FreeArewaPen original
ƊAURIN ZUCI
- 1views
- 46chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
HAUSA NOVELS WRITER
Sample · Chapter 1
*** 𝙕𝙐𝘾𝙄❤️🔥🔐 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔& 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙄𝙉𝙂𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍 ⭐**** *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️*(J.W.A)*_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ƊAURIN ZUCI FREE BOOK.KATSINA NIGERIAGaba ɗaya idanuwanta sun gama kullewa ba ta iya ganin komi face duhu, duhunta shi ya mamaye raunataciyar zuciyarta har ta makance akan abin da ba ta san makomarta ba a nan gaba. Sake damƙe hannun shi ta yi a ƙirjinta da ke hawa da sauka tana jin zuciyarta na gab da tarwatsewa akan mugun ɗaurin da ake neman yi mata. Kafin ta samu damar dawowa a hayyacinta ta sake tsinkayar muryar shi yana faɗi a kausashe. "Dole ki zaɓi ɗaya, zaɓin ki shi zai tabbatar da cigaba da zamanmu da ke ko akasin hakan, shin kin zaɓi mu aura maki shi da sharaɗin za ki nesanta kan ki da mu, bi ma'ana za ki fita daga rayuwarmu domin kuwa mun sallama mashi ke." Ba iya harshenta ba hatta da fatar jikinta karkarwa take yi, ta so ace tana da damar yin tunani wataƙila da ta hangi abin da suke ƙoƙarin nuna mata, sai de kuma lokaci ya riga da ya ƙure mata ba ta da sauran wata damar a yanzu dole ne ta tabbatar da abin da take ganin shi ne daidai.Ba ta iya ganin kowa saboda idanuwanta a rufe suke amma tana iya hasashen yanayin da ke kan fuskarsu a sanda ta soma magana. "Zan bi shi zan zauna a tare da shi zamu rayu tare, na haƙura da komi nawa idan na ce komi ina nufi komi ciki harda abin da ba ku yi tunani ba."Wani makirin ɓoyayyen murmushi ƙasaitaciyar macen da ke hakimce akan sofa ta saki, sai kuma ta marairaice fuska tare da kallo magidancin da ke zaune ɓacin rai bayyane ƙarara akan fuskar shi, cike da kissa ta ce. "Haba Daddynsu tun da dai har ta kafe ina ga lokaci yayi da zamu barta ta yi rayuwarta kamar yanda ta zaɓa, mu bita da fatan alkairi kawai shi ne mafita." Da wani irin sauri Fari tas ɗin matashin da ke tsaye damuwa bayyane akan fuskar shi ya ce. "A,a Momma please kar ku yi haka a sake ba ta dama dan Allah."Ya faɗa da alamun roƙo tsoro na bayyana akan fuskar shi. Wani banzan kallo me cike da gaegaɗi Mommah ta watsa ma shi sannan ta ce fusace. "Shin ka na so mu shiga haƙƙin marainiyar Allah ne, sau nawa zamu taure ta akan ra'ayinta gaskiya a wannan karon ina bayanta ya kamata ayi mata adalci." Wani irin harbawa zuciyar matashin ta yi jin abin da Mommah ta faɗa, ji yake kamar ya ɗora hannu aka ya rusa ihu dan yasan muddin aka tafi a haka shi ne a ruwa tsullu...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.