaba ne sosai Shugaba ya ce babu nisa zama a iya zuwa a ƙafa."

Kama kumatun Afnan ta yi sannan ta ce.
   "Aiko dai can zance a maida ke ko babu komi za ki yi tafiyar a ƙafa tunda na lura duk gidan nan kin fi kowa son jiki."

****
A fili ta furta kalmar "Shinkafi." tana sake yawata idanuwanta tana ƙarewa yanayin titin unguwar daya miƙe shaltan, ga mutane nan musamman masu sana'a kowa nata hada-hadar kasuwanci.

Motsa hannunta ta yi kaɗan wanda ya jiƙe da zufar riƙon da ya yi mata, sake kallon fuskar shi tayi cikin ɗan hasken fitilun security light ɗin da suka yiwa titin ƙawanya.

   "Mouhan." Ta kira sunan shi da wani irin sauti wanda ya fito da rauninta muraratan, can ƙasan zuciyarta kuma tana jiran ya musa kamar yanda ya saba yi da zarar ta kira shi da hakan.
    Kamar daga sama ta tsinci sautinsa a dake yana faɗin.

"Muhammad."

Dariya ta yi wacce tai kama da yaƙe tana gingina kafiya da ra'ayin riƙau irin na shi.
    Tun daga sanda ƙaddara ta haɗa ta da shi har zuwa yanzu da take jin ya zama wani ɓangare na rayuwarta bai taɓa amsa sunan da take kiran shi da shi ba, sau goma zata kira shi da Mouhan sau goma zai ce da ita Muhammad.
Daidai lokacin da ta samar musu da matsuguni a gefen hanya domin gabaɗaya ta gaji da tafiyar a kuma lokacin ne tunaninta ya koma da ita kwanaki ƙalilan baya.


Ranar Alhamis ranar a garin Katsina an tashi da yanayin hadari, ga shi lokacin safiya ne sosai 07:00am.

A ranar ne kuma Afnan suke gama Exam ɗin su ta last term, tun da suka tashi da hadari Afnan ke bin bayanta tana jadadda mata lalai ita zata kaita school ta kuma jira a taso ba ta so driver ya kaita zai sa su yi lati wataƙilama har ruwa ya doke ta.
    Da yake Afnan ba dai tsoron ruwa ba koya ruwa ya daketa sai ta yi zazzaɓi.
 
    "Ba dai School ba ne ki shirya zan kai ki da kaina kuma zan jira har ki gama mu dawo tare  amma kafin nan ni ma zan je office zan kai saƙo."
    Cikin abin da bai rufe mintuna ashirin ba suka shirya tsaf, yayinda Afnan ta fito cikin uniform ɗinta da ke ɗaukar ido saboda gugar da suka sha, ita kuma Zunaina ta shirya tsaf cikin cikin shigar farar doguwar rigar abaya, wacce ta sake fito da hasken fatarta me shiga ido.
     Isar su wajen motar da za su fita ne suka taras ba'a wanke ba gudun kar su ɓata lokaci ya saka kawai suka fice domin tarar ɗan sahu.

A ƙalla sun kwashi mintuna goma ba tare da sun samu abin hawa ba, ga iska me ƙarfi da aka soma yi alamar ruwa na shirin ɓallewa kodayaushe.
    Ga kuka da Afnan ta soma yi akan ita dai su koma gida ta haƙura da exam ɗin.
   A daidai lokacin ne kuma garin waige-waige idon Zunaina ya sauka akan fuskar shi, kuma a daidai lokacin ne suka samu ɗan sahu, wata iriyar mummunar dokawa zuciyarta ta yi sanda idonta suka sauka cikin na shi.
    Afnan ce ta shaidawa me Napep ɗin inda zai kai su ba ta kuma jira cewar shi ba ta afka tana share guntun ƙwallarta.

      A wanin  da suka biyo bayan gama mamakon ruwan da aka yi sun zama awanni masu tsawo a wajen Zunaina, tana jinta a matuƙar takure kamar wacce ta yi mantuwa, mantuwa irinta abu me muhimmanci, tana jin kamar akwai wani abu wanda ta manta da shi can baya amma kuma ta gagara gane mene ne wannan abin.


Zuciyarta ta ci gaba da dokawa a hargitse a sanda suka sauka bakin hanya, kawai ta zaro kuɗi ta biya me napep ita kanta ba ta san ko nawa ba ne, baima samun amsar maganar da yake yi mata na, kawai de tasan ta damƙi hannun Afnan cikin nata ne da ƙarfin da sai da ta saki ƴar ƙara.
   "Auch Anty za ki ɓalla min hannu da zafi."
   Ba wai dan ta ji abin da Afnan ɗin ta faɗi ba ne ya saka ta saki hannunta, kawai dai ta ji zuciyarta na barazanar ɓallowa ne daga ƙirjinta ta fito ta baki, hannu bibbiyu  ta saka ta dafe zuciyar tare da tsayawa cak tana kallon shi da wani yanayin.


Tun daga kan gashin kan shi har zuwa tufafin jikin shi gabaɗaya a jiƙe yake, babu abin da ya sauya daga ganin da tayi ma shi ɗazu, ba ta san abin da ya ja ta zuwa gare shi ba kawai ta tsinci kanta da soma takawa tana tunkarar inda yake.

Bata da ƙwarin guiwar yi mashi magana bayan tsoro da firgice gabaɗaya jinta take yi kamar ba ita ba kamar ana ƙoƙarin sauyata ne daga ainahin yadda take.

****

Gwauron numfashi ta sauke, tare da janye idonta daga kallon shi tana ji  kanta na yi mata matsanancin ciwo kamar yana barazanar tarwatsewa, ba ta da wata mafita kamar yanda bata da madafa domin kuwa du abin da ya faru ita ta jawa kanta, kuma tana tsamanin faruwar wasu abubuwan waɗanda suka fi haka hatsari ga rayuwarta.....

********
Kallon ƙaramin tauraron da ke hannun shi yake yi, baƙar fuskarsa na turewa daga duhun ɓacin rai farinciki na baibaye shi.

A hankali ƙaramin tauraron ya soma sauya kala daga ainahin kalar shi baƙi yana komawa launin ja, kamar yanda ya ɗauki tsayin lokaci yana jiran zuwan wannan rana hakan ya saka nan take ya tashi daga tsugunnen da yake ya isa gaban wani wawakeken miro me ƙyalli, wani abu ya dannan yana wasu surutai marasa kan gado, nan take miron ya soma ɓacewa yana disashewa wani baƙiƙirin na bayyana a wajen.

A cikin madubin wani me suffa shigenta mutane ne mara kyawun gani ya bayyana yana ɓaɓɓaka dariya, daga cikin madubin ya huro wata baƙar iska nan ta fito tare da ɗaukar star ɗin sai ga ta ta bayyana a gabansa.

  "Lokaci ya yi, lokacin da muke jira ya ƙarato lokacin nasara da cikar buri, lokaci mutuwar wulaƙanci tare da wulaƙanta ya zo.

Jini ya gauraya da ɗan uwansa jini daga yanzu komi zai sauya sauyin da babu sauyi.".......✍🏻

MINENE ZAI SAUYA, WANE SAUYI NE WANDA BABU SAUYI A CIKIN SHI?

SHIN WAI ME ZUNAINAH TA AIKATA NE?

WAYE MUHAMMAD

Gaba ɗaya rankatakaf ɗin amsoshinku na cikin wannan labari me cike da sarƙaƙiya me taken ƊAURIN ZUCI.

Ku kasance da tauraruwarku domin jin yanda za ta kaya.

Sannan kar ku manta wannan littafin FREE BOOK ne daga farko har ƙarshen shi ina fatan zaku bani haɗin kai ta hanyar danna min like sannan ku taya ni share bayan haka ku zo ku kashe ni da zafaffan comment domin inji ƙwarin gwuiwar kawo muku wannan daddaɗan labarin da ya zarce Zuma a zaƙi.

Nice taku
MARYAM STAR

***
Chart only🤌🏻